Showing 273001 words to 276000 words out of 288773 words

Chapter 92 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1070

duniya yaji a jikin shi jinin shi suna yawo a doron k'asa inda suke ne bai sani ba.
Bamu yarda ba har Allah ya kawo lokacin da yaran suka zo neman shi da kansu. Hak'ik'a surayyah munyi nadama munyi Allah wadai da abinda muka aikata miki na rashin fahimta da makircin shaid'aniya Aysha da suka shirya komai don kawai k'anwarta ta auri Suraj, lallai duk Inda gaskiya take bada jimawa ba take fallasa kanta, wannan shine dalilin da yasa mukayi hanzarin mayar da auren ku, kamar yadda yake fad'a ya tabbata ke kad'ai ce matarshi a duniya tunda bai tab'a karb'ar wata mace bayan ke ba.
Surayyah da tayi shiru mik'ewa tayi tsam bayan gama sauraron momma ta shige d'akinta da ba kowa ra rufe kanta.....

**** Raihana ta d'ago tana amsa sallamar khaleefa dake tsaye daga k'ofa, shikam k'arasa shiga yayi yaja stool na gaban mirrow ya zauna idon shi akanta. Tunda yake bai tab'a shigowa d'akinta ba sai yau, abinda su duka biyun suke ayyanawa cikin ransu.
Nauyin shine ya cikata ta fara gaishe sa daga inda take kishingid'e.
"Matar da take mantawa da mijinta inta samu mutane shine take gaishe sa kuma a bayan idon su?".
Kamar ta kyalesa sai kuma tace, "waye mijin?".
"Okay tambaya na kike ma?".
Bata kula saba duk da Yana da kyau ta dinga tuna mishi abinda yake mantawa dashi, "kinyi shiru kina jina kuma?".
"Bansan abinda kake son ji daga gare ni game da tambayar da kasan amsarta ba".
"Kamar ya kenan?". Ya sake tambaya.
Ganin abun nashi nayi ne saita dire k'afafun ta k'asa tace, "wasu lokutan sai ka bani mamaki kamar kana manta matsayin auren mu....".
Murmushi ne ya sub'uce saman fuskarshi har fararen hak'oran shi na bayyana, ya d'auki adadin wasu mintuna shiru kafun yace, "yanzu idan nace matar boge ta zama ta gaske nayi laifi?".
"Babba ma kuwa?". Ta fad'a kamar ba ita tayi maganar ba.
"Hakane?".
"Eh saboda zaka ruguza mata plan d'inta, burikanta....muradanta.... A k'arshe ka sata rusa alk'awarin data d'aukar ma wani mutum mai muhimmanci a gurinta, abun da bata tab'a yiba sab'a alk'awari".
Ya gano inda zancenta ya tafi kaf don haka saiya mik'e ya nufi hanyar futa daga d'akin, saida ya kai k'ofa sannan ya juyo ya kalleta, "zan shiga gurin su ummie mu gaisa anjima da yamma, idan zaki iya jerawa da mijin boge saina jira ki muje tare".
Bata kula shiba har ya k'arasa futa don batasan abinda zata ce dashi ba a wannan gab'ar. Ba don ta zurfafa tunani ba, ba zata d'auka ummie tata mahaifiyarta yake magana ba.

Suhaana kuwa saida ta tabbatar khaleefa ya futa sannan ta dawo gurin raihana suka d'an tab'a hira kafun su huce gurin mama haleema su kama mata aikin abincin dare.
Da yamma tasa suhaana tayi sabon shiri, itama ta shirya suka zauna jiran khaleefa don tasan halinsa yana ganin basu shirya ba zaiyi gaba abunsa. Cike da d'oki take zaman jiran shi zata ga ummienta.
Suna zaune a parlour suka shigo tare da Ayman da shigar manyan kaya iri d'aya.
Raihana ta sake jan gyalen kayanta ganin irin kallon gargad'in da khaleefa ke mata, duk da ita ta gyara gyalen ba don shiba sai don ta suturta jikinta gaban wanda ba muharraminta ba. Ayman kam tab'o khaleefa yayi, koda ya juyo saiya nuna mishi suhaana a fakaice yana shafo k'eyarshi. Khaleefa yace, "itace kenan?". Sai ya gyad'a mishi kai yana murmushi. Shima murmushin yayi yana ci gaba da kallon shigar gimbiyarshi ta yau. Ko kad'an ba zaice ya tab'a ganinta da kwalliya irin cab'a cab'a d'in nan ba, amma kullum dressing d'inta abun ayi ta kallo ne.
Ita kuwa ganin sunja tunga sun tsaya saita d'auko tray ta d'aukar musu drink's masu sanyi.
Ruwa kad'ai suka sha Ayman yace, "muje ko?". Sai duk suka taso, bayan khaleefa ya rufe sashen sallama raihana da suhaana Suka ma mutanen gidan. Haka dai raihana ta tafi da tunanin yanayin da take ganin auntie kadaran kadahan har ta futo a sashen.
Kasancewar Ayman ke tuk'a motar sai khaleefa ya shiga baya, har suhaana ta bud'e bayan zata shiga sai taga mijin raihana ne a ciki ta juya, da sauri yace, "Bismillah shigo mana". Ta juya sashen da raihana take sai taga tayi mata murmushi, hakan ya bata kwarin gwiwar shiga ita kuma ta shiga mazaunin kusa da driver.
Suna tafe a hanya khaleefa ke tambayar suhaana matakin karatun ta da wasu abubuwa da suka shafe ta da harshen Arab. Ko a ranta bata kawo komai ba haka ta dinga bashi amsa ganin ya saki jiki da ita, Sam bata d'auka ya iya magana haka ba da taga iya gaisuwa ke had'a ta dashi a duk zaman nan da sukayi.
Wannan abu da khaleefa yayi ba k'aramin sosawa raihana rai yayi ba, amma ko a fuska ba zaka tab'a ganewa ba, hasalima hira suke da Ayman jefi jefi tana murmushi.
Kafun su k'arasa gidan saida suka tsaya a store d'in kusa da anguwar, lokacin da zasu futa k'in futa raihana tayi a cewarta ba tada abin siya, ganin haka sai suhaana data futo ta fara k'ok'arin komawa.
Khaleefa ya hanata, duk yadda taso haka ta hak'ura lokacin Ayman har yayi gaba, Koda suka jera suna ci gaba da hirar su saida khaleefa ya juyo ya kalli raihana, ta kuwa zuba musu ido tana kallon su, ganin ya juyo kuma ya sata d'auke kanta da sauri tana jin wani irin abu na soya mata a k'ahon zuci.
Haka suka d'auki adadin wasu mintuna sannan suka dawo da kaya masu yawa a hannuwan su suka zuba a boot.
Suhaana ta shiga mazaunin ta na d'azu tana ma raihana magana, "uhm!". Kawai tace mata taci gaba da duba wayarta. Suhaana ta d'auka bata ji taba sai take tambayarta, "kinji abinda nace kuwa?".
Khaleefa yace, "kinga rabu da ita wannan yanzun in kin samu miji zaki iya hak'ura da karatun kiyi aure?". Ya sauya akalar zancen gaba d'aya kuma cikin harshen turanci yadda raihana zata iya ji. Suhaana kam jikinta a sanyaye take ci gaba da hirar dashi har motar su ta parker a k'ofar gidan alhaji salis Abdallah.
Khaleefa ne ya fara futowa ya zagaya boot ya ciro wasu cikin ledojin ya mik'awa suhaana data futo, wasu kuma ya mik'awa raihana da take gyara yafen gyalenta da jakarta. "Ni ai banyi siyayyah ba". Ta fad'a tana kallon ledojin.
"Ki karb'a mana ai bakya je musu hannu rabbana ba, kin d'auko hanya mai nisa". Ayman ne me yin wannan maganar.
Madadin ta karb'a saita fara tafiya zata bar gurin, khaleefa yabi bayanta da sauri ya sak'alo hannunta cikin nashi yasha gabanta yana kallonta, kauda fuskarta tayi gefe, bai damu ba ya d'anka mata ledojin cikin hannunta muryarshi can k'asa yadda ita kad'ai da take kusa dashi zata ji abinda yake fad'a, "in ke na bawa sai kice bakya so, amma wannan nasu al'ameen ne". Yana fad'in haka yaja jikin shi baya kusa da Ayman yana kallonta. Suhaana da taga duk abinda ya faru ta matso kusa da ita tana mata dariyar shak'iyan ci da tsokana, "soyayyah dad'i! Kinga irin kallo kamar ku biyu kad'ai a gurin".
Ita kam sake jin haushin tama tayi, sai bata ce komai ba ta fara takawa suhaanan tabi bayanta.
Suka shiga gidan kusan a tare suna kwad'a sallama, da gudu su hibba duk suka futo jin muryarta, aikuwa ta saki ledar hannunta ta rungume yaran tana jin kewar su, abin gwanin burgewa haka suhaana ta tsaya tana kallon su. Ummie da take kitchen ma futowa tayi tana mamaki. "Ashe da gaske ke d'in ce". Ta fad'a daga bayan raihanan.
Saita juya gurinta da sauri ta fad'a jikinta tana fad'in, "I miss you ummiena". Sai kuma ta fashe da kuka.
Ummie ta d'ago kanta cike daso da k'auna tana share mata hawaye da fad'in, "Nima nayi kewarki raihana amma meye na kuka daga shigowa kuma, gashi naga ma tare kike da bak'uwa". Ta k'arasa fad'a da janye raihana a jikinta tana ma suhaana data tsaya kallon su gwanin burgewa iso.
Sai bayan sun zauna a parlon sun gaisa ummie ta gane bak'uwar raihanan bata jin hausa sam, raihana ta gabatarwa suhaana y'an gidan su, suma ta gabatar musu ita suka sake gaisheta. Ta fara sauraren shiriritar su al'ameen ummie ta tambayeta, "Ina fatan dai ku kad'ai kuka zo ba shanya bawan Allah kikayi a waje ba irin waccen ranar".
Sai a lokacin ta tuna ta mik'e don tayo mishi iso shima, ummie ta d'auko hijabinta tasa tana mamakin wannan al'amari na raihana, yanzu da bata tambaya ba haka zai ta tsayuwa a waje ta manta dashi.
Lokacin data futo suna gaisawa da Abba Abubakar, ta k'arasa itama suka gaisa sannan ta musu iso zuwa cikin gidan.
Har parlon ummie suka shiga wannan karon ma aka gaggaisa, su al'ameen suka gaishe su, sun tab'a hira da khaleefa kafun suyi sallama zasu tafi.
Raihana tayi banza dasu ba kuma ta da niyyar tashi har saida khaleefa ya magantu, "zamu jira ku a waje saboda zamu k'arasa gidan iya mu gaisheta kafun mu tafi".
"Kuje kawai zan biyo ku". Ta fad'a don tana son kafun ta tafi taga abbanta, sai gashi kuwa maganarta karaf a kunnen ummie, ta kuwa yi mata tatas sannan tasa tabi bayan shi lokacin har sun futa ma.
Ba don ranta yaso ba haka ta turawa su al'ameen ledojin da suka shigo dashi tace, "gashi akace mu kawo muku".
Ummie tace, "toh mun gode Allah amfana shida baya gajiya".
Har ta futo fuskarta a d'aure, saida zasu shiga gidan iya ta saki ranta, nan ma saida khaleefa ya had'a su da shopping su kai mata.
Iya kam washe da baki take kallon su tana al'ajabin bak'in nata na yau kamar an wurgo su har su hud'u haka. A parlour ta ajiye su ta kawo musu kayan soye soyenta da bata rabo dasu, sai zolayar suhaana take wai ta koyi hausa ko taji dad'in Zama a Nigeria don tafi son ta samu miji a garin nan.
Khaleefa da yake sauraron iya yayi zaraf yace, "ai tama samu insha Allah".
Ras! Gaban raihana ya fad'i har saida yanayinta ya sauya sosai. Saita mik'e don in taci gaba da zama komai zai iya faruwa, ta dubi iya tace, "Ina d'akina da mai ran k'arfe ya shirya mun".
"Ga satar miji ga d'aki? Gatan ai sai yayi miki yawa, sai dai in na baki aron nawa amma ba kyauta ba, shima saboda zuciyar musulunci ne, don kishiya ba abar goyo bace". Murmushi tayi ta nufi d'akin da iya ta nuna mata.
Tana shiga ta kwanta a gadon iya ta rufe fuskarta da hannunta.
Khaleefa ne ya dubi iya duk da akwai sauran lokacin sallah amma sai cewa yayi bari zan shiga ta bani ruwa nayi alwala.
"Kaji dashi ai, waini zai rainawa hankali da wani guntuwar gulmar shi". Iya ta fad'a. Ayman dai yayi dariya, shikam bai kula zantuttukan iya ba yace da d'an uwan shi, "na fara share maka hanya fa".
Ayman cikin jin dad'i yace, "ah haba? ai naga alama d'azu fatan dai madame ba fushi tayi ba naga yanayinta ya sauya lokaci d'aya".
Khaleefa yana murmushi yace, "zata sauko ne kada ka damu da ita, so nake ta k'aryata kanta da kanta".
Ayman yace, "lallai ne amma dai kabi ta sannu mata duk Inda suke saida lallab'awa".
Murmushi kawai khaleefa yayi daga nan ya nufi d'akin ba tare daya sake ce dashi komai ba, Ayman kuma ya fuskanci suhaana kamar wani jarumi.

Raihana tana kwance taji turo k'ofa, saita rufe idonta da sauri don ta d'auka ko suhaana ce ta biyo bayanta. Daga k'amshin turaren da yake kusantota ta fahimci ko waye, saita sake d'auke numfashi rauninta na sake bayyana, haka tana jin yadda wani abu ke tasowa tun daga k'asan ranta mai kama da fushi ko fusata.
Tana jinshi ya k'araso ya d'auke k'afafunta ya mayar kan jikin shi ya tsura ma face d'inta ido. Sosai yake k'are mata kallo yana nazarinta, yasani dama raihana tana son shi, abinda bai sani ba kawai yaushe wannan soyayyar ta fara ginuwa a zuciyarta har tayi k'arfin da idonta yake rufewa kan kishin shi. Koda yake ba abun mamaki bane tunda shima yake jin fiye da haka akanta, inda Allah ma ya taimake shi tasan ciwon kanta, wayewarta a b'oye take da kallo d'aya ba za'a tab'a fahimtar taba sai an zauna da ita. Nutsuwa, Kamala, hankali, tarbiyyah da wadataccen ilimin addini dana zamani babu wanda ta rasa, lallai itace irin macen data dace dashi, irin macen da zai iya sakarwa ragamar tarbiyyar y'ay'an shi ba tsoro ko d'ar. Lallai ba k'aramin kuskure yaso tafkawa ba d'aukar Saleema matsayin mace. Sai yaja doguwar ajiyar zuciya ya lumshe idon shi ya bud'e yana sake godewa Allah a cikin zuciyarshi, yayi gyaran murya kad'an sannan yayi magana, "Ina son magana dake Raihanatu". Bata amsa shi ba, "nasan kina jina sarai". Nan ma bata tanka ba sai ruwan hawaye daya ciko idonta.
Shima bai sake cewa komai ba ya durk'usar da kanshi ta yadda har numfashin su na had'uwa, ya d'ago kanta kad'an ya tallafe fuskarta da hannun shi biyu ya had'e fuskarsu har hancin su na gogan juna, abu na gaba da yayi shine fara kissing d'inta gently. Duk yadda raihana taso dakewa a wannan karon kam kasawa tayi, ba tare da neman izinin taba hawayenta ya soma kwaranya, ta bud'e idon tana kallon shi kafun ta tura shi kad'an ta tashi zaune ta cusa kanta tsakanin gwiwowin ta ta fashe da kuka mara sauti. Khaleefa bai yi k'ok'arin hana taba don yasan yadda kuka yake a gurin wanda Allah yake ba damar yi, don rahama ne yinshi a wasu lokutan.
Ganin kukan nata ba mai k'arewa bane sai ya haura gadon ya zauna kusa da ita sosai ya d'ora hannun shi a gadon bayanta yace, "I'm sorry". Bata kula shiba yasan za'ayi haka, sai ya d'ago kan nata yasa tafin hannun shi yana share mata hawayen yana sake bata hak'ori. Da kyar ya samu ya lallab'a ta tayi shiru, sai a lokacin ya samu damar tambayarta ba'asin kukan nata.
Da murya mai rawa ta fara fad'in, "na gaji, na gaji da halinka khaleefa! Tunda na aure ka baka tab'a bani damar zuwa gidan mu na wuni tare da familyna na sake kamar kowacce mace ba, Ina da k'anne, Ina da y'an uwa, Ina da kakanni amma baka bani damar zuwa musu takanas sai in na shiga na futo kana jirana a waje, Ni duk wannan ma bai dame niba kamar yadda nayi tafiya mai nisa na dawo amma na shiga gidan mu kamar bak'uwa ko gama gaisawa da ummiena banyi ba bare naga Abbana da bai ma dawo kasuwa ba ka azalzala na futo..... I'm tired wallahi na gaji". Ta k'arashe maganar da rawar murya tana sake fashewa da wani kukan.
Khaleefa da mamakinta yau ya cika shi jawo ta jikin shi yayi ya rungume yana bubbuga bayanta, "shine kad'ai laifina ko akwai wani?". Ya tambayeta har lokacin yana rungume da ita.
Ita kuwa kamar ta mishi maganar suhaana saita basar karya d'auka kishin shi ma take. Madadin haka saita janye jikinta ta jingina da fuskar bed ta lalubo wayarta tana dannawa.
Shi kuwa sauka yayi a gadon jin malam ya kwala kiran sallah a masallaci. Agogon hannun shi ya cire ya d'ora mata kan cinya ya ajiye hular kanshi ma ya shiga bathroom don d'auro alwala.
Bayan ya futo ya maida agogon shi da hular shi ya fuce a d'akin, tabi bayan shi da munafukin kallo tana jin wani tarin k'aunar shi a zuciyarta. Ita kanta tuhumar kanta take yaushe har ta shak'u dashi take jin wani abu game dashi haka.
Kasancewar ba sallar zata yiba saita sake kwanciya tana buga game a wayarta, abu na k'arshe da saita matuk'ar rasa abinyi ta kanyi. Kafun suhaana ta shigo ta hanata game d'in da hira.

Ta b'angaren khaleefa kam bashi ya dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, suka futo tare da malam suna tattakawa, sai a lokacin malam yake shaida musu an maida auren iyayen su, ba k'aramin farin ciki sukayi ba kuwa don abun yazo musu da wuri ba yadda suka d'auka ba.
Sun shiga gidan suka samu iya raihana da suhaana suna hira a parlonta, rabin hirar ma abun dariya don itace a tsakiya tana musu tafinta.
Zuwan su ya dakatar da hirar, iya ta kawo musu abincin su su biyu, shi kuma malam ya shige d'akin shi, sai ya zamana daga iya sai su a gurin.
Sunyi hira da iya sosai kafun su mata sallama zasu tafi, lokacin bacci duk yaci k'arfin raihana da kyar ta iya lallab'awa ta futo amma suna shiga mota ta fara bacci. (Da yake wannan karon tafiyar ba kamar wancen lokacin ba, duka mazan suna gaba matan a baya).


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login