Showing 21001 words to 24000 words out of 288773 words

Chapter 8 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1044

ta iya".
"Tab lallaima ya Ayman d'in nan toh wallahi ni bansan ma yazo ba kuma yau da safe mun had'u amma koda wasa bai fad'a mun ba".
"Allah sarki bari kiga kayan ma". Sai tayi cikin d'akinta na k'asa ta futo da k'atuwar leda me d'auke da tambarin well care. Tsabar shock sai raihana ta kasa cewa komai sai kallon kayan cike da d'unbin mamaki. A haka yuseep ya sauko zai futa kasuwa cikin shiri, Salma ta nuna mishi kayan da raihana ta kawowa babie, yayi ta godiya yana yaba mata ita da take ta kanta shine hadda wata hidima haka kamar dole, raihana tana dariya tace, "dole ne mana, kyautar y'a guda fa Allah ya bani, kuma ni ban takura kaina ba naga Ina dashi ne inda bani dashi ai ba zanyi ba".
"Gaskiya ne Auntie toh muna godiya Allah ya k'ara rufa asiri". Ita dai batace dashi komai ba har ya fuce.
Hayaniyar hirar suce ta tashi ummaa daga nannauyan baccin data fara ta futo tana wara idonta da fad'in, "a'a wannan kuma daga Ina?".
Daga k'auyen bagwai, raihana ta fad'a tana kallon ummaan, "a'a sai dai k'auyen bichi irin wannan hargitsae hargitsae ba'a dawowa haka in anje bagwai". Dariya raiha da Salma sukayi tana taya su, bayan ta zauna sun gaisa ta dubi raihanatu da kyau sannan ta fara maganar ta, "Anya kuwa raihanatu? Har yanzu ba zaki cire komai a ranki ki saki jikin ki da rayuwa ba, dubi fa yadda kika rame kamar ba ke ba".
Shiru tayi ita dai batare da tace komai ba, a naseehance kakarta ummaa ta sake kwantar mata da hankali ta hanyar misali da mutane daban daban. Ranar yini tayi suna hirarsu ita dasu Salma cike da farin ciki da annashuwa ga y'an uwa da suke ta zuwa barka, hadda wad'an da raihana ta jima bata had'u dasu ba. Da yamma ta shirya zata tafi gida saboda maganar da sukayi da Ayman ta shigeta matuk'a, kuma dama saida ummie ta bata shawarar k'in d'auka tayi tana ganin kamar ba matsala har ta koma ba zata samu wata matsala ba.
Rikici Salma tasa akan lallai sai dai ta zauna mata gobe ta huce makaranta daga gidanta, da kyar tayi mata bayani ta lallab'a ta kamo hanyar tafiya gida. Kusa da magrib ta isa anguwarsu, har zata huce ta gidan iya sai kuma ta dawo. Da sallama ta shiga cikin gidan, malam na zaune kan carpet kusa da k'ofar parlour iya na gefen shi tana dama mishi fura. "a'a raihanatu ce a garin yau?".
"Eh wallahi malam jiya nazo gobe kuma Zan tafi".
Raihana ta fad'a tana zama gefen iya, a nutse ta gaishe da tsofaffin biyu ma'abota nutsuwa da kamala.
Sun tab'a hirar makarantar su a gurguje da zata tafi iya ta cika ta da gyad'a.
Ita kam a kunyace ma ta karb'a saboda yau bata kawo musu komai ba, zuwan ne na bazata.
A k'ofar gidan Abba abubakar taga babban yaron shi Mansoor da ya dawo daga kasuwa as usual yana danne_danne a waya, wuf tayi bata yarda ya ganta ba ta shige gidan su.
Ummie ce kad'ai a gidan tana k'arasa had'a miyar abincin dare.
Kusa da ummien taja kujera ta zauna.
"Sannu da gida ummie".
"Ke za'a yiwa sannu raihana ya masu jegon".
"Masu jego suna can suna zuba tab'arar su son rae kamar basu girma ba". Dariya ummie tayi tace, "hum ba dai Salma bace ai kad'an kika gani, kwanaki gab da zata haihun nan tattaro kayanta tayi wai tazo gida haihuwa da wanka, nace ahir maza ta kama hanya ta koma baza ta zauna ta haihun mun a nan ba, mijinta ya dinga mana sallama safiya dare, raana".
Kyalkyalewa da dariya raihana tayi tace, "toh aikuwa ummie kuna can a blacklist tace a gidan nan kaf babu wanda yaje mata barka".
"Zata gaji ta goge mune don nikam ba inda zanje yanzun su khausar kuma sun tafi ba jimawa na d'auka ma kun had'u dasu".
Raihana tace, "a'a munyi sab'ani, ummie kinji yaa Ayman da k'ok'ari har yaje wa Salma barka jiya da dare, bakiga uban kayan daya kaiwa babie ba".
Cike da mamaki ummie tace, "ooh shikam bawan Allah baya gajiya da hidima, toh Allah ya saka da alkhairy ya k'ara rufa asiri".
Da, "ameen" raihana ta amsa, sunci gaba da hira rabi duk ta Salma da rigimar tane, abinda takeyi ko khausar ba zatayi ba balle raihana. Saida aka kira sallar magrib sannan raihana take fad'awa ummie gobe da sassafe zata koma school, "Allah ya kaimu". Shine abinda ummien ta fad'a ta k'arasa d'auraye k'afarta ta shige parlour.

Sai dare abbansu yaje yaga babie ya taho dasu muhibba, jidderh da al'ameen gida gaba d'aya khausar kuma dole ya barta saboda magiyar da Salma ta dinga yi mishi.
Yau raihana da wuri ta kwanta, shiyasa bata zauna doguwar hira da kowa cikin su ba, dama kayanta a had'e suke yadda tazo.
Har tayi addu'ar bacci ta kwanta sai ta tuna da Ayman lallai da gaske yayi fushi tunda gashi har war haka bai kira taba.
No shi ta dannawa kira sai dai taji shi busy, sai kawai ta rubuta mishi gajeren sak'o kamar haka, "kayi hak'uri Yaya Ayman na fahimci abinda kake nufi tun a lokacin, nasan duk shawarar da zaka kawo gareni mai amfani ce ba wadda zan cutu ba, sannan naga abin alkhairin daka yiwa new born babyn mu Allah ya saka da alkhairy ya ninka dubun su ngd".
Tana sending ta koma tayi kwanciyarta, babu jimawa kuwa bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita.

@@@@@@@


Ayman kuwa suna rabuwa da raihana office ya nufa, ya tarar da aikin daya sha kanshi shi yasa Sam bai samu damar yin komai ba yinin ranar sai aiki.
Da yamma ya taso a gajiye lis zai huce gida, yana son zuwa ya ga nuriyyah amma ya gaji abinda yafi buk'ata a yanzu shine yaje gida yaci abinci ya huta, jinin jikinshi ya koma Normal. Driving yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali har ya k'arasa gida. Babu motsin kowa a gidan nasu yau, jakar system d'inshi kawai ya ajiye ya nufi kitchen ko zai samu abinda zaici.
Babu komai haka yayi ta bud'a warmers yana Jan tsaki, yau ranshi in yayi dubu goma ya b'aci, shida ake bin kanshi da abinci a fai fai yana sharewa shine yau yake neman koda cikin cokali ne amma babu. Bashi da zab'i banda ya had'a abu na k'arshe da sai ta kure yake ci a gidan. Sai dai yana mik'ewa wayar shi na soma ringing, koda ya duba Auntie ce, ba b'ata lokaci ya d'aga sai dai yana kara wayar a kunnen shi muryarta ta katse mishi hanzari, "ka kuwa san an kwantar da Nur a hospital?".
Cikin tashin hankalin daya dito mishi lokaci d'aya yace, "subhanallah yaushe kuma? Ayyah shiyasa d'azu da safe na kira wayarta ban samu ba a kashe".
Asibitin da take aikine shiyasa ko kayan jikinshi bai tsaya sauyawa ba ya zari mukullin motar shi yayi gaba.


_Comment and share_
24/03/23, 2:00 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merheeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page seven 7️⃣


Tafiyar minti k'alilan ce ta d'auke shi ya k'arasa general hospital d'in, no Auntie ya kira ta kwatanta mishi d'akin da suke.
Da sallama ya shiga, a d'arare ya samu guri ya tsaya daga gefen su, A d'akin mamie ce sai Khadija da haidar wanda shima zuwan shi kenan. Auntie kuma na zaune gefen bed d'in da Nur ke bacci tana cin abinci a take away, fara cin abincin nata kenan saboda rashin samun nutsuwa tun d'azu, har k'asa Ayman ya durk'usa ya gaishe da mammie ya tambayeta me jiki, ta amsa mishi da, "jiki alhamdulillah ta samu sauk'i".
Hannu ya mik'awa haidar sukayi musabiha, Khadija ma ta gaishe shi.
"k'arasa kaga jikin nata mana". Haidar ya fad'a ganin yana shirin sake rakub'ewa gefe. Shi kuma nan kunyar Mamie ce duk ta dabaibaye shi, amma da yadda yake ji tuni ya k'arasa har gaban gadon ya ganta.
"Kaga al'amarin ubangiji ko Ayman? Lafiya Lou aka kwanta da ita daren jiya amma da safe ta kasa tashi zazzab'i mai zafi da ciwon k'irji sai d'auko ta akayi aka kawo mun ita nan".
Auntie ce take fad'a ma Ayman haka, "to ai ni kaina munyi waya da ita daren jiya". Inji cewar Ayman
Mamie data ke jinsu ce tace, "dama haka al'amarin ubangiji yake, da mutuwa ce ma tazo hakan ne zai kasance, don ubangiji cikin second yake shafe mutum ya zama tarihi a ban k'asa".
Da sauri Ayman ya rintse ido saboda fad'uwar gaban data ziyar ceshi lokaci guda, duk da maganar data fad'a gaskiya ne idan kwana ya k'are babu tsimi babu dabara sai an tafi amma shi baya fatan Nur ta mutu ta barshi a wannan lokacin, saboda sonta yake fiye da yanda yake son kanshi, ji yake zai iya sadaukar da komai daya mallaka a wannan duniyar muddin Nur zata ci gaba da kasancewa tashi har abada.
Basu bar hospital d'in ba sai dare, kuma har Suka tafi nuriyyah bata farka ba.
A gajiye ya kwanta saman bed hannun shi d'aya dafe da kanshi da yake mugun sara mishi. Ya jima a kwance kafun ya lallab'a yayi wanka, bayan ya shirya cikin kayan bacci farare Sol masu taushi, part d'in Auntie yayi, saida yayi knocking ta bashi izinin shiga sannan ya tura k'ofar ya shiga da sallama.
Tana zaune tana k'arasa had'a mishi kisir abincin k'asar su na Sudan da ake iya yinshi sharp sharp aci don maganin yunwa. Kusa da ita ya k'arasa a sanyaye ya zauna.
Kallon shi tayi kamar zata yi magana sai kuma ta share. Sai data gama had'a abincin ta mik'e ta Isa ga deep fridge da yake kusurwar parlon ta d'auko mishi fruity mai tsaka tsakiyar sanyi ta cika mishi wani glass cup taf ta mik'a mishi, "oya take".
Ba musu ya amsa ya kai baki, saida ya shanye tas sannan ya ajiye kofin, yayi Bismillah ya fara cin kisir d'in a plate guda da ita.
Bai wani ci na kirki ba saboda yanayin da yake ciki na tashin hankalin ciwon Nur ya zare hannu, itama dama ba wani yunwa take ji ba sosai sai kawai ta rufe abincin gefe.
Kwantar da kanshi yayi jikin sopa da Auntie ke zaune hannun shi kan k'afafun ta ya lumshe idanun shi.
Tab'a jikin shi tayi taji ko akwai zazzab'i a tare dashi, jin babu komai sai ta kirawo sunan shi da kulawa, "Abbana". Bai amsa ba sai d'aga kai da yayi yana dubanta, "are you alright?".
Girgiza mata kai yayi, "ko kana da ciwon kaine Cox naji jikin ka babu zazzab'i".
Sake girgiza mata kan yayi, "toh me yake damunka?".
Rausayar da kai yayi ya kasa cewa komai sai idanun shi da suka tara ruwan hawaye.
"Yaa Salam! Ayman tell me what's happening?".
Auntie ta fad'a cikin shiga rud'ani har tana saukowa k'asa.
Zata sake yin magana wayar shi ta d'auki ringing, ya kasa duba wayar ma sai ita ta d'auka don ganin mai kiran, ganin khaleefa ne sai tayi picking, "yaa man lafiya kake kuwa? Yau kwana biyu ko waya bamuyi ba fa". Khaleefa ne me yin wannan maganar, ajiyar zuciya mai tsayi Auntie taja kafun tace, "ba shi bane khaleefa nice".
"Ah! Afwan Auntie tun safe Ina Kiran wayarki bakya d'agawa, yanzun ma tunani na idan muka gama waya da Ayman ya kai miki a muyi maganar s tashi".
"Ayyah yau na shiga uzuri khaleefa ko wayar ma ban duba ba har yanzu, kasan Nur ce ta tashi da zazzab'i da ciwon k'irji zancen da nake yi maka yanzun haka ma tana asibiti an bata gado".
"Subhanallah yau kenan?".
"Kwantar da hankalin ka ban dad'e da baro taba jikin yayi sauk'i sosai, wallahi yau da safe ta tashi da jikin".
Ajiyar zuciya khaleefa ya sauke yace, "toh Allah ya bata lafiya, yanzun Ina Ayman d'in yake?".
Sake duban inda yake tayi, ya had'a kai da gwiwa yayi shiru, "khaleefa Ina ganin kamar akwai abinda yake damun twin bro d'inka, kuma ni baya son naji, gashi kuyi magana tunda kaine watak'ila ya fad'a maka".
Tana gama fad'a ta ajiye mishi wayar saitin kunnan shi. Ajiyar zuciya yake ta sassaukewa a jejjere, shi kuma khaleefa a can sai tambayar shi matsalar yake hankali a tashe.
Da kyar ya iya shanye damuwar da yake ciki yace, "yaa! Bro how far".
"Me yake damun ka ne Ayman ko auntie bata fad'a munba nasan akwai damuwa mai yawa tare da kai".
K'ak'alo murmushi yayi yace, "ba komai yaya khaleefa kawai na tsorata da yanayin yadda naga jikin nuriyyah ne a yau, bazan b'oye maka ba khaleefa wallahi Ina tsoron rasata, idan har ta tafi ta barni bazan tab'a samun wadda nake so kwatankwacin yadda nake sonta ba, please khaleefa watanni nawa suka rage ka gama ka dawo ayi maganar auren mu?".
Auntie murmushi tayi ta sake ja baya daga kusa dashi tana jin wani k'arin farin cikin. Da alama komai yana tafiya fiye da yanda suke fata.
Daga can b'angaren khaleefa kuwa murmushi yayi wanda ya bayyana kyawawan jerarrun hak'oran shi kafun ya tambaye shi, "wannan shine kad'ai matsalar ka Ayman?".
"Eh ya fad'a yana satar kallon Auntie".
Kau da kanta tayi gefe tana sake murmushin da yafi komai nuna asalin kyau da kyawun zuciyarta.
"Toh aikuwa indai wannan ne kad'ai matsalar ka kusan samun abinda kake so Ayman, daga yanzu ka soma lissafi zuwa nan da watanni shida masu zuwa".
Cikin farin ciki Ayman yace, "really?".
"Sure" khaleefa ya fad'a mishi cikin tabbatarwa.
"Toh amma khaleefa kai ta b'angaren ka kana da wata ne?".
"Kamar ya kenan Ayman"
"Ina nufin kamar wata wadda kake so haka".
Murmushi ya sake yi yana tuno Saleema cikin zuciyar shi, "ba yanzu ba akwai sauran lokaci", abinda ya ayyana cikin ranshi kenan shiyasa ya sauya akalar abinda yayi niyyar fad'i ta hanyar cewa, "saurin me kake Ayman? Insha Allah bazan dawo ba saida kyakkyawan labarin da kake son ji".
"Toh shi kenan bro Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Duk suka amsa da Amin. Sunci gaba da tattaunawa su uku har Auntie kafun Ayman ya mik'e cike da kwarin gwiwa yayi mata sallama ya tafi makwanci rai fes.
Har yayi Shirin kwanciya bacci sai ya duba wayarshi ko raihana ta kira, aikuwa sai ga missed call na kiran da tayi suna waya da khaleefa a lokacin da kuma text message d'inta.
Murmushi yayi bayan gama karanta sak'on.


@@@@@@@@


Yauma kamar kullum raihana ta gama duk ayyukan gidan su da wuri har breakfast, da yake Salma ta rik'e khausar sai ya zamana ita kad'ai tayi duk ayyukanta.
K'arfe 6:30 dai dai ta gama shiri cikin doguwar riga ta atamfa, d'inkin ya zauna mata da kyau kuma ya fudda ainahin shape na jikinta gaba d'aya. Medium d'in gyale ta yafa kalar takalmin da zata saka, ta d'auko jakar kayanta da handbag d'inta, tana futowa Abban su yana futowa shima ummien su a bayan shi, har k'asa ta tsugunna ta gaishe su, suka amsa ummie na tambayarta "sai tafiyar kenan?".
"Eh ummie ba wahala Zan samu mota akan in anjima".
Kud'i masu yawa abbanta ya k'ara mata, yayi mata addu'a had'e da sa albarka ta d'auki hanya ta futo. Ummie har hanyar futa ta rakota tanayi mata addu'a, koda wasa bata yarda ta juyo ba, hawayene fal idonta har yanzu ta kasa sabawa a duk lokacin da tazo gida hutu ko yini guda ne idan zata tafi sai tayi kukan nan.
Abinda ya mutukar bata mamaki bai huce ganin motar Ayman a k'ofar gidan suba, tana tunanin a rayuwarta Ayman yafi ta damuwa da komai daya shafe ta, shiyasa baya mantawa da duk abinda take ciki, yake kuma taimakawa da jikin shi da zuciyarshi da aljihun shi.
Silently taje ta bud'e front seat ta shiga ta zauna.
Suna had'a ido ya sakar mata lallausan murmushi, ba b'ata lokaci ta mayar mishi da martanin murmushin shi a sanyaye tayi k'asa da kanta ta soma gaishe shi. "Ina kwana".
"Kin so ki makara fa".
"Toh ayi hak'uri yaya Ayman "Ina kwana". Ta sake maimaita gaisuwarta. "lafiya Lou Ina fatan kin tashi lafiya".
"Nima Ina lafiya Lou" ta fad'a a sanyaye.
Daga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login