Showing 207001 words to 210000 words out of 288773 words
Chapter 70 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
a d'aya daga orthopedic hospital da suke dashi zan baka details d'inshi idan komai ya kammala".
Sake Gyad'a mata kai khaleefa yayi bayan gama sauraron duk jawabanta.
Itama daga haka bata sake cewa komai ba ta futa a office d'in.
Saleema kuwa koda ta futa a harabar asibitin ta zauna taci kukanta ta godewa Allah, ta dad'e tana sakawa da kwancewa kafun a k'arshe ta samu mafuta d'aya, no Amna ta lalubo cikin wayarta don tasan a hannunta kad'ai zata samu abinda take so tunda itace ta kawo mata wancen labarin da bata san dashi ba. (Wato ranar dole sai dole)
Bugu uku Amna ta d'aga, shiru duk sukayi kafun Saleema ta nisa tace, "ki turon da address d'in gidan khaleefa".
Shiru Amna tayi a nata b'angaren tana tunanin abinda zaije yazo idan taje gidan, ganin ba zata iya aiwatar da komai ita kad'ai ba sai tace mata tana zuwa bari ta duba taga. Tana katse kiran direct layin Ahmad ta kira duk da tasan yana office kuma bai cika d'aga waya ba a lokacin aikin shi. Tana shirin katsewa ya d'aga ya ce, "fad'i maganarki idan bata huce minti biyu ba Cox Ina tsakiyar aiki".
"A'a ba doguwar magana bace Saleema ce ta buk'aci address d'in khaleefa kana ganin na bata".
Da sauri Ahmad yace, "a'a maman shi tana gari batasan komai ba, kice mata zaki turo mata gobe ni kuma in na futa office zan kira ki sai muyi magana". Yana gama fad'a ya tsinke wayar.
Haka kuwa akayi Amna ta fad'awa Saleema duk yadda sukayi da Ahmad. Ba don ta gamsu ba ta hak'ura zuwa goben sai don ba yadda zatayi.
***Da yamma lik'is ta shigo gidan yauma tana tafe a matuk'ar gajiye, ta samu auntie a parlon suna ta hirar su da yasmine da take mugun yinta, don tace matar tayi a rayuwa ga ado ga k'amshi da girki kamar Raihana. Suna ganinta duk suka fara mata maraba, ta zauna kusa da auntie tana mata barka da gida.
Auntien sai tarairayar ta take yi kamar ta maida ta ciki, sai kace ita ta haifa ba mijin taba, kafun wani lokaci ta cika ta da tea da abincin data dafa da drinks masu sanyi.
Cikin jin dad'i taci abincin suka ci gaba da hirar da sukeyi har ita data zo yanzu na taya su. Labarin k'asar Sudan da al'adun su take basu suna ta mamaki da al'ajabi.
Bata bar gidan ba saida su Ahmad suka dawo suka huce tare bayan auntie ta wanko mata plask d'in abincin data kawo mata da safe, ta had'a da bata kyautar turarukan data had'o mata. Aikuwa taita godiya har Ahmad na tayata sai kace shi aka bawa turaren 😂.
Khaleefa da yake zaune a parlon kam sharewa yayi kamar baisan badalin da ake ba, a tare dashi ga gajiya ga yunwa ga tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya. Sama sama sukayi sallama da Ahmad ya tafi shi kuma ya tashi tsam ya shige d'akin shi.
Daga auntie har raihana suka bishi da kallo, kafun auntien ta dubi raihana tace, "Raihana lallen k'afar ki da hannun ki ya futa ga makarantar nan ta sako ki a gaba".
Murmushi mai kama da yak'e raihanan tayi har zatayi shiru sai kuma dai tace, "Ni bana tunanin ci gaba da yin lallen nan saboda khaleefa baya so".
"Na sani tun yana yaro baya son lalle, kuma ba lalle kad'ai ba abubuwa da yawa ma baya son su amma a hankali ya sauko, shima lallen da sannu zai sauko ya mik'a wuya saboda haka cikin kwanakin nan kiyi k'ok'arin maida shi". Gyad'a mata kai tayi cikin karb'ar umarnin auntien.
"Yanzu ki kai masa tea da kisr d'innan, ki had'a mishi ruwan wanka masu kyau". Da toh ta amsa cikin karb'ar umarnin auntien ta mik'e zata nufi kitchen. Har ta d'au hanya auntie ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, "Raihana". Ta amsa da, "Na'am" tare da waiwayowa, "ki rage jin kunyata don nima maman kice".
Murmushi tayi tare da gyad'a kanta.
Yana zaune a gefen bed ya had'a kanshi da gwiwa a lokacin data nemi izinin shiga d'akin, bai iya bud'e bakin shiba sai tashi da yayi da kanshi ya bud'e mata k'ofar, ganinta da tray saiya bata hanya ta shiga ya maida k'ofar ya rufe.
A k'aramin table ta ajiye komai ta nufi hanyar bathroom d'inshi. Ta had'a mishi ruwan mai d'an zafi duk da batasan da irin wanda yake wanka ba.
Ta futo ta same shi yana zaune gefen gadon ya sake had'a kanshi da gwiwar.
A gefe d'aya ta tsaya tayi shiru tana tunanin abinda ya dame shi cikin kwana kin gaba d'aya har yasa baya iya gane kanshi.
Kamar me tsoron wani abu tace, ruwan wankan ka zai iya hucewa fa. Kamar mai ciwon k'afa haka ya mik'e ya nufi cikin bathroom d'in. Ta sauke ajiyar zuciya ta kalli sashen data ajiye tray d'in nan, tasan yana matuk'ar jin yunwa kuma muddin bai samu tabbaci daga wanda tayi girkin ba tsakanin ita da auntie bazai ciba, k'aramar paper ta samu da biro ta mishi gajeren sak'o kamar haka (kisr! girkin da auntie tayi da hannunta don farin cikin ka) ta ajiye takardar inda zai gani ta fuce a d'akin.
Khaleefa ya jima yana wanka kafun ya futo, duk da ruwan data had'a yaso mishi zafi da yawa amma saida yaji dad'i data nuna kulawa a gare shi, baisha wahala wajen ganin takardar ba, hakan yasa yana shiryawa ya d'auki abincin yayi saving kanshi ya fara ci.
Yaji dad'in abincin sosai shiyasa yaci da yawa, tabbas ya tabbata girkin auntien shi don yasan wasu kayan amfanin da za'a had'a kisr d'in tazo dashi ne daga Nigeria.
***Da dare raihana ta shirya cikin kayan bacci pitch colour doguwar riga mai sakakken jiki da k'aramin hannu, bayan ta shafe jikinta da turaruka masu k'amshi ta d'ora hijab a saman kayan ta yiwa auntie sallama ta tafi sabon d'akin baccinta.
Yau a kwance ta same shi rungume da pillow ya lula duniyar tunani, bata ce mishi komai ba ta zauna daga k'arshen gadon kamar yadda ta kanyi kafun ta kwanta bacci, kwana biyun nan da batayi magana da y'an gidan su ba duk sai take jin kewarsu na damunta, gashi wayarta tasan ta tashi a aiki, shi kuma baya cikin nutsuwar da zata rok'i ya bata aron wayarshi.
Tun tana jingine da fuskar bed har bacci yaci k'arfin idonta ta kwanta sosai ta lula duniyar bacci.
***Washe gari raihana ta tashi da mugun ciwon kan nan da take yi cikin kwanakin da suka gabata, a haka dai ta daure tayi duk ayyukan gidan ba tare da nuna gazawa ba.
Akayi sa'a yau har khaleefa sukayi breakfast kafun ya futa, sau biyu kenan daya tab'a cin girkinta tunda suke tare dashi a gidan.
Kusan tare suka futa yau shiya huce asibitin su ita kuma tayi makaranta.
*****Amna kamar yadda tayi alk'awari haka ta tura mata address d'in, sai dai na makarantar su raihana ta bata da hoton raihanan kamar yadda suka shawarta da Ahmad. Bata gane kan komai ba hakan yasa ta tambayi ba'asi, nan Amna ta k'arasa yi mata gundarin bayani har dai dai lokacin da raihana zata futo lecture yau.
Duk da Saleema ba haka taso ba haka dai ta hak'ura, don taso ace address d'in gidan ne yadda zata iya zuwa kowanne lokaci, toh amma hakan ma ba laifi tunda ai a gidan ma gurinta zata je.
Tun saura mintuna 20 su futo lecture Saleema take tsayuwar jira a kusa da k'ofar futa makarantar har suka futo, tafe take ita da wata yarinya y'ar asalin k'asar India suna hira akan darasin su na yau, sanye take da lafaya data zauna a jikinta kamar an zanata, tayi matuk'ar kyau. Har Saleema saida taso razana data mata kallon farko kafun ta matso kusa. Sai dai koda tazo kusa taci gaba da kallonta sai taga ba wata shahararriyar kyakkyawa bace har ta fara tunanin abinda khaleefa zaiyi da wannan yarinyar gata ba fara ba duk da ba zata shiga cikin bakake ba, gata ba za'a ce mata siririya ba bayan shi siririyar mace yake so kamarta, ta tashi ta lafto irin wannan kaya kamar a k'auyen Nigeria 😜. Duk wani abu da khaleefa yake so a tare da mace raihana bata dako d'aya amma wai a haka ya aureta?.
Ita kuwa ba tare da tasan da wanzuwarta a gurin ba tayi sallama da yarinyar ajin sun tazo zata gifta ta kusa da ita, aikuwa Saleema ta wani fuzgo ta baya tana mata makaskancin kallo tun daga sama har k'asa.
Da mamakin wannan fuska da inda ta santa ya kwanta mata tace, "wacece ke?".
"Matar da mijin ki khaleefa zai aura". Saleema ta bata amsa kai tsaye.
Hard'e hannu raihana tayi a k'irji tana kallon ikon Allah.
Yanayin yadda take kallonta kad'ai ya sakawa Saleema shakkun tunkararta don idanunta babu alamun tsoro ko dar ga wani kwarjini da tayi mata.
"Iya abinda kika tsayar dani ki fad'a mun kenan?". Raihana ta mata tambayar tana jifanta da wani kallon banzan.
Yamutsa fuska tayi ta sake tattaro kwarin gwiwarta tace, "aini raina ajin ki nayi kuma nazo ne in tabbatar miki dama ki tattara kayan ki tass! ki fuce daga gidan khaleefa kafun zuwana".
Sai a lokacin raihana tayi wani miskilin murmushi tace, "kin gama?". Ta fad'a tana k'ok'arin kewayeta ta huce, tsabar mamakinta da takaici don saleema rasa yadda zata yi da ita, duk wani rashin mutumci da buhu buhun wulak'anci data tattaro zata yiwa raihana kwarjinin ta ya tokare ta ta ko'ina, Sam abinda ta fad'a bashi ta shirya fad'a ba kawai diriricewar da tayi ne yasa maganganun suka futa yadda bakin ta ya furta ba yadda ta tsara ba.
Ganin raihana ta d'auki hanya zata bar mata gurin sai tabi bayanta da hanzari ta dafa kafad'arta ta baya da k'ok'arin fuzgo ta kamar yadda tayi mata d'azu.
Da wani irin sauri raihana ta janye hannun Saleema a jikinta tare da tsinka mata tagwayen maruka hagu da damanta, ta fara murza yatsunta uku a gaban fuskarta tace, "ya zamo second and last da k'azamin hannunki zai k'ara gangancin tab'a jikina, matsalar ki da khaleefa ne bada raihana ba.... Soo ta tsaya tsakanin ku can". Ta k'arasa fad'a cikin jaddada kashedinta kafun ta juya ta bar mata gurin.
Saleema durk'ushewa tayi a gurin don tsabar shigar da marin ya mata k'afarta rawa take tama kasa tsayawa, wacece wannan yarinyar? Y'ar uban wace da har zata d'aga hannu ta zabga mata mari a public irin haka? Lallai kuwa saita sakata nadama a irin wannan gurin tayi alk'awari.
Raihana tafiya take amma cikin tsananin b'acin rai da takaicin abinda Saleema ta mata, tunda take a rayuwarta in aka d'auke abu na k'uruciya bata tab'a rigima da wasu har ta kaiga anci kwalarta haka ba sai yau ata sanadiyyar mutumin da bata da wata alak'a kyakkyawa ta kusa kota nesa dashi ba.
A inda ta saba hawa motar haya a duk lokacin da tazo makaranta zata koma gida ta tsaya, ajiyar zuciya ta dinga saukewa akai akai har tana mamakin kanta da k'arfin halin da tayi..... Sai a lokacin ta tuna inda tasan fuskar yarinyar, lallai hoton ta ta gani a fuskar wayar khaleefa, sannan bata raba d'ayan biyu itace yarinyar da yake matuk'ar Soo Saleema.
"Ya Allah" ta fad'a tare da dafe kanta da hannunta.
Ranar har ta dawo gida yanayinta a dame yake, duk da k'ok'arin data dinga yi wajen ganin ta saisaita kanta.
Koda auntie taga sauyin yanayi kad'an a tare da ita bata tambayeta ba'asin komai ba saboda yau da gobe sai Allah, watarana mutum haka nan zai tashi yaji baya jin dad'in jikin shi.
****Amna ce kare da waya a harabar gaban d'akunan su bayan ta gama bawa Ahmad labarin komai daya faru a makarantar su raihana yau, bayan ta gama bashi labarin ta d'ora da cewa, "naji tsoro fa sosai wallahi don yadda naga yarinyar so silent na d'auka Saleema zata iya ci mata mutumci kan abinda bata jiba bata gani ba, sai gashi ta bakin yarinyar ta nuna mata zarrah".
Daga d'aya b'angaren da mamaki sosai Ahmad yace, "Ni kuma marin da kika ce tayi ne yafi bani mamaki, in hakane raihana tayi fiye da abinda nake tsammani, nifa abinda yasa na yarda a bata address d'in raihana saboda nasan ba zata tab'a kula taba har tayi duk haukar ta tafi, kuma koba komai an d'auke mata hankali har zuwa lokacin da auntie zata bar Germany ba zatasan komai ba,,, amma dama Saleema ai tayi kuskure data fara d'ora hannunta jikin matar mutane,,,,, raihana tana da nutsuwa k'arshe fiye da yanda duk zanyi miki bayani sai dai dama da ganinta kinsan ba zata d'auki raini ba, sai dai amma fa marin nan zai b'allo ruwa mai fad'i.....".
"Abinda nake son fad'a maka kenan yanzu, Saleema taci alwashin rama ninkin abinda tayi mata har ta fara had'a gang na wasu cikin k'awayenta za'a had'u aje makarantar su raihana cikin weekend idan ta shiga discussion aci mata mutumci".
Shiru Ahmad yayi kafun can ya nisa yace, "ki kyale su ke dai kici gaba da bibiyar su har ki samu tabbacin ranar da suka shirya aiwatar da komai ki fad'a mun, Ni kuma nayi alk'awarin zaki ga yadda wasan zai juya kanta har yanzu bata san waye khaleefa ba shiyasa take wasa dashi.......".
Amna tace, "toh Allah yasa a wannan karon ta gane gaskiya tabi". Ahmad yace, "ameen kam, zan shiga gida saina jiki".
Amna tace, "alright a gaishe da madame". Yace, "zata ji" daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye waya.
Ranar khaleefa bai samu shigowa gidan ba sai dare, a lokacin daga raihana har auntie suna parlon, duk da babu wanda yayi maganar jimawar shi cikin su a zahiri amma a zuciya duk abu d'aya suke tunani.
A nutse ya murza key ya shigo, a kan raihana idanun shi suka fara sauka, tana zaune amma ta had'a kanta da gwiwar k'afarta idonta na kallon k'asa, sallamar shice ta sata d'ago kanta tare da gyara yafen jikinta.
A gefe d'aya ya tsaya ya amsa sannu da zuwan da tayi mishi. Auntie kam tambayarshi ta fara, "lafiya kuwa yau ka jima baka dawo ba?".
Lumshe idanun shi yayi ya dafa kanshi yana jin yadda yake tsananin sara mishi kafun ya bud'e idon yace, "da wuri na tashi akwai inda na biya ne?". Ya k'arasa fad'a idon shi akan raihana data k'araso gaban shi ta mik'a hannu zata karb'i jakar system d'inshi, bata jakar yayi ya bita da kallo har ta shige d'akin baccin shi sannan ya sauke b'oyayyen ajiyar zuciya.
Auntie data gama kallon shi a sace tray na kayan shayi ta tura mishi gaban shi, ya kalli shayin ya girgiza kanshi ba tare daya zauna ba yace, "ban jin shan tea d'in nan yanzu".
"Kuma shine dai dai dakai yadda ka dawo a gajiyen nan". Auntie ta fad'a tana kallon shi.
"Okay toh bari na futo" ya fad'a tare da yin gaba, duk da yunwar da yake ji amma baya jin cin komai, yaji ma da tension d'in nan daya dame shi.
Yana k'ok'arin shiga tana k'ok'arin futowa, sai kuwa karaf sukayi karo kanta ya daki k'irjin shi, da sauri duk sukayi baya kowa na k'ok'arin ba d'an uwan shi damar kaucewa. Ganin ta koma ciki sai ya k'arasa shiga ya maida k'ofar ya rufe ya tsare ta da ido yana kallonta.
Ita kuwa abinda ta aikata ga masoyiyar shi d'azu ne ya shiga dawo mata, a ranta ta fara ayyana watak'ila ya samu labari shiyasa yake jifanta da kallon tuhuma da kashe di🙆♀️
A hankali ya fara nufarta tana ja baya har ta kai k'arshen bangon d'akin ta jingina tare da rintse idanunta tana jiran saukar mari irin ko ninkin wanda ta yiwa budurwar shi d'azu.
_tab raihana ta kwakwaso da yawa🤭_
_kuyi hak'uri ban samu damar shigo muku weekend ba kamar yadda na fad'a, k'arshen makon ne ya same ni da abubuwa da yawa_
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page fifty nine 5️⃣9️⃣
Yatsun hannun shi ya murza saitin fuskarta, ta bud'e idon da kyar a d'arare tana kallon shi, shi abun ma dariya ya bashi hakan yasa yayi murmushin gefen baki ya juya kurum ya shige bathroom.
Ajiyar zuciya ta sauke tabi bayan shi da kallo har ya shige, da gaske ta tsorata da yanayin shi ta d'auka dukanta zaiyi.
Kasa futa tayi