Showing 228001 words to 231000 words out of 288773 words

Chapter 77 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1053

sa take yi duk haka, amma yanzu daga yau ya fara fahimtar babu rashin wayewa ko d'aya a tare da raihana, komai tana yinshi da saninta ne.....
Yak'i yayi da zuciyarshi ya yakice komai ya ajiye gefe ya tashi daga gurin ya koma parlour ya bud'e system d'inshi da take charging ya tsura ma pic d'in Ayman idanu, hoto ne daya turo mishi tun lokacin da yake karatu, abubuwa masu tarin yawa suka shiga dawo mishi cikin kanshi daki daki tun daga kan rabuwar su shiya taho karatu har kawo jiya da suka jima suna waya dashi suna tattauna batu irin wanda sukan jima basu tattauna shiba, matsalolin da suke kewaye da rayuwarsu data mahaifiyar su,,,,,, ga kuma Raihana.......

Bayan ya gama zaman tunanin rufe computer daya kasa tab'uka komai cikinta yayi ya kalli sashen da raihana take aikin gyaran inda suka ci abinci.
"Ki shirya zamu futa". Ya fad'a da muryar data b'oye asalin yanayin da yake ciki.
Raihana hijab kawai ta zubo saman kayan jikinta ta futo rik'e da wayarta, kallo d'aya khaleefa ya mata ya d'auke kanshi yaci gaba da wayar da yake har ta rufe k'ofar tabi bayan shi suka fara tafiya shi kuma yana ci gaba da wayarshi cikin harshen jamus.
Sunyi tafiya mai d'an tsayi kafun su tsaya a k'ofar wani gida, ya ciro wayarshi yayi magana ta minti uku zuwa hud'u ya ajiye wayar.
Basu jima ba wani matashin saurayi Nigerian yazo ya bud'e musu k'ofa yana ma khaleefa magana da hausa, "Man sai yau Allah ya nufa kenan?".
Raihana tana jin haka tasan abokin shine, khaleefa ya mik'a mishi hannu sun gaisa sannan itama ta russuna tana gaishe shi.
"Au kema daga nan madame khaleefa?". Raihana tayi murmushi kanta a k'asa.
Shi yayi musu iso har cikin gidan, tsarin ginin su ya banbanta da nasu khaleefa don wannan gidan yafi wanda suke ciki wadatar d'akuna da komai.
Matarshi ta kawo musu abincin Nigeria daya sarrafu da kyau ga drinks data had'a duk na gargajiya wanda suka nuna dukkan alamun tasan da bak'uncin su.
Muhammad sun gaisa da raihana da matar shi nadeeya, ba laifi itama tana da kirki ga nutsuwa, basu jima sosai ba don k'in cin komai sukayi sai ruwa har suka tashi zasu tafi.
Nadeeya ta rako ta har bakin k'ofa tana mata godiya ita da Muhammad tare da Alk'awarin zuwa bada jimawa ba.
Suka tafi kowa na farin ciki da ziyartar juna.
Kamar yadda suka zo haka yanzun ma suka koma, sai dai raihana kasa hucewa gidanta tayi a lokacin da taga k'ofar yasmine, tayi zaton khaleefa zaice su shiga sai taga yayi gaba, ita kam tana son duba ta tunda jiya bata je mata ba gaba d'aya, "Ina son duba yasmine". Ta fad'a da d'an k'arfi tana bin bayan shi da sauri.
"Ba zaki jeba, mijinta yana gida zai kula da ita". Ya bata amsa ba tare daya tsaya ba.
"Don Allah Ina son na ganta". Ta fad'a bayan ta matsa kusa dashi kad'an,
A dai dai lokacin Ahmad ya futo daga gidan shi, basu lura dashi ba kwata kwata.
Khaleefa fasa bud'e gidan yayi (dama keyn yana gurinta) ya matso daf da ita yace, "okay zaki je ki fad'a musu ke baki da wanda yake buk'atar kulawarki kenan?".
Zancen gaba d'aya a bai bai raihana taji shi, hakan yasa ta sake had'e fuskarta ta turo k'aramin bakinta gaba, "Eh ai ba wani abun zanyi maka ba a gidan.....".
Yadda tayi da bakin kamar zata shagwob'e ba k'aramin tafiya tayi da tunanin shiba har ya fara shagala a kallonta , da sauri kuma kamar wanda ake gargad'a ya d'auke idon shi ya sake matsawa kusa har hucin numfashin shi na sauka ta saman fuskarta ya kamo tafin hannunta, laushin hannun ya kai sak'o na kai tsaye har cikin kwakwalwar shi.
"Man a hanya kuke fa" Ahmad ya fad'a da d'an k'arfi yadda zasu jiyo shi yana had'awa da musu dariyar shak'iyan ci.
Zare keyn gidan da yake hannunta khaleefa yayi yaja jikin shi baya da sauri ya nufi k'ofar gidan ba tare da ko waiwayen inda Ahmad yake ba.
Raihana ma gaba d'aya jikinta yayi sanyi shiyasa ta janye k'udurin ta tabi bayan suka shige salin alin.
Direct kitchen ta dire ta had'a musu simple recipe don daga ita har shi ba abinda suka ci a gidan nadeeya sai ruwa.
Lokacin data gama bata tsammanin ma yana gidan, saboda haka a nutse ta shirya mishi abincin kan k'aramin table da yake tsakiyar parlon ta d'auki nata ta fara ci. .
Tana cin abincin zuciyarta na hasaso mata khaleefa a lokacin daya matso gab da ita k'amshin turaren shi ya cika mata hanci tafff! Hucin numfashin shi na ci gaba da sauka a fuskarta kamar lokacin yake tsaye gabanta.
Cokalin ta ajiye tare da sauke doguwar ajiyar zuciya.
Bud'e k'ofar parlon akayi khaleefa ya shigo da kaya niki niki zai huce kitchen, daga inda take zaune ta yi mishi sannu da zuwa, koya amsa ko bai amsa bama oho.... "Raihana" da taji an kwala kira yasa ta mik'ewa tare da nufar kitchen d'in da sauri, ta shigo ya nuna mata nama da kifin daya zuba cikin fridge "kisan yadda zaki yi da wannan kada su lalace". Gyad'a mishi kai tayi, ya futa ita kuma ta shiga jera komai a inda yake, saida ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar riga armless ta d'ora k'aramin hijab a sama sannan ta fara aikin ta.
Tana gamawa ta d'ora da girkin dare, haka ta k'are kusan rabin yinin a kitchen tana aiki ranar, gashi tana da research da take son yi ta manta shap saida tayi kaca kaca da aiki a kitchen ta tuna.
****Da dare bayan ta had'awa khaleefa tray na abinci da shayin shi a dinning hucewa d'akinta tayi ta fara aikinta tun kafun bacci yaci k'arfin idonta.
Bayan ta gama futar da ma'anar komai a littafi shiru tayi tana nazarin ta inda zata samu k'arin bayani, khaleefa ba b'angare d'aya suka karanta ba bare ta tambaye shi, gashi tun asali sunyi da meerah zasu had'u da k'arfe biyu a makaranta, tasan sunyi ta jiranta har sun gaji tunda cikin su bame no ta. Hijab ta d'ora saman kayan baccin jikinta ta futo parlon, yana zaune yana cin abinci.
Saita k'arasa futowa ta samu gefe guda ta zauna, bai kalleta ba har ya gama cin abincin ya rufe sauran, ya tsiyaya shayi a glass cup yasha.
Sai a lokacin ya maida hankalin shi kanta yasan duk yadda akayi akwai magana a bakinta, itama ganin ya gama saita futo da littafin hannunta daga hijab, "dama k'arin bayani nake so kamun, ban sani ba ko zaka gane".
Mik'a mata hannu yayi, ta bashi littafin, saida ya gama dubawa sannan yace mata, "matso kusa".
Matsawar tayi amma ba yadda zata dame shiba, ya fara mata bayani dalla dalla da harshe biyu don tafi ganewa. Yadda yake zuba bayani sai raihana ta saki baki tana kallon shi, sai taga ko lecturer da yake musu lecture albarka.
"Raihana ba'a kaina zaki saka idon kiba". Khaleefa ya fad'a yana kallonta.
Sunkunyar da kanta k'asa tayi cikin jin nauyin yadda ya kamata tana kallon shi hadda tafiya tunani....
Har ya k'arasa mata bayanin ya mik'a mata littafin bata daina mamakin shi a zuciyarta ba.
"Kin fahimta kuwa?". Ya tambayeta.
"Eh" ta bashi amsa kanta akan littafinta data karb'a a hannun shi.
"Then explain". Ya fad'a bayan ya kwantar da kanshi baya ya lumshe idanun shi duka biyu.
A nutse ta fara maimaita abinda ya fad'a dai dai gwargwadon fahimtarta.
"Raihana kina da sharp brain, ki godewa Allah".
"Har na kai ka? Kaida kayi mun bayanin abinda babu shi a cikin karatun ka, ba'a tab'a zaunar da kai an karanta maka ba.....".
Murmushin gefen baki yayi yace, "toh ai in aka ce health ana magana akan gaba d'aya sassan jikin d'an Adam, ka biya karatu a d'auke shi kafun ka gama sauƙe numfashi is something different.... Zamu iya kiran shi baiwa irin wadda ba kowanne mutum Allah yake yiwa ba".
"Toh aikuwa indai ni y'ar baiwa ce, kai kuma za'a iya kiran ka da asalin baiwar.....".
Murmushi kawai yayi ba tare da ya sake ce mata komai ba.
Itama had'a littafanta tayi ta mishi godiya da sallama ta huce d'akinta.

****A saudiyyah auntie ta duk'ufa tuk'uru tana addu'a babu dare babu rana kan Allah ya kawo mata sauk'i da rangwame, cikin harkokinta da al'amuran rayuwarta da yaranta gaba d'aya, more especially raihana da khaleefa, tana son mutanen nan su tsaida hankalin su guri d'aya su karb'i juna a yadda k'addara tazo ta had'a su, Sam bata son auren nan ya katse da sunan raihana zata futo ta auri Ayman. Wannan wani kwad'o ne dako bayan ranta bata fatan a had'a shi.
Ranar data cika kwana biyar a k'asar ta futo daga masjid da dare tana tafiya taji an rik'e hannunta an kira sunanta, "surayyah". Kafun ta juya taji kamar tasan muryar.
Koda ta juyo ido hud'u tayi da matar mukhtar (yayan su Suraj). Da sauri ta shanye al'ajabin ta na ganin matar tace, "hajiya lafiya?".
"Surayyah kina nufin baki gane niba?".
"Wata Surayyahn kike nema bayan wadda kuka kashe tun shekaru talatin da suka gabata? Malama sake mun hannu na huce....". Ganin bata da niyyar sakinta sai ta fizge hannun ta juya ta bar mata gurin, sauri sauri ta b'ace mata a zuciyarta tana jaddada lazim ma ta bar k'asar nan tunda har dangin Suraj sun fara ganinta.
Ita kuwa fasa shiga masallacin tayi ta koma masauki sauri sauri, ta dinga kiran layin mukhtar baya picking, saida ta tsaida hankalinta ta jiyo ring d'in wayar na tashi cikin d'akin baccin su, ta k'arasa ta d'au wayar tare da dafe kanta da hannunta.
Mukhtar yana shigowa ko zama bata barshi yayi ba ta tarye shi da maganar, "surayyah! Mukhtar yau naga surayyah da idona, da idona na ganta wallahi".
Kama ta yayi ya zaunar da ita yace, "kinga ki nutsu tukun sai kiyi mun bayani yadda zan fahimta, kina nufin surayyah matar Suraj kika gani a k'asar nan?".
"Eh wallahi naga surayyah matar Suraj da idona har munyi magana da ita".
"Toh fah, Suraj ya tafi surgery Germany, ke kuma kinga surayyah da idon ki a nan, idan har Suraj yaji labari cewa surayyah tana nan, toh zai ajiye komai ya taho nan koda ba zai same taba, ke koda zai rasa hannun ma gaba d'aya k'arewar ciwo, Soo Ina ganin yadda za'ayi mu duk'ufa nemanta da kanmu ko zamu sameta.... Mtss! Koda yake neman me ma zamuyi mata bayan komai ya k'are tsakaninta da Suraj.....". .
Matar shi tace, "ta ina komai ya k'are bayan kullum Suraj yana fad'in ta tafi mishi da wani abu mai daraja da muhimmanci a rayuwarshi,,,,,, mukhtar ko don farin cikin Suraj ya kamata mu nemi surayyah".
Mukhtar yace, "haka ne kuma? Toh amma yanzu ta ina kike ganin zamu fara nemanta, k'asa sama da mutum dubu.....".
Duk sunyi shiru kafun ta sake cewa, "Ina da wata shawara".

******Gaba d'aya cikin kwanakin da suka biyo baya raihana bata samu damar ci gaba da bibiyar labarin auntie ba, duk da kullum dashi take kwana take tashi a ranta, kullum ta shiga school bata samun lokacin kanta, haka da zarar ta dawo gida ma aikin gida ba zai barta ta nutsu ba.
Khaleefa ma ta b'angaren shi kusan hakan ne, tuni andal ta karb'e ragamar aikin Suraj a hannun shi ta mik'awa Ahmad, don dama shine na biyun khaleefa a kwarewa, tunda suke surgery a asibitin ba'a tab'a samun matsala ba.

Yauma kamar kullum raihana ta dawo school a gajiye, da yake yau da wuri ta futa kuma lecture d'aya sukayi shine har ta samu kanta, tayi tunanin shiga gidan Ahmad sai kuma ta tuna kamar khaleefa baya son taje kwana biyu, hakan yasa tayi shigewarta gida. Wanka kawai tayi tasha tea ta d'auki littafin auntie zata ci gaba da dubawa, yau ko girkin ba zatayi ba kowa ya hak'ura da yunwar cikin shi kamar yadda ta hak'ura da tata. Auntie taci gaba da cewa👇
"Ashe duk hasashen da nake kan tsanar da Suraj yake mun abun ya zarce tunanina, ban tab'a d'auka zai iya yanke igiyar aurena ko guda ba sai gashi ya yanke har uku akan abinda bansan hawa ba bansan sauka ba......". Da matuk'ar mugun sauri raihana ta ajiye littafin gefe ta tallabe kanta da hannunta bibbiyu, take idonta ya kawo ruwan hawaye..... Banda innalillahi babu abinda take maimaitawa a bakinta.
Saida taci kuka ta gode Allah sannan ta d'auki littafin taci gaba da dubawa, "ko kad'an idona bai kawo hawaye ba, saboda zuciyata ta bushe a lokacin, haka duniyar ma ta fuce mun a rai ban k'iba nabi bayan iyayena, tun a lokacin na hak'ura na saddakar babu wani mai Amana da rik'on gaskiya daya rage a duniya, mutanen kirki sun k'are saina banza, fajirai majanunai da basa son abinda addinin islama zai ci gaba.
Ki futa surayyah! Suraj ya dawo dani hayyacina ta sanadiyyar fad'in hakan cikin daka tsawa. A lokacin murmushi nayi na Isa har gaban shi nace, "Naga mutane iri iri a duniyaa, amma ban tab'a ganin mayaudari maci amanar k'auna irin kaba, ashe akwai ranar da zaka yi mun irin wannan butulcin? Ashe soyayyah ba tana nufin sadaukarwa da kyakkyawar fahimta ga juna ba?, Insha Allah soyayyata saita azabtar da kai ba zata tab'a bari ka huta a rayuwarka ba, kamar yadda Allah yayi alk'awarin jarrabar duk wanda ya saki matarshi cikin fushi, saki irin wanda kayi mun da zazzafar soyayyarta......".
Cikin takaici Suraj yace dani, "soyayyarki ba zata tab'a azabtar dani ba saboda ban yaudare kiba, hasalima sai dai soyayyata ta azabtar dake, Ina sonka! Ina sonka! Ina sonka Suraj, wannan kalmar kin dinga maimaitata kenan har k'arshen numfashin ki.....".
"Kamar yadda surayyah zata tafi maka da abu mai tsada da daraja da muhimmanci na rayuwarka.....". Na juya ga sauran mutanen gidan nace, "ban zalince kuba amma duk wanda yazo mun da sharrin tsafi ba zan tab'a yafe mishi ba abadaan.....".
Wannan shine maganata da had'uwata ta k'arshe da mutanen gidan su Suraj Abdallah.
Bazan ce mutanen gidan su Suraj sun zalince niba, saboda komai d'orawa sukayi daga samun fuska a gurin Suraj, dad'in dad'awa bansan abinda aka k'ulla a lokacin da nayi tafi gurin aminiya y'ar uwa a gareni wato andal,,,, sai dai koma meye nasan ya k'aru ne da fushin dana tafi na barshi yana yi..... Ko yanzu aka tambaye ni wanene Suraj abinda na sani game dashi zan fad'a, ya kasance bahago kuma baud'ad'd'e mai baud'ad'd'iyar fahimta da kasa fahimtar gaskiya cikin sauri.......
Raihana kowanne d'an Adam tafe yake da ajizanci, nima ta b'angarena hakan ne, fushin zuciya yasa nayi alk'awari akan abinda ba hak'k'ina ba ni kad'ai, na taho da cikin su khaleefa, na haife su a inda ba'a iya gani ayi shiru ba har mutanen gari suna kallon su da kiran su da kalma mafi muni da had'ari wato *shegu*.
A zahirin gaskiya tun kafun aje da nisa soyayyar Suraj ta fatattaka zuciyata ta hana na kalli kowanne namiji da sunan soyayyah, na kasa aure duk da nasan nida Suraj har abada sai gani sai hange daga nesa. Sai dai nayi gagarumin kuskure, na yiwa yaran k'arya da cewa mahaifin su ya mutu alhalin yana raye, sannan kowanne uba yana da hak'k'i akan yaran shi kamar yadda nake dashi amma shi na hana shi wannan hak'k'in,,,,, raihana ko yanzu Allah ya d'auki rayuwata zan tafi da soyayyar Suraj da kuma hak'k'in yaran shi dana tauye.
Raihana naga abubuwa da yawa a tare dake irin wanda na jima ban gani a tare da wani mutum ba, shiyasa na yanke hukuncin had'a ki da gagarumin aikin bayyanawa khaleefa gaskiya cikin sauk'i ta yadda zai fahimta har su kai kansu ga mahaifin su don ni kam nayi alk'awarin bazan tab'a kaisu gare shi da kaina ba, sannan bazan gajiya da rok'on ki sadaukar mun da soyayyar da kike yiwa Ayman ta zama ta khaleefa ba, ki mantar dashi d'aci da bak'in ciki had'e da rad'ad'in daya yake cikin soyayyah irin wanda ya kurb'a, ki sashi yayi aman gubar daya sha da sunan soyayyah, ki nuna mishi ke tukuici ce kuma kyauta ga wahalar da yasha a rayuwar shi ta baya.

A k'arshe Ina fatan ku kafa sabuwar daular soyayyar da babu irinta a gaba d'aya arewacin Nigeria. Allah yayi miki albarka daughter......
Your mother's ever surayyah Adam.

(Dama ba kowanne labarin soyayyah ne yake k'arewa da abinda mutane suke so ba, yawancin soyayyar data cika bata k'arewa da kyau irin yanda zamu ga hak'oran mu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login