Showing 126001 words to 129000 words out of 288773 words
Chapter 43 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
taya ta su dara tare. Tafiyarta nursing school da yadda suka ci gaba da rayuwa cike da kulawa da mutunta juna har zuwa kan yadda kishin zata auri Imran yasa ya janye jikin shi daga gareta a hankali, bai sani ba a wancen lokacin ashe damace aka bashi, irin damar da masu iya magana ke cewa sau d'aya take zowa mutum a rayuwa. Sai ya daki k'asan d'akin da hannuwan shi, bai damu da yadda suke zugi da rad'ad'i ba ya fara magana cikin muryar kuka, "me yasa zaka yimun haka khaleefa! Meyasa!! Meyasa!!!" Ya k'arasa fad'a yana kifa kanshi jikin gadon shi yana jujjuya kanshi. .
★★★★ A daren ranar ran auntie yakai mak'ura wajen b'aci a lokacin data ritsa khaleefa bai shirya ko kayan da zaisa na d'aurin auren gobe ba,,,, kanshi a k'asa har ta gama bambaminta sannan ya bata hak'uri tare da kawo mata uzurin baya jin dad'i, baya ga haka ma baya tunanin zai samu zuwa gurin d'aurin auren gaba d'aya, wannan karon kallon shi kawai ta dinga yi zuciyarta naci gaba da raya mata abubuwa da yawa na manufar auren raihana da khaleefa ya shirya zaiyi.
Sun jima shiru kafun ta mik'e ta bashi umarnin ya biyota zuwa sashenta.
Set d'in akwatuna ne guda biyu, amma kalar su mabanbanta, bakwai iri d'aya bakwai iri d'aya. A gefe ya zauna yana sauraron maganar da auntie take yi bayan gama nunnuna mishi kayan cikin akwatunan.
"Wannan kayan lefen kune dana dinga had'awa a b'oye, naka dana Ayman da ban d'auka wani cikin ku zai iya riga wani fara yin aure ba,,,,. Toh yanzu tunda al'amura sunzo a juye Ina ganin zamu barwa raihana duka wad'annan kayan...." Maganarta ta k'arshe ta d'au hankalin khaleefa har baisan lokacin daya juyo ya dube ta ya sake duban kayan ba. Ta gane kallon da yake sarai amma tayi kamar bata gane manufar shiba taci gaba da bayaninta.
"Da farko nayi niyyar yi muku bazata da wad'annan kayan lefen a lokacin da auren ku zai taso, amma yanzu tunda matar ka kad'ai za'a barwa dole ka biya farashin su, kayana masu kyau da tsada ne, kusan duk ba'a k'asar nan na had'a suba, da kud'in su da kud'in aure da sadaki duk kai zaka biyawa kanka babu wanda zan iya d'auke maka a ciki, tunda Allah yasa akwai kud'i a gurinka....".
Fuskarshi sam bata sauya daga yanayin yadda take ba, bare auntie ta fahimci yadda ya karb'i zancen, da dakakkiyar murya ya tambayeta, "meye total na duka kud'in". Wani murmushin mugunta tayi ta d'anyi jim tana had'a lissafin jimillar kud'in a ranta, kafun ta fara mishi bayani dalla dalla.
"Dubu d'ari biyu na kud'in aure (kasan hausawa suna kai kud'in gaisuwar iyaye), dubu d'ari da hamsin kuma na sadaki, sai kyautar motar million biyu ko biyu da rabi haka da nake son kayi mata.....".
A wannan karon khaleefa kasa hak'uri yayi har saida ya tambayeta da mamaki, "Toh ni yanzu ina zan samu motar da zan tabbatar da ingancin ta har ayi cikini a biya kud'inta kafun gobe?, Sannan motar ita kuma ta meye...?".
Murmushin gefen baki tayi tace, "Kaine nake son ka aureta da daraja har haka khaleefa, saboda kafi sanin muhimmamcinta, sannan mota kada ka wani damu na sameta already har anyi ciniki kud'i kawai zaka musu transfer a kawota".
Kanshi ya rik'e da hannun shi biyu yana juya maganganun auntien, toh meyasa auntie take yin hakane wai, so take ya aureta da tsada saboda kada ya saketa ko meee? Shin batasan auren deal bane da bazai huce wa'adin shiba?
"Khaleefa kai nake saurare shin ko akwai abinda baiyi maka bane a cikin abubuwan dana lissafa a soke.... Duk da sokesu yana dai dai da soke auren gaba d'aya..... Ga lissafin kayan lefe, duka mu barshi 1.5million".
Wayarshi da take aljihu ya zaro ya tambayi account d'inta, tana fad'a yayi mata transfer 4million, ya tashi zai tafi ta dakatar dashi.
"Ka tabbatar ayman ya rakaka inda ake siyar da ready made, ka karb'o farar shadda hula da takalmi, don gobe in bakaje wajen d'aurin auren nan ba....." Sai ta gyad'a kai kurum.
Futa yayi amma kuma ya kasa shiga cikin d'akin, sai ya tsaya daga jikin k'arfen benen yana lissafa auren da zaiyi gaba d'aya tare da aza shi bisa mizani, har yanzu baiga wani kuskure ko wani abu da yayi ba dai dai ba akan maganar auren nan, sai dai tsoron shi d'aya Auntie data fara gindaya mishi tsauraran sharud'd'a tun kafun aje ko'ina.
Hango tahowar Mama haleema yasa shi saurin kaucewa daga gurin, don yanzu sai ta hau zolayarshi tana addu'ar da bai sata ba.
Ko k'asa ko sama ya rasa Ayman a gidan, gashi sai kiran wayarshi yake a kashe. Bai sanar da kowa ba yayi kwanciyarshi don baiga abun tashin hankali da zai wani damu kanshi kan lallai sai ya nemo wasu fararen kaya a yammacin nan ba, shi kuma Ayman maybe ya futa ne yaje ya dawo zuwa jimawa.
Auntie kuwa mayar da kayan tayi ma'ajiyar su tana tuna yanayin da khaleefa ya shiga akan maganar kud'ad'en data lissafa, tana sane tayi charging shi kud'i masu yawa saboda aljihun shi ya jijjiga sosai ta yadda ko sunan raihana bazai so yin wasa dashi ba bare aurenta.
*****Washe garin ranar suka tashi da bak'i k'awayen Auntie y'an biki da wad'an da zasuyi jagorancin kaiwa su malam kayan lefen har gida, don a can auntie ta shirya gudanar da yininta tare da tsirarun abokan aikinta, duk daba wani yawa ne dasu ba amma hayaniyar su duk saita damu khaleefa saboda maganar ba a hankali suke yinta ba, shi sai ya dinga jin ma kamar har wata y'ar shewa shewa akeyi a gidan nasu yau.
Ita dai Auntie tana zaune tsakiyar su duk jikinta a salub'e, rabin hankalinta yana kan khaleefa da tunanin ko yayi abinda ta umarce shi jiya?
Ganin ta lula duniyar tunani sai d'aya a cikin su ta kira sunanta, "surayyah".
Bata amsa ba sai d'ago kanta da tayi ta kalleta, "kamar akwai damuwa a tare dake, sannan ni tunda nazo nake son tambayarki Ina sameera naga ban ganta ba..".
Murmushin yak'e tayi a lokacin da doctor Rabi'a ta kai aya, don kore musu zargi sai tace, "kwana biyu bata da lafiya, amma Ina tunanin anjima in jikinta yayi sauk'i zata zo...".
"Toh Allah ya sauwak'e" suka bata amsa a tak'aice.
"Minti biyu don Allah ina dawowa". Ta fad'a a lokacin da take mik'ewa tsaye.
A nutse take takawa zuwa b'angaren nasu, babu kowa a parlour, hakan yasa tayi knocking k'ofar bedroom d'in khaleefa, wanda a dai dai wannan lokacin yana zaune gefen gadon shi ya had'a kanshi da gwiwa, ya rasa abinda yake mishi dad'i a duniya gaba d'aya, ga yawan fad'uwa da gaban shi yake yi.
Jin kamar ana tab'a k'ofar shi, sai ya tashi da sauri, instead of ya futo yaga me k'ok'arin shigowa, sai ya d'au towel ya fad'a bathroom da mugun sauri.
Koda auntie taga bashi da niyyar bud'ewa, tura k'ofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama da murya k'asa k'asa, babu kowa a ciki, sai wayoyin shi zube a gefen bed, d'akin duk a hargitse ya futo da rabin kayan shi ya jibge saman bed d'in.
K'arar ruwa da taji ya tabbatar mata wanka yake yi, saita sauƙe b'oyayyen ajiyar zuciya ta koma da baya ta futa.
Kamar zata huce, saita tuna da Ayman yau ko gaisheta baije ba, hakan yasa shima ta buga mishi k'ofa kafun ta shiga, babu kowa a ciki, sai dai d'akin neat dashi, shedar me aikin nan tayi aikinta tuntuni a ciki,,,, batayi tunanin bai kwana a gidan ba, shiyasa hankalinta kwance taci gaba da harkokinta, duk da a k'asan ranta tana tunanin abinda ya hana shi zuwa ya gaisheta yau
★★★K'arfe goma da mintuna biyar, khaleefa yana zaune gefen gadon shi k'afar shi d'aya a k'asa, d'aya kuma a saman gadon, yayi maseefar kyau cikin shadda sky blue, (D'aya daga cikin kayan da Dad ya d'inka musu ne, wannan ita ce kusan babbar riga da tazo da malum malum a duk cikin kayan nasu, basu tab'a sasu ba shida Ahmad saboda sun barsu cikin kayan da zasuyi amfani dashi a bikin Ahmad).
Hularshi brown, haka takalmin shima, tsintsiyar hannun shi d'aure da agogon fata da kallo d'aya zai tambara maka kud'in shi, wayarshi rik'e a hannun shi ya zubawa d'aya daga hotunan birthday d'inta ido, a zahiri idanun shi suna kallon tane, amma ta cikin zuciyarshi sam ba ita yake tunani ba a lokacin, tunanin shi gaba d'aya ya karkata ne ga Ayman da tunanin abinda yake faruwa cikin rayuwarshi, sannan ina ya tafi ya barshi shi d'aya a rana irin wannan, koda ba auren gaske bane zaiyi ai ya kamata ya kasance tare dashi a gefenshi.
Sai ya ajiye wayar gefe ya sake kwantar da kanshi jikin fuskar gadon da yake zaune, zuciyarshi na k'una da suya a duk lokacin daya tuna wani abu da yake shirin faruwa dashi nan da mintuna k'alilan.
Sallama yaji da muryoyi kamar nasu Ahmad, bai motsa ba saboda yana zaton ko gizo ne kunnuwan shi suke yi mishi.
Amma jin muryoyin na k'ara kusanto d'akin da yake ciki, sai ya bud'e idanun shi da har sun fara sauya launi ya zubawa k'ofar shigowa. Da d'aya da d'aya suka fara shigowa, su kusan biyar duk sanye da shadda mabanbantan kaloli. Kai da ganin su zakasan matasan y'an boko ne da suka k'oshi da ilimin addini dana zamani, wayayyu da yanayin mu'amular su da mutane ya bayyana wayewar su. "Ango! Ango!!" Ahmad ya fad'a bayan ya hard'e hannuwan shi a k'irji yana kallon khaleefan, bai iya ce musu komai ba, sai hannu daya dinga basu yana gaisawa dasu.
Kayan kan gadon shi ya janye gefe don su samu gurin da zasu zauna.
Da kanshi ya tafi parlour ya kawo musu drinks masu sanyi. Suka k'ara gaisawa sai zolayarshi suke "Ashe wai duk zai riga su shiga daga ciki?".
"Yae da wannan beb d'in za'ayi ne ta makaranta..?" Wani cikin su ya tambayeshi bayan Muhammad ya jefa mishi tashi tambayar,,, bai iya ce musu kanzil ba sai Ahmad da yake jefawa kallon tuhuma, don shi babu wanda ya gayyata cikin su.
Tuntuni Ahmad ya gane abinda yake nufi amma sai ya basar don abinda khaleefan yake so sam ba mai yiwuwa bane, ko a tarihin iyaye da kakanni baiji wani tarihi makamancin wannan ba, dad'in dad'awa kuma a jiya auntie tayi mishi bayanin komai yadda ya kamata.
Kusan Ahmad ne dasu Muhammad sukaita hirar su amma babu khaleefa da ya raba hankalin shi gida da yawa.
Kiran auntie ya alamta mishi lokacin tafiya wajen d'aurin aure yayi, sai ya turawa Ahmad gajeren sak'o kamar haka, "ka tattaro su lokaci yayi da zamu tafi......". Ahmad ya kalle shi bayan gama duba text d'in, yana tsaye still fuskarshi kadaran kadahan, kamar bashi za'a d'aurawa aure nan da lokaci k'alilan ba.
Ahmad ne ya fad'a musu lokacin tafiya wajen d'aurin aure yayi, aikuwa wani cikin su ya dinga yiwa Ahmad tsiya, wai shine bakin khaleefa da komai shi yake fad'a ba khaleefan ba, wannan ai wakilcine me wahala ya baka, yanzu ba don Allah yasa ka tuna da cards d'in mu daka karb'a a hannun shi ka tafi ba, daga baya kazo kana kiran mu a waya d'aya bayan d'aya na, da baza musan ya d'aura aure ba ma wannan mutumin.
Muhammad yace, "aikuwa fa".
Tare suka jero kowa da abinda yake fad'a a cikin su, ko yanzu kafun ya futa saida ya k'ara duba d'akin Ayman ya ganshi wayam. Jikin shi a mugun sanyaye yaci gaba da jan k'afa har zuwa harabar gidan. Da motar shi da wadda Muhammad yazo a ciki sukayi amfani wajen tafiya gurin d'aurin aure.
★★★★A dai dai wannan lokaci raihana tana zaune sanye da doguwar rigar shadda fara, da akayi mata aiki da golden zare da stones, ta yafa wadataccen gyale da takalminta da jaka match da kayanta.
Fuskarta ba hayaniya light make up ne shima da kyar ta yarda akayi mata shi, tana zaune a sitting room k'awayenta kewaye da ita suna ta zolayarta, kamar yadda yake dabi'ar da yawa daga y'an matan amarya, yayinda ita take zaune kamar an dasata, gaba d'aya ruhinta da zuciyarta basa tare dasu a dai wannan lokacin.
A can cikin gida kuwa ummie na hango da kafatanin yaranta har al'ameen sunyi ankon shadda butter milk, a cikin su Salma ce kawai tayi kwalliya sai k'anwar ummie k'aramar su, sun gama aikin gidan tuni, abinci kuwa dama aikin shi ta bayar, an gama tunda jimawa an kammale shi cikin coolers, gidan cike yake dam da mutane, sai shiga ake ana futa. Abinda y'an uwan Abba suka jima basuyi ba wato shigo mata a lokacin da ake wata sabga, shi sukayi yau, don kuwa zugarsu guda har da innah da sauran jama'ar gidanta suka zo, so suke suga kwal uwar daka, da suka tara jama'a haka,,, dawa zasu d'aurawa yarinyar aure, bayan ance wancen ya fasa.
Wata yayar ummie ce taga shigowarsu, ta taho da hanzarinta tana yi musu sannu da zuwa, ko amsawa innah batayi ba tace, "Ina ita ruqayyahn take? Ko kuwa ita ta turo ki ki tarye ni saboda gata isashshiya ban kai matsayin da zata zo ta bani masauki ba.....".
"Haba Innah akwai mutane fa y'an biki kada ki tada hatsaniya a gidan nan don Allah...." ziyada ce me yi mata wannan maganar k'asa k'asa.
Aikuwa ta daka mata tsawa, "rufe mun baki ni.... Lusara da bata san ciwon uwarta ba...".
Dole taja bakinta ta tsuke, aikuwa taci gaba da hargagi da kwala kiran ruqayyah! Ruqayyah!!
Da gudu gudu sauri sauri ummie ta katse abinda takeyi ta taho gurinta.
"Sannu da zuwa innah", ta fad'a da ladabi, da kanta ta shiga parlour ta tashi na gurin tayi musu iso zuwa ciki.
Tana bambami tana komai ta shiga ta zauna, su umma salaha ma aka shiga ita da y'arta ana ta rarraba idanu.
Cooler guda da lemuka ummie tasa aka kawo musu duk don ta toshe mata baki kada tayi mata irin tijarar data saba cikin mutane.
"Ita magajiyar bak'in halinki ba zata zo ta gaishe niba?". Innah ta tambaya, a lokacin ummie har ta kai k'ofa zata futa.
Ummie ta gane wadda take nufi, don haka tace, "Bari naje na turo miki ita". Ta futa jiki na b'ari. Tab'e baki innah tayi, ziyada kuma tabi bayan ruqayyah da kallo cike da tausayinta.
Raihana tana zaune ummie ta shigo da sallama, duk y'an matan suka amsa mata har suna yi mata sannu da aiki, saboda tun cikin dare data farka bata sake kwanciya bacci ba, "ku raka ta taje ta gaishe da innah". Abinda ta fad'a kenan ta futa.
Akaci sa'a Salma tana gurin, aikuwa ummie na futa salma tace su bari tana zuwa, Nemo inda hajiya innah take tayi, taje suka gaisa ta fad'a mata raihana tana da ciwo a k'afarta da kyar take iya taka k'afar, shiyasa ba zata samu zuwa gaisuwar ba,,,,,, salati Inna ta saki hadda tafa hannuwa, "wato ke kece marar kunyar da ruqayyah ta turo tayi mun diban albarka....." Sai ta mik'e tsaye, "Ina ita raihanatun take?". Salma bako d'arrrrr tace, "Tana sitting room". Aikuwa ta d'auki k'afafu bushur bushur tayi gaba wasu ciki na take mata baya.
A dai dai k'ofar shiga sitting room d'in ta tsaya turus ganin ana shigo da akwatuna daga k'ofar waje, "wannan kuma daga Ina?" Ta fad'a tana kallon matasan yaran, "cewa akayi mu shigo dasu nan". Suka bata amsa.
"Ku biyo ni" ta fad'a tana juyawa inda ta futo, "dama mune bamu ga lefen ba, saboda tana bak'in cikin kada ta bamu zannuwan mu da aka saka da sunan mu".
Aiko aka dinga jibge akwatuna a parlour, ita dai umma salaha sai binsu da kallon mamaki take, don sam wad'annan akwatuna basuyi kama da wanda tazo ta gani ba kwanaki, ga k'arin mamakinta, suna kirge saida aka shigo da akwatu goma sha hud'u ciff.
Sai kuma aka shiga kallon kallo tsakanin Inna da y'an majalisarta.
A can k'ofar gida kuwa jama'a ne mak'il y'an d'aurin aure, duk da auren a masallacin anguwar za'a d'aura, amma anan k'ofar gidan alhaji salees za'a had'u,
Koda suka Isa masallaci Abba abubakar shiya bada auren raihana ga malam da wani abokin shi, su kuma suka damk'a sadakinta a hannun Abba Abubakar da tunda yazo yake ta mamakin sauye sauyen da aka samu, amma bai kai ga tambaya ba saboda komai yana buk'atar nutsuwa.
A wannan rana ta juma'ah d'aruruwan mutane suka shaida d'aurin auren Raihanatu salees Abdallah da angonta Abdallah Suraj Abdallah tofa akan sadaki naira dubu d'ari biyu da mukullin mota lakadan ba ajalan ba.
Nan fa guri ya sake hargitsewa