Showing 36001 words to 39000 words out of 288773 words

Chapter 13 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1081

Sai ya kife kanshi a tafin hannun shi yaja dogon numfashi ya fesar da iskar ta bakin shi, "a gaskiya har na fara tunani anya kuwa kin d'auke ni irin yadda na d'auke ki a cikin zuciyata? Raihanatu anya kina kallo na da fuskar d'an uwanki abokin ki abokin shawarar ki....".
Shiru tayi jigum tana sauraron maganganun shi da take ganin bai fahimtar ta bane kawai, kuma yanzu tunda ya fahimceta ba dai dai ba, bazai tab'a gane abinda zata fad'a cikin sauk'i ba, sai kawai ta had'a hannuwanta tace, "I'm sorry Yaya Ayman, I'm really sorry, insha Allah zan tabbatar maka da gaskiyar yadda komai yake, da sannu zaka gane matsayin ka ya huce na yadda duk kake zato ko tsammanin baka kaiba".
"Toh Allah yasa raihanatu". Sunyi shiru kafun raihana tace, "ya Auntie da Nur?".
"Auntie tana lafiyarta qalou, Nur ko jiya da yamma ms muna tare, kinsan auntie weekend ne lokacin bibiyar business d'inta, sauran ranakun tana wajen aikinta, to Ina kwance kawai naji zaman gidan ya isheni shine na tafi gurinta muka sha hira ta d'eben kewa, yauma Auntie bata san na taho nan ba saboda tun safe ta futa solving wani case".
"Allah sarki nuriyyah ma kwana biyu bamu gaisa ba, ya karatun ta kuwa? Sun kusa gamawa ko?".
"Ina fa.... da saura sosai, almost a year ma".
"Ayyah na d'auka course d'inta ai 2 years ne"
"A'a 3 years ne ba 2 ba".
Raihana tace, "toh Allah ya basu sa'a suma? Yasa a gama lafiya musha biki".
Zaro ido Ayman yayi yace, "au kina nufin har sai nan da shekara za kusha bikin? Bayan kema auren ki zakiyi ba da jimawa ba ki tafi ki barni".
Raihanatu tace, "eh idan zaka iya jira har shekarar dama nake nufi, idan kuma ba zaka iya ba zaku iya yin auren ku ko yanzu in yaso saita k'arasa a hankali a gidanta".
Ayman yace, "Ina kinsan Allah raihana ban k'i ba ko yanzu a d'aura mana aure da Nur, amma ba komai insha Allah nan da watanni shida za'a yi maganar auren mu, dalili d'aya ne zai kaini ma jiran wata shida ko bakwai nan gaban".
Raihanatu cikin taya shi murna sosai tace, "Kai Masha Allah ai haka nafi so nima Allah yasa bikin mu ya zama lokaci d'aya......". Sai kuma ta k'arasa fad'a slowly da sagaggen gwiwa a ranta tana fad'in, to nida ba lallai wannan d'in ma ayi dashi ba.
Shima jikin shi a sanyaye ya amsa mata da "ameen". Jin tayi shiru sai Ayman ya tambayeta, "raihanatu kina lafiyarki kuwa?". Raihana cikin basarwa ta k'ak'alo murmushi ta wanzar a saman innocent face d'inta.
Ayman tsayawa yayi yana kallonta a lokacin da ta ware fararen hak'oran ta tana murmushi mai kama da dariyar yak'e da sunan farin ciki. Yana tunanin ba abinda yafi k'ara mata kyau da futo dashi kamar dariya ko murmushi, shiyasa yake son yaga dariyar raihana ko murmushinta a lokacin da suka kasance tare.
"Wata nawa aka sa auren ki?".
D'an sassauta yanayin tayi ta juyo opposite d'in shi tace, "wata uku ne".
Dum! dam! K'irjin Ayman ya bada, sai ya kasa fahimtar kanshi a lokacin shin farin ciki yake ko akasin haka, cikin bak'on yanayin daya farmakeshi lokaci guda yace, "yanzu fa shikenan da kinyi aure mun rabu ko?".
Sai lokacin itama gabanta ya fad'i, tayi shiru tana kallon shi eyeball to eyeball, abubuwa da yawa suke tunani a ransu a lokacin kafun yayyafin ruwan sama ya fara sauka a kansu.
Sai a lokacin duk suka ankara suka baro cikin duniyar mafarkin da suka fara shiga, suka mik'e tsaye suna kallon yadda gari ya had'a hadari bak'ik'irin, toh duk me sukeyi haka basu ankara ba?
Ayman ne yace, "raihana mu k'arasa cikin motata kada ruwan nan ya tab'a ki ki soma wannan murar da zazzab'i da basa jin magani".
Tsayawa raihana tayi tana kallon shi maganar da sukayi da auntie na kai komo a cikin ranta.
"Taho mu tafi mana raihanatu".
Jikinta duk a sanyaye tabi bayan shi lokacin tuni ruwan ya soma k'arfi saida gudu gudu suka k'arasa motar ya bud'e musu gidan baya suka zauna.
Raihana kwantar da kanta tayi jikin kujerar motar tana sauraron daddad'an k'amshin turaren shi daya kama motar.
Hijab d'inta duk ya jik'e da ruwa da yake roba ne sai duk ya fara lik'ewa a jikinta.
Kallo d'aya Ayman yayi mata a yanayin ya d'auke kanshi yana duba cikin motar, akwai k'aton bargon auntie sai ya bata ta sauya hijab na jikinta dashi.
Hannunta biyu rungume duka a k'irjinta ta kwantar da kanta tana jin yadda ruwa me k'arfi yake zuba kamar da bakin kwarya a lokacin, shi kuma Ayman ya d'auko wayar shi yana dannawa, a wannan yanayin raihana tayi bacci wanda yasa har aka gama ruwan bata sani ba.
Tsayawa Ayman yayi yana kallon fuskarta saboda dad'in bacci har bargon ya zame daga kanta sai manya manyan kitson kalba da suka sauko saman kafad'arta suna shek'i, a hankali yaja bargon ya k'ara rufe mata kanta ruff sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Agogon hannun shi yake dubawa lokacin sallah yayi har ya huce ana ruwan nan.
A datsin lokacin raihana ta farka ta dubi Ayman da idanunta da suka sauya kala, sai kuma ta watstsake fuskarta sosai, "yaaa Salam yau na rik'e ka ko?"
"Bake kika rik'e niba raihana ruwan da akayi ne".
Tare suka futo daga motar ita dashi hannunta d'auke da jik'ak'k'en hijab d'inta shi kuma leda, gabanta ya kewayo ya mik'a mata ledar ta karb'a tana yin godiya.
A gurguje sukayi sallama saboda duk gari ya d'au sanyi.

Raihana tana shiga hostel raheela ta tarye ta tana fad'in, "Amma dai ba'a inda kuke zama da Ayman yauma kuka zauna ba, saboda ana ruwan nan da hankalina yak'i kwanciya har lek'a ku nayi naga bakya nan".
Hijab da ledar hannunta ta ajiye, fatima tace, "ai da kin daina tunanin saurayin tane raheela, bashi bane Yaya Ayman ne tunda naga wannan ledar me tambarin M".
Matsowa raheela tayi kusa da ita tace, "har naji hankalina ya d'an kwanta indai Yaya Ayman ne ai munsan shi shekara da shekaru da sauk'i, wancan d'in ne dai har yanzu bak'o a gurin mu bamu gama sanin shiba tukun"
Raihana da fatima duk dariya sukayi mata.
Ledar daya bata ta zazzage turaruka ne masu tsada guda biyu, da kayan kwalliya na mata dangin su powder da janbaki, sai chocolates masu tsada guda hud'u.
Turaren d'aya ta d'auka, ta basu d'aya, powder da sauran tarkacen ta zuba su cikin kayan shafar su tace mun k'ara samun na shafawa, ta d'auki chocolate biyu ta basu dai d'aya.
"Ummm! Gaskiya raihana Yaya Ayman yana ji dake, kinji dad'in chocolate d'innan kuwa?". Raheela ce me yin wannan maganar.
Kallonta raihana tayi hadda wani lumshe ido take tana cin chocolate d'in da iya gaskiyarta, zungurar fatima raihana tayi tace, "kisawa mutuniyar ki waigi". Fayima tana dariya tace, "lallai kam Yaya Ayman ya iya kyauta, Allah kisha kiji da gaske take chocolate d'in da dad'i ba wai Santi bane".
Raihana tana zaro ido tace, "au kema?".
"Allah gata irin wadda kike so less sugar kuma creamer".
Guda d'aya ta d'auko cikin wanda tayi nufin ajiyewa muhibba mayyar kayan zak'i, ko data gutsira itama ala dole ta lumshe idanunta, raheela ta dafa kafad'ar ta tace, "raihana kinji ko? Wallahi Yaya Ayman ya iya kyauta, gaskiya ya kamata ki kirasa ki k'ara yi masa godiya".
Girgiza kai raihana tayi bayan ta gama cinye ta bakinta tace, "wannan ba kyautar Yaya Ayman bace, ta Auntie ce".

_Monday Tuesday, Thursday and Friday_


_comment and share_
24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page Eleven1️⃣1️⃣


"Wacece Auntie kuma?".
Raihana tace, "Kae! Auntie fa mahaifiyar Yaya Ayman ce".
"Au wai dama maman su kike nufi in kuna waya inji kina tambayar ina auntie". Fatima ce me yin wannan tambayar tana jefa chocolate baki.
Ita kam raihana murmushi kawai tayi ta gyad'a mata kai.
Haka dai suka yita cin chocolate suna magana kamar wasu tab'ab'b'u, a daren ranar raihana bata kwanta bacci ba saida sukayi waya da Ayman suka k'ara tabbatar da komai ya huce tsakanin su.


@@@@@@


Tun daga wannan rana raihana da Ayman suka ci gaba da zama lafiya kamar yadda suke a da, karatun su raihana ya d'au zafi saboda k'aratowar final year exams d'insu. Zuwan Imran biyu bayan wancen zuwan, shima duk bada amincewar taba sai dai ta ganshi unexpected, amma ana katari duk cikin zuwan bai tab'a zuwa ranar lahadi ba shiyasa basa had'uwa da Ayman da duk Sunday sai yazo har yanzu ba fashi.
Sosai Imran yake kashewa raihana kud'i har account no ta ya d'auka da wayo a wayarta yayi saving a wayarshi, lokaci bayan lokaci yana mata transfer na kud'i masu nauyi, ita dai raihana bata tab'a d'aukar irin kud'ad'en shiba har tsoro take ji ta nuna a gida, don tasan fad'a za'ayi mata ace tana sane ta bashi account d'inta, ba zasu tab'a fahimtar komai cikin sauk'i ta waya ba, amma tayi alk'awarin data koma gida zata fayyacewa ummie komai yadda zata fahimta.

@@@@@@


Rana na sauri wajen bada kwana, yayin da kwana yake saurin taruwa ya had'aa satittika, haka satittika suka bada watanni har gashi yau watanni biyu sun cika cif.
Raihana sun zana jarrabawar k'arshe lafiya har ana maganar a gobe in Allah ya kaimu za'a d'anka musu kwalin kasancewar su cikakkun malaman jinya wato (nurse), sunyi shirye shiryen su na d'alibai komai ya kammala, haka gidansu raihana ma shiri suke babu kama hannun yaro, saboda gida biyu da hidimar tasu ta kasu hadda na bikin khausar a week after raihana's graduation.
A daren ranar raihana kwana sukayi basuyi bacci ba suna koke koken rabuwa da juna da zasuyi, kowa ka gani cikin su idonta a kumbure saboda yawan kuka, ba dama d'aya ta kalli d'aya su had'a idanu sai kawai su b'arke da kuka, har cewa suke dama iyaye d'aya ne suka haife su su duka ukun.

_nace sai hak'uri dama haka sabo da shak'uwa suke_

Misalin k'arfe takwas na safe suka shirya cikin white and black uniform dukkannin su d'alibai 200 da za'a yaye a wannan rana.
An gayyaci manyan mutane masu muk'ami daban daban sunyi jawabai, haka wasu daga cikin d'alibai ma sunyi jawabin su. Abun gwanin burgewa da k'ayatarwa gurin kallo.
Basu tashi taron ba sai kusan 12 bayan ai baiwa kowa result d'inta a cikin su.
Nan fa kowa yayi gurin familyn shi don su gana, raihana da Ayman ta fara cin karo a lokacin da take futowa, kusa dashi Nur ce tayi kwalliya cikin wata tsadaddiyar doguwar riga maroon, tayi kyau sosai. Tun daga nesa data hango raihana take washe baki tana d'aga mata hannu, raihana ma tana murmushi ta k'araso suka rungume juna, "kece yau har garin mu Nur? Ni yaushe rabon ma dana ganki".
Nur tana murmushi ta karb'i kwalin hannun raihana tana fad'in, "ai dole nazo raihana tunda ta kama ni dole".
Duk sukayi dariya, sai lokacin raihana ta gaisa da Ayman daya kafeta da idanu yana kallon duk wani motsinta, tayi mishi kyau k'arshe sanye da kayan kamar ba uniform ba.
Sun tayata murna a nan kafun su futo tare su k'arasa inda y'an gidan su suke. Ga mamakin raihana sai taga auntien su Ayman tare da ummienta da iya suna hira k'asar rumfar da aka tanada domin bak'i, sai y'an matan familyn su dangin ta y'ay'an yayyen ummie guda biyu, har k'asa raihana ta durk'usa tana gaishe su, Suka amsa suna tayata murna, iya nata zolayarta, ita dai nauyin surayyah duk ya hanata kula iya yau, a gurin ma kasa tashi tayi saida auntien ta kamo k'afad'un ta duka ta mik'ar da ita zaune.
Kusa da ummienta ta k'arasa ta zauna gefenta ta kwantar da kanta a kafad'ar ummien, ummie ta dafa kanta tana tayata murnar kammala karatunta lafiya, jidderh da muhibba ma saida sukayi mata congrats, raihana ta mannawa auta jidderh peck a kumatu tace, "thank you auta".

Sunyi hotuna da wayoyin su na hannu da photographer da Abban raihana ya turo don shi bai samu damar zuwa ba, daga ummie sai muhibba da auta jidderh ne a y'an gidan su sai su hapser da sukazo su biyu.
Ragowar family suna gida suna dakon isowarta.
Basu bar makarantar ba saida raihana ta nemo su raheela suka gaisa da y'an gidan su, suma ta gaisa da nasu familyn. Sun rabu akan sai sunzo bikin khausar.

Wajen tafiya ummie da motar Abba suka koma, don a ita suka zo, surayyah kuma ta d'auki iya, raihana tabi motar su Ayman da Nur bisa takurawar Nur d'in. Suna tafe suna hira da nuriyyah da take front seat gefen habeebynta, duk rabin hirar akan banbance banbancen karatun su nema da wahalar da suke sha akan common diploma, Nur tana tayi mata complain na nadamar da tayi data sani ma degree ta nema tun farko kamar yadda auntien ta shaheeda tayi. Yayinda raihana take ganin diplomar ma ba laifi don dai an had'a suda wahalallen course me cin lokaci ne.
Suna k'arasawa anguwar su kowa yayi nashi guri don surayyah ko gidan bata shiga ba sukayi gidan iya ita dasu Ayman,
(Surayyah da ruqayyah suna huld'a amma irin baya bayan nan, idan abu ya faru na farin ciki ko jaje da taya murna, sukan jewa juna in sun samu labari, haka idan sun had'u suna gaisuwar mutumci, tsakanin su kowa na ganin girman d'an uwan shi).
Raihana kam godiya da sallama tayi musu ta shige gidan su.
Can ta tarar dasu Salma da baby samha, y'an uwan ummie da y'ay'an su duk sunzo anyi girke girke na alfarma, nan fa raihana aka had'u da family ana ta hirar yaushe gamo. Ummie komai da sukayi na taro saida ta aikawa su auntie dashi gidan iya.
Babu dangin abbansu ko mutum guda, sai abun ma yafi musu dad'i akan suzo suna d'auki ba dad'i. Haka sukayi taron su suka gama cikin lafiyar Allah. Dama a daren ranar raihana kashe wayarta tayi saboda takurar kiran wayar Imran.


**********


Washe garin ranar duk yadda Raihana take da sammako kasa tashi tayi saboda gajiya, duk jikinta banda nuk'urk'usa babu abinda yake yi. Koda ta tashi a late ta gabatar da sallolinta komawa tayi ta kwanta, har eleven tana bacci saida ummie tasa a taso ta kada yunwa tayi mata lahani sannan.
Bayan tayi breakfast ummie tasa aka d'auko kayan lefen khausar ta gani, babu laifi guy yayi k'ok'ari kusan set shida na akwatuna masu kyau da daraja, haka kayan ciki ya zuba kaya best quality masu tsada da kyau.
Raihana addu'o'i tayi sosai ta taya y'ar uwar tata murna da fatan samun zaman lafiya mai d'orewa a gidan aurenta.

A satin gadan gadan aka kama hidimar biki ba kama hannun yaro, shiri suke bana Wasa ba suna b'atar da kud'i kamar ba'a tab'a bikin wata yarinya a gidan ba
Family na kusa dana nesa duk sun hallara ana I gobe traditional sitting, Salma kuwa dama tun kwana uku da suka gabata ta tattaro tazo, gida ya cika Masha Allah sai son barka.
Ana I gobe kamu da safe ummie ta rabawa su raihana ankon su da aka kawo daga gurin d'inki, atamfa ta yini sai less da shadda, a hakan ma ummie complain take da ba'a yiwa raihana les d'in ba saboda sababbin kayanta ma da bata tab'a sakawa ba sun kusa goma. D'an kunne kuwa da sark'a ba'a k'aro mata ko guda ba, taji da wanda auntien Ayman ma take aiko mata lokaci bayan lokaci.
Salma da take karyawa a lokacin tayi ta mata dariya, tana fad'in in bata so a tattaro mata ita tunda ta k'i sawa.
Ummie da take zaune a parlon har lokacin tace, "Eh ke kuma ki kai naki tsumman ina? Ba gara raihana ba za'a ce rashin samun lokaci ne duk abinda za'ayi tana makaranta ko an mata anko sai dai a ajiye dole, ke kuwa kayan ne gasu nan lifdi lifidi ba kyauta ba sadaka wasu ma kin manta dasu suna can suna tsine miki a wardrobe".
Hucewa d'aki raihana tayi da kayanta tana dariya k'asa k'asa. Dama ummie ce maganin Salma ai wani lokacin.
Duka riga da skirt ne d'inkin sai shaddar akayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login