Showing 132001 words to 135000 words out of 288773 words

Chapter 45 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1098

ta tafi har zatayi driving ma, Saida iya ta gama fad'an ta tsab sannan ta bata hak'uri tare da kawo mata uzurin ita a matsayin jita jita taji labarin bata da tabbaci a kai, sannan ai koba komai ya kamata ta sani ko akwai abinda zata iya tunda itama likita ce da tasan aikinta.

Gaba d'aya y'an biki sai suka koma jingun jingun a lokacin data fasu kowa yaji abinda ake ciki.
Doctor surayyah kam haka taje ta had'u dasu malam suka dinga safa da marwa, duk likitan daya futo su bi bayan shi suna tambayar shi halin da ake ciki. Sai dai Kash babu wata gamsashshiyar amsa bare makama d'aya da zata nuna abinda ya faru dashi. Ko kafun wani lokaci mutane sun cika emergency kamar ana wani kwarya kwaryan biki.
Duk cikin su malam da khaleefa, Auntie da Ahmad babu wanda bai rikice ya rud'e da wannan hali da ake ciki ba, sunci gaba da tsaiwa har zuwa lokacin da aka futo dashi kwance kamar baya numfashi aka nufi wani d'aki dashi na daban.
Aikuwa khaleefa da auntie suka bi bayan likitan zasu shiga su ganshi ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, "we are sorry please! But we cannot allow any of you to see him right now, maybe after some hour's in munga yanayin jikin nashi ya daidaita.....". Duk sai suka tsaya turus suna kallon shi, "calm down your self jikin shi da sauk'i amma yana buk'atar hutu, saboda stress ne ya had'u da deffresion ya kayar dashi k'asa har ya suma.
Sai a lokacin suka sauke y'ar b'oyayyar ajiyar zuciya, "thank God da Allah yasa yana raye har yanzu".
Auntie ta fad'a cikin ranta.

Gaba d'aya sun manta da wani abu da akeyi na daga harkar biki, abu d'aya dai data tuna mama haleema ta kirata a waya ta fad'a mata inda ta ajiye mukullan b'angaren amarya saboda za'a kai kayanta, kasancewar an k'ara sabunta fentin gurin Mukullin suna kusa batayi nesa dasu ba,
Sunci gada da tsayuwa har zuwa lokacin da auntie ta fahimci yamma ta fara yi, malam ya sallamu abokan ango saboda zasu je taho da amarya, Sannan gurin sam ba gurin zama bane, ga mutane y'an dubiya suna ta zuwa, sun sa likitoci sai fad'a sukeyi musu.
Auntien ma bayani yayi mata saboda in aka kawo amarya su waye zasu taryeta, dole ita d'in ce dai da iya zasu karb'e ta.
Da haka dai aka lallab'ata ta tafi ya rage daga malam sai khaleefa dako me za'ayi bazai tab'a barin asibitin ba.

***** Ahmad ne ya d'auko amarya da iya da doctor seera da take ta faman waya da surayyah lokaci bayan lokaci don taji ko zasu isa gidan a dai dai. Sai yayar ummie Auntie Aysha.
Ragowar motocin kuwa duk k'awayen amarya aka d'auko da y'an uwan su.
Doctor surayyah na zaune kan d'aya daga kujerun parlonta, gefenta su mama haleema da sauran mutanen biki ne y'an tsirari da basu gama tafiya ba, kallo d'aya zakasan bata cikin cikakkiyar nutsuwarta da hayyacinta, hannunta tallabe da habarta zuciyarta nacan tare da habeebqalbeenta Ayman,,,,, "Allah ya baka lafiya,,,, ya tashi k'afad'un ka Ayman d'ina". Abinda take nanatawa kenan a cikin zuciyarta tunda ta zauna.
Duk cikin gurin jigum jigum sukayi kowa zuciyarshi cike da tausayinta.
A dai dai lokacin da aka shigo da raihana iya na rangad'a gud'a kamar ta fasa bangon gidan, raihana sake k'ank'ame jikinta tayi guri d'aya tare da sake fashewa da wani irin wahalallen kuka marar sauti.
Duk da auntie bata cikin yanayin farin ciki amma saida ta fad'ad'a fuskarta da fara'a, da kanta ta isa gare su ta rik'e hannun raihana ta kawo ta har kan kujerar da take kai ta zaunar da ita kusa da ita, su auntie hajara da sauran y'an kawo amarya manya da suka tako musu baya duk guri suka samu suka zauna ana gaggaisawa, har suna tambayarta me jiki, ko a yanzu saida raihana taji kamar ta tambaye su waye ba lafiya amma bata da wannan yancin da zarrar. Basu b'ata lokaci ba suka mik'a amanar raihana a hannun auntie da iya.....

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics,toh maza garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page thirty seven3️⃣7️⃣


Daga nan sukayi da amarya b'angarenta dake a k'asa, da k'afar dama su auntie hajara suka sata ta fara shiga, da Bismillah d'auke a bakinta, kanta rufe da lullub'i haka aka ratsa parlon gidan inda su zee ke zaune aka shiga da ita har d'akin baccinta, a gefen gado auntie hajara ta zaunar da ita.
Suka kewayeta suna mata naseeha mai kashe jiki game da rayuwar aure, har a lokacin raihana kuka kawai takeyi duk jikinta a sanyaye.
Suna futa ta kwanta tare da rufe k'afarta da bargo ruff! Saboda kanta da yake wani irin sara mata, so take taji waye ba lafiya a gidan sai dai bata da mai bata amsa ba tare data tambaya ba, ita kuma batasan wa zata tambaya ba. A haka y'an matan suka shigo d'akin duk suka haye kan gadon suna kuzuzuta mata kyan da gidanta yayi. Da farko banza tayi dasu, amma duk da haka basu rabu da ita ba saida suka sa ta mik'e zaune ta zauna sosai tana kallon su, kusan kafatanin y'an matan k'awayenta ne suka yo mata rakiya, har dasu Fatima da raheela, Salma ma tazo amma bata ga khausar ba, hakan yasa ta tambayi zainab, "Ina khausar?". "Bata samu damar zuwa ba mijinta yazo sun tafi tun yamma, amma yace zai kawota da kanshi in an kwana biyu....". Zuciya bata da k'ashi, kuma tsakanin d'an uwa da d'an uwa akace sai Allah, sai Raihana ta ji ba dad'i da bai barta tazo mata rakiya ba.
Kamar Salma tasan abinda take tunani kenan a ranta, sai ta k'arasa kusa da ita ta zauna, "khausar fa ummie ce ta azalzala mata ta tafi ba don taso ba, saboda kamar bata jin dad'i don a kwance ta yini ma yau, kinsan jinin ku iri d'aya ne bakwa son shiga hayaniyar mutane".
Murmushi raihana tayi ba tare da tace komai ba amma a cikin ranta taji sanyi tunda ai rashin lafiya bai huce kan kowa ba, sannan dad'in dad'awa tasan halin khausar tun ba yanzu ba, sun d'anyi shiru kafun ta tambayi su raheela, "Amma dai ba yau zaku tafi ba ko?".
"Eh sai gobe da sassafe insha Allah". Fatima ta riga raheela bata amsa.
"Shikenan ma sai ku kwana anan kafun goben ku huce...."
Duk kwalalo ido sukayi suna kallonta, ameena ta kalli xee suka had'a ido kafun su kwashe mata da dariya.
Had'e rai raihana tayi tace, "kufa ba mutumci kuka cika ba meye abun dariyar kuma....".
Fatima tace, "a'a rufa mu ki sayamu raihana, da inba hakabba ina mu Ina kwanan gidan amarya?".
Zee tace, "aikuwa dai kam". Sai suka sake fashewa da wata dariyar.
Salma data gama goya samha a bayanta tace, "Ni kam Ina nan har sai kun gaji dani kun kore ni da kanku keda angon, zan kira Abban samha shima ya taho".
Wata cikin cousin d'insu tace, "zaki aikata, don daga ke har mijin ki irin ku d'aya, sai ki kira shi maza ya had'o muku kayan ku....". Aikuwa suka sake saka dariya.
Cikin had'e fuska Salma tace, "haba auntie hapsert haka ma zaki ce salon kisa su auntie zee su samu abin yi...".
"Aikuwa dai don gasu nan kashe da kunnuwa....". Wata ta fad'a cikin su.
Mik'ewa tsaye zainab tayi tace, "toh ni kuma Salma Allah na tuba astagfirullah meye naki ban sani ba?...aike d'innan rufe k'ofa ce, har yanzu in kikayi abu kamar y'ar bayan ki".
Duka cikin d'akin ba wanda baiyi dariya ba har raihana data ja gele ta rufe rabin fuskarta gudun kada ta aikata laifi, musamman da suka ga abinda Salma takeyi da fuska, exactly kamar samha yadda zee d'in ta fad'a dai.
Salma tace, "ai shikenan ba wani abu, habeebty mu tafi ko tunda korar mu sukeyi...". Ta fad'awa samha dake bayanta.
"Kunji ba da samha take shawara fa wai!". Zee ta k'ara fad'a tana nunata.
Suka sake yin wata dariyar, ita kam salma Jakarta ta d'auka ta fuce zuwa parlour gurin su auntie hapsert k'arama.
Itama raihana tashi tayi jin an kira sallah a masallaci.

Nikam na tafi lek'o muku gidan amarya😜 bedroom uku cikin k'aton parlour da aka rarrabashi kowanne guri daban, daga can gefe guda wata kusurwa k'awataccen gurin dinning ne, kalar milk, labulaye da carpet duka maroon, sai kujerun parlonta da k'aton carpet masu kyau da tsada suma milk. Three bedrooms kuwa da suke cikin d'akin, set na kayan gado ne guda biyu d'aya maroon, d'aya kuma fari sol. Duka an shimfid'a bedsheet mai tsada da kyau, d'aya d'akin kam basu saka komai a ciki ba sai carpet da curtains brown colour, kitchen kam ba'a magana, komai an k'awata shi da kayan amfani sahihai sai d'aukar ido sukeyi kamar kaga hoton kanka a jiki, gashi wadatacce duk da komai na gidan babu k'untata bare k'untatawa, dede da sitting room an shirya shi da kayan furnitures na alfarma. Ko'ina ba abinda yake tashi sai k'amshin sabunta daya had'e dana room freshener da aka fesa.

Ranar haka su Fatima suka dad'e suna d'ebe mata kewa da shaftarsu har saida su Ahmad suka dawo d'aukar su zasu mayar dasu. A lokacin zee ta zage tana ta basu dariya wai ita a lallai lecture takewa amarya.
Auntie Sarah d'aya daga cikin k'annen ummie na shigowa d'akin duk sukayi shiru suna kallonta kamar marassa gaskiya, itama kallon su tayi kafun ta k'arasa shiga d'akin, kusa da raihana ta zauna ta fara yi mata magana da tattausan kalami, "alhamdulillah raihana yau gaki a gidan auren ki, kai tsaye bazan ce auren dole akayi miki ba don ummienki tace mijin da kika aura zab'in kine ba wanda yayi miki dole cikin su. Toh daga yanayin uwar mijinki da mijin ki a d'an sani da tarbar da muka samu a gurinta mun fahimci mutanene masu son zaman lafiya da lumana, kuma kema nasan ba mutum bace me matsala, sai dai yau da gobe da akace bata bar komai ba, shiyasa nake rok'on ki don Allah kiyi iya yinki ki tabbar baki sauya daga yadda muka sanki ba, ki rungumi rayuwar auren ki, ki kyautata ibadar ki, don shi aure dukan shi ibada ne, a k'arshe Ina miki fatan kasancewa macen data fi kowacce mace nagarta....." Saita dawo da dubanta ga sauran y'an matan, "naseeha ta ba iya raihana na yiwa ba, nayi ne ga dukkannin ku don nan da lokaci k'alilan dukan ku zaku riski kanku a irin matsayin data hau kai yanzu....".
Duk ba wanda jikin shi baiyi sanyi ba a cikin su, sai suka tsaya kurum suna sauraronta a ransu suna gasgata maganarta.
"Abokan ango sun dawo inda wad'an da zasu tafi yanzu cikin ku.... Muma hucewar zamuyi saboda Ina tunanin ango bazai samu damar zuwa akan kari ba saboda shi aka baro akan hussainin shi da yake kwance a gadon asibitin......".
Wani irin rass! Raihana taji a cikin zuciyarta tunda taji kalmar k'arshe data futo bakin auntie Aysha, Yaya Ayman bashi da lafiya toh me yake damun shi? Ta tambayi kanta a zuciyarta, duk jikinta a sanyaye take kallon su a lokacin da suka gama yi mata sallama suka fuce. Haka tana ji tana gani kowa ya tafi aka barta ita d'aya.

Misalin k'arfe goma da rabi na daren ranar, raihana tana kwance kan lafiyayyen gadonta ta nad'e k'afafunta da bargo idonta na kallon saman d'akin, ta lula cikin duniyar tunani, abinda ya assasa har bata ji knocking k'ofarta da akeyi ba.
Mama haleema kam jin tana ta tsaiwa a cikin parlon ba alamun akwai wani mutum mai numfashi, saita fara duba bedrooms d'in dake cikin parlon. A sa'a d'akin data fara shiga (don shi kad'ai ta gani a bud'e) ta samu raihanan, ta k'arewa d'akin kallo ta cikin hasken daya mamaye d'akin, daga inda take ta kwad'a uwar sallama, raihana bata iya amsawa ba sai mik'ewa zaune da tayi. Mama haleema k'arasa shiga tayi amma ba ciki da nisa ba ta tsaya daga jikin k'ofa tace, "Ina yuni amarya".
Raihana kallonta tayi, ganinta babbar mace sai taji nauyin amsawa, a madadin haka sai ita ta gaisheta, "sannu Ina yini...". Mama haleema ta amsa da, "lafiya Lou, dama auntie ce tazo na kawo miki abinci, idan zaki iya kwana ke kad'ai shikenan, idan ba zaki iya ba kuma sai kije side d'inta saboda khaleefa ba zai samu dawowa akan lokaci ba", kamar jira takeyi kuwa zumbur ta mik'e ko kayan jikinta bata tsaya sauya ba ta zura hijab d'in da tayi sallah.
Kallonta mama haleema tayi kamar ta kyaleta sai tace, "Amma dakin sauya kayan jikin ki zuwa na bacci ko....".
Ita kanta raihana zata so hakan, don kayan sunyi mata nauyi zasu iya hanata bacci tunda ba sabawa tayi ba, wardrobe d'inta ta fara duddubawa saboda d'azu taga Aunty Sarah tana zuba wasu kaya har tana fad'a mata wanda zata sauya ne in tana da buk'atar hakan, cikin sa'a ta samu wasu riga da wando cotton milk colour masu kyau ta ciro, zata shiga bathroom mama haleema tace, "Bari na jira ki a parlour". Ta gyad'a mata kai, ko bayan ta sauya kayan tayi ta zura hijab d'inta dogo ta bi bayan ta. Saida suka kulle k'ofar futa sannan suka fara haura stairs, k'awataccen parlon Auntie tabi da kallo, ba abinda yake tashi sai k'amshin turaren ta irin na Sudanes mai kama komai na gida har bango, "nan zaki shiga". Mama haleema ta fad'a tana nuna mata k'ofar wani d'aki, ba musu ta shiga d'akin, a gyare yake ko'ina fes fes, babu yawan tarkace daga k'aramin gado sai sallaya da labulaye. A gefen gadon ta zauna, mama haleema ta kawo mata abincinta ciki.

A daren ranar kasa runtsawa tayi kamar yadda ta kasa saka komai a cikinta, Babu abinda take sai juyi zuciyarta fal da tunane tunane, kowacce amarya akan kawo ta gidanta da yarda da yak'inin ta rabu da duk wasu matsaloli na yaudarar maza, bisa amanna kan cewa tazo din din din babu abinda zai rabata da mijinta sai mutuwa, sab'anin nata auren da tazo da nufin futa nan ba da jimawa ba tabi sahun matan da ake kira zawarawa, ta yaudari iyayenta da wannan mutuniyar kirkin ma'abociyar nutsuwa da kamala, matar data tsaya kan jiki kan k'arfi wajen ganin d'anta ya aureta da darajar data zarta ta sauran mata...... Shin ya auntie da ummienta zasu ji idan akace dasu yau khaleefa ya saketa?..... Bisa wace hujjar za'a rattaba sakin?.
Ganin tunani zai haukatata da hankalinta saita sauko daga kan gadon ta d'aura alwala ta fara jero sallolinta na dare. Tayi addu'a sosai akan Allah ya futar da ita lafiya da auren khaleefa, ta yiwa Ayman addu'a duk da batasan abinda yake damun shi ba, haka y'an uwanta da iyayenta har ma auntie data fara zama wani sashe nata a yanzu bata manta da kowa ba cikin addu'o'in ta.

*****Khaleefa kam a zaune ya kwana a d'akin da aka maida y'an biyun shi bayan numfashin shi ya dawo dai dai jikin shi ya fara karb'ar treatment d'in da ake mishi, tunda ya saka kujera ya zauna gaban gadon da Ayman yake kwance bai runtsa haka bai motsa ba yana rik'e da hannun shi yana noticing duk wani motsin shi, Ahmad ma da yake tare dashi kusan sai can nisan dare ya samu damar kwanciya.
Shi kuwa khaleefa kwana yayi d'aga wayar auntie duk bayan wani lokaci sai ta kira taji yadda ake ciki.
Koda aka kira sallahr asuba da kyar ya iya tashi suka yi jam'i shida Ahmad anan ciki, ji yake kamar inya futa ya barshi kafun ya dawo zai tarar ya mutu.

Misalin k'arfe bakwai da y'an mintuna Ayman ya farka bakinshi d'auke da salati, da fuskar khaleefa ya fara tozali yana jero mishi sannu da tambayar ya yake jin jikin shi.
Ya motsa bakin shi da kyar yace, "da sauk'i....".
"Alhamdulillah" khaleefa ya fad'a a k'asan mak'oshi.
Shiya taimaka mishi ya mik'e har ya shiga toilet. Koda ya futo sallayar dasu khaleefa sukayi sallah ya shimfid'a ya fuskanci alk'ibla, saida ya rama duk sallolin da suka huce shi sannan ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana wassafa wasu al'amura a cikin zuciyarshi, zuwa yanzu ya gama cire rai da raihana, don yasan ta dad'e da zama mallakin khaleefa har ta kwana d'aya a gidan shi, ba don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login