Showing 153001 words to 156000 words out of 288773 words

Chapter 52 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1106

Raihana kallon shi tayi da mamaki tana al'ajabin wannan k'arfin hali da k'arfa k'arfa, shi ko kunya bwyq ji wayar ma har sai ya fad'a mata adadin lokacin da zata d'auka, ba don kada ta dinga ja dashi su samu matsala ba da ba zata d'aga kiran ba.
Da sallama ta kara wayar a kunnenta, sautin muryarta daya ratsa dodon kunnen shi ya assasa mishi lumshe idanun shi tare da jin wata fad'uwar gaba, jin shiru sai raihana ta sake maimaita sallamar ta. Da kyar ya iya bud'e bakin shi da rawar baki da murya yace, "Raaiihaaanaaa". Saida ta saci kallon inda khaleefa yake zaune, hankalin shi kacokan yana kan wayarshi, sannan tace "wayee?". Ta tambaya ba wasa a tattare da muryarta.
"Imran ne raihana.... Ina yi miki fatan alkhairy,,,, na kira ki ne kawai don naji muryarki karo na k'arshe a tarihin rayuwata......". Raihana batasan lokacin data zare wayar a kunnenta ta kira sunan shiba, "Imrana?". Shi kuwa tuni ya katse kiran ya had'a da kashe wayar duka, kanshi ya had'a da gwiwa a lokacin shi kad'ai yasan abinda yake ji. Ita kuwa raihana cike da tausayin shi ta sauke wayar tana maida ajiyar zuciya.
Duk abinda ya faru a idon khaleefa, saiya tab'e baki don shi a tunanin shi saboda shi ta katse wayar.
"Dama ina son ki shirya gobe da dare zamu futa". Khaleefa ya fad'a bayan ya mik'e yana shirin futa daga parlon. Abin ma takaici yaba raihana, wai ta shirya zasu futa bama yau ba gobe, ta d'auka wata k'atuwar maganar yazo da ita shine hadda gindaya mata sharad'i haka.
Tab'e baki itama tayi ta tashi ta shige d'akinta ta rufo.

*****Kamar kullum washe garin ranar ma raihana kafun ta tashi auntie ta aiko musu da break. Bayan ta gama gyara d'akin gadonta zuwa bathroom, don shine kad'ai aikinta a gidan, shiryawa tayi cikin riga da zani na wata atamfarta mai kyau, ta d'auki hijab d'in sallarta ta saka ta futo parlon donta samu sukunin cin abincinta.
Koda ta gama bata koma d'akin ba, ta kunna kayan tivi tana kallon wani series. Sanye da jallabiyyah fara sol ya futo yana mik'a da salati,,,, kallo d'aya raihana ta mishi ta juyar da kanta tana duba lokaci, Sha d'aya saura y'an mintuna. "Ina kwana?". Raihana ta fad'a tana duba wayarta da sak'o ya shigo. Bata ji amsar daya bayar ba don daga labban shi sai hak'urin shi suka san ya amsa.
"Aslm,,, raihanatu fatan kin tashi lafiya,,,, yau ban futa office ba saboda na tashi bana jin dad'in jikina, sai dai na futo babu komai naci a gidan auntie ta tattare komai ta aiko part d'inku keda mijin ki kuci ku rayu mu ko oho!!!".
Saida murmushi ya sub'uce mata a lokacin data gama karanta sak'on, Yaya Ayman yana gida bai futa ba kenan? Saita tashi a nutse ta shiga kitchen d'inta ta d'auko plate, yana zaune kan dinning yana cin abincin shi ta k'araso a nutse,,,,, abinci ta zuba mai d'an dama ta juya tabar gurin.
Babu kowa a part d'in Auntien sai mama haleema da bata dad'e da zuwa ba itama. Suka gaisa da raihana ta ajiye plate d'in a k'aramin center table dake tsakiyar parlon ta futa, saida ta koma ta tura mishi k'aramin sak'o, "kamar yadda ka buk'ata,,,, abincin ka yana part d'in Auntie,,,,".
4 mint da tafiyar sak'on ya turo mata, "thanks".
Murmushi tayi ta sake gyara zamanta tana ci gaba da kallon ta.

Hajiya tafeeda tana hakimce a parlonta na k'asa dai dai lokacin da Imran yake saukowa daga saman shi, ko yanzu daya ganta saida gaban shi ya fad'i, yasan saboda shi ta kasa ta tsare anan. Instead of ya huce ga abinda ya futo dashi, sai ya k'arasa cikin parlon ya durk'usa gefe yana gaisheta. Yamutsa fuska tayi ta kyab'e baki, "da ka bar gaisuwar ka Imran har zuwa lokacin da zaka gane gaskiya ka daina gaba dani,,,,,".
"Kiyi hak'uri Mom" abinda ya fad'a kenan ya mik'e zai futa.
"Dakata! Ina son magana da kai ai". Inda ya tashi ya koma ya durk'usa kamar wani maraya ko marar gata ya rakub'e.
"Zuwa kayi zaka had'a mun case da baban ku saboda kai shashasha ne ko? Toh na soke tafiyar ka Lagos gaba d'aya, kuma auren ka bazai huce nan da wata d'aya ba insha Allahu,,,,, sai kaje ka sake yi mishi bayani.... Wannan karon ma in kaje kace mom ce ta hana kaga yadda zamu kwasheta da kai a gidan nan".
Baice mata komai ba ya yink'ura ya tashi,,,,, ko kad'an baiji b'acin ran komai a ranshi ba, daga soke tafiyar har takurarren auren data shirya. Tunda ya rasa raihana gaba d'aya rayuwar shi ta dawo hopeless. Komai ya rasa yana ganin ba zai kai raihana daraja da tsada ba.

Yana futa daga parlon ta lalubi number sameera ta kira, bata jima tana ring ba ta d'aga, bayan sun gaisa anji lafiyar juna take tambayarta ko Nur ta amince kuwa?
Girgiza kai sameera tayi tace, "ki bari kawaii! Wallahi yarinyar nan ta k'i amincewa fafur, Ni har na fara tunanin ko mu maida auren kan y'ar uwarta kawaii".
Shiru hajiya tafeeda tayi tana hamdala a cikin zuciyarta, don dama ita harga Allah shaheeda taso Imran ya aura ba nuriyyah ba,,,, Amma tunda maman su ta nuna ta bashi Nur don a rage mata rad'ad'i da tunanin masoyinta Ayman saita hak'ura dasu haka, yanzu kuma da Nur d'in tak'i amincewa sai tace falillahil hamdu. Sun ajiye waya da alk'awarin zata zo gidan in aka jima.

******Zaune take gaban mammie da hajiya tafeeda da suke kira mom, tayi ladab tana sauraron duk bayanan bakin su, "kamar yadda muka shawarta da mahaifiyar ki, tunda Nur ta k'ek'asa ta nuna sam bata son auren Imrana, mun yanke shawarar maida auren Imran da Nur kan ki, amma yanzu mun kira ki muyi shawara dake ne,,,, idan har kin amince ba b'ata lokaci mu dawo da magana izuwa ga mafarinta, Ina fatan kina sane da komai ko?".
Shaheeda shiru tayi bayan ta gama jin duk abinda mamien ta fad'a, "idan har kin amince ga hajiya nan ki fad'a mata da bakin ki....".
Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "yadda kuke so mom na amince". Cike da farin ciki tafeeda ta dafa kanta tana fad'in Allah yayi miki albarka shaheeda, yasa kece abokiyar arzik'in Imrana.
Mik'ewa tayi tana murmushi ta huce side d'in su, tana zuwa inda zata shiga bedroom d'insu ta sauya yanayinta zuwa na jimami sannan ta shiga, Nur tana kwance rub da ciki tana operating system d'inta shaheeda ta shigo, saita tashi zaune tana kallonta a lokacin data zauna gefen katifah ta had'a kai da gwiwa.
Da taushin murya Nur ke tambayarta "meya faru Yaya?".
D'ago kanta tayi tana kallon k'anwar tata kafun tace, "na amince da auren Imrana,,,,, indai hakan zaisa su hak'ura su barki da muradin ki".
Cike da tausayinta Nur tace, "ayyah kada kiyi haka Yayaa,,,, don Allah kada ki saka kanki cikin matsala saboda ni,,,,,,,".
Dafa kafad'arta shaheeda tayi tace, "kada wannan ya dame ki k'anwata insha Allah ba abinda zai biyo baya sai alkhairy,,,,, Zan iya sadaukar miki da komai kamar yadda kike yi mun... Fatan Allah yasa hakan ya zamo silar samun cikar burin ki...".
Sai suka rungume juna Nur tana kuka tana yi mata godiyaaa..........

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*

_shin kuna bibiye da littattafan in-identical twins,,,, in-identical twins sun shirya tsab wajen ganin sun nishadantar da mabiya littattafan su, merhreeyaert lerwerl da littafinta na👉🏻 JARUMAR UWA, sai doctor Ferhyeez m usmern da littafin👉🏻 DARAJAR HAK'URI masoyan mu kune alfaharin mu😍😍😍_

May all our dreams come true 🤲Happie juma'ah Mubarak,,,,,,,,,



_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty three4️⃣3️⃣


Koda ta fahimci mama haleema ta d'ora girkin dare kitchen d'in tayi, duk da auntie ta hana ta shiga tace zatayi girki amma sabo da karakaina irin tata sam ba zata iya zaman ba, ita ma mama haleeman data ganta saida ta kwab'e ta, "kaddai kice girki kika zo taya wa".
Tana y'ar dariya tace, "mama niba girki nazo ba kawai nazo na taya ki hira ne".
Mama haleema tace, "hirar ma na yafe kije ki taya miskilin mijin ki gashi can kwance parlon Auntie wai yunwa yake ji"
Raihana kujera taja ta zauna tana murmushi tace, "mama kinji abinda kika ce fa, miskili, miskilan mutane basa son magana da yawa bare wani tayin hira".
Mama haleema tayi dariya, "aikuwa dai musamman irin su Khaleefa, nifa tsawon lokacin dana d'auka Ina aiki a gidan nan, bamu tab'a hirar minti goma cikakke dashi ba" cikin jinjinawa raihana tace, "Hun un".
Mama haleema taci gaba da cewa, "Ayman ne dai na mutane,,,, shi kowa nashi ne". Raihana tana wanke mata albasar data yanka tace, "ai Yaya Ayman akwai son mutane, dama kinsan kowa da yanayin shi". Mama haleema tace, "sosai ma kuwa,,,, Kai raihana wannan ai wayon aiki ne, ga can shayin dana had'awa y'an biyu ki kai musu, akwai snacks a tray ki kaiwa Ayman me sugar khaleefa kuma me gishiri".
Ba don taso ba ta tashi zata kai musu kamar yadda ta umarta.
Suna zaune a parlon, khaleefa yana operating system shi kuma Ayman yana bashi labari, da gaske kamar yadda ya fad'a bashi da lafiyar, don ga zahiri nan har idon shi ya fad'a ciki.
A gefen kowa ta ajiye mishi nashi, zata tafi Ayman yace, "thanks matar twin bro".
Saita juyo ta mishi murmushi ta k'arasa futa daga parlon.
Ko data koma dole mama haleema ta barta sukayi aikin tare har zuwa lokacin da auntie ta dawo taje mata sannu da zuwa, kallon khaleefa tayi a lokacin da raihana ta shigo ta fahimci ba inda suka je tace, "haka mukayi da kai?".
Kallon inda raihana take zaune yayi, sannan ya kalli auntien yace, "zamuje zuwa dare, da ranan ne banjin futa".
"Meyasa kake yin haka khaleefa?..... Ka kai yarinya tun safe da yamma ka koma ka d'auko ta kake jin kyashi?" Shiru yayi kanshi a k'asa bai iya ce mata komai ba, raihana kam futa tayi daga parlon. Ayman da yake zaune ganin ran Auntie ya b'aci sai yace, "kiyi hak'uri Auntie! Khaleefa yana da gaskiyar shi, maybe ya bari suje da daren ne saboda yana jin kunyar had'a ido dasu ummie da rana....".
Wani kallo da Auntie ta mishi yasa shi sunkunyar da kanshi ba shiri, shi kanshi yasan ya fad'a ne kawai don ya kare d'an uwan shi, amma ba don ya fad'i abinda yake gaskiya ba.
Mik'ewa tayi a lokacin da zata shige d'akin gadonta tace, "ka tabbatar kana yin sallah dama ku tafi".
Kai ya gyad'a had'e da bata hak'uri. Ta shiga d'akin su kuma suka tashi don sauke farali.

Raihana tana zaune bayan ta idar da sallah kan darduma a d'akin gadonta khaleefa ya turo k'ofar, bai shiga ba amma wani mayataccen k'amshi ya mishi sallama,,, irin mayen k'amshin turaren auntien shi da yake matuk'ar so, tunda take a gidan bai tab'a lek'a d'akinta ba sai yau,,, itama saita tsaya tana kallon shi da tunanin abinda ya kawo shi, ko wanka ya sakeyi oho ita dai ta ganshi da sabuwar shiga ta manyan kaya hadda hula.
"Ke nake jira". Abinda ya fad'a kacal ya juya ya futa.
A hankali ta futo a shiryenta, ta kukkule k'ofofin part d'in, auntie take son yiwa sallama sai dai khaleefa ya hana ta a cewar shi zata sake ja mishi delay.

Har sun fara tafiya taga sun tsaya a wani babban mall, ita kam zamanta tayi a mota bata da niyyar futowa, ganin haka sai khaleefa ya tambayeta, "ba abinda zaki siya musu?". Tambayar mamaki taba raihana kwarai, wai ba abinda zata siya musu? Toh su suwa? Girgiza mishi kai tayi, yayi hucewarshi ita kuma taci gaba da zamanta.
Bai jima sosai ba ya dawo da manyan ledoji biyu ya saka a booth suka ci gaba da tafiyar su.
Ko kafun raihana ta banbance anguwarsu khaleefa yayi parking a k'ofar gidan su, saita kalle shi ta kalli k'ofar gidan. Lallai ma khaleefa! Dama gidan su auntie tasa ya kawo ta tun raana? Sannan su yake tambaya ba abinda zata kai musu kamar wasu bak'i a gurinta.
A nutse ta yink'ura zata futa daga cikin motar ya dakatar da ita ta hanyar cewa, "wait! Idan muka shiga zakiyi musu bayanin tafiyar mu Germany tare nan da y'an kwanaki,,,,, sannan ki tattaro duk wasu takardun makarantar ki,,,, fatan kina sane da alk'awarina?".
Kai kawai ta gyad'a mishi jikinta a matuk'ar sanyaye, toh yaushe tayi da khaleefa zata bishi wata uwa can duniya? Saita dafe kanta da hannunta tana tunanin yadda zata iya binshi wani guri me nisa..... Shin wacce irin rayuwa zasuyi a inda babu idon wanda yake shakka kamar auntie? Wai a haka ma yana rage wasu abubuwan saboda kada a gane ba son juna suke yi ba, shine har zai d'auke ta a motar shi ya futa da ita ya kaita tayi uzurinta ya jira su dawo tare kamar gaske.
A nutse ta d'ago jin abu me nauyi saman cinyarta, babbar leda ce guda d'aya ya d'ora mata, "lokutan ki suna tafiya faa". Ya fad'a yana duba agogo.
Sai a lokacin raihana ta kalle shi, yana daga waje amma hannunshi hard'e a k'irjin shi.
Itama futowa tayi tana kallon shi tace, "yaushe mukayi da kai zan bika wata uwa duniya?".
Murmushi khaleefa yayi yace, "dallah dallar bayani ne banyi miki ba amma na fad'a miki tun a ranar da muka fara had'uwa,,,, na fad'a miki zan samu yarinyar da nake sone kad'ai idan na cika wani sharad'i a gurin mamana, sharad'in bana komai bane face aure, gashi kuma na cika itama zata cika mun nawa, Ina fatan kin tuna.....". Ajiyar zuciya ta sauke ita kam ba zata iya fad'awa su ummie wannan maganar tafiyar ba..... Wane irin mutum nema khaleefa wai.
Kamar wadda ta shekara bata zo gida ba haka taji a lokacin da take taka k'ofar gidan su. Ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi ta k'arasa shiga gidan da sallama.
Kusan su al'ameen gaba d'aya suka runtumo da gudu sukayi kanta, ta rungume su tana murnar ganin su.
Tun kafun ta shiga parlon ummie suke faman bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Ita dai rabi ma duk ba ganewa take yi ba saboda baza ido da son zak'ulo inda ummienta take.
Ajiye ledar hannunta da khaleefa ya had'o ta da ita tayi, ta zauna tare da zaunar da hibba ma kusa da ita ta tambayi al'ameen, "Ina ummie?".
Kafun ya bata amsa hibba ta riga shi da cewa, "tana d'akinta tana muraji'a bari na fad'a mata kinzo Auntie raihana!". Ko amsar da raihana zata bata tsaya jira ba ta mik'e da gudu ta tafi, da ummien taci karo tana shirin shiga ita kuma tana shirin futowa. "ummie auntie raihana ce tazo.... Gata can tana jiran ki". Hibbah ta fad'a cikin tsananin farin ciki tana nuna mata inda raihana take zaune.
Kamar yarinya haka raihana ta tafi da gudu ta rungume ummie cikin farin cikin ganinta da tarin k'auna.
A nan parlour suka zauna, da mak'urar farin ciki suka gaisa da ummie taji lafiyar kowa cikin jama'ar gidan har abban su, shaf ta manta da wani khaleefa suka zo saida ummie ta tambayeta ya auntie da me gidan nata.
"Ohh! Na manta ashe tare muka zo yana k'ofar gida...". Da mamaki ummie ke kallonta kafun tace, "wannan wane irin shashanci ne? Mijin naki kika bari a tsaye a titin Allah kamar wani bak'o?". Da muryar shagwob'a tace, "ummie toh ai mantawa nayi".
"Aikuwa maza kije ki shigo dashi". Ummie ta fad'a da fuska ba wasa.
Kamo hannun jidderh tayi ta mata rakiya suka futa inda yake waje. Yana nan tsaye yadda ta barshi.
Har k'asa hibba ta durk'usa ta gaishe shi lokacin da suka k'arasa, abun ya burge khaleefa kwarai musamman yadda yara k'anana suka san su martaba babba irin haka.
Ya amsa tare da d'ago kanta yana kallonta, yarinya k'arama amma ma'abociyar hankali da nutsuwa.
"Ka shigo,,,,," raihana ta fad'a tana juyawa zuwa ciki. Shida jidderh suka jero har cikin gidan. Duk su al'ameen sun nutsu a gefe d'aya suna jira ya shigo su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login