Showing 135001 words to 138000 words out of 288773 words

Chapter 46 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1127

dalilin rashin lafiya da tasa khaleefa kwana tare dashi a nan ba da zuwa yanzu yasan wani zancen ake ba wannan ba.
Sai yaja k'ak'k'arfar ajiyar zuciya tare dasa k'arfi yayi facali da wannan tunanin daga cikin zuciyarshi.
Khaleefa yana daga inda yake amma kusan tunani ne fal kwanyarshi, abubuwa da yawa yake tunani game da Ayman da nuriyyah y'ar mammie k'awar auntie. Yana son yiwa Ayman maganar amma har yanzu bai samu nutsuwar da zai tunkare shi da zance irin wannan ba, tunda komai da muhallin shi. Amma fa a zuciyarshi yana yabawa jarumtar shi da k'arfin halin shi ainun. Kuma tun can dama Ayman yana da dauriyar ciwo.

★★★★★

Kamar yadda raihana ta kwana ba tayi bacci ba, haka auntie ma baccinta rabi da rabi ya kasance, mintuna k'alilan sai ta kira khaleefa taji yanayin jikin Ayman har zuwa lokacin da tayi sallar asubah. Ko data idar kitchen ta shiga direct ta fara had'a sauk'ak'k'en abinci da patient zai iya ci.
Tana cikin aikin mama haleema ta shigo, ganin bata da wani kuzari aikin ma da k'arfin zuciya takeyi, saita taimaka mata suke aikin tare, saida suka kammala ta had'a tea mai zafi tasha, rabonta da abinci harta manta ko ruwa ba zata iya tuna when last tasha ba.
Daga nan wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga tayi rolling da gyalenta, wayarta kawai ta d'auka da Mukullin motar ta ta futo a dai dai lokacin Ahmad ya shigo. Saida ya tsaya suka gaisa har ya k'ara kwantar mata da hankali akan ciwon Ayman sannan ya huce ciki don ya watsa ruwa ya sake komawa.
kan kujera auntie taci gaba da zama, yayinda Mama haleema take ta aikin gyaran parlon, "ko raihanatu ta tashi bacci kuwa?". Auntie ta tambaya
Mama haleema tace, "Bari na duba miki ita....." Ta fad'a tana nufar d'akin da aka sauki raihanan jiya, bata shiga ba saida ta kwad'a sallama har biyu, a lokacin ta kwanta kenan taji sallamar mama haleema, saita mik'e zaune tana amsa mata,
Koda ta shiga gaisheta raihana tayi, ta amsa tana tambayar lafiyarta.
"Dama auntie ce tace nazo na duba ko kin tashi?".
Tana jin abinda ta fad'a saita sauko gaba d'aya daga kan gadon, ta tambayi mama haleema '
"tana Ina?"
"Tana parlour" ta amsa mata
Kusan tare suka futo mama haleema a gaba ita tana bin bayanta. Auntie tana ganinta ta fad'ad'a fara'ar fuskarta. A k'asan carpet ta zauna ta fara gaishe da auntien cikin girmamawa, ta amsa tana tambayarta bak'unta. Tayi murmushi kanta a k'asa, tana son tambayar auntie meya samu Yaya Ayman akace mata yana asibiti ba lafiya amma ta kasa saboda nauyinta da take ji.
Surayyah kam gyara zama tayi ta fara magana da fad'in, "kinzo kin same mu a hargitse raihana, khaleefan ma can ya kwana a asibiti tare da Ayman, amma alhamdulillah khaleefa yace mun jikin shi da sauk'i har ma ya tashi yayi sallah da safen nan". Tunda ta fara magana raihana ta zuba mata ido kurum tana kallonta gabanta yana tsananta fad'uwa, da kyar ta harhad'a kalmomin bakinta tace, "yanzu yana can asibitin shi Yaya Ayman d'in?".
"Eh amma jikin da sauk'i sosai khaleefa ya fad'a mun.... Duk da nima yanzu zanje gurin shi, ga breakfast nan ki daure ki karya kumallo sai kije kiyi wanka".
D'an Jim tayi ganin har Auntie ta mik'e zata tafi sai tace, "Auntie zan biki naga jikin nashi". Shiru auntie tayi kafun tace, "jikin shi da sauk'i ki kwantar da hankalin ki, anjima kad'an y'an uwanki zasu zo kada mu tafi Kuma suzo su tarar bakya nan...".
Mik'ewa tsaye tayi tace, "ba damuwa koda sunzo zasu jirani....". Auntie ganin da gaske take bintan zatayi saita koma ta zauna, "tom jeki shirya amma fa ki tabbatar kinyi break...." Kai ta gyad'a mata ta nufi hanyar futa daga side d'in duka.
K'asa da minti talatin tayi wanka tayi brush da sababbin kayan wankan data gani a bathroom d'inta.
Ta shirya cikin wata atamfarta sabuwa d'aya daga cikin kayan da Abba ya d'inka mata sababbi da bata tab'a sakawa ba. Riga da zani ne d'inkin, saita zura k'aton hijab daya saukar mata har k'asa tasa takalmi ta futo a gurguje bayan ta rufe k'ofar parlon. Tana zaune inda ta barta tana amsa waya, bata tsaya gurinta ba ta nufi dinning inda mama haleema ta jera kayan abincin. Tea ta had'a mai zafi tasha, ta d'anci chips kad'an ta tashi.
"Gaskiya ban yarda da wannan karin ba....". Auntie ta fad'a tana kallonta, murmushi tayi cikin sanyin muryarta tace, "Allah na k'oshi alhamdulillah".
"Tohm na yarda muje, ita ta d'auki basket d'in suka yiwa mama haleema sallama suka futa.

*******Hajiya tafeeda zaune da safiyar ranar juma'ah a katafaren parlonta tana kallon labaran safe imran ya sauko sanye da jallabiyyah fara, gaba d'aya ya rame yayi duhu kamar bashi ba, tunda abun nan ya faru har yanzu bashi da wata cikakkiyar lafiya ko nutsuwa, gaba d'aya a gidan an daina ganin walwalarshi kamar ba wannan ma'abocin faram faram da barkwancin ba. A gefen d'aya daga kujerun da suka yiwa parlon k'awanya ya zauna, idonshi na kallon wani b'angare na d'akin yace, "gani Mom ance kina son ganina...".
Kallon shi tayi na wasu sakanni sannan ta tab'e baki tace, "yanzu fisabilillah Imran haka kurum zaka k'untatawa rayuwarka ka kwarzabi kanka ba gaira ba sabab da tunanin banza da wofi?, raihana ce tuni anyi zancenta an gama ta zama tarihi, ka k'addarawa ranka ma baka tab'a sanin wata mai kama da ita ba a duniya gaba d'aya..... Ga matanan tururu a gari sai wadda ka zab'a fa, wallahi in da zaka bi ta tawa da saika riga ta yin aure ma don taga tabbacin bata gabanka kuma ajinka yana nesa da nata".
Tunda ta fara magana Imran bai nuna ma alamun yana sauraronta ba har ta gama, wayarshi dake rik'e a hannun shi ya bincika ya duba hoton invitation card da aka mishi sending ta wattsapp jiya ya nuna mata.
Karb'a tayi tana dubawa kafun zuwa can ta tambaye shi, "abokin ka Abdallah zata aura kenan? Oho dai aiko banza Abdallah bai kai mahaifin ka kud'i da suna ba,,,,".
Imran cike da takaicin halayen mahaifiyar shi a wannan karon yace, "ba Abdallah da kika sani bane,,,,, wannan yayan Ayman ne d'an doctor surayyah,,,,, finally burin ki bai cika ba don gashi raihana ta rigani aure, da mijin daya zarce tsara, miji na nunawa sa'a,,,, da haka nake rok'on ki don girman Allah ki barni inji da jinyar rashin mace ta gari ma'abociyar addini da kiyaye dokokin ubangijinta irin raihana da nayi.... Mom duk yadda zanyi miki bayanin raihana ba zaki tab'a ganewa ba, don ta huce kafatanin tunanin ki.... Sai abu na k'arshe da na manta ban fad'a miki ba, munyi magana da Abba last week zan koma can Lagos na kula da harkokin kasuwancin shi na can har zuwa wani lokaci da zan gama jinyar zuciyata, and kibar son k'ak'abamun kowacce yarinya don ban shirya aure yanzu ba.".
Ya k'arasa maganar shi tare da mik'ewa ya haura stairs inda ya futo. Sakatoto hajiya tafeeda ta tsaya tana kallon shi kamar wata sakarai har ya huce.
Wanene khaleefa kuma d'an Doctor surayyah da Imran yake magana akai? Ba dai surayyah data sani k'awar sameera ba?


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page thirty eight3️⃣8️⃣


Kasa zama hajiya tafeeda tayi a lokacin sai safa da marwa kawai tsakanin farkon parlonta zuwa k'arshe, ta kira sameera kusan sau biyar amma ba tayi picking ba, so take taji tabbacin abinda Imran ya fad'a mata yanzun daga gareta don tasan dole zata sani.
Tana ta tsaiwa har ta gaji ta samu guri ta zauna.
Can jimawa sameera ta biyo kiran, tana d'agawa ta fara magana a hargitse, "Wai kinsan abinda naji kuwa? Tukunna ma ina kika shiga nayita neman no ki bana samu?". Hajiya tafeeda ce meyin wannan maganar a rikice.
Ta b'angaren sameera ma hankalinta a tashe ta fara bata amsa, "Humm bana auren khaleefa da raihana ba? Naji yanzun nan daga bakin haeydar wai ashe har d'aurin auren yaje yanzun nan ya dawo ma, ni dama tunda ta bani catin mother's day da akayi jiya nasan akwai wata a k'asa, in ba haka ba me zai had'a surayyah da ruqayyah matar salees? lallai surayyah ta d'au zafi dani da yawa kina gani fa komai nata ta tureni gefe ita kad'ai take harkokinta.....".
Tab'e baki hajiya tafeeda tayi, cikin kyashi tace, "ai wallahi naso a fara yin auren Imran da shaheeda, banso raihana ta riga shi yin aure ba, koda yake ma to meye Allah na tuba astagfirullah yaran da basu da asali.....".
"Kinga dakata don Allah! Kinsan abinda yake had'a mu dake kenan tun farko tafeeda, kiyi magana akan abinda ya shafe ki kad'ai ba ruwanki da surayyah da yaranta don itama ba damuwa tayi da al'amuran kiba....". Sameera ce meyin wannan maganar cikin d'an fusata.
Ita kam sake tab'e baki tayi kamar tana ganinta tace, "oho dai ku kuka sani keda ita, anjima in kina nan Ina so zan shigo don an samu matsaya a maganar da muka fara yi sake Imran yana son b'allo mun ruwa".
"Anya kuwa Ina nan? Da Ina son zanje asibiti duba jikin Ayman, ance ana gama d'aura aure ya yanke jiki ya fad'i akayi hospital dashi baya numfashi....". Sameera ta bata amsa.
Tafeeda tace, "Toh sai dai gobe kenan na shigo ko?"..
Sameera tace, "eh toh Allah ya kaimu". Daga haka sukayi sallama kowa ta ajiye wayarta.

*******A zaune take cikin k'aton d'akinta ita d'aya, tunda Mamie ta karb'e wayarta hankalinta ya kasa kwanciya, gani take kamar akwai abinda mammien take b'oye mata, banda haka ya zata sauya mata rana tsaka harda tsauraran matakan tsaro, daga makaranta sai gida komai ma ta hana ta zuwa, Ayman kuwa tace duk ranar data ari wayar wata k'awa ta kira shi Allah ya Isa bata yafe mata ba.
Gaba d'aya ta maida kanta sukuku ba wani armashi bare jin dad'i.
Yau kam ma tunda ta tashi taji bata jin dad'in jikinta ko makarantar bata jin zuwa saita nad'e kan katifarta abinta, duk yadda heedaya ta dinga zargadilar kiranta tazo ta karya k'in tashi tayi, a k'arshe ma data takura ta saita dinga mata maseefa don dole ta hak'ura ta barta.
Har ta fara bacci mammie ta shigo da kanta d'akin, jin kamar muryar mammie saita tashi zaune tana kallonta.
A shirye take da alamu futa ma zatayi, a gefen katifar ta zauna tare da zuba mata ido tana kallonta.
"Anya kin d'auki hanyar da zata b'ulle miki kuwa Nooriyyah? Yanzu saboda kawai na hana duk wata hanya da zaki had'u ko kiyi magana da Ayman shine kika takura rayuwarki haka kamar shi yayi silarki zuwa duniya?".
K'asa tayi da kanta murya a sanyaye tace, "ba haka bane mammie kawai yau na tashi bana jin dad'in jikina ne".
Kallon d'akin tayi tace, "toh ai shikenan, yanzu ki tashi ki shirya kizo ki karya zaki rakani wata y'ar anguwa, amma fa idan zaki iya".
Ba don kar tayi mata musu ba da tace kawai ta d'auki shaheeda ta rakata, don ita kam bata son futa ko nan da can.
"Kinyi shiru ko bazaki bane?". Mammie ta tambayeta.
Saita girgiza kai da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa don ta sauka daga saman katifar.
Cike da tausayinta ta bita da kallo har ta shige cikin bathroom ta rufo k'ofa, Allah yasan tafi kowa son auren Nur da Ayman, sai dai kash surayyah tana shirin ruguza da lalata duk wani burget nata, taso ace ta nemo dangin tsohon mijinta anyi sulhu komai yazo k'arshe ata silar auren Ayman da nuriyyah,,,, kamar yadda taso ta zama silar gyara duk wata b'araka dake tsakanin su,, sai dai kash tun ba'aje ko'ina ba alamu sun nuna hak'arta bazai tab'a cimma ruwa ba ta hanyar data biyo, tunda gashi har mutanen gari wagairahun da basu tab'a doguwar mu'amula da ita ba sunyi mata abinda ita data had'a rabin rayuwarta tana binta da alkhairy tana wahalta mata ta kasa yi mata, tabbas mijinta ya fad'i gaskiya da yace, ko buta batayi tsiran komai ba ai tayi na ruwan alwala, ya kamata ace tayi dogon tunani kafun yanke hukunci.... Ajiyar zuciya ta sauke ta mik'e tsaye jikinta a sanyaye ta futa daga d'akin, a ranta tana fatan komai ya huce tsakaninta da surayyah a wannan karon idan ta tunkareta.
Cikin mintuna k'alilan Nur ta shirya cikin doguwar rigar material milk da Ash, ya haskata sosai tayi kyau tamkar ba itace kwance yanzu hargitsai hargitsai ba. Saida ta tuttura abinci sannan suka d'auki hanya ita da mamie ko heedaya gurin shaheeda aka barta saboda a yau bata son wanzuwarta a gurin don zata damu mutane da maganarta mara amfani ne.

★★★★A parking lot surayyah ta Parker motarta ta futo, raihana ma futowa tayi ta bud'e k'ofar baya ta ciro basket d'in da aka shirya abincin karin a ciki.
Murmushi Auntie tayi tana kallonta tace, "sannu da k'ok'ari". Cikin jin nauyi tayi k'asa da kanta don ita bata ga wani k'ok'ari da tayi ba, abincin daba ita ta dafa ba sai dako ya zama aiki.
Tare suka shiga ward d'in, Auntie a gaba raihana tana bin bayanta.
Ayman yana zaune kan gadon da aka kwantar dashi, khaleefa kuma tsaye a gefe yana sauraron bayanin da Ayman yake rattabowa likitan da yake tsaye gaban shi suka turo k'ofar suka shigo da sallama. Kusan a tare su duka ukun suka juya suna kallon su, Ayman da likita suka amsa sallamar su a fili, yayinda khaleefa ya amsa su a zuciyarshi.
Ko a yanzu wani irin yanayi Ayman yaji a lokacin da idanun shi suka sauka akan raihana da take tukunta cikin nutsuwar data zama jini a jikinta.
Khaleefa dama kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi, a baya da inda suke ta tsaya ta fara gaishe su, a ciki likitan ne kawai ya amsawa, ganin haka sai taja bakinta ta tsuke, dama ta manta ne amma Ayman akwai tsohuwar gaba a tsakanin su dashi, gabar da har yau batasan abinda ya assasa taba, shi kuma khaleefa har yanzu bak'o ne a gurinta.

Surayyah ta gaisa da likitan tana tambayarshi jikin Ayman, yace, "ah jiki da sauk'i hajiya anjima kad'an ma zaku iya tafiya dashi gida kamar yadda yake so, sai dai matsala d'aya ce koda ya koma gidan muddin bai bi sharud'd'an da zamu gindaya mishi ba toh fa za'a dawo dashi ranga_ranga fiye da yadda aka kawo shi da farko, Saboda kamar yadda nayi muku bayani rashin cin abinci ya tashi mishi ulcer, ta had'u da stress da deffresion sukayi sanadiyya har ya yanke jiki ya fad'i k'asa a sume.... Duk da alhamdulillah yanzu mun shawo kan komai amma fa dole saiya cire damuwar da take ranshi ko kuna ganin shi lafiyar Allah kamar yadda yake a baya".
Shiru tayi tana nazarin maganganun likitan kafun ta nisa tace, "alright insha Allah zai kiyaye".
Saiya mik'awa khaleefa takardar magungunan daya rubuta yace, "malam kai kuma kayi k'ok'arin samo mana wannan".
Ya amsa tare da matsawa baya, a karo na biyu idanun shi suka sake sauka akan raihana da take tsaye still hannunta rik'e da basket. D'auke kanshi yayi ya nemu guri nesa da inda take ya zauna..... Damuwa! Damuwa!! Damuwa!!! Ya rasa wacce irin damuwa ce take bibiyar rayuwar Ayman da har take barazanar raba su dashi a wannan duniyar, gashi yace sam ba matsalar Nur da mammie bace damuwarshi a halin yanzu.
Likitan ma sallama yayiwa auntie ya futa bayan ya sake gargad'inta akan a kula dashan magungunan shi a k'a'ida.
Juyawa tayi tana kallon raihana tace, "a'a raihanatu kamar wata bak'uwa kike ta tsayuwa salon kisa k'afafun ki su k'age, kinga zauna a can ki zuba musu abincin don nasan khaleefa ma ko da safe jiya bai karya ba haka yake ta zaune da yunwa". Auntie ta k'arasa maganar tana zama tare da kallon khaleefa daya had'a kanshi da gwiwa.
Kamar yadda auntie ta mata umarni zama tayi a nesa dasu ta fara had'a musu tea me zafi a cups, Ayman ta fara kaiwa, da sanyin muryarta tace,. "sannu Yaya Ayman ya jikin naka?", d'agowa yayi ya kalleta kamar ba zaice mata komai ba sai kuma yayi k'asa da kanshi yace, "da sauki" tace, "Allah ya k'ara sauk'i". Bai kuma amsa taba saboda ruwan hawaye da suka cika a idanun shi, shayin ma kamar wanda zai tab'a wuta haka ya karb'a a d'arare, ganinta ba k'aramin dagula mishi lissafi yake ba.
Ajiyar zuciya ta sauke a b'oye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login