Showing 213001 words to 216000 words out of 288773 words
Chapter 72 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
Bayan sun tashi meeting khaleefa bayan doctor andal yabi, har ta mishi nisa ya k'ara da sassarfa yana mata sallama. Ta amsa tare da tsayawa, "khaleefa is there any problem?". Ta tambayeshi .
Sunkuyar da kanshi k'asa yayi yace, "noop kawai Ina son sanin real name na mutumin da kika gama maganarshi yanzu".
"Wayyoh Allah!" Ta fad'a had'e da zare farin tabaran idonta tana sake duban khaleefa da kyau a zuciyarta tana sake maimaita sunayen nasu duka a tare.
"Sorry ba kowanne patient nake rik'e sunan shiba, amma zan duba maka bayanan shi kafun zuwan shi surgery".
"Yauwa nagode doctor". Ya fad'a tare da yin gaba. Har yayi nisa doctor andal tana tsaye a gurin, tafiyarshi tabi da kallo wani abu daya tab'a faruwa shekaru talatin da d'oriya na dawo mata daki daki cikin kanta.
****Khaleefa kuwa yana futa sak'o na shigowa wayarshi, Koda ya duba Ahmad ne yake mishi tuni kan zuwa makarantar su raihana. Shi har ya manta ma ba don ya tuna mishi ba.
Raihana ta futo daga libry rungume da littafanta hannunta rik'e da k'aramar hand bag. Tafe suke ita da matashiyar yarinyar nan da take son karatu kamar ita suna d'an hirarrakin su. Ko kad'an bata lura da Saleema data tattaro k'awayenta kusan biyar har ita ta shida ba, saida tana cikin tafiyarta taga ansha gabanta.
Cak ta tsaya tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya, kafun tayi wani yink'uri sun kewayeta sun tunkud'e k'awarta meerah da take tambayar me raihanan ta musu.
Wani banzan kallo Saleema ta mata a ranta tana tunanin abinda zatayi da zai k'ololuwar b'ata mata rai taji ta tsani kanta da sake nunawa mutane fuskarta. Ga gurin ya fara tara mutane y'an kallo don babu wanda ya tambayesu ba'asi.
"Yau gaki a hannuna, zanga ko zaki iya kwatar kanki boss?".
Murmushi raihana tayi duk da y'an matan sun kewayeta amma bata ji tsoron suba ko d'ar, k'arshe dai tasan suce zasu daketa.
Ganin ba zata kula taba sai ta janye madaidaicin gyalen abayar jikinta, take kuwa tulin gashinta data parking a k'eyarta ya futo waje mutane suna kallo. Raihana saida ta rintse idanunta sannan tace, "kuyi mun duk abinda zaku yimun amma kada ku kuskura kuce zaku tsiraita ni".
Dariya sosai Saleema tayi, abinda ta tuna kenan, don taga yadda ta rufe jikinta ruf waccen ranar, da yadda ta dinga gyara yafen lafayarta su suka tabbatar mata jikintane bata so a gani, shiyasa ta yanke shawarar bud'e ta tsirara ga wad'an nan samarin da suke kewaye da gurin, tasan shine kad'ai zata ji sanyi a ranta, taji ta huce takaicin abinda sukayi mata ita da khaleefa.
"Guys ku yage mun rigar jikinta ta ganta tsirara a wannan gurin.
Aikuwa cikin amsar umarninta suka rirrik'e hannun raihana wata taja zif d'in gaban rigar tayi k'asa dashi........🙆♀️😨
Ita kuwa raihana cikin saddakarwa ta rintse idanunta tana girgiza musu kanta hawayen da suka cika idonta suka soma sauka bisa kuncinta.
_haba madame khaleefa kin manta in aka ga mace y'ar uwarki tsirara kamar ke aka gani🤔_
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty 6️⃣0️⃣
K'ok'arin fizge jikinta take amma ta kasa don sosai suke gwada mata k'arfi, an dire zip d'inta k'asa amma daga ta ciki akwai doguwar riga armless data fara sakawa kafun ta d'ora abaya a samanta, wannan riga ita ta ceceta ta suturta ta ba'a ganta duka a waje ba.
Ganin haka sai bak'in ciki ya sake kama Saleema tace, "ku cire ta saman had'e da ta cikin ma, soo nake yau na ganta tsirara....". Ta k'arasa fad'a tana murmushi da kallon yadda raihana tayi la'asar kanta a k'asa sai ruwan hawaye daya k'i tsayawa a idonta.
Raihana yau kam tasan babu mai ceton ta sai Allah, tana ji tana gani suka fara jan rigarta baya zasu fizgeta. Ta sake rintse ido da sauri tana jujjuya kanta alamun suji tausayin ta.
Cak! Numfashinta ya nemi tsayawa jin hannu ata gaban rigarta an rik'e gaban rigar gam rik'o bana wasa ba,,,,,, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da hancinta ya shak'o daddad'an k'amshin turaren shi, bata gama tantance komai ba ta tsinci kanta tsakiyar k'irjin shi hannun shi saman gashin kanta. Wani mugun fusataccen kallo ya fara jifan Saleema da tawagarta dashi, take kuwa duk suka fara k'ok'arin barin gurin cikin tsiro, ita kuwa mutuwar tsaye tayi ganin khaleefa rungume da wata mace a gabanta ko kunyarta baya ji saboda tsabar yaudara.... Bata dawo daga tunanin taba ta tsinkayi muryarshi cikin kunnuwanta. "hak'ik'a nayi nadamar sanin ki a rayuwata Saleema, kuma ban tab'a sanin ke mahaukaciya ce ballagaza ba sai yau, idan baki sani ba Ina so ki sani.... adadin yawan haukan da kike yi adadin nisan da Abdallah yake wa rayuwarki...... Shin kun d'auka itama irin kuce data saba nunawa kowanne banza da wofi jikinta? Toh ita jikinta mai daraja ne daba kowa ke gani ba sai halaliyar shi.... Ku bani gyalenta". Ya kai k'arshen maganar yana sake binsu da kallo d'aya bayan d'aya. Wata a cikin suce ta iya k'arfin halin d'auko vail d'in da yake yashe a gefe ta kawo mishi. Ya fizge tare da saurin rufa mata gashin kanta dashi, da kanshi ya durk'usa ya maida zip d'in rigar da suka zuge mata, ya d'aukar mata littafinta da jakarta ya kamo hannunta ya d'auki hanyar barin gurin.
Tsabar bak'in ciki yasa Saleema yin suman wucin gadi, babu abinda yafi tsaya mata kamar rungume yarinyar da khaleefa yayi a k'irjin shi da maganar daya fad'a wai sun saba rabawa maza jikin su a titi..... Tabbas wannan abu biyu ya tsaya mata har yasa ta kasa hak'uri saida ta biyo bayan su tayi magana da k'arfi yadda zai iya jiyo ta, "tabbas ba kayi k'arya ba muna rabawa maza jikin mu, amma maza ire iren ka ba wanda suka san ciwon kansu ba...... Sannan koda kake kallonta a haka ba tsira kayi ba don babu macen da zaka samu bata rabawa maza jikinta ba kamar yadda muka rayu da kai haka itama ta rayu da wani.....".
Duk da sunji abinda ta fad'a amma cikin su babu wanda ya nuna yaji ta bare har su juyo.
Suna futa suka tarar da motar Ahmad tana jiran su.
Gidan baya suka shiga su duka shi kuma yaja motar ya fara barin gurin.
Har suka k'arasa gida raihana kuka takeyi yayinda khaleefa ya kwantar da kanshi a seat d'inshi yana sauraron kukan nata kalaman Saleema na amsa kuwwa cikin kunnen shi, ko a shifcin gizo bai tab'a tunanin Saleema zatayi duk wad'annan abubuwan ba, ko yanzu ba don ya ganta da idon shiba in fad'a mishi akayi saiya iya k'aryatawa.....
"Sai dai kiyi hak'uri raihana, Allah ma ya taimake ki man yazo akan lokaci".
Bata iya furta komai a gare shiba, sai sautin kukanta daya k'aru. Ganin haka sai taba khaleefa haushi ya futo a motar a zafafe cikin fad'a yace, "ai saiki futo mu tafi ko tunda hak'urin ne baza ki iya ba".
Babu musu ta zuro k'afarta ta futo, khaleefa ya bita da kallo ganin ta d'auki hanyar tafiya gida tana ci gaba da kukan.
Ahmad ya dafa kafad'ar shi yana mishi magana amma sam baya fuskantar me yake cewa, burin shi d'aya kada raihana ta shiga gidan a yanayin da take. Ganin da gaske so take ta tona mishi asiri sai ya zame hannun Ahmad yabi bayanta da sauri.
Tana gab da k'ofar shiga gidan ya rik'o hannunta tare da jawo ta ta baya har saida gefen jikin su ya had'u, electric shock yabi ta jinin jikinsu ya isarwa da kwakwalwar su sak'o cikin seconds, ture hannun shi take son yi amma ya hana mata damar haka saima hannun shi daya kewaya ya rik'e k'afad'un ta duka biyu ya fara mata magana da taushin murya me kama da rad'a kusa da kunnenta, "kiyi hak'uri mana raihana..... Duk wanda kika ji ance yayi hak'uri an cuce shi, sannan duka laifi nane tunda ni na jawo miki komai amma don Allah ina mai neman afuwarki....".
Madadin tayi shiru saima ta sake rushewa da wani kukan, lamarin daya sake tsinkewa khaleefa zuciya hankalin ya sake k'ololuwa wajen tashi, baisan kuma me zaiyi mata tayi shiru ba indai har bata hak'uri da fatar baki bazai wadatar ba.
Sunyi shiru tsawon lokaci a gurin kafun khaleefa ya juyo da ita suna fuskantar juna, zuba mata narkakkun kwayar idon shi yayi yana kallon yadda ta rufe ido amma sala salar hawaye na sauka bisa kuncinta, tafin hannun shi yasa yana share mata hawayen but still hawayen nata yak'i tsayawa.....
Duk wani abu da yasan in yayi zata sakko ta hak'ura ranar khaleefa yayi amma ta kasa daina kukan, yanzu babu sautin kukan ma sai hawaye kurum da ajiyar zuciya da take saukewa a jejjere.
A matuk'ar fusace da al'amarin nata wannan karon ya fizgi hannunta har k'ofar gidan Ahmad, a waya ya kira shi yasa ya kawo mishi mukullin motar shi. Yana futowa bai amsa mishi magana ko guda d'aya ba ya karb'i key d'in ya huce da ita ya bud'e front seat ya jefa ta shima ya shiga mazaunin driver ya fizgi motar a 360.
Ahmad da yake tsaye ya kama hab'a tare da bin bayan su da kallo a zuciyarshi yana fad'in, "aifa yau aiki ya samu Man.........
Tafiya yake ba tare da yasan inda yake tunkara ba har saida ya yiwa anguwarsu nisa da yawa sannan yayi parking motar gefen titi ya had'e kanshi da steery.
Raihana takure jikinta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya still idonta Yana futar da ruwan hawaye, kota k'uduri niyyar hak'ura ta daina kukan da zarar ta tuno tozarcin da Saleema tayi mata a bainar nass sai taji ranta ya sake k'ololuwa gurin b'aci, da aga jikinta da take tattali da b'oyewa ta gwammace su taru su mata d'an banzan dukan da zata kasa tashi,,,, sai ta sake yin wata sheshshekar da tasa khaleefa dukan steering da duka hannuwan shi kafun ya had'a hannuwan waje guda yana kallonta bakin shi har rawa yake gurin fad'in, "toh kawai ma ki cinye ni indai hakan zaisa kiji sanyi a ranki har kiji kin hak'ura......".
Tsit tayi ba tare data shirya aikata hakan ba, cikin matuk'ar tsorata da yanayin nashi ta zuba mishi idanunta tana kallon shi tana zazzare nata idon.
Gaba d'aya yanayin shi ya sauya daga asalin khaleefa zuwa wani fusatacce tamkar mayunwacin zaki..... Idonshi yayi jaa haka fuskar nan tamkar bai tab'a murmushi ba.
Ganin yadda ta dawo kuma sai duk ta bashi tausayi,,,, yasan tabbas abinda Saleema ta mata shine k'arshen cin mutumci a gurin dukkan wata d'iya mace da tasan mutumcin kanta, musamman ita da kullum cikin saka zurma zurman mayafai da hijabai tana b'oye jiki,,,,, toh amma tunda har abun nan ya faru bisa tsautsayi ai sai ta d'auki hak'uri ko? Yawan kuka maganin me zaiyi inba ya k'ara mata damuwa da tashin hankali ba.......
*After 15 minute*
Ruwa ya d'auka a ciki ya Bud'e murfin motar ya futo ya kewaya ya bud'e k'ofar side d'inta, ta gane abinda yake nufi don haka ba musu ta futo. Ruwan hannun shi ya bata ta karb'a tana son jin k'arin bayani.
"Kisha ki wanke fuskarki".
Nan ma batayi musu wajen aiwatar da duk abinda ya umarceta ba. A hankali ta dinga jin wata nutsuwa na kwaranya ruhinta tana bata sabon kwarin gwiwa.
Ranar basu koma gida ba saida ya tabbatar ta dawo dai dai yadda auntie ba zata fahimci komai a muryarta ko yanayin taba, abinci ma tare suka ci a gidan cin abincin shi daya zamewa babban customer. Yayi mata shopping na kayan mata masu kyau da set na kayan shafa masu gyara jiki da mayukan gyaran gashi ganin gashinta d'azu yaji a ranshi tana buk'atar su. Ita kam auntie ta zab'a ma irin abinda tasan zata so na daga kayan mata da amfanin yau da kullum. Khaleefa dai banda kayan amfanin gida bai d'auki komai wa karan kanshi ba.
Saida ya tsaya a k'ofar gidan Ahmad yayi parking motar ya kira shi a waya ya bashi key suka fara tattaki don su k'arasa nasu gidan.
Raihana tana daga bayan shi yasa key ya bud'e gidan suka shiga da sallama hannun shi rik'e da siyayyarta, ita kuma rik'e data auntie.
A lokacin da suka shiga auntie bata parlon amma jin shigowarsu yasa ta futo daga d'akin baccin raihana. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta musu sannu da dawowa.
Suka amsata kusan a tare. Sun zauna ita kuma ta shiga kitchen ta kawo musu ruwa da shayi. Ta cikawa kowa k'aramin glass cup da tea ta basu, babu wanda yayi magana cikin su suka amsa kawai suka shanye.
"Hankalina har ya tashi da naji shirun yayi yawa ashe kuna tare?". Auntie ta fad'a.
Kafun raihana tayi magana khaleefa ya karb'e zancen da fad'in, "eh ta makarantar su naje muka d'an zagaya taga gari..... Kumaaa muka yi siyayyah".
Yakai k'arshen zancen kamar mara gaskiya yana kallon inda raihana take zaune, sam yi tayi Kamar bata ji shi bama tana k'ok'arin mik'awa auntie kwalin siyayyar da suka mata.
Ta karb'a tana tambayar "hadda ni! Toh ina godiya Allah ya kawo zuri'a d'ayyiba".
K'asa k'asa khaleefa yace, "ameen" yana ma raihana kallon kasan ido, itama kallon shi tayi sai kuwa karaf suka had'a ido, da sauri ta d'auke kanta tare da mik'ewa ta shige d'akinta da siyayyar ta.
Shima khaleefa mik'ewar yayi sai dai auntie ta hana shi d'arawa ko'ina saboda tace tana son magana dashi.
Bayan ya tattara duk hankalin shi a kanta ta kira sunan shi ba wasa tattare da muryarta ko yanayinta, a duk lokacin da auntie tayi magana da seriousness toh lallai ba maganar wasa zatayi da mutum ba, hakan yasa ya sake shiga taotayin shi fiye da a farkon maganarta.
"Nan da kwanaki uku zan tafi sai dai ba gida zan koma ba zan huce saudiyyah ne umrah saboda na rok'i Allah sauk'i da sassauci cikin al'amuran rayuwata da suka fara d'aukar mun zafi cikin kwanakin nan..... Game da zamantakewar ku da raihana kuma ina sane da komai, da farko ka aureta don ta zamo maka tsanin da zaka taka ka tsallake zuwa ga samun cikar muradin ka, babu laifi idan kun shirya wani abu kaida ita wanda Allah ne kad'ai ya sani, sai dai Ina son ka sani aure ba'a shirya shi dako wacce manufa inba ta yad'a sunnar ma'aiki ba, watak'ila zuwa yanzu ka d'ago wani abu cikin maganata ko?".
Girgiza mata kai yayi cox da gaske bai fahimci komai ba.
"kwanakin baya ka nuna mun hoton wata yarinya da sunan itace kake so ka aura shin meye gaskiyar magana a kanta?".
Shiru khaleefa yayi yana nazari..... A duniya yana tsoron irin wannan titsiyen na mahaifiyar su, don a irin wannan zaman take kama mutum da laifi ba tare daya farga ba.
"Wato har yanzu in ana magana dakai sai an maimaita maka zance sai bibiyu uku uku kake iya bada amsa!". Auntie ta sake fad'a tana kallon shi.
Numfashi yaja mai tsayi kafun yace, "wannan maganar ta huce a gurina tun lokacin dana kai miki maganar auren raihana".
"Kenan ka yiwa magabatan ita waccen yarinyar bayani? Ko kuma ka kyalesu suyi ta kallon ka suna ganin ka yaudare musu yarinya".
"A'a ai ban kaiga ganin magabatan ta bama, sannan zuwa yanzu itama tasan na rabu da ita.....". Khaleefa ya fad'a da saka ran ya kawo k'arshen tambayoyin nata gaba d'aya.
Itama tsura mishi ido tayi, tasan inba ita d'in ba ba uban daya isa ya zaunar dashi yana mishi irin wannan titsiyen. Saboda haka sai tayi wani killer smile tace, "toh Masha Allah! Sai dai ina da wani sharad'i da zan gindayawa auren ku kaida raihana kafun tafiyata zan fad'a maka.....Amma yanzu ina fatan kana sane da tafiyata tare da raihana ko?".
Gyad'a mata kai yayi bayan ya kauda komai da yaji daga ranshi.
"Good zaka iya tafiyarka".
Da haka suka kawo k'arshen hirar ya tashi a gurin salin alin ya shige d'akin shi na gado ya rufo k'ofar.
Shiru yayi yana nazarin maganganun da sukayi da raihana akan Saleema daren ranar, duk abinda ta fad'a gaskiyane tunda ita ta riga ta mishi nisa kuma bawai dama sun shirya