Showing 120001 words to 123000 words out of 288773 words

Chapter 41 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1052

kullum tana kwance, ba laifi yanzu kumburin k'afar tata ya ragu amma ciwon dai sai a hankali duk da tana taka k'afarta tafiya ba mai nisa ba sosai.
Yanzun ma bata jima da futowa daga wanka ba tasha magani ta kwanta ko abinci bata iya ciba duk da yadda ummie take yawan fad'a akan zamanta da yunwa.
Ta fara bacci me dad'i hayaniyar Salma da y'arta suka tashe ta. Ta bud'e idonta da yake ciki da bacci fal ta dubi Salma da itama take kallonta tace, "Wai ke har yanzu ba zaki girma ba?".
Shagwob'e fuska Salma tayi tace, "haba auntie raihana don Allah, bikin kifa akeyi, ya kamata ace by now kin manta yadda ake yin bacci gaba d'aya saboda shiga busy, amma kika zo nan kika kwanta, ba k'unshi ba kitso kamar ba amarya ba, haba dubeki fa don Allah! yanzu ma ummie take fad'a mun ba abinda kike shirin yi, ko make-up yanzu bakiyi booking ba? salon duk y'an biki su fiki kyau....." Ta k'arasa fad'a slowly tana kallon k'afar raihana dake nad'e da bandage. Sai kuma ta kai hannunta k'afar tace, "ayyah meya same ki haka a k'afa".
Raihana yamutsa fuska tayi ba tare da tace komai ba ta janye k'afarta, ta karb'i baby samha tana yi mata wasa cikin k'arfin hali. Yarinyar kuwa ta dinga b'angala mata dariya.
Salma ce ta mik'a hannunta ta karb'e samha a hannunta ganin sai magana take bata sauraronta, "ki saurareni anan please,,, ya za kije gurin event d'in gobe da lanjererren k'afar ki haka?".
Sai a lokacin tayi magana, "don Allah Salma ki barni naji da abinda yake damuna ni haba daga zuwanki zaki fara damuna....". Tsura mata ido Salma tayi tana nazarinta kafun ta mik'e ta bar mata d'akin, ba tayi wani dogon tunani ko nazari ba, shiyasa bata kawo komai a ranta ba don tasan tun asali haka raihana take bata fiya damuwa da komai ba.
Ita ta dinga shige da fuce a ranar don ganin tayi duk abinda ya dace wanda zai futo da amaryarh gobe da kyau sosai.
Ko zuwa yamma gida ya cika taf da jama'a da y'ammatan amarya su zee. Ai saida raihana taji kamar ta gudu tabar musu gidan don hayaniyar da suka dingayi ta hau kanta fiye da kima.
Da dare kuwa d'akin su muhibba ta shige tun da wuri tayi kwanciyarta cikin su, dama wayarta tun ranar data had'u da wancen accident d'in take a kashe.

★★★ Washe gari su zee suka gyare gidan fess suka had'a break,,, har inda take suka kawo mata nata suna yi mata sannu, tunda suka fahimci da gaske bata da lafiya sai suka kama kansu suka shafa mata lafiya,,,, k'arfe tara d'aya daga ma'aikatan Zahra saloon tazo har gida bisa umarnin Salma aka zana mata bak'in lalle iya hannayenta. Aka yiwa ragowar y'an biki ma, auntie ma aka zaunar da ita akayi mata ja.
Sosai amarya ta haska ita kanta sai jujjuya hannunta take.
Khausar ma tazo, Amma kwana biyu mijinta ya amince tayi, shima da kyar.
Aikuwa Salma ta fara mita hadda bata shawarar ta k'ara lallab'a shi ko kwana biyu ya k'ara mata akai, saboda zasu taya ummie kintsa gida bayan tafiyar y'an biki.
Akayi sa'a Salma tayi shuka idon ummie, aikuwa ta mata tatas kan karta sake jin abu makamancin irin wannan, bayan biki zaman uban me zasu zauna suyi mata, toh ita d'in ma da an kai amarya ta tabbata ta kwashe duk wasu shirginta ta bar mata gidanta.
Hak'uri duk suka bata ganin da gaske ranta ya b'aci.

Misalin k'arfe biyu na rana y'an gidan su amarya sai shirye shiryen tafiya kamu suke don 3pm akasa a catin, amma amarya tana zaune bata da niyyar tashi kamar ba itace jigon duk wannan taron ba.
Zee data gama had'a kaya zatayi gurin kwalliya tana ta zolayarta, "wai daga gobe ta zama Mrs Imrana". Ita dai kallonta kawai takeyi, duk lokacin da wani yayi mata maganar Imran sai taji gabanta ya fad'i, don yanzu ba maganar shi akeyi ba ta khaleefa ne,,,, saida gabanta ya fad'i saboda ambaton sunan khaleefa musamman data tuna aurene suka shirya bisa yarjejeniya,,,,, ita duk har yanzu ma ta kasa gasgata bikinta akeyi tare da wani wanda bata tab'a zama dashi ko hira ta wani lokaci ba, mutumin data d'au wasu shekaru bata ganshi da idanunta ba, a k'alla fa ana maganar kusan shekara goma sha d'aya, kuma a karo na farko data had'u dashi ya fara da jifanta da mummunar muguwar kalmar data tsani taga an danganta wani ma da ita ba ita ba, musamman musulmi d'an uwanta da ita wato hauka!,,,
Anya ta aure shi kuwa ta yiwa kanta adalci? Sai ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya a lokacin da ummie ta shigo d'akin, sai da duk suka futa sannan ta fara magana da ita cikin taushi, "nasan har yanzu akwai abinda kike b'oyewa a ranki raihana, wanda nake da tabbacin shiya haddasa miki shiga damuwar da kike ciki da kika kasa shanyeta a fuskarki har kika fara janyo hankalin mutane kanki suna tambayar ko akwai abinda yake damun ki bayan ciwon k'afar?". Jinjina kai ummie tayi taci gaba da fad'in, "ban nemi jin komai daga gare kiba raihana, Soo kada ka ki fara yink'urin kawo mun uzuri ko dalili, shawara ce dai guda d'aya nake son na baki, duk abinda zakiyi a rayuwa kiyi shi domin Allah, ba don ki kuntatawa wani ko ki burge wata ba,,,,,".
Damn! K'irjin raihana ya bada, kalaman ummie sunyi mata tasiri a jiki sosai har sun sake assasa mata laushin jiki da sagewar gwiwa, da ummie tayi wannan maganar, sai taji kamar tasan abinda take shirin aikatawa ne. Jikinta yayi sanyi lakwas, koba komai yana da kyau ta warware wannan auren kafun komai ya faru tazo tana data sani.
Har ummie ta tashi zata futa, tayi saurin rik'o hannunta, sai ta tsaya tana kallonta.
Ita kuwa k'asa tayi da kanta tana tunanin ta inda zata fara warware mata komai dai dai da yadda zata fahimta.

Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman (maman almustapha) tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 👉🏻 08028175615



_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page thirty four3️⃣4️⃣


Zama tayi kusa da ita cike da tausayinta tace, "ya akayi ne raihana?".
Idonta taji ya ciko da hawaye, bakinta ya kasa furta abinda tayi niyya da farko, k'arshe ta k'are da fad'in, "ummie ki yafe mun?". Ta k'arasa fad'a tare da fad'awa jikin ummie ta fashe da kuka mai ban tausayi.
Rungume ta ummie tayi tsam a jikinta tana shafa bayanta alamun rarrashi, ta kasa furta komai sai hawaye da idonta ya tara itama.
"Kiyi hak'uri raihana kowacce mace da haka ta tafi kuma ta saba, Ina fatan zaki saka hak'uri da juriya a ranki tun yanzu.....". Sai data share hawayenta sannan cikin rawar murya tace, "ummie zanyi kewarku in na tafi".
Ummie tace, "muma zamuyi kewarki raihana, amma na y'an kwanaki ne kowanne a cikin mu zai d'au hak'uri ya dangana, ki tashi ki sake yin wanka bari na had'a miki ruwa, nan da 20 mint Auntie zata zo d'aukar ki,,,, dama ki tabbatar kin had'a duk wani abu naki me muhimmanci saboda bak'i, kuma ki kunna wayarki nasan mutane sunata neman ki".
A sanyaye muryarta har yanzu tace, "Salma ta had'a kayan jiya, wayar ma tana hannunta d'azu na bata". Ummie tace, "yauwa"
Ko data had'a mata ruwan sai data taimaka mata saboda dad'ewar da tayi a zaune.
Sharp sharp ta sake yin wankan ta shirya cikin doguwar riga milk, ta zura wadataccen hijab, ko zama batayi ba ummie ta turo a fad'a mata auntie tana jiranta a waje.
Sai ta zura flat shoe a k'afarta ta futo ta yiwa su ummie da auntie hajara sallama ta nufi k'ofar gida.
Bata ga kowa ba sai mota ash glass d'inta mai duhu ba'a iya ganin na ciki. Auntie tana ganinta ta k'arasa kusa da ita ta sauke glass d'in gaba. Suna had'a ido ta sakar mata murmushi, ita kuma tayi k'asa da kanta. Da d'ingishi ta k'arasa har mazaunin gaba ta bud'e ta shiga, cikin ladabi ta gaishe da auntien, ta amsa mata cike da so da kulawa tana tambayarta k'afarta.
Tace, "ai naji sauk'i". "toh Allah ya k'ara sauk'i".
Ta amsa da, "ameen" k'asa k'asa.
Satar kallon auntie ta k'ara, kamar ba ita ta haifi su Yaya Ayman ba, tayi kyau sosai cikin wani dandatsetsen less pitch and golden, doguwar riga ce sai madaidaicin gyale data yafa a saman kanta, Suna tafe tana mata hira jefi jefi har suka k'arasa wani babban studio.
Ta gyara parking suka futo su duka, amma ita hannunta rik'e da wata y'ar madaidaiciyar jaka, tana gaba ita kuma tana binta a baya har cikin k'awataccen gurin kwalliyar.
Wata macce y'ar gayu wadda shekarunta ba zasu gaza talatin zuwa da biyu ba na ganin su ta taho da hanzarinta ta taryi auntie tana mata barka da zuwa, ta basu gurin zama suka zauna, tasa yaranta suka cika su da drinks, duk suka gaisa da ita cikin faram faram da barkwanci. Auntie tace, "ga y'ar tawa fa munzo sai dai bama son delay".
Kallon raihana tayi har lokacin fuskarta da murmushi tace, "doctor surayyah y'ar ki ko k'anwar ki, naga bakwa kama kuma bama zaki haifi kamarta ba". Y'ar dariya kawai auntie tayi tana kallonta da mamakin maganarta, matar tace, "Allah da gaske likita". Ganin abun nata na gaske ne sai tace, "na fad'a miki tun farko bama son delay fa".
"Toh angama ranki shi dad'e"
Ta gama fad'a tana murmushi, sai ta yiwa raihana magana ta mik'e tabi bayanta zuwa gaban wani glass da kayan cosmetics cike fal, raihana tsayawa tayi kurum tana kallon komai na gurin.

Ita kam auntie wayarta ta d'auko tana tunanin yadda komai yake sauyawa yana tafiya ba yadda ta tsara shiba, da farko taso ace yaranta duka biyu tare zasuyi aure a rana d'aya, ayi gagarumin biki na gani na fad'a mai kyau da k'ayatarwa, irin wanda zai girgiza ya gigita zuciyar maƙiya, sai gashi da farkon farawa khaleefa ya dawo da juyayyun al'amuran shi, a lokacin sai tayi tunanin watak'ila sai Ayman yayi aure har matar ta haihu khaleefa baiyi aure ba yana zaune k'asurgumin tuzuru dashi, nan ma ta shiga damuwa, ashe bata sani bama khaleefan ne zai riga Ayman d'in aure.
Sai ta k'ara sauƙe ajiyar zuciya tana tunanin ko sameera zata zo gurin bikin kamar yadda ta bata cati da pass na traditional sitting d'in yau. Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa tana ganin yadda auren raihana ya sake raunata y'ar rud'ad'd'iyar zamantakewar gidan ya sake wargaje su gaba d'aya, kowa ya kama gaban shi cikin su. Har Ayman gwanin juriya da shanye abu a wannan karon ya kasa saisaita yanayin shi. Gashi tayi iya yinta amma har yanzu bata gane abinda khaleefa yake b'oyewa ba, batasan mak'asudin shi na neman auren raihana ba, bayan ta ganshi a pic yana jifan wata kyakkyawar yarinya da kallon so da tsantsar k'auna, ta kuma tabbatar zai auri raihana babu soyayyar juna ko guda a cikin ran kowannen su. Ga Ayman gaba d'aya ya sauya, sauyin da kullum safiyar Allah saita tambayi musabbabin shi amma yak'i fad'a mata komai.
"Kai wannan rayuwa! Allah yayi mana maganin abinda yafi k'arfin mu" ta fad'a k'asa k'asa.
Wayarta ta d'auko daga jaka bayan ta gyara zamanta ta fara duba sak'onnin da aka ajiye mata.

Ita kuwa me kwalliya ba jimawa ta gama tsantsarawa raihana kwalliya mai kyau da d'aukar hankali had'e da aji, yadda ta futo tayi kyau abun ba'a cewa komai sai son barka.
Ita ta dawo gurin auntie ta karb'i kayan da amarya zata saka, wata tsadaddiyar lafaya ce milk and brown duk jikinta walwali yake na d'aukar ido da hankali sai rigarta ta ciki doguwa brown, da takalmi me matsakaicin tudu da jaka duk milk, sai su jeweleries na gold masu kyau sosai suma.
Saida ta shiga wani kewayyen guri ta saka kaya sannan ta futo aka k'arasa had'a ta, ko da suka gama sai da akayi mata short videos da pics sannan aka futo da ita inda auntie take zaune tana jiranta.
"Masha Allah" shine abinda Auntie ta fad'a a lokacin data ga yadda raihana take walwali da d'aukar ido kamar an sauyo ta.
Hotuna akayi musu tare anan gurin, duk da raihana tak'i sake jikinta saboda kunya, kafun auntie ta sallame su su futo daga gurin, duk da k'afarta ta warke amma har yanzu tana d'ingishi kad'an.
Wannan karon gidan baya ta bud'e mata tace ta shiga, raihana bata ce mata komai ba amma sai taji kunya da nauyin aikata hakan, madadin tayi kamar yadda tace, sai ta rufe ta koma mazaunin ta na d'azu ta shiga ta zauna. Ita kanta auntie sai data ji dad'i da hankalin yarinyar, wato tana jin nauyin ta shiga baya ita ta zama drivern ta. Hakan yasa ta sake jin yarinyar a ranta fiye da koda yaushe ma,,,,, lallai hajiya tafeeda ba k'aramar asarar suruka ta gari tayi ba, yanzu kowacce za'a je a d'ebo mata kuma oho?
Koda yake ita duk ba abinda ya shafeta bane.

*****Wani katafaren hall na gani da aka shirya table table kewaye da kujerun zama, a k'alla d'akin taron zai iya cin mutum d'ari biyu zuwa da hamsin haka. Ya cika makil kuwa mutane rukuni rukuni, waje waje, da y'an taya murna da kuma y'an ganin kwakwaf.
Can gefe guda na hango umma salaha dasu innah da y'ay'an kishiyar innan, sai mom ziyada da y'ay'anta biyu. Sai sauran jama'ar su duk gasu nan a zazzaune.
kowanne a cikin su ya zura ido yaga yadda zata kaya, musamman ma umma salaha da har lefen da aka mayar taje gidan hajiya tafeeda ta gani ta kuma tabbatar. Shine yanzu ta taho don taga kwal uwar daka da idonta, tasan dai maybe kawai pretending zasuyi gudun kada mutanen gari suyi musu dariya. Saita kyalkyale da dariya ita kad'ai a ranta tana ayyana idan sun b'oye yanzu ai zata ga yadda zasuyi gobe ranar d'aurin aure, tunda dai ba'a tab'a d'aura aure ba miji, duk da tayi mamakin yadda suka iya mayar da lefe ba tare da an sanar da Abba abubakar mijinta ba, abun nan ya girgiza ta matuk'a.
Tana cikin wad'annan y'an tunane tunanen uwar amarya ta k'araso tare da wasu mata guda biyu, dukkannin su sanye da shiga ta alfarma ta gayu. Har kusa da seat d'in amarya ta ajiye su. Kowa cikin y'an hall d'in kallon ummie take, barin ma su innah da sauran maƙiya da basa sonta. Duk da ba kwalliya tayi ba, Amma tayi kyau cikin tsadadden leshin data sa jikinta.
Tayi kyau sosai kamar ba maman amarya ba. Mutane sai kallon kallo suke, su fa har yanzu sun kasa gane abinda suke son gabatarwa a gurin.
Gashi dai jama'a sunzo iyaye da k'awaye. Su Fatima da raheela ma sunzo tuni har Salma ta basu front seat.
Sai dai duk cikar hall d'in nan da batsewarshi ba sautin kid'a ko guda, sai hayaniyar mutane, gashi lokaci nata tafiya har an fara kawo abinci lafiyayye mai kyau da dad'i.
Nan ma kwalalo ido kawai sukayi suna kallon yankan nama manya manya rabin plate, ga ruwa da lemuka a karo na biyu ana sake rabawa.
Ummie tana ta gaisawa da mutane dake yi mata Allah sanya alkhairy, daga can ta wani kusurwa na gano sameera a zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya gefenta shaheeda ce zaune. Danne dannenta take a waya amma rabin tunaninta yana wajen abinda ya had'a surayyah da ruqayyah har ta aika mata da catin bikin raihana, sannan raihanan da tafeeda ta shiga ta futa da masifa da bala'i ta hana d'anta aurenta, aka mayar musu da komai na auren su magana ta rushe ita d'in ganau ba jiyau ba, cikin kwana biyar Ina ta samu wani mijin ma da har za'ayi biki?, Toh ko Ayman surayyah ta nemawa auren tunda ta hana shi auren Nur? Sai kuma yanayin fuskarta ya sauya har ta kaiga ta ajiye wayarta kan table tana tunanin gaskitar hasashenta ba tare data sani ba, in kuwa hakan ya tabbata lallai Nur tana cikin matsala,,,,, duk da har yanzu bata yadda sunsan gundarin abinda yake faruwa ba, don har gobe tana jin takaicin yadda surayyah ta d'auki zafi har take shirin futa hanyar ta gaba d'aya, har take maganar a raba duk wani business da sukeyi tare kowa yaci gaba da tafi da nashi. Tasan kuwa lallai idan ya tabbata Ayman zai auri raihana, Nur sai ta kusa yin hauka a garin nan saboda tashin hankali, don ta tabbatar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login