Showing 261001 words to 264000 words out of 288773 words
Chapter 88 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
a idon ku tun kafun na mutu.....".
Khaleefa kasa magana yayi sai Ayman ne ya bashi amsa da, "tana can cikin kewarka......Amma Bana tunanin ta rik'e ka a zuciyarta don har gobe ba tayi aure ba, watak'ila saboda zaton zaku had'u watarana ku maida auren ku...".
"Ni kuma bana tunanin haka.....". Khaleefa ya fad'a ba tare daya shirya ba. Kallon shi mahaifin shi yayi sai yaga shima shi yake kallo.
"Meyasa kace haka Abbana?".
"Saboda kayi mata abinda bata tab'a zato ba, a kaf cikin tarihin soyayyarku bata d'auka zaka iya rabuwa da ita ba, ta tsane ka tsana mai tsanani shiyasa bayan ta kashe ka a baki ta k'ara da binne duk wani abu daya shafe ka, har gobe Auntie tana kallon ka matsayin....." Sai yayi k'asa da kanshi saboda kalmar tayi mishi tsauri wajen fad'a, "am sorry but kaima bai kamata kayi saurin yanke igiyar auren kuba, at least ya kamata ka d'aga mata k'afa kafun yanke mata hukunci......".
Suraj dafa kafad'ar yaron yayi yana kallon shi da idanun shi da suka tara ruwan hawaye..... Kafun yayi magana da raunatacciyar murya, "k'addara! Shine abinda ya faru tsakanina da mahaifiyarku....". Sai ya share hawayen shi, "ku tashi ku kwanta haka saboda dare ya fara nisa, zuwa gobe zaku bani labarin yadda kuka rayu tare da Auntien...".
Duk mik'ewa sukayi da sanyin jiki suna mishi murmushin yak'e, shi ya fara haura stairs suma suka bi bayan shi, sai dai har sun fara tafiya khaleefa yace yana zuwa ya koma da baya. Ayman yayi murmushi yaci gaba da tafiya, sai dai shima har ya shiga babban bedroom d'in ya futo ya tsaya ta balcony yana kallon inda twin d'inshi ya nufa, kafun ya biyo bayan shi cikin sand'a har zuwa part d'in hajiya momma, ya tsaya daga inda zai iya gano shi.
Shi kuwa khaleefa raihana yake nema ido rufe, don a d'an zaman da sukayi ba tare ba kewarta ta cika shi fal, and yana son had'uwa da ita ya jaddada godiyar shi gare ta don ta gama yi mishi komai a rayuwa.
Babu kowa cikin gidan sai wata matashiyar yarinya da yaga ta fara saukowa daga stairs rik'e da system. Tana ganin shi ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "Yayaa d'an biyu kana neman wani abu ne".
Murmushi yayi jin sunan data bashi yace, "amm ina neman wata cikin y'an matan da muka zo dasu".
Shiru tayi tana nazari kafun can tace, "na d'auka ai d'aya matar aure ce dai kamar akace ko, d'aya kuma budurwa....". "Yauwa to matar auren don Allah....".
Yarinyar tace, "okay ai tana tare da hajiya momma, na kira maka ita?".
"Aikuwa da kin taimaka". Ya fad'a yana murmushi.
Itama murmushin tayi ta koma da baya.
Raihana tana tare da suhaana suna ta hira a b'angaren momma cikin d'aya daga d'akunan baccinta yarinyar ta shigo ta fad'a mata wani cikin y'an biyu yana nemanta. A lokacin rikicewa tayi a zuciyarta tana tunanin khaleefa ne ko kuwa Ayman? Tasan dai Ayman ba zai turo kiran taba inba wani muhimmin al'amari ne ya taso ba..... A lokacin sanye take da doguwar rigar bacci mai kauri da santsi milk, kanta zagaye da d'an k'aramin hijab daya sauka zuwa kafad'un ta, mik'ewa tayi ta fara neman babban gyale ko hijab, sai a lokacin suhaana ta fahimci abinda ake ciki ta tambayi yarinyar mai suna ihsan da harshen turanci, "wa yake nemanta". Yarinyar ta mayar mata da amsa, "Eh Ina ga ko mijin tane cikin twins ne dai ni da yake ba gane su nake yi ba".
Da sauri suhaana ta fizge hijab d'in da sukayi sallah dashi d'azu da raihana ta lalubo zata saka tace, "mijin naki ma sai kin saka mishi hijab da tsohon daren nan? waye ma zai ganki gida kowa yayi bacci?".
"Don Allah ki bani.... Bansan fa wanda yake nema na ba, khaleefa nasan tuni yayi bacci maybe sai dai ko in Ayman ne.....". .
Suhaana ta sake b'oye hijabin tace, "ba wani Ayman da zai kira ki hajiya wanda ya kasa bacci saboda tunanin ki da kewar kine..... Don haka gwara ki tafi ma tunda wuri kafun ya gaji ya shigo neman ki da kanshi.
Masu iya magana suka ce fad'an da yafi k'arfin ka....... Duk yadda raihana taso suhaana ta bata hijabin hanata tayi, dole a k'arshe haka ta hak'ura ta futo da sand'a tana laluben inda zata hango mai kiran nata, don ihsan tuni tayi nata guri.
Khaleefa tunda ta futo ya ganta sai dai fahimtar da yayi bata ganshi ba ya sashi ja baya yana ci gaba da kallonta har ta futo sosai. Kusan saida ya d'auke numfashi a lokacin daya ganta gaba d'aya cikin parlon, babu inda bai bincike da idanun shiba a jikinta kafun ya tafi slowly ya rungume ta ta baya.
A tsorace ta fara ture shi tana shirin kwalla k'ara, ya rufe mata baki da hannun shi ya fara mata magana cikin kunnenta, "kwantar da hankali, inba niba wa kike tunanin yake da zarrar aikata haka gare ki?.....". Saita dafe hannunta a k'irjin ta tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha tsere don bilhak'k'i ta tsora ta. Koda ya sake ta ma kasa tsayawa tayi da k'afarta yadda ya kamata, sai ya rik'e k'afad'un ta ya jingina ta da bango ya tokare ta da hannun shi duka biyu yana kallonta at the same time yana furzo mata hucin numfashin shi mai d'umi ta saman fuskarta. Kallon daya mata nauyi ga kusancin da suka samu ya fara bada wani yanayi na daban wa gangar jikinta da zuciyarta.
"Hak'ik'a kalmomin da zan fad'a da fatar baki sunyi kad'an su bayyana adadin yadda nake jinki cikin zuciyata kona d'auke ki, Raihana u mean a lot to me.... Ina matuk'ar alfahari dake da samun ki matsayin mataaa.....". Ya k'are zancen yana sake kusanta kanshi gare ta, tana son cewa a'a gare shi amma zuciyarta Eh take cewa, abun gaba d'aya ya zarce zato da tsammaninta, kafun ta gama rarrabe asalin abinda take ciki taji saukar hannun shi a bayanta, the next thing kuwa lips d'inshi ya sauka jikin nata cute lips d'in yana gogan shi.... Tana bud'e baki da nufin cewa wani abu ya k'arasa had'e bakin su guri d'aya.......
Ayman da yake kallon su yayi saurin juyawa ya d'aga hannun shi sama yana fad'in, "alhamdulillah! Alhamdulillah Allah!!.". Sai ya nufi hanyar futa a parlon, cikin sauri ya huce cikin d'akin shi da mabayyanin farin ciki.
Khaleefa kuwa wani irin tattausan kiss yake sake mata mai d'auke da ma'anoni da dama, cikin mantawa da inda suke bare kuskuren abinda yake yi ga matar da yake ik'irarin zai iya barwa d'an uwan tagwaitakar shi yake kissing d'inta passionately, bai barta ba saida ya tabbatar da tayi laushi, sak'on shi ya gama keta zuciyarta yayi male male da kaka gida sannan ya janye.... Ya zuba kwayar idon shi a fuskarta yana son lalubo kwayar idonta amma fafur ta hana mishi damar haka, don gam gam ta rufe idanunta hannunta dafe da bangon da take jingine k'irjinta yana up and down. For the first time da wani abu makanmancin wannan ya tab'a faruwa da ita..... Khaleefa daya tsare ta da ido murmushi yayi ya kira suna ta da gentle and cool voice, "Raihanatu". Bata iya amsawa ba kuma still bata yarda ta kalle shiba.
"Say something mana, ko you need more....". yayi tambayar yana yin shafo hannunta zuwa kafad'arta, ai bata bari ya k'arasa inda ya nufa ba ta rik'e hannun shi gam gam tace,, "please stop it....".
"Whyyy?". Ya tambayeta da murya can k'asa. Sai a yanzun ta kalle shi ta motsa lab'b'anta, "I don't like it....".
"Sure". Ya tambaye ta yana sake kallonta yana ji kamar su dawwama a haka.
"Ka bani hanya bacci nake ji, sannan wani zai iya ganin mu a haka kuma.... Kuma... Sai ayi tunanin wani abun daban...".
Wani murmushi mai kyau ne yayi escaping saman lips d'inshi yace, "Raihanatu kefa matata ce, waye zai ce wani abu don ya ganmu tare".
Narke mishi tayi ganin da gaske yau yana shirin juye mata zuwa wani mutum na daban tace, "Ni dai ka bani hanya,,, Allah bacci nake ji".
"Then give me something in return sai kiyi tafiyarki tunda bacci yafi miki hira da mijin ki dad'i".
"Ba haka bane, na gaji ne kawai". Ta fad'a a matuk'ar shagwob'e don da gaske ta gaji da tsaiwar haka.
"Ni kuma kinga ko kwana zamuyi a haka bazan tab'a gajiya ba..... Raihanatu zan iya b'ata iya tsawon rayuwata tare dake ba tare dana gaji ba a kowanne mataki na rayuwa, kamar ruwan sama mai sauka kamar da bakin kwarya, da tsayuwa cikin tsakiyar rana mai zafi over 40°C, zan jure yunwa da k'ishin ruwa ko halin rashin lafiya, raihanatu kallon fuskarki kad'ai zai bani dukkan farin cikin rayuwata, sauraron daddad'an sautin muryarki kuwa zai sanya mun nutsuwa marar iyaka ciki da bai.... Raihanatu ke haske ce mai yaye duhun dake cikin rayuwar Abdallah, na ganki cikin mafarkina tun ranar farko dana fara d'ora idona a kanki a lokacin da naje gidan iya.....".
Tunda ya fara magana raihana take kallon shi, lallai da ace ta fara bacci kiran shi ya risketa zata ce cikin mafarki duk haka take faruwa ba'a zahiri ba, wai itace yau khaleefa yake fad'awa duk wad'annan kalaman? abun al'ajabi.
Shiru ya sake biyo ba, shi ya shagala a kallonta ita kuma ta kasa kallon kwayar idonshi, gashi sunyi kusanci sosai don har yanzu hannun shi tokare yake da gefe gefen bangon da take jingine jiki.
Ja baya yayi yace, "na barki ki tafi ko?".
A hankali ta fara takawa, "ba zaki barmun abinda zan dinga tunawa dake ba duk tsawon dare...?". K'ara sauri tayi sannan ta waigo tace, "Saida safe kawai".
Murmushi yayi da yaso hanata ci gaba da tafiya Allah yasa tayi maza ta yak'i zuciyarta taci gaba da tafiyarta da sassarfa. Bai bar gurin ba har saida ya daina ganinta, ya juya ya fara haura stairs yana murmushi.
Itama lokacin data shiga suhaana tana kwance, ta d'auka bacci take, saita lallab'a ta kashe glove tayi kwanciyarta tana sakin murmushi mai kyau tana tariyo duk abinda ya faru mintuna biyu zuwa uku kafun yanzun.
"Allah sarki Soyayyah, ta karb'e ka ta saka farin ciki, akasin haka kuma ta kusa tura ka lahira". Maganar suhaana ta shiga dodon kunnen raihana, saita juya tana kallonta ta cikin duhun daya mamaye d'akin, murmushi tayi mata, itama ta mayar mata da martani, saita mik'e zaune tana kallonta ta jingina da fuskar gadon, "kamar kina son cewa wani abu?".
Murmushi suhaana ta sake yi, "Man yaci rabin lokaci, ya kamata ki kwanta zuwa da safe sai muyi magana kada mu k'arar miki da daren gaba d'aya".
Raihana tayi y'ar dariya tace, "Ni bana da matsala da bacci, akan abu mai muhimmanci ina iya k'arar da gaba d'aya dare ba tare dana rintsa ba".
Jinjina kai suhaana tayi, "banyi mamaki don matar aure kamar ki ta aikata haka ba, amma kada ki damu da safe zamuyi magana.....".
Dariya raihana tayi tace, "Allah ke ko?".
Itama suhaanar dariya tayi, haka kurum taji raihanan tayi mata tunda suka had'u, tana jimawa kafun ta sake da mutumin da bata sanshi ba sosai, amma ga raihana sai gashi zuciyarta ta aminta da ita a zaman rabin wuni da kwana d'aya kacal!
Ta b'angaren khaleefa baisha wahala wajen gano muhallin da twin d'inshi yake ba, Koda ya tura k'ofar ya shiga a makeken gadon d'akin ya hango mahaifin shi da Ayman suna bacci sadidan, saiya k'arasa ya rufe musu hasken d'akin ya kwanta a d'aya gefen mahaifin nasu suka sashi a tsakiya.
Sai dai gaba d'aya bacci yayi k'aura a idanun shi sai tunanin moments d'insu na yanzu yanzun nan, yana tuna komai step by step yana murmushi mai bayyana tsananin farin cikin da yake ciki. Yayi nisa a juye juye da tunanin matarshi kafun wani tunani ya fad'o ranshi..... Saiya mik'e zaune zumbur ya cusa hannun shi cikin sumar kanshi yana yamutsawa da tuhumar kanshi da zak'ewa cikin lamuran raihana, yayi over acting irin wanda bai tab'a yiba don a lokacin daya kusanceta mantawa yayi gaba d'aya da Ayman, Banda su biyu baya hasaso kowa a gefe, ita gundarinta yake gani a zuciyarshi tallin tal!
_wannan page sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin *JARUMAR UWA* Ina fatan kowanne team sun fara gane inda makamar su take...._.
May oll our dreams come true🤲happie juma'at Mubarak
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page seventy five 7️⃣5️⃣
Washe garin ranar suka had'a d'an kwarya kwaryar shagali na yiwa y'an biyu barka da dawowa gida, isu isu matasan yaran gidan suka shirya komai, babu wanda ya iya futa office cikin mutanen gidan rankatakaf. Khaleefa duk inda raihana tasa k'afarta zai bita da kallo gaban kowa ba tare da yasan ma yanayi ba, kaffa kaffa yake da ita da samarin gidan kamar ya tsame ta a cikin su, da Allah ya taimake shima ita d'in ba mai rawar kai da son shiga mutane bace, shiyasa ana jimawa ta zame jikinta ta koma gurin ammie (andal) tayi zamanta tare da ita suna ta hirar su har suhaana ta same su tare aka ci gaba da hirar har ita.
Kusan ta b'angaren Ayman ma abinda ya dinga faruwa kenan, bai samu salama ba saida suhaana tabar cikin su tabi bayan raihana. Ya fahimci wani matashi cikin yaran gidan gaba d'aya ya fara takura mata, don yana yawan ganin su suna magana lokaci bayan lokaci, daga k'arshe duk inda tayi saiya bita kamar wani jela. So yake ya samu damar da zaiyi magana da ita kafun wani ya riga shi amma baisan tayaya ba, don bai tab'a tsaida budurwa ba tunda yake. Ko Nur ba direct ya tunkareta ba su auntie ne suka gabatar dashi a gurinta, kuma dama suna gaisawa sosai musamman in tazo hutu gidan su.
Su kuwa yaran gidan kowa ya gabatar mishi da kanshi a gurin su, babu abinda yafi basu mamaki kamar ganin tulin familyn su amma suke rayuwa daga su sai mahaifiyarsu, ashe sun futo daga babban family da cikakken asali ake tayi musu gorin uba, kusan Ayman kasa jurewa yayi saida yayi kuka, wasu cikin yaran masu irin zuciyarshi na taya shi.
Bayan sun k'are budurin su suka samu zama da manyan iyayen su na gidan, aka tattauna dasu akan yadda za'a samu ganin surayyah cikin sauk'i don kowa cikin su a gidan yana son ganinta, Ayman ne ya basu shawarar kada kowa yaje cikin mutanen gidan, tafiyar ya kamata ta kasance ta mahaifin su da ammie, (doctor k'awarta kenan) sai khaleefa ya musu jagora don shine kad'ai yake iya fad'a mata gaskiya komai d'acinta, musamman a case irin wannan daya kamata a tsage gaskiya kowa ya karb'i laifin shi.
Da wannan shawara duk sukayi na'am aka ajiye maganar tafiyar zuwa nan da kwana ki biyu da zasu zo.
Suraj bayan ya koma part d'inshi number sauban ya lalubo ya tsurawa ido, tsawon lokaci rabon da su gaisa kota waya, sunyi rabuwa irin wadda ba ta yiwa kowa cikin su dad'i ba, amma bai tab'a goge lambar daga wayarshi ba, don cire no dai dai yake da cire duk wani abu na surayyah data tafi ta gadar mishi, su kuma gadon surayyah tamkar soyayyar surayya suke gare shi, soyayyar surayyah kuwa mahad'in rayuwar shine, babu ita tare dashi yana nufin ba ruhi a gangar jikin shi.
Sai yaja gwauron numfashi ya gwada dialling no yaji ko tana aiki har yanzu. Aikuwa sai gashi ta tafi, a lokacin sauban yana zaune a office yana aiki kiran ya riske shi, koda ya duba bai tabbatar da abinda idanun shi ke gani ba saida yasa medical glass d'inshi, "Suraj Abdallah kuma?". Ya fad'a a fili tare da picking call d'in, ya kara wayar a kunnen shi ba tare da yace komai ba, daga can Suraj ya mishi sallama, ya amsa shiru ya sake biyo baya kafun Suraj ya kuma tambayar lafiyar shi data iyalin shi.
Ya amsa kamar zaice ya fad'a mishi dalilin kiran direct, "dama kira nayi mu gaisa na kuma nemi yafiyarka".
"Ayyah Nagode amma komai daya faru ni ya huce a gurina tun lokacin".
"Toh Masha Allah! Sai dai ina son zan shigo cikin satittikan nan idan ba damuwa.....".
Sai a lokacin raunin sauban ya bayyana, yanayin shi ya sake sauyawa cikin k'arfin hali da dauriya yace, "kayi hak'uri amma ina ganin mubar maganar zuwan nan, ni da kaina zan neme ka inta kama".
Suraj yace, "Toh ba damuwa Nagode ma'asaalam".
Ya ajiye wayar a sanyaye tare da zare farin tabaran idon shi gefe, ya juyo da hoton ta da yake kan table d'inshi yana kallonta, tunda k'uruciyarta akayi hoton tana dariya da hak'oranta farare tas da suka bayyana a waje.....
Hoton ya d'auka ya sumbaci forehead d'inta yace, "I miss you dear sister".
Sai ya maida hoton gefe ya fara share ruwan hawayen