Showing 90001 words to 93000 words out of 288773 words

Chapter 31 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1095


Taci gaba da kwanciya har bacci yayi nasarar d'auke ta, a cikin baccin ne kuma taji kamar ana kiran sunanta. Tana bud'e idonta taga ummie tsaye a kanta, saita tashi zaune tana mutstsitstsike idanunta, "kina son baccin la'asar d'innan raihana kuma bashi da amfani, kije Imran yana jiran ki a sitting room". Da mamaki tace, "Imran kuma? Toh yaushe ya futo daga asibitin?". Ummie da take kallonta tace, "toh ni ina nan taya zan sani?". Sai kuma ta mik'e sum sum ta shige d'akinta, hijab ta zubo zunbulele akan kayan jikinta ta yiwa auntie sallama ta nufi sitting room d'in.

Yana zaune ya jingina kanshi da kujerar da yake zaune kai, idon shi a lumshe ya fuskanci sama, k'amshin turaren ta kad'ai yaji ya tashi zaune sosai ya zuba mata ido. Ta samu guri nesa dashi ta zauna ta zuba mishi ido itama, saida ta gama karantar yanayin shi gaba d'aya sannan ta sauke ajiyar zuciya tace, "ya jikin naka yaushe aka sallamoka ba labari". Shima ajiyar zuciyar yayi yace, "jiya da daddare, na kasa hak'uri raihana, na kasa hak'uri gaba d'aya shi yasa na taho na ganki, ko a gida ba'a san na taho ba daga tattaki na yo nan, Alhamdulillah yanzu kam tunda na tabbatar kina cikin k'oshin lafiya na samu nutsuwa". Yak'e raihana tayi Wanda yafi kuka ciwo, Imran ya rame kwarai sai dai ya k'ara haske, bawan Allah yana can yana mafarkin aurenta, maman shi kuma tana shirin raba su, yana asibiti yana jinya baisan har warning ta turo musu ba, ita dai kam data kalli idon wannan bawa me nuna kulawa gareta da tarin Soyayyah tace ta fasa auren shi, gwara ta aure shi duk abinda maman shi zatayi daga baya tayi hak'uri ta karb'a, dama ita tuni ta saddak'ar da rayuwar nutsuwa a gidan miji bayan aure, tasan yadda ummienta ta rayu cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali gurin dangin abban su itama haka zata rayu, sai kawai ta lumshe idanunta, tana karanta duk addu'ar da tazo bakinta a lokacin har Allah yasa ta had'iye kukan ta.
Ta bud'e idonta akan Imran da yake faman tambayarta lafiya take kuwa, ta k'ara k'irk'iro wani murmushin tace, "lafiya Lou nake naji dad'in ganin ka dear a k'alla nima hankalina ya kwanta na tabbatar kaji sauk'i kamar yadda kasha fad'a mun a waya". Murmushin shima yayi yana ta kallonta, har kallon yaso tsorata raihana ta tafa hannu a saitin fuskar shi tace, "ya dai?". "Ina tunanin kwanakin da suka rage a d'aura auren mu ni dake, raihana yanzu a duniya bani da wani burin daya huce a d'aura auren nan na ganki a gidana matsayin matata, Kai Anya zan iya barci kuwa a wannan rana? Kwana zanyi Ina mik'a godiyata ga Allah subhanahu wata'ala, domin samun ki babbar nasarar rayuwata ne, rasa ki kuma zata zama mafi munin asara a tare dani?".
Raihana sake lumshe idonta tayi tana jin shigar kowanne harafi cikin kunnenta, zancene na gaskiya da gaskiya Imran yake yi, abinda ya fad'a har zuciyar shi haka yake, wani irin dad'i taji a ranta koba komai idan Imran yana sonta zata samu wani sassaucin.
Kusan duk hirar shi ta yau bayyana mata yadda yake sonta yake da alk'awarin kasancewa da ita muddin ranshi, saida raihana tace za'a iya neman shi a gida sannan ya tafi da kyar, don har waje ta raka shi tana d'aga mishi hannu.
Ko data dawo Bata koma d'akin ba ta zauna a k'ofar kitchen inda ummie take aikin had'a abincin dare, shiru tayi kanta a k'asa tana tariyar kalaman Imran na yanzu a kwanyarta, "kin fara wannan tunanin naki ba?". Ummie ta fad'a tana kallonta, "a'a ummie me zan taimaka miki dashi". Kallonta tayi kurum sai kuma ta mik'o mata albasa a kwando da wuk'a, "yanka wannan ki zuba a naman can", ba musu ta fara yanka albasar kamar yadda ta umarce ta.
Kusan tare suka gama girkin ta zuba wanda zata iya ci ta zauna, lokacin gidan ya cika da hayaniyar su jidderh da suka taso makaranta babu abin dake tashi sai sautin muryar al'ameen da muhibba, ganin sun hanata jin gari saita gudu d'akin auntie ta zauna kan drower mirrow tana cin abincin tana duba watsapp d'inta, hira suke yi da Imran don yanzu ba yawan waya sai text ko chat. Kuma dama ita bata son yawan wayar saboda bata fiya son takura ba, yawan d'aga waya kuma Yana daga abinda yake takura ta.

_ranar da muke ciki, ci gaban labari_

Washe gari tana wankin gida d'an aiken malam yazo ya sanar da ita malam yace yana son ganin ta anjima zai bata wani sak'o.
Da toh ta amsa taci gaba da aikinta, bayan tayi wanka, wata doguwar rigarta ta zura ta zauna a parlour tana karya kumallo tana kallon program d'in da akeyi a channel d'in da ta kama, ita da kallo bai dame taba sai gata yanzu bata iya zama shiru sai da tivi, koda yake yanzun ma ba komai take fahimta ba donta ragewa kanta tunani ne kurum.

Bayan ta gama har ta kwanta a d'aki sai ta tuna da kiran malam, ta zura hijab ta rufe fuskarta da nik'ab ko wayarta bata d'auka ba ta fad'awa ummie kiran da malam yake mata ta tafi.
Tana futa taci karo da matar wan babansu tsaye ita da wasu mata uku suna magana k'asa k'asa, umma salaha na ganinta ta fara nuna musu ita da baki, aikuwa duk matan suka kalleta, ita kam d'auke kanta tayi tana tunanin kamar taga wad'an nan fuskokin lokacin da taje duba Imran a asibiti, toh meya had'a su da matar Abba Abubakar kuma? Koda yake su suka sani ba damuwarta bace su k'arata can.
A k'ofar gidan iya taga sabuwar mota, tasan maybe malam ko iya ne suka yi bak'i, har tayi nufin komawa sai kuma taga ita da zata karb'i sak'o bari ta shiga kawai aiba zama zatayi ba, tun a tsakar gida take kwad'a sallama, hango takalma a sitting room sai ta fahimci bak'in suna ciki, don haka kanta tsaye ta nufi d'akin iya tana fad'in, "nazo cin gyad'a". Iya da take aikin k'ulla gyad'ar ta sake baki tayi tana kallonta da fad'in, "wannan kuma waye haka? Ni har na manta dake ma".
Tana k'arasa shiga parlon tayi dariya tare da zama a hannun kujera, bata d'aga nik'ab d'inta ba don ba zama zatayi ba, a haka suka gaisa da iya. Saida ta nutsu sosai ta ga Ayman a parlon, yana zaune ashe ta shigo yana jinta ya ganta da idon shi? Abun mamaki amma yayi kamar baisan da shigowarta ba? wato abun har ya ta'azzara haka? Anya kuwa ba wani laifin tayi mishi yak'i fad'a mata ba, k'arshe ya yanke alak'a da ita haka ba! Duk a ranta take wannan tunani, Har tayi nufin kyale shi sai taga kada su zama d'aya in shi ya manta da ita, ita ba zata tab'a iya mantawa dashi da tarin alkhairan shiba, zata bud'e baki iya ta riga ta da fad'in, "kinyi shiru raihanatu ya gidan ya maman ku? Fatan kowa yana lafiya". Sai ta sake murmushin da ita kad'ai tasan tayi abinta ta cikin nik'ab tace, "duk suna lafiyar su qalou, Ina me ran k'arfe d'azu ya aiko yana nema na ai".
Iya tace, "yana ciki akwai lazimin da yake ya bada sak'on ki na ajiye miki don nasan shi kika zo karb'a da baza mu ganki ba sai in mun had'u a gurin biki, shine zaki zo hadda wani yimun siyasa wai kinzo cin gyad'a sai kace in an baki ci kike da gaske".
Wata y'ar dariyar ta sake yi ta saci kallon khaleefa da zaton Ayman ne, wayar shi rik'e a hannun shi har lokacin kamar baisan da wanzuwar su a gurin ita da iyan ba. Abun yana d'aure kanta, Anya kuwa Ayman....... Maganar iya ce ta k'ara d'aukar hankalinta, "ki duba kitchen d'ina kan drower ta farko zaki ga jarka a bak'ar leda ki d'auko". Mik'ewa tayi har zata huce ta gaban khaleefa saita tsaya ta d'an lek'a cikin wayarshi k'asa k'asa muryarta tace, "Yaya Ayman yau ko magana babu? Hala chat kake da mutuniyar? To a mik'a sak'on gaisuwata gareta". Sai a lokacin khaleefa ya d'ago cikin takaici yaja mata tsaki! Har tayi gaba taji tsakin shi sai ta waigo ta kalle shi kanta a d'aure da al'amarin Ayman na yau "au wato abun har ya kai da yimun tsaki haka Yaya Ayman?" D'auke kanshi yayi ya kwantar bayan kujera ya rufe idon shi kamar me yin bacci, taff ta cika shi da takaicinta, a ranshi yake mitar shi Ayman kowacce ballagama kulawa yake, banda tsabar bata san abinda takeyi ba shi zata kalla ta kira da Ayman, ga wani k'arin takaicin ta wani nane fuskarta da wannan bak'in abun sai kace ita tafi kowa kyau a duniya, sai ya sake Jan wani tsakin idon shi a rufe still, iya data gane kan komai ce tace da raihana da take tsaye satoto da baki tana kallon khaleefa, "kema da neman maganar ki kije ki d'auko sak'on ki ki rabu da wannan". Har ta d'auko sak'on ta futo tana jin sautin tsakin shi a kunnenta, Wai Ayman ne yau hadda yi mata tsaki?. Kawowa iya sak'on tayi, ta fad'a mata rubutu ne malam yayi mata na kwana uku, ko bata samu damar futowa ba ta turo gobe da jibi a karb'ar mata, tsarin jikine dai. Har k'asa ta sake yiwa iya godiya kafun tayi mata sallama ta tafi.

Tana futa Ayman yana futowa? har lokacin kare yake da waya yana magana da Nur, kusa da khaleefa ya zauna shi kuma ya tashi zaune sosai ya had'a kai da gwiwa, Ayman kamar wanda aka zabura ya shiga dube dube a d'akin, lokaci d'aya ya dakatar da wayar da yake yace, "iya raihana ta shigo gidan nan". Kallon shi duk sukayi kafun iya tace, "Kai mu ba wata raihana data zo mana, ka gama cin gyad'ar dana baka data Allah ya Isa?!". "ba maganar wasa iya da gaske raihana ta shigo gidan nan har parlon nan naji hakan a jikina". Abun har mamaki ya ba iya, so da yawa haka tasha faruwa tsakanin shi da raihanan, a duk lokacin da tazo ta futa indai bata fi minti ashirin ba yana shigowa zai fad'i cewar tazo, ta rasa ta yadda yake gane hakan.
Shiru iya ta mishi madadin ci gaba da kula shi saita je dubawa khaleefa malam, tana futowa tace ma khaleefa, "ya gama zaka iya shiga ciki yanzun". Ba musu ya mik'e ya zura wayar shi a aljihun wandon shi ya nufi d'akin da malam yake".
Ayman da yayi shiru kamar me tunanin wani abun arzik'i ta kalla ta tab'e baki, ta kasa fahimtar wannan majagular tasu Sam, taso ace lokacin da ta tab'a yiwa surayyah maganar Ayman suna soyayyah da raihana ya amince, tun kafun ta fara wannan makarantar, lalacewar maganar aurenta na uku, sai ya k'aryata, da yanzu shine zai aure ta ba wani ba, gashi yanzu tana lura da yadda yake shirin shiga wani yanayi na daban don zatayi aure, sukam suna taya ta murna, baza suso Kuma ta k'ara samun irin waccen matsalar ba a wannan lokacin.
Khaleefa kuwa bayan sun gaisa da malam shiru yayi a gaban shi tankwashe da k'afafu kanshi yana kallon k'asan d'akin, "Ina jinka likita bokan turai fad'i abinda ya kawo ka don nasan wannan shirun akwai magana a bakin ka".
Sake gyara zama yayi yace, "malam wata alfarma ce nazo rok'a gurin ka fatan zaka yi mun". Malam da yake kallon shi yace, "insha Allah khaleefa in dai ba abinda yafi k'arfina bane". Sai yaji kwarin gwiwa yaci gaba da fad'in, "wato malam wani k'ulli ne ya d'aure mun kuma duk duniya babu wanda zai kwance mun shi sai kai, shiyasa na taho kai tsaye gareka da kokon barana, Ina fatan zaka share mun hawayena da hannun ka bibbiyu, sannan Ina son maganar da zamu tattauna da kai ta zamo sirri bana son kowa yaji musamman ma auntie".
Shiru malam yayi yana nazarin yaron, a kullum ya kalle shi sai yaga wata b'oyayyar baiwa ta daban a tare dashi wadda ba kowa yake iya gani ba, a zahiri surayyah suna kallon shi baud'ad'd'e amma yafi su tafiya sak.
"Ina jinka khaleefa tuntuni nace ka fad'i buk'atar ta indai bata fi k'arfina ba .......".
"Insha Allah! Malam zuwa nayi ka fad'a mun gaskiyar abinda yake b'oye a kan mu, ma'ana ka warware mun iya abinda ka sani game damu da mahaifiyar mu da marigayi mahaifin mu, nayi maka alk'awari wannan maganar da zamuyi indai ba kai ka fad'awa auntie ba zata zama sirri a gurina har abada babu mai ji".

_toh fah! khaleefa yana son ya had'a jagwal tsakanin Ayman da raihana, shin ko malam zai fad'a mishi gaskiya gashi dai ya d'au alk'awari_


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JvifMdt9UyYA2lbehzAMbO

*JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page twenty six2️⃣6️⃣


Malam kam shiru yayi yana kallon yaron, tun suna yara da ana rigingimun nan ya fad'awa surayyah za'a iya samun matsala fa idan suka girma, tace ba wani abu zatayi duk yadda zata iya ta shafe musu zargin komai a ransu, ba zata bar musu k'ofar da zasu zarge ta akan wani abu ko dede da kwayar zarrah ba, kuma yasan tayi k'ok'ari wajen kula da yaran da tarbiyyar su kamar yadda ta alk'awarta, tayi aiki tuk'uru ba dare ba rana don ganin ta sama musu ingantacciyar rayuwa, ta basu tatacciyar tarbiyya wadda za'ayi alfahari dasu a cikin al'umma, sai dai yana ganin yanzu lokaci yayi da abinda take b'oyewa zai futo sarari, lokacin da zata nuna musu mahaifin su indai har yanzu bai mutu ba yana raye, koda ya mutu dole ta d'anka su ga ahalin shi, abinda ya faru baya ta hak'ura ta yafe mishi ta d'auka hakan a matsayin k'addarar ta kamar yadda ta d'auka tun farko, sai yaja gwauron numfashi, lallai wani abu mai girma yana tunkaro surayyah.... Gyaran murya yayi ya ajiye carbin hannun shi gefe ya fara magana da fad'in, "Toh fa wannan shi ake kira alk'awari kan alk'awari, a zahirin gaskiya khaleefa ba zan b'oye maka ba nayi alk'awarin bazan tab'a yin magana a kanku ba tun kafun kuzo duniya, ko a iya nan na tsaya nasan kasan girman alk'awari akan bawa idan ya d'auka, toh kaga kenan bazai yiwu na fad'i abinda na yiwa kaina alk'awarin bazan tab'a futar dashi ba, duk bama wannan ba ya kamata da farko nasan abinda yasa har kazo mun nan da wannan maganar bayan a shekarun baya bamu tab'a yin maganar da kai ba".
Khaleefa kam tunda yaji maganar farko da malam ya fad'a yaji zuciyarshi ta karye, lallai ba k'aramin shiri auntie ta yiwa girman suba, sai kawai ya k'ak'alo murmushin yak'e a fuskarshi yace, "wato malam zahirin gaskiya naji hakane tun lokacin dana fahimci duniya taci gaba, kan mutane ya waye, yanzu ba da komai ake ado ba saida uba, na fara jiye mana tsoron sharrin mutane idan har akace yau munyi aure mun haifi y'ay'a, muma ana fad'in ba'a san asalin muba, ana kiran mu shegu kaga yaran mu sun zama y'ay'an shegu kenan?, zasu tashi ba k'ima ba daraja ana goranta musu a gari, shine kawai dalilin ba wani abu ba". Saida ya gama jinshi tsab sannan yace, "toh maganarka abun dubawa ce khaleefa, sai dai kayi hak'uri ka bani lokaci kad'an zansan ta yadda zan binciko maka abinda kake son ji Insha Allah".
Khaleefa ya sake cewa, "na gode sosai malam Allah ya k'ara girma, sai abu na gaba bance lallai sai ka nemo mun wani abu data bunne bata son muji ba, kawai ka had'a ni da dangin mahaifin mu ko a b'oye ne sai naje na binciko komai ta yadda ba zata san kai ka fad'a mun ba don Allah na rok'e ka malam ko iya wannan alfarmar ce kayi mun.....".
Ina ruwan sabatta juyatta, toh shi yasan dangin tane ma bare wasu dangin ubansu? uban da iya zaman su sun san dai ita kad'ai ba zata tab'a samar dasu ba faqat amma banda sunan shi har gobe ta k'i yarda tace wani abu a kanshi, shine yau za'a ce su fad'i inda za'a samu dangin shi?. Cikin hikima da son kwantar wa yaron hankali malam yaci gaba da mishi magana da hikima, "toh da yake kasan yadda rayuwa ta koma, anyi watsi dasu tsawon shekaru ko kamannin ku basu sani ba, yanzu kai tsaye ka tafi gare su ai abun saiya tashi kura, irin k'urar da mahaifiyarku ta nisanta kanta da ita tun tsawon lokaci, kayi hak'uri dai khaleefa mubi a hankali ta kanta har ta sauko ta yafe su a zauna qalou, tunda kaga a matsayinta na uwa dole mu bata hak'k'in ta, zuwa yanzu nasan ita kanta hankalinta ya kusa zuwa inda naka yaje, nan bada jimawa ba zata kai ku gare su da kanta dole,,, k'iris ya rage ka k'ara hak'uri dai". Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace, "toh Allah yasa malam,,,, nagode sosai da shawara insha Allah zan bi a sannu kamar yadda ka buk'ata". Malam yace, "yauwa Allah yayi maka albarka kaida d'an uwan ka da mahaifiyar ku gaba d'aya". Khaleefa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login