Showing 138001 words to 141000 words out of 288773 words
Chapter 47 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
ta koma da baya ta d'auki d'ayan cup d'in, khaleefa kam koda ta mik'a mishi saida ya d'auki some seconds kafun ya amsa ba tare daya kalleta ba, sai dai adanun shi da suka sauka akan yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle.
Auntie duk tana lura dasu. Abincin Kam bata yiwa kowa tayin karb'a ba ta ajiye mishi a gefen shi ta koma mazauninta.
Khaleefa sam bai tab'a komai ba saida yaga Ayman ya fara shan shayin da aka bashi, sannan shima yasha nashi, abincin kam bai iya ciba duk da Yana kallon yadda Ayman yake tuttura nashi, gashi yana matuk'ar jin yunwar sai dai dole sai yayi brush sannan zaici wani abu ya zauna cikin shi lafiyar Allah, tashin zuciya bai biyo baya ba.
Sunci gaba da zama shiru kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi, kafun sallamar su sameera ta katse musu zaren tunanin su. Banda khaleefa da yake aikin latsa wayarshi amma kowa a d'akin saida ya d'aga ido ya kalleta a lokacin da take shigowa ita da Nur data zuba ma raihana ido tana kallonta da tunanin abinda ya kawota nan, koda yake ashe fa k'awar Ayman ce,,, ta tuna hakan a ranta, take b'acin rai yayi karan tsaye akan fuskarta. Saita sake d'aure fuskarta tam.
Surayyah ba yabo ba fallasa ta tarye su hadda basu gurin zama, suka zauna Nur tana gaishe da auntie, sameera ma gaisawa sukayi tana tambayarta, "ya me jikin? Tun jiya fa naso zuwa Allah bai nufa ba kinga sai yau".
Surayyah tace, "ayyah ai komai sai Allah ya nufa, jiki da sauk'i kam".
"Toh Allah ya k'ara sauk'i yasa kaffara". Tace, "ameen". Kusan a tare Ayman da khaleefa suka gaisheta, ta amsa tana sake tambayar shi jikin shi, yace, "da sauk'i Alhamdulillah!".
"Allah yasa kaffara" ta sake fad'a ya amsa mata da ameen.
Sai a lokacin raihana ta gaisheta, ta amsa tana zolayarta da amarya tasha k'amshi, ita dai raihana bata ce da ita komai ba sai murmushi data wanzar a saman fuskarta. .
Nur kuma ta sake binta da kallon mamaki, amarya kuma? Ba Imran zata aura ba aka fasa toh yanzu kuma me takeyi tare da auntie? Sannan amaryarwa ake nufi? Yaushe ma tayi aure basu da labari? Sannan ga Ayman har da kwanciya a gadon asibiti? Duk bata da labari, ita dai tana fatan ba Ayman ta aura ba ake b'oye mata, Kai dole wani abu yana faruwa ta wani gefen.
Saita gyara zamanta ta kalli saitin da Ayman yake zaune tace, "sannu Yaya Ayman ya jikin naka?". bai d'aga ido ya kalleta ba yace, "da sauk'i" ta sake cewa "Allah ya k'ara sauk'i".
Bai amsa mata ba sai plate d'in abincin shi daya ajiye gefe don abincin ya k'ara fucewa daga ranshi.
Sun d'anyi jim kafun Auntie ta dubi khaleefa da duk ya takura a gurin tace, "ko zaku fara yin gaba kaida raihana kada y'an uwanta su dawo basu sameta ba, sannan Ahmad ma kace ba sai ya dawo ba tunda muma ba jimawa zamu taho gidan gaba d'aya".
"An sallame ku kenan?" Sameera ta tambayeta.
"Umm!" Kawai surayyah tace.
Khaleefa saida yayi kamar kar ya tafi sai kuma dai ya mik'e ya lalubi mukullin motarshi, ganin raihana bata da niyyar tashi sai auntie tace da ita, "maza ki tashi ku tafi tare, nasan abinda ya hana shi cin abinci anan, dama da kunje ku huce side d'inku ki had'a mishi ruwan wanka me zafi, ki sama mishi wani abun da zaisa a cikin shi me sauk'in sarrafawa....".
Cike da jin kunya raihana ta gyad'a mata kai ta mik'e a lokacin kanshi yana kusa da Ayman yana yi mishi magana k'asa k'asa da babu wanda yaji kaf cikin d'akin har ni duk bin kwakkwafina.
Saida ta yiwa su mammie sallama sannan ta futa ta jira shi a wajen d'akin.
Wasu maza biyu har sun gota ta sai suka dawo da baya, d'ayan yace, "wooww! Kaga wata had'ad'd'iyar beb a nan?".
D'auke kanta tayi da sauri, a lokacin matasan suka k'araso suna yi mata magana, banza ta musu tana neman tsari daga shaidan abin k'i. Sun tsaya sai zuba mata zance suke yayinda tayi banza dasu kamar bada ita suke ba, ita tsoron ma bud'e bakinta take bare tace musu wani abu taje ta aikata haramci.
A haka khaleefa ya futo kare da waya a kunnen shi, kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi ya fara nufar hanyar futa daga Ward d'in, da sauri sauri tabi bayan shi har kamar zata ci tuntub'e ta fad'i, basu fasa bunta suna maganar suba har suka isa inda khaleefa yayi parking motar shi, "ba dai tafiya zakiyi ki barmu ba y'an mata, haba ai ko phone numberki kya tsaya ki bamu mana please...". Yadda yasha gabanta yana maganar saura k'iris taci tuntub'e ta fad'a kanshi ga k'afarta data hard'e, tayi saurin ja baya tare da satar kallon inda khaleefa yake tsaye, akayi sa'a idonshi a kansu yanzun ma don bai shiga motar ba yana jingine jikinta hannun shi a samanta yana ci gaba da wayarshi duk da fuskarshi ta nuna alamun damuwa, watak'ila ba magana mai dad'i ake fad'a mishi a wayar ba.
Kewaye shi tayi da sauri ta isa inda khaleefa yake waiko zai zamo mata garkuwa su rabu da ita in suka gane tare take dashi.
Isowarta yayi dai dai da gama wayarshi, hakan yasa ya bud'e front seat ya zauna, kamar ta bud'e gidan baya sai taga kada yaga ta raina mishi hankali, madadin haka saita bud'e front seat gefen shi ta zauna. Mutanen nan suna tsaye don maseefa suna kallonta har yanzu sunk'i matsawa, khaleefa har zai tashi motar sai ya k'ara ankara dasu, kamar sune ai suke bin ta tun daga ciki. Saiya fasa tashin motar yace,
"Wad'annan ba zaki saurare su kiji da wadda suka zo ba?". Ya tambayeta ba tare daya kalleta ba.
Wani irin rass! Raihana taji har batasan lokacin data d'aga ido ta kalleshi ba, wane irin mutum ne wannan? Da aurenta yake nufin ta dinga kula kowanne kare da doki?
Ya ankara da irin kallon da takeyi mishi ta gefe, wanda suka alamta mishi na rashin fahimta ne, sai ya tattaro duka nutsuwarshi ya tsaida idanun shi a kanta a karo na biyu a tarihi daya kalleta face to face irin haka yace, "kada ki manta sharad'in auren mu har ki nemi takura kanki da tunanin igiyar aure na da bata da maraba da rehu a kanki,,,, munyi yarjejeniya duk lokacin da kika samu wani namiji daya kwanta miki a rai har kika ji zuciyarki ta aminta kan cewa zaki iya auren shi, toh zaki bashi duk wata dama don ku fahimci juna... Don haka kada ki cuci kanki, idan har sunyi miki ki basu dama don wulak'anci bashi da kyau, idan kuma basuyi miki ba ki basu hak'uri sai Allah ya had'a kowa da rabon shi.....".
Shiru raihana tayi tana jujjuya maganganun khaleefa da sukayi mata nauyi a kwanyar kanta kamar zasu rinjayi gangar jikinta, sannan shi yana yin wannan maganar ne da iya gaskiyar shi, tabbas sunyi yarjejeniya kamar yadda ya fad'a amma ita ba zata iya aikata irin abinda yake nufi da igiyar auren shi a kanta ba, ta yadda dai duk ranar da suka rabu ta samu wanda nutsuwarshi da hankalin su yazo d'aya ta saurara amma fa bada igiyar auren shiba, don ba zata fara gangancin kai kanta wuta da k'afafun taba, gaba d'aya aure ba abun wasa bane bare ita ta fara yin wasa dashi irin haka.
Ganin bata bashi amsa ba sai ya tab'e baki ya fara k'ok'arin tada motar a nutse, yana ganin shikam ya futa har ga Allah.
Har suka d'auki hanya bata ce dashi komai ba saida suka Isa gida, a lokacin an bud'ewa Ahmad get zai futa da mota su kuma suka k'araso.
Yana yin parking ta futa, shi kuma Ahmad ya k'araso yana zolayarta, "amaryah gaskiya dole muci tarar Ayman daya futar dake a washe garin ranar da aka kaiki gidan mijin ki.... Kai kuma fa laifin nashi ma shi ai da yawa, sai dai babban ciki shine rik'e miki ango da yayi ya kwana gurin shi hospital a ranar da aka kai ki gidan shi....". Murmushin yak'e tayi ta russuna ta gaishe dashi, ya amsa yana shirin sake cewa wani abu ta d'auki hanyarta da sauri don sam bata jin zata iya tsayawa magana dashi a yanayin da take ciki, tana hucewa Ahmad ya maida akalar zolayarshi kan khaleefa, "fuskar ka kad'ai dana kalla ta tabbatar mun lallai Ayman ya samu".
Khaleefa yace, "alhamdulillah kam anjima kad'an zasu taho Ina ganin ma basai ka koma ba".
"Anya kuwa zasu barshi a yau?".
"Zasu barshi ai ya warware". Khaleefa ya fad'a mishi.
Tare suka jera zuwa saman b'angaren su gaba d'aya, Ahmad yana ta zolayarshi irin yadda ya zolayi raihana, shidai bai kula shiba don ba abinda yake gaban shiba kenan.
Raihana kuwa kamar yadda auntie ta mata umarni haka tayi, kai tsaye part d'in su ta shiga, tana bin komai na d'akin da kallo, sai yanzu take gasgata maganar su Fatima da suke ta kod'a gidanta da yaba kyawun shi.
D'akin da aka ajiyeta jiya ta shiga ta shiga bathroom, bata jima ba ta futo ta fara duba ragowar d'akunan, d'aki na kusa da nata ta shiga, gidan fes fes ba datti ko d'aya, saboda jiya saida suka gyara ko'ina kafun su tafi, ruwan wanka masu matsakaicin d'umi ta had'a mishi ta fuce daga ciki zuwa wanda ta fara zama ta nemi gefen bed tayi kwanciyarta, ba jimawa wani bacci mai mugun dad'i ya fusge ta yayi awon gaba da ita......
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page thirty nine3️⃣9️⃣
Shima khaleefa ta b'angaren shi bai kula Ahmad da zancen shiba ya shige bedroom d'inshi ya watsa ruwa a daddafe ya futo, ko kanshi da yake matuk'ar sara mishi bai bi ta kai ba ya samu gefen gadon shi ya kwanta sai bacci, ko abincin bai ciba, baya ji da ganin komai a wannan lokacin sai bacci.
A asibiti kuwa raihana da khaleefa suna futa sameera ta fuskanci surayyah da kyau ta fara magana da duka nutsuwarta ta fuskar neman salama da lumana da k'awartata a yau, "duk da laifina mai girma ne a gare ki surayyah, nasani sam banyi miki adalci ba kamar yadda na kasa fahimtar ki, na munana miki zato akan abinda ko a mafarkina na gani zan k'aryata na tashi da gudu na wanke fuskata nace k'arya ne.... sai gashi abun kunya nice da kaina na fara bada k'ofar da wasu ma zasu mara mun baya, duk nadama da kunya sun rufe ni musamman da naga ruqayyah ta aikata abinda ni ya kamata ace na aikata shi tun farko, ruqayyah ta d'auki y'arta mai tarbiyyah da nutsuwa had'e da nagarta kwatankwacin ta yaranki ta bawa khaleefa aure, kuma ba tare da sun kallesu ta wata fuska daban ba, tabbas wannan abu yana daga abinda ya sake hanani sukuni har naji bazan iya k'asa a gwiwa ba sai nazo na nemi yafiyarki, don Allah surayyah kiyi hak'uri komai ya huce muci gaba da mu'amular mu kamar yadda muke da farko....".
Tunda ta fara magana surayyah take sauraronta har ta dire, sai a lokacin ta saki wani miskilin murmushi ta kalleta tace, "Toh ni me kika yi mun ma sameera? Kin fad'i iya gaskiyar kine fa, kuma ni ko a lokacin sam banga laifin kiba Kuma banji haushin kiba shiyasa ban tab'a rik'e ki da komai ba...".
Shiru ta sakeyi jikinta a sanyaye kafun ta sake cewa, "haka dai kika fad'a surayyah amma a aikace ai kin nuna haka, in badon haka ba nasan ba yadda za'ayi a tsaida maganar auren khaleefa da raihana baki fad'a mun ba, sannan muna business dake shekara da shekaru bamu tab'a maganar zamu raba hanya ba ko a wasa, sai da abun nan ya farun kika ce a raba hanya kowa ya zamana yana juya kud'in kanshi da kanshi,,,, kuma kice duk baki rik'e ni da komai ba".
Wani murmushin ta sakeyi tace, "sameera kenan! Ai gani nayi lokaci yayi daya kamata kema ki rik'e jarin kanki, auren khaleefa kuma yazo ne duka a hargitse shiyasa ba wanda na fad'awa engage d'in sai goron biki dana bayar".
Nur dai tana sauraron komai tana ba tambayoyin bakinta amsa.
Sameera tayi kamar tayi shiru, sai dai ba zata iya ba, shirunta yana nufin komai ciki hadda rashin Ayman da Nur zatayi.
"Toh yanzu ya maganar auren su Ayman d'in? Nina hak'ura zan bawa Ayman Nur ko daga iya ni sai kene....".
Wannan karon wani irin kallo surayyah tayi mata carmly tace, "lallai sameera har yanzu baki gama sanin wacece surayyah ba, bana zance d'aya, kamar yadda bana yaudara a rayuwata, idan na baki tarihina kikaji abunda ya raba ni da Suraj harma nak'i neman dangin shi da nawa nake rayuwata kamar wata marar galihu sai kinyi mamaki kwarai, mamaki irin wanda watak'ila har ki gama rayuwarki ba zaki daina shiba, don haka ki ajiye maganar Nur da Ayman a gefe, a gurina ta dad'e da zama tarihi bansan ba ko shi a gurin shi tunda gashi nan yana jin mu aiba yaro bane....".
Yadda sameera take kallonta da mamaki haka nuriyya ma ta zuba mata ido gabanta yana tsananta bugu.
Ta kalli auntie ta kalli Ayman da kanshi yake k'asa kamar abinda ake tattaunawa bai shafe shiba. "Ya rabb me yake shirin faruwa dani ne? Auntie don Allah kada ki yanke hukunci cikin fushi irin wannan, wallahi nida Ayman muna son junan mu.... Ayman ka fad'a musu kar su raba mu don Allah".
Nur tayi wannan maganar cikin tashin hankali tana rarraba idanunta tsakanin su mamie da Ayman.
Babu wanda ya kulata cikin su har Ayman, hakan yasa ta sake gigicewa da shiga rud'ani, saita mik'e tsam ta isa gadon da Ayman yake zaune ta dafa k'arfen ta kira sunan shi. Da kyar ya iya amsawa ba tare daya d'ago ya kalleta ba.
"Ka fad'a musu kana sona kaima don Allah kar ka bari su rabamu". Tayi maganar cikin rawar murya kamar zata fashe da kuka zuciyarta na up and down.
Har yanzu kanshi yana k'asa, baya tunanin akwai wani abinda ya rage dazai iya furta mata a halin yanzun, koda yana sonta bazai tab'a iya aurenta ba, saboda yana da matuk'ar zuciya, bece zai rik'e mamie a ranshi ba amma zaiyi wahala ya manta da maganganun data fad'a mishi, ta kasance mutum ta farko data tab'a goranta mishi rashin uba tun bayan wanda akayi mishi lokacin yana yaro, sannan itace ta fahimtar dashi abinda sanin shi sam bai mishi amfani a rayuwa ba, hasalima sai maseefa da yake k'ok'arin zame mishi, in badon ya danni zuciyarshi k'arshe ba da bazai tab'a iya ci gaba da gaisawa da d'an uwanshi khaleefa ba, bare har yayi mishi cikakken kallon arzik'i, yaci gaba da kallonshi matsayin d'an uwa, raihana!!!! Khaleefa ya zamo silar rabuwarshi da raihana a lokacin da yake gab da cimma burin samunta matsayin matar auren shi. Lokacin da yazo dai dai nan a tunanin shi, zaren tunanin katsewa yayi, sai ya sake runtse ido yana ambaton sunan Allah a cikin zuciyar shi.
"Kiyi hak'uri Nur, tun asali kinsanni farin cikin mahaifiyata shine gaba da kowanne farin ciki nawa,,,, sannan na amince da soyayyar kine dama saboda mahaifiyata....a yanzu kuma data nuna auren mu ba mai yiwuwa bane Ina ganin sai mu hak'ura da juna kurum".
Nur tsabar tashin hankali sam batasan lokacin data d'ora hannunta aka ta rushe da ihu ba, "wayyoh Allah Ayman, don Allah kada ka juya mun baya, wallahi niko daga sama ka fad'o Ina sonka zan zauna dakai....". Ta k'arasa fad'a tana durk'ushewa a gurin.
Daga auntie har mamie ba wanda baiji tausayinta ya dirar mishi a cikin zuciya ba, haka shima Ayman d'in don yasan dama dole za'a cutar da ita, bilhak'k'i take son shi da zuciya guda irin soyayyah marar algus!
Tsam sameera ta mik'e a dai dai lokacin da ummie da Abba suka yi sallama a d'akin. Bata tsaya kallon suba ta kamo hannun Nur ta d'auki Jakarta, saitin inda surayyah ke zaune ta tsaya tace, "shikenan surayyah duk hukuncin da kika yanke dai dai ne a k'arshe Allah ya had'a kowa da rabon shi na alkhairy.....". Saita kalli Ayman shima tace, "Allah ya k'ara lafiya Ayman nagode.....".
Daga nan ko amsoshin bakin su bata tsaya jiba ta d'auki hanyarta ta fuce daga d'akin a zafafe har kamar zata buge su ummie da suke tsaye daga wajen k'ofa.