Showing 69001 words to 72000 words out of 288773 words

Chapter 24 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1093

iya shiga bane, da farko dai ita Saleema ka ajiye ta a gefe, ni har yanzu bansan ta inda zan fara fassarata ita da soyayyar ta gare kaba, kai tsaye bazan ce ta yaudare kaba, saboda ni ban tab'a ganin yaudara a idanunta ko a tare da ita ba, sannan a aikace bata nuna maka hali na adalci ba, ta yadda ta yanke alak'ar ka da ita farat d'aya ba tare da dogon nazari ba. Abu na biyu sai dai kayi hak'uri amma akwai k'amshin gaskiya a zancenta, ni bance ku ba halastattu bane amma lallai mahaifin ku yana raye kamar yadda Saleema ta fad'a, shiyasa Auntie tak'i yarda ku ga hoton shi, take ta b'oye muku komai game dashi, maybe kuma ya rasu kamar yadda ta fad'a amma akwai rikici mai girma tsakanin ta da familyn mahaifin ku shiyasa tak'i yarda ta nemo su kota had'a su daku, khaleefa a cikin biyun nan dole za'a samu d'aya, sannan idan ka duba da kyau zaka ga babu kama kota farce tsakanin Auntie, iya, da malam, iya da malam suba farare bane kamar auntie, sannan iya tana d'an jin fulatanci kuma bata iya larabci ba, auntie kuma tana jin larabci bata iya fulatanci ba, toh ta Ina kenan kake ganin sun had'u? Daga kamannin mahaifiyar ku, ko makaho ya shafa tsantsar kyawunta da hasken fatar ta zai gane ta futo ne daga jinsin Arab, sam bata kama da Nigerians........ Lallai ya kamata ku fahimci hakan tun kafun Saleema ta fad'i waccen maganar ta b'atan ci gare ku, da cikin sauk'i baka fad'a mata tarihin kaba......".
Shiru khaleefa yayi yana k'ara d'aukar haske kan yadda mu'amular su ta dinga tafiya da auntie a gidan iya, shi dama ya dad'e da fahimtar akwai wani abu da take b'oye musu shiyasa take takatsantsan dasu duk tsawon wad'an can shekarun, shine dalilin da yasa tasa suka yi mata alk'awarin basu ba sake tambayarta wani abu game da mahaifin su ko dangin shi. Sai ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, "innalillahi wainna ilaihi rajiun, Ahmad maganar ka fa gaskiya ce, yau na sake ji a jikina lallai mahaifin mu yana raye.... Ahmad na tabbatar da haka....."
Zuba mishi ido Ahmad yayi cike da tausayin shi kafun yace, "yanzu Ina matsayar soyayyar ka da Saleema?".
Girgiza kai yayi cikin takaici ya nemo SMS d'inta ya mik'awa Ahmad sannan yace, "har abada ba zan tab'a daina son Saleema ba saboda sonta a jinin jikina yake, kuma itace mace ta farko dana fara Soo a rayuwata, sai dai bazan k'ara k'ulla wata alak'a tsakanina da ita a yanzu kota gaisuwa ba, zan duk'ufa wajen neman ahalin mahaifina na gabatar musu da kaina, su da kansu nake so suje nemo mun aurenta k'asar su gurin mahaifin ta, Ahmad koda ya kasance Auntie bata samar damu ta hanyar halas ba bazan tab'a b'oyewa familyn Saleema ba, idan sun so su bani ita a haka, idan kuwa suka hanani aurenta to tabbas ya tabbata bani da rabo a soyayya da aure".
Maganarshi ta k'arshe ta tab'a zuciyar Ahmad sosai, khaleefa yana nufin idan har bai same taba bashi ba sake yin soyayyah bare aure?
_tirk'ashi_

Ahmad bayan ya jinjina al'amarin kallon shi ya sake maidawa kan khaleefa yace, "kada kayi saurin yanke hukunci insha Allah zaka samu Saleema ni kaina Ina jin haka a jikina, duk wata soyayyar data cika soyayyar gaske ta asali tafe take da k'alubale, kuma dole ku shiga cikin sa ba zaku kub'uta ba, sai dai Ina ganin anya babu kuskure kace zaka yanke alak'a da Saleema kamar yadda take so? Idan bayan wani lokaci ta amshi soyayyar wani fa? Tunda mu bamu san kai tsaye inda zamu samu y'an uwan mahaifin naka ba? Bare mu k'ayyade lokaci, bamu san ainahin tsayin lokacin da zamu d'auka wajen neman suba?".
Murmushin takaici khaleefa yayi yace, "kamar baka duba sak'on ta sosai ba? Insha Allah zamu samu nasara a k'asa da shekara guda ma".
Cikin K'arfafa gwiwa Ahmad yace "insha Allah"
Sunci gaba da tattaunawa duk akan yadda zasu shawo kan lamarin.

@@@@@@@@@

Saleema kam tana can taci gaba da rayuwarta cikin tarin damuwa da sauraron tunanin da k'awarta Amna take akan matsalar ta, ganin har kwanaki goma sun shude Amna bata ce da ita komai ba sai ta fara tunanin tambayarta kota manta da lamarin ta ne ma, gashi ko a hanya bata had'uwa da khaleefa bare a cikin school ta ganshi taji sanyi a ranta, sai yanzu take ganin kuskurenta na yanke hukuncin datse alak'ar da take tsakanin su rana tsaka, ta d'auka abu ne me sauk'i da zata iya, sai gashi ya zamo abu mafi wahala ga zuciyarta da ruhin jikinta, ga wutar son shi sai k'ara ruruwa take a cikin zuciyarta, sai yanzu da suka rabu take iya fahimtar tsananin son da take mishi, gashi abu na farko da take tunani game da jin shirun shi shine, tasan mutum ne shi me tsananin zuciya, duk abinda ya bari baya tab'a waigen shi har abada! Tsoronta d'aya kada dai khaleefa yana nufin ya rabu da ita ne har abada kamar yadda taso da farko. A zaune take saman stool sai gata ta silmiyo k'asa wanwar ba tare data sani ba, glass cup da yake hannunta ya sunlube ruwan zafin ciki ya kwaranye saman cinyarta, ko zafin ruwan ba taji ba saboda rad'ad'in da yake zuciyarta yafi k'arfin wannan rad'ad'in nakan fata da zai iya warkewa cikin sati d'aya zuwa kwana goma.
A wannan yanayin Amna ta futo daga kitchen ta ganta, sai ta taho gurinta da sauri, "subhanallah Saleema meya same ki kuma? Yanzu fa na barki lafiyar Allah a nan?". Kallon Amna tayi da idonta da suka sauya launi tace, "Amna da gaske zaki nemo mun mafuta ko kuma zaki barni nayi asarar miji mai nagarta kamar Abdallah?".
Murmushi Amna tayi cikin son ganin ta kwantar mata da hankali tace, "haba mana dear wannan shine kad'ai damuwarki? Ina nan ina nemo miki mafuta as I promise, sai dai ina son na fara jin ta bakin shi tukun in na had'u dashi, Soo cool down your mind insha Allah khaleefa mallakin kine k'awata, kuma y'an gidan ku zasu fahimci irin son da kuke yiwa juna su barki ki aure shi naji hakan a jikina tabbas".
Cikin muryar kuka tace, "don Allah Amna kada ya zamana kina fad'ar haka don kawai ki kwantar mun da hankali......". Sake k'ak'alo murmushi Amna tayi tace, "wannan naji ne a jikina ba hasashe nake ba Saleema". Kwantar da kanta tayi a gefen kafad'ar Amna tace, "Ina alfahari dake k'awata ina k'ara neman gafarar ki akan abinda na aikata gare ki kwanakin baya". Amna da kulawa tace, "ki daina damuwa da haka mubar abinda ya huce har abada please". Saleema cikin farin ciki ta rungume Amna tana kuka sosai a gabanta, itama Amna kuka take yi cikin tausayin k'awartata da wannan badakalar soyayyah tasu.


***********


*Nigeria*

Surayyah ce zaune a madaidaicin office d'inta tana rubuce rubuce jikin wani file na wata marar lafiya da aka kawo, irin mutanen k'auyen nan da idan suka ji ciwo basu san suje hospital ba sai jike jiken magungunan gargajiya har sai abun yaci k'arfin su su taho asibitin cikin birni a haukace.
Tana duba file d'in tana jinjina wannan al'amari na bayin Allahn nan, sanye take da riga da zani na atamfa sai labcourt a saman kayan da k'aramin gyale, tuntuni wayarta take ring tak'i dubawa saboda tayi aikin da yake gabanta cikin nutsuwa, bayan ta mik'a musu takarda mik'ewa tayi don gabatar da sallar zuhr da tayi a lokacin, ko data futo ba'a fasa kira ba har tayi sallah taje donta ziyarci gidan cin abinci tayi lunch. Still wayar taci gaba da ringing, sai ta d'auka donta duba me kira a lokacin, Ayman ne, da sauri tayi picking tasa a kunnenta, "yaa Ayman hope ba jikin bane?". Ayman da yake office a lokacin yace, "eh auntie nasha magani kafun na futo Ina office amma duk hankalina yak'i kwanciya shine na kira naji lafiyarki".
Duk da gabanta ya fad'i amma sai da ta sauke ajiyar zuciya tace, "Ina lafiya Lou Ayman, yanzu haka zan futa yin lunch ne, fatan kaci abinci ba aiki kamar agogo ba". Yana daga inda yake zaune yace, "in na futa sallah zan tabbatar nayi yadda kike so kafun na koma office". Tace, "good!" Daga nan suka yi sallama ta futa don yin abinda zata yi.

★★★★★★

Da yamma koda ta tashi office bata je gida ba saida ta tsaya gurin doctor Salihu suka sake magana akan aikin khaleefa da yake gab da dawowa k'asar, ya sake bata tabbaci akan ba za'a samu wata matsala ba insha Allah, indai kwalin yaron yazo da kyau irin wanda suke so.
Cike da farin ciki da jin dad'i ta futo, ta gaji sosai amma sai taji tana son biyawa gidan sameera k'awarta don ta tayata murnar wannan kyakkyawan albishir. Don haka saita juya akalar motar ta zuwa anguwar......

A dai dai wannan lokacin sameera tana zaune tare da wata k'awarta hajiya tafeeda, hajiya tafeeda irin matan nan ne masu son kansu, babu ruwan su da kowa kansu kawai suka sani suke Soo, a dai dai wannan lokacin labarin abinda ya dame ta take ba sameera, yayinda ita kuma sameeran take sauraronta kurum tana jinjina zallar son zuciya dake ƙunshe cikin furucinta, ko dana kasa kunne magana take cikin fushi da b'acin rai, "ai wallahi ya had'u da rashin zaman lafiya daga gare ni shida mahaifin nashi da yake goya mishi baya, sakaran yaro kawai, yanzu da yabi yadda nake so da ba shaheeda zai zo ya aura ba, yarinya Masha Allah irin wadda mazan garin Kano ke rububi, shine ya b'ige da yarinyar da mutane da yawa sun tabbatar da bata da tarbiyyah, ance idonta fa a bud'e yake......". Sai a lokacin sameera ta tari numfashinta, "toh ke waya fad'a miki duk wannan? Kada ya zamana fa kema kin shiga sahun mutanen da suke yadda da jita jitar mutanen gari y'an hana ruwa gudu da basa son suga an k'ulla abun arzik'i?".
Wani irin kallon takaici ta yiwa sameera taci gaba da maganar ta, "humm ba zaki gane ba maman haeydar, kinsan Allah da gaske yarinyar ance bata da tarbiyyah, kina ji wani k'aton saurayi ta k'ulla alak'a dashi tun bata kai haka ba da sunan wai aboki, uwar kuma wata banza gagaso ta sakar mishi basa nan basa can gaba d'aya fa ance ya gama lalata mata rayuwa har makarantar da tayi a wani gari yake binta yayi kwanaki suna gantalin su sannan ya dawo, haka in zata dawo gida ma shi yake d'auko ta ya dawo da ita su d'ora daga inda suka tsaya, kar kiso kiga zuciyata da naji labarin irin dukiyar da suka narka ga wannan gantalalliyar yarinya suka kai da sunan lefe.....".
Ita dai sameera cike da al'ajabi take sauraron tafeedan saboda tana ganin zallar wauta a kalamanta, magana take akan Ayman da raihana wanda ba wai don surayyah tata bace zata iya rantsewa da girman Allah surayyah bata daga cikin iyayen da suke zubawa yara ido suna yin abinda ransu yake so a gari ba. Koda yake itama ba tayi magana akan surayyah ba duk buhun k'iyayyar ta akan raihana da mamanta take saukewa, wannan kuma matsalar suce can da ita da zata zamo surukar su.
Ta bud'e baki zata yi magana taji ihun heedaya tana kiran Auntie! Auntie!! Sai ta maida idonta k'ofa tana jiran taga ta inda aminiyar tata zata b'ullo. Aikuwa sai gata rungume da heedaya ta d'auko ta, saman kujera ta ajiye ta tana nishi, sameera tace, "sannun ki da k'ok'ari kema yanzu wannan garsamemiyar budurwar kika wani d'auko?". Tana murmushi ta shafa kan heedaya tace, "ke kike kallonta garsamemiyar budurwa ni a gurina har yanzu y'ar jaririya ce". Duk dariya sukayi abun har yaba heedaya kunya ta shige cikin gidan da gudu tana b'oye fuska.
Gaisawa suka yi da sameera sannan tafeeda ma dai suka gaisa sama sama, don tasu bata zo d'aya ba sam, sameera sawa tayi aka kawowa auntie ruwa da abinci, ta dai sha ruwan amma abincin babu gurbin shi. Sameera ce tace, "kinsan yanzu nake niyyar kiran ki a waya kayan nan sun iso ummie zata yi clearing komai ta tafi ma tuni".
Surayyah tace, "Masha Allah amma sunyi ba zata". Sameera tace, "sosaima".
Daga nan suka yi shiru, surayyah ta zaro wayarta tana dubawaa don bata son amayar da abinda yake cikinta gaban wannan magananniyar matar don ita sam bata son mutum mai irin halinta.

_dubun godiya da jinjina ga d'aukacin mabiya litattafan *in-identical twins* hak'ik'a muna jin dad'in comment d'inku na so da nuna goyon baya 100% fatan alkhairy gare ku baki d'aya_.


_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page twenty 2️⃣0️⃣


Ita kam tafeeda ganin sunyi shiru ci gaba da bata labari tayi, duk wani k'anzon kurege da k'aryar da ake kawo mata ta hau ta zauna daram. Shiyasa ta tsani raihana kamar ta soka Mata wuk'a ta kashe ta a huta.
Auntie da take zaune wayarta take dannawa tana harkokin gabanta hankalinta sam baya kansu, kuma dama itama sameera abinda take so kenan, don wannan kwab'a da jik'a aiki da tafeeda take da ta jita kam ba zata ji dad'i ba, surayyah ganin tafeeda nata magana bata da shirin tafiya gashi har lokacin komawarta gida zai k'ure tana waje, saita mik'e ta yi musu sallama ta tafi.
Ko bayan futar ta tafeeda kallon sameera tayi tace, "nifa sai dai kiyi hak'uri amma wannan k'awar taki sam bata yi mun ba, ruwan munafukai ne da ita, ga shegen jin kai da d'aukar kai wata tsiya bayan duk mutanen gari sunsan bata da cikakken asali, haka tazo garin Kano da cikin da babu wanda yasan ubansu suka had'a kai da malam yusha'u da iya suna fad'awa mutanen gari wai y'ar shi ce, koda yake ke duk abinda zan fad'a ma ba yarda zakiyi ba tunda ga yaran nan sun girma kina shirin d'aukar y'a ki bayar sabo........." Ai da sauri Saleema ta d'aga mata hannu bata bari ta k'arasa ba, "kinsan abinda yake yawan had'a mu dake kenan ko tafeeda, toh wallahi ki iya bakin ki ba ruwanki da tsakanina da ita, tsakanin mu dake daban tsakanina da surayyah ma daban, ku kullum mutanen garin nan in baku jefi mutum da mummunar kalma ba ba kuji dad'i ba, toh bari kiji tafeeda su wanda suke kawo miki gutsiri tsomar suka hana ki zama k'alau da mutane in kin sake had'uwa dasu ki fad'a musu ba nuriyyah kad'ai zan bawa Ayman ba har khaleefa da yake karatu a Germany zan bawa auren shaheeda, sai su samu sabon abun yad'awa, Soo gwara ma tun wuri kibar Imran ya auri raihana in Kuma ba haka ba zaiyi babun bad'ilahu, ba wan ba k'anin".
Tunda sameera ta fara magana cikin fushi da fusata bata dakata ba har saida takai Aya, cikin sanyin jiki tafeeda tace, "oooh k'awata wannan sababi haka daga magana? Toh Allah dai ya baki hak'uri ni tashi ma zanyi in tafi".
"Ai kece bakya iya kiyaye harshen ki tafeeda, kowanne kare da doki in yazo miki da gulma da funafunci sai ki share guri ki zauna ki saurara duk gashin nan ai sun gurbata miki tunani kema kin fara zama irin su".
Tafeeda tace, "ke wani abun fa ba maganar munafunci bane gaskiya ce tsagwaronta bakya son a tab'a masoyiyar k'awar kine kurum, yanzu ke sameera in tambaye ki? Tunda kuke da ita ta tab'a baki labarin rayuwarta? Ko asalin tushen yaranta? A'a ko kuwa ta tab'a nuna miki dangin uban su da ta cika gari da k'aryar cewa ya mutu, ko kuwa ta fad'a miki yadda ta sami yaran? Toh kinga ashe har yanzun nan da kuke Shirin k'ulla zumuncin auratayya bata gama yarda dake ba, tunda gashi har zata iya b'oye miki sirrikan ta bayan ke kin yarda da ita babu sirrin ki da bata sani ba......". Tafeeda ko data gama maganar ta bata tsaya jin dogon sharhi ba ta d'auki jakarta, don tasan yadda ta mulmulo wannan uwar magana lallai zasu iya fad'a da sameera kafun ta tafi, ita kuma ba abinda ya kawo ta ba kenan.
Har ta yiwa sameera sallama ta tafi bata motsa daga yanda take ba, abubuwa da yawa ne suka fara mata yawo aka, amma cikin k'arfin hali bata yadda shaidan ya rinjayi tunanin taba a lokacin ta yakice komai ta zubar taci gaba da harkokinta.
Surayyah kam koda ta futa direct gida tayi, a parlon k'asa ta samu haleema da bak'i, suka gaisa ta haura stairs. Ayman da bai jima da dawowa office ba yana zaune da remote a hannu yana ta sauya channel kamar wanda aka sa dole, fuskarta washe da fara'a ta zauna opposite d'inshi tace, "engineer! Ya jikin naka fatan akwai sauk'i ko?". Girgiza mata kanshi yayi yace, "babu wani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login