Showing 258001 words to 261000 words out of 288773 words

Chapter 87 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1122

da juna sai dai kowa a cikin su yayi nisa ne cikin zuzzurfan tunani, Ayman ne ya fara nisawa ya d'ago kanshi da yake k'asa idon shi har ya fara sauya launi yace, "kana nufin har yanzu kana nan akan bakan ka?".
Khaleefa ya d'ago yana kallon shi da wani irin yanayi yace, "bana da wani zab'i bayan haka....".
Wani irin murmushi Ayman yayi wanda yafi kama da yak'e ya kalli d'akin da raihana take ciki kamar zai ganta sannan ya sake maida duban shi ga khaleefa yace, "yanzu ya kake son ayi kenan?".
"Kai zan tambaya Ayman!".
"Well zaka sake ta kawai na aureta amma sai bayan kun amsa mun wasu tambayoyi kaida ita da amsa ta gaskiya.... Firstly kirawo ta dai ayi komai a gaban idonta....".
Dukkan su suka sake d'auke wuta... Kamar wanda ake umarta haka ya tashi ya nufi d'akin, koda yake umarnin nema.
Daga inda yayi knocking ta bud'e ya buk'aci ganin ta ya koma cikin parlon ya zauna yana jiranta, ba jimawa itama ta futo a sanyaye ta zauna suka gaisa da Ayman.
Sunyi shiru kafun Ayman ya fara cewa, "tambaya ta farko, shin a iya zaman da kukayi da raihana da igiyar auren juna wani abu na auratayya bai tab'a shiga tsakanin kuba.....?".
"I don't get you? Wani abu ya faru zance zan saketa ka aureta?". Khaleefa ya fad'a cikin katse mishi hanzari a d'an fusace.
"Calm down mana, yada d'aukar zafi tun kafun aje da nisa kuma? Raihana ke ki amsa mun tambayana".
Satar kallon inda khaleefa yake zaune tayi sannan ta maida kanta k'asa tace, "a'a".
Shiru Ayman yayi yana nazarinta, dama yasan hakan bata kasance ba, shima yana sane yayi tambayar, sai ya sake cewa, "alhamdulillah as i expected! Sai abu na gaba how many kiss and hug? Nasan ba zaku saka mun duk wad'annan a wancan lissafin ba shiyasa zan muku dalla dalla...".
"Aymaaaannn! What a silly question". Khaleefa ya fad'a yana mishi wani kallo. Ita kam raihana kunyar Ayman d'in taji, tunda suke dashi magana makamanciyar wannan bata tab'a futowa a bakin shiba, amma yau..... Bata k'arasa tunanin ba maganar Ayman ta katse ta.
"Sai kayi hak'uri amma fa dole a amsa mun tambayar nan".
Tunani khaleefa ya tafi na lokacin daya dinga attempting kissing d'inta yana kwab'ar kanshi. Itama irin abinda ta fara tunawa kenan.
Ganin suna shirin barin duniyar da muke ciki zuwa wata ta daban sai yayi gyaran murya yace, "ba amsa kenan?". "Ayman joke aside please, raihana kije zamu k'arasa magana dashi". Khaleefa ya fad'a da sanyayyayyiyar murya. Kamar an zare mata k'aya haka taji, aikuwa ta bar gurin sauri sauri, khaleefa yabi bayanta da kallo har ta shige sannan ya sauke b'oyayyen ajiyar zuciya.
Ayman da yake kallon shi ta k'asan ido yayi murmushi yana lissafa shi, kafun yace, "Ina ganin mubar maganar nan zuwa wani lokaci, yanzu ina zamu tafi k'arfe ukun inta cika?".
"Ni kaina ban sani ba, in lokaci yayi zamu gani nida kai........".

At exactly 3pm suka futo su dukkannin su, suna gaba raihana na bin bayan su, sanye da wadataccen mayafi saman kayan jikinta, suna Isa reception Ayman da ita ya fara tozali, yanzun ma sanye take da doguwar riga dark blue data haskata, tayi rolling da bak'in gyale, fuskarta ko powder babu amma tayi kyau duk da haka. Doctor andal da take tsaye daura da ita sai dai ta yane har fuskarta da gyalen kayan sai idonta kawai ake gani. Da hannu ta yafuto raihana, ta k'arasa don ganin mai kiran nata, saida taje kusa ta gane likitan ce, tayi murmushi tare da russunawa tana gaishe ta.
Bayan sun gaisa ta kalli suhaana da take gefe ta gabatar mata da Raihana. Ta mik'a mata hannu suka gaisa sannan ta fad'awa raihana full address na anguwar kamar yadda auntie ta tab'a bata a rubuce.
Raihana komawa tayi gurin su khaleefa ta fad'a mik'a mishi address na anguwar, ya karb'a ba tare daya ce komai ba sukayi gaba ta sake take musu baya.
Wata irin tafiya sukayi marar armashi sam a wannan karon ma, kusan tsiran su dasu doctor andal ba yawa suka sauka a katafaren gidan da yafi kama da gari guda. Sun tsaya a gurin har doctor andal ta k'araso, sai a lokacin ta bud'e fuskarta khaleefa ya ganta zahirinta, dama shi tuni ya gane itace zuba ido yayi kawai yaga iya gudun ruwan su, yayinda a zuciyarshi yake ta al'ajabi da tunanin abinda ya shigo da likitar cikin labarin su.
Sun gaisa da ita a tak'aice, sukayi shiru likitar na neman layin Suraj a zuciyarta tana fata da addu'ar samun shi a gari a gida tunda ai weekend ne. Khaleefa daya fara gajiya da tsayuwa ya tunkari k'ofar shiga gidan, ya yiwa d'aya daga securities na gidan sallama, suka amsa ya mik'awa d'aya cikin su hannu suka gaisa, shiru yayi yana nazari kafun can yace, "nan ne gidan late Abdallah tofa ko?". Securityn yace, "baka gani ba a rubuce? Just go ahead ka fad'i abinda ya kawo ka?".
"Munzo ganin Suraj Abdallah ne". Ya fad'a ba d'ar da zullumin komai".
"Yasan da zuwan kune?".
Ya girgiza mishi kai, "a'a sai dai munzo daga nesa, kayi mana alfarma mana mu ganshi......".
"Ka gafarceni amma yallab'ai baya ganin wanda bashi da appointment dashi ko daga bangon duniya mutum yazo.......". Ya gama fad'a tare da juyawa ciki. .
Da sauri khaleefa yabi bayan shi zuwa cikin gidan, wasu cikin securities suka taso suka rik'e shi suna tambayar meye haka zai shigo ba izini.
A wannan karon hak'urin khaleefa gazawa yayi, zuciyarshi ta dake ta yadda yake jin sam bazai koma da baya ba tunda yazo sai yaga wannan mutumin daya tara suna sak dana mahaifin shi, he most be his father ma wallahi.
"Kome zakuyi mun bazan tafi ba saina ganshi tunda nazo....". Ya fad'a da dakakkiyar murya sam ba tsoro.
Wani d'an babba a cikin sune ya k'araso kusa yana mishi kallo na kusa na gaske bayan yasa sun sake shi, ya jima yana nazarin shi hadda kama hab'a kafun ya tambaye shi, "ya sunan ka?".
"Abdallah". Khaleefa ya bashi amsa.
"Your full name I mean".
"Abdallah Suraj Abdallah tofa....". Ai tun kafun ya k'arasa fad'a mutumin ya matso kusa dashi ya rik'e k'afad'un shi da duka hannuwan shi biyu, sai kuma yaja da baya yana sake mishi kallo tun daga sama har k'asa. Duk sauran abokan aikin shi sun tsaya ne suna kallon shi kurum da mamakin abinda yake kallo gurin yaron, shi kuwa da sauri ya juya ya nufi b'angaren da zai sadashi da ubangidan shi.
A lokacin yana oarlom shi na k'asa yana tattaunawa mai muhimmanci through system shida wasu abokan business. Tsabar gigitar da securityn yake ciki yasa bai tsaya knocking ba ya cusa kanshi cikin parlon, ya d'ago yana kallon shi, sai ya russuna yace, "sorry boss akwai muhimmin abinda nake son fad'a maka kana da bak'i a waje......".
"Haka ya kamata ka shigo mun ko sallama babu, and kafi kowa sanin bana ganin duk wani wanda bani da appointment dashi".
Sake russunawa yayi yace, "kayi hak'uri yallab'ai nima nayi yink'urin sallamar su amma d'aya cikin su ya nuna lallai lallai kai yake son gani saboda sunzo ne daga nesa......".
Kama hab'a yayi kawai yana kallon shi, tunda har yaga ya ajiye su watak'ila abu mai muhimmanci ya kawo su, sai ya maida kanshi ga abinda yake yi yace, "ka fad'a musu su jirani in zasu iya".
Ci gaba da tsaiwa mutumin yayi har saida Suraj d'in ya d'an fusata yace, "yaushe muka fara haka da kai?".
Wannan karon durk'usawa yayi kan gwiwowin shi biyu, idon shi still a k'asa yace, "Wanda yazo ganin ka ko makaho ya shafa zai tabbatar da jini iri d'aya ke yawo tsakanin ku, saboda a duniya ni ban tab'a ganin wani mutum da yayi kama da kai sak kamar shiba, sannan yace sunan shi Abdallah Suraj Abdallah tofa wanda yazo d'aya da sunan gidan nan........".
Ai tun kafun ya dire zancen shi ya mik'e yana kallon shi, cikin son tabbatar da abinda kunnuwan shi suka jiye mishi ya nufi hanyar futa a d'akin da sauri, mutumin ya mara mishi baya. Khaleefa yana tsaye kyam a harabar cikin gidan ya hard'e duka hannuwan shi a baya. Tun daga nesa daya hango shi gaban shi yake tsananta fad'uwa har yazo dab dashi, a lokacin yaron ya lura da zuwan shi shima ya d'ago yana kallon shi. D'auke wuta Suraj yayi na a k'alla wasu dak'ik'u kafun ya iya motsa lab'b'an shi, "waye kai?". Duk da tambayar ta zowa khaleefa a wani yanayi sai bai fasa bashi amsar data kamata ba, "Abdallah Suraj d'a ga Suraj da surayyah......".
A wani irin gigice ya k'araso ya rungume d'an nashi cikin jikin shi yana kiran sunan shi ruwan hawaye na wanke fuskarshi. Abun Kamar a mafarki haka suka jishi su duka biyu, securityn daya fara kasadar sanar da Suraj zuwan khaleefa shiya shigo da ragowar ma ciki. Ayman yayi surrender daga inda yake yana kallon mutumin daya juya bayan shi, da khaleefa da yake rungume jikin shi tsam tsam yana share hawaye.
Da hannu khaleefa ya kira shi, saiya k'arasa a sanyaye ta inda zai ga fuskar mutumin, aikuwa sai ga idon su cikin na juna a sa'a, sakin khaleefa yayi yana kallon Ayman dashi kanshi khaleefan, kamar mai tsoron wani abu ya tambaye shi, "shi d'an biyun kane? Sai a lokacin ya tuna takardar da surayyah ta bar mishi mai d'auke da shaidar scanning da result na y'ay'a biyu. Mik'awa Ayman hannu yayi ya k'arasa kusa suka rungume juna, koda baisan komai da yake faruwa ba amma yaji a jikin shi wannan mutumin jinin sune ko daga kamannin da yake dasu zai tabbatar da haka. Sun jima a haka suna kuka raihana da suhaana na jere tare suna kallon su cike da tausayawa, doctor andal kanta hawayen tausayin su take yi. Tana hango tashin hankalin da zasu shiga a gaba, ranar da mahaifin su ya had'u da mahaifiyar su ga soyayyah amma ba aure har abada......
Saida suka jima sannan suka janye jikin su ya tambayi Ayman sunan shi, ya fad'a mishi, sai ya sake jinjinawa surayyah, mahaifinta da mahaifin sa ta samarwa takwarori.
Sai a lokacin andal ta k'arasa inda suke tsaye tace, "finally gashi na cika alk'awarina, wad'annan yaran y'ay'an kane, mallakin ka halak malak....".
Da sauri Ayman ya nuna shi, "kina nufin wannan shi ya haife mu? Toh waye kenan wanda auntie take nufi ya mutu?".
"Magana ce mai tsayi da ba zata yiwu a nan ba". Andal ta fad'a tana kiran su raihana da musu alamun su matso kusa.
Suraj ya kalli y'an matan biyu sannan ya kalli andal, "wannan matan sune?". Ta girgiza mishi kai ta nuna raihana ta mishi bayanin itace matar khaleefa, ita kuma wannan suhaana y'a tace, Ayman baiyi aure ba tukun.
Ya sake jinjina girman hukuncin ubangiji, ya gama sarewa a rayuwa ba zai tab'a ganin irin wannan ranar ba, ya gama hak'ura da zai ga surayyah a rayuwar shi bare abinda ta tafi dashi a cikinta.

Ganin suna ta tattauna abubuwa masu yawa a nan, sai ta buk'aci su k'arasa ciki. A babban parlon gidan ya musu masauki, ba kowa sai wasu matasa guda uku a mabanbantan gurare kowa da abinda yake yi. Suna ganin shi suka mik'e suna kallon shi da russunawa suna mishi barka da futowa.
Bai iya amsa musu ba don baya da nutsuwar da zai banbance komai bayan wanda yake gaban shi, "Ina grandma take?". Ya tambaye su, "yanzun nan ta haura stairs". Da kanshi ya nufi matakalar ya haura. Ya sameta tana ta gyara wata y'ar k'aramar baby girl, (wata y'ar dattijuwar mace data manyanta shekarun ta sukayi nisa na gani) bai fayyace mata komai ba ya d'auko yarinyar ya buk'aci data biyo shi don ganin bak'in da yace sunzo ganinta. Turus ta tsaya tun kafun ta gama saukowa tana kallon fuskokin mutanen da suke parlon. Tsabar shock daya shigeta saida taji kamar ta yanke jiki ta fad'i don kanta gaba d'aya juyawa ya fara yi. Saita k'arasa futowa a daddafe tana rarraba ido tsakanin matasan y'an biyun da Suraj tace, "Suraj wad'annan yaran fa? Dama kana da yara bamu sani ba?".
Kamo ta yayi ya zaunar da ita ganin duk ta diririce yace, "carm down your mind momma zanyi miki bayani dalla dallah".
"Wane bayani kuma bayan gaskiyar dana gani da idona, ai wad'annan yara kam jinin kane abinda kawai ban sani ba shine yaushe aka haife su kuma wacece ta haife su, shin wani auren kaje kayi bamu sani ba?".... Duka ta jera tambayoyin cikin son sanin gaskiyar abinda yake shirin faruwa.
Murmushi Suraj yayi har lokacin yana gabanta yace, "duka babu d'aya, wannan yara ne daga matar da a duniya banda kamarta, matar data tafi da dukkan walwala ta, farin cikina, zuciyata d'ungurungum ma....". A hankali yanayin fuskarta ya fara sauyawa, ta sake kallon shi da yaran kamar mai tsoro ko koyon magana tace, "surayyah Adam?".



_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy four7️⃣4️⃣


"A ina ka nemo surayyah Suraj kayi shiru ba tare daka had'a mu da ita mun nemi yafiyarta ba?...... Kana nufin wad'annan yaran ita ta haifa maka su? Dama da gaske kana sane da surayyah ta tafi da cikin ka mune bamu sani ba, shiyasa koda yaushe kake cewa kasan kana da y'ay'a inda suke ne baka sani ba?". Saita mik'e har tana tuntub'e ta tafi gurin da suke zaune suna rarraba idanu da kallon ikon Allah har ta k'araso kusa dasu da murya mai rawa tace, "ku matso gare ni y'an biyu nice grandma d'inku.... Ku matso inji jinin surayya da Suraj da yake yawo a jikin ku.....". A sanyaye suka nufe ta suka rungume ta su duka biyun.
Kuka take yi karurus, irin mai d'aga hankali da ban tausayin nan tana had'awa da sambatu, ita kanta ba zatace tasan abinda take fad'a ba cox she's out of her sense.

A take a gurin ta fara kiran wayar yaran gidan tana fad'a musu suzo maza wani abu muhimmi na faruwa a gida, ko zuwa lokacin da zasu futo daga masallacin gidan bayan sun idar da sallar la'asar gida ya cika fal da yaran gidan hadda jikoki da basuyi aure ba. Babu wanda wannan al'amari bai jijjiga ba musamman matar mukhtar da suka had'u da surayyah a saudiyyah.
Fad'in adadin farin cikin da wad'annan Ahali suka shiga a wannan rana ma b'ata baki ne, sunji dad'i sunyi farin ciki sun kuma taya Suraj murna. Kowa sonsu yake da nuna musu kulawa a wannan family, sai ya zamana a gaba d'aya gidan kowa sai haba haba yake dasu cox sunzo gwanin burgewa kamar uwarsu data kasance ta daban. A irin maganganun mutanen gidan andal ta fahimci asalin nadamar da sukayi akan abinda suka yiwa surayyah, da alama tun kafun aje da nisa hak'k'i ya kama sadiya shiyasa a gidan babu ko mai kama da ita.
Suraj ya shaida raihana don ba fuska ce da zai iya mantawa ba cikin sauri, don komai k'ank'antar alkhairin mutum a gare shi baya tab'a mantawa, sai a lokacin ya gane dabarar andal da yadda ta shirya komai a sannu sannu bada gaggawa aikin shaid'an ba.
Ranar basu suka samu nutsuwa ba sai dare bayan sun nuna buk'atar su ta komawa masauki sai dai da alk'awarin zasu dawo gare su da safe, tun kafun Suraj ya nuna rashin yardarshi momma ta daka tsalle ta dire tace sam ba zasu yarda su koma d'akin hotel ba, saboda tana tsoron kada su b'ace musu murna ta koma ciki, tasan idan har haka ta faru ta mawuyacin abu ne su sake samun Suraj.
Duk yadda suka so fahimtar da mutanen gidan k'in fahimta sukayi, a k'arshe dole suka hak'ura aka wakilta wasu matasa biyu da suhaana da zata musu jagora a d'auko musu kayan su da suka zo dasu. Ayman ba don yaso ba yabar suhaana ta tafi da matashi d'aya da budurwa cikin jikikon gidan, sai don yasan ba za'a tab'a barshi ya futa ba amma yana tsoron matashin nan ya mishi shigar sauri don tunda suka zo yake mata wani irin kallo.
Suna zaune cikin parlon mahaifin su a daren ranar, a duk yinin gaba d'aya sai yanzun ya samu damar keb'ewa dasu. Yanzun ma saboda dare ya fara nisa ne kowa ya tafi makwanci, suma sunyi shirin kwanciyar cikin tausasan kayan su mabanbanta, suka same shi a zaune bai kwanta ba ya rafka uban tagumi.
Sam baisan da wanzuwarsu gurin ba saida suka zauna kusa dashi. Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon su sannan a sanyaye yace, "ya doctor surayyah take?".
Ayman yace, "tana lafiyarta".
"Sai dai tana can cikin b'acin rai da bak'in cikin abinda nayi mata ko? Har yanzu tana ci gaba da gaba dani ko? Shiyasa ta b'oye ku daga gareni tsawon wad'annan shekarun ta maida ni matacce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login