Showing 267001 words to 270000 words out of 288773 words
Chapter 90 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
dawo, amma wannan zuwan na bazata..... Ina fatan komai lpy".
"Wa nake gani kamar raihana?". Auntie ta fad'a tana kallon su da mamaki bayan ta ajiye ledar hannunta daga bayan su.......
_Kuyi hak'uri jiya wayata bata samu chargy ba shiyasa ban bud'e datan ba gaba daya_
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page seventy six 7️⃣6️⃣
Shiru tayi sai mama haleema ce tayi k'arfin halin cewa, "ba ita kad'ai tazo ba, ragowar suna jiran ki a parlour".
Ras! Taji gabanta ya fad'i, tsoronta d'aya kada ya zam khaleefa sakin y'ar mutane yayi, (kunji wani tunani kuma🤔) hankali a tashe ta nufi parlon, tun kafun ta k'arasa ta cire mayafinta ta rik'e shi a hannu don gumi ne yake keto mata tako ina, sai gyararriyar sumar kanta kawai a waje tana d'aukar ido.
Cak! Kwakwalwarta ta tsaya da aiki, numfashin ta ya d'auke na hucin gadi, haka duk jikinta babu inda baya rawa a lokacin da tayi 4eyes dashi.
"Su...ra...jjjj". Ta kira sunan shi kamar me koyon magana, shima mik'ewa yayi ya fara takowa zuwa gabanta har saida yazo daf suna kallon juna ido cikin ido sannan tayi k'asa da idonta ta juya a sukwane zata fuce, ya rik'e gefen rigarta da sauri, sai ta dawo tana fuskantar shi, ba wasa ko tsoro a fuskarta tace, "malam waye kai? Taya ma zaka shigo mun har k'arshen gida ba tare da neman izinina ba, silently move out tun kafun na kira maka police...". Ta k'are zancen tana nuna mishi k'ofa.
Murmushi yayi duk da jikin shi yayi sanyi, bashi da wani kwarin gwiwa daya rage mishi yace, "kiyi hak'uri! Tabbas ni mai laifi ne a gare ki surayyah, nasan na cutar dake na karya miki zuciya bayan tarin k'aunar da kika nuna mun, I'm serious sorry kiyi hak'uri ki gafarta mun".
D'ago kanta tayi ta kalle shi cikin son sake kwararawa kanta gwuiwa tace, "sorry for yourself, ka futar mun a gida malam don bansan shirmen da kake magana a kai ba".
Kama hannuwanta yayi duka biyu yana kallonta da rauni sosai ya sake cewa, "surayyah ki kalli cikin idona kice baki sanni ba da gaske".
Idanun nashi ta kalla, ta bud'e baki da nufin cewa wani abu khaleefa ya rigata ta hanyar mik'ewa tsaye yace, "enough! Ya isa haka Auntie! Ki daina duk wannan pretending d'in, koda kika kasance nesa da Abba! Soyayyar shi tana nan da ita kike rayuwa tsawon shekarun da kika kwashe, auntie don Allah ba tare da dogon jan aji ko yanga ba ki koma ga Abban mu mijin ki, don auren ku bai k'are ba ni naga shaidar hakan.....".
Duk kallon shi suke da mugun mamaki. Ganin irin kallon da suke mishi sai ya gyad'a musu kai cikin tabbatarwa, "nasan me nake fad'a don na samu hujjar ne daga gurin ki, kin tab'a fad'a mun Abban mu was a reasonable person, baya komai saida ajiyayyen hujja, shiyasa na duba cikin muhimman abubuwan da yakan ajiye cikin computar shi, a ciki na samo sak'on sakin ki da adadin nadamar da yayi bayan sakin da komai daya biyo baya, a nan naga abun ban mamaki da al'ajabi don ya k'are rayuwarshi yana neman ki da begen ki, Naga ninkin k'auna sau dubu akan wadda kike yi mishi,,,,,, auntie kamar yadda kika rayu babu aure haka Abban muma ya rayu babu mata, watak'ila ubangiji ya hallici ruhin kune don su kasance tare da juna, shiyasa zuciyoyin ku suke azabtuwa da rashin juna akan wani k'atoton abu daya gifta muke kiran shi k'addara..... Auntie ki duba da kyau ki auna shin a duniya zaki samu masoyi na gaskiya kamar Abban mu?, he's one in earth ba don ya kasance shi ya haife muba sai don babu kwatankwacin shi a halacci da soyayyah, shin kina tunanin kowane zai zauna cikin tsammanin warabbuka akan mutumin da bakasan bama koya mutu, ko yabar nahiyar da kake gaba d'aya....". Sai ya sake matsowa gaban su, "kiyi k'ok'ari ki fahimci waye shi Auntie, zan baku lokaci ku k'arasa warwarewa juna komai, ina zan samu mukullin b'angaren mu?".
Jikinta a sanyaye ta sake jan jikinta baya ta jingina da bango tace, "bedside drower ta bedroom d'ina". Sai ya juya a nutse ya d'auko mukullin, ya sake dawowa ya kewaye su ya huce ya futa yabar su a tsaye kamar bak'in juna. Bai nemi raihana ba ya bud'e part d'in ya shiga ya zauna ba tare daya damu da k'urar data cika ko'ina bare tunanin zai b'ata mishi kaya ba, kwantar da kanshi yayi ya lula duniyar tunani....
Ta b'angaren doctor surayyah khaleefa ne ya sanyayar mata jiki kwarai har ta rasa d'an kwarin gwiwar data fara tattarowa zatayi yak'i da suraj, maganganun shi sunyi tasiri a ranta da zuciyarta gaba d'aya sun k'arasa narke ta, musamman da yace akwai ragowar igiyar auren su bai k'are ba? Shin da gaskiya ya fad'a ko kuma yayi haka don kawai ya lausasar da ita? Taya ma hakan zata kasance bayan a gaban idonta momy ta umarce shi da yayi mata saki ukun? Duk da ita a lokacin bata yiwa takardar cikakken karatu ba ta sawa zuciyarta saki uku yayi mata ne a lokacin kawai shiyasa.
"Tunda khaleefa ya shammace ni ya binciko abinda nake son bawa mutane mamaki dashi sai ki zauna muyi magana ko?". Suraj ya fad'a a tausashe. A sanyaye ta k'arasa cikin parlon ta zauna a k'asa, shima gefenta ya zauna, bayan d'aukar wani lokaci shiru ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana cikin nutsuwa, "tabbas nayi kuskure, kuskure mai girman da bazan tab'a iya yafewa kaina inba ke kika yafe mun ba, a waccen ranar kina tafiya gaskiya tayi halinta, na duba duk Inda nasan zan same ki amma ban same kiba, nayi jinya mai tsayi har na fudda rai da rayuwa, surayyah komai ya faru cikin rashin sani da yanke hukunci cikin fushi...... Surayyah yaran mu sun bani labarin irin rayuwar da kukayi dasu da sadaukarwa da kikayi a kansu, babu abinda zance sai Allah ya saka miki da jannatul firdaus, yaci gaba da haskaka rayuwarki.....". Shiru tayi kafun can ta motsa bakinta kamar zatayi magana saita kasa.
"Surayyah sai dai Ina neman wata alfarma a gare ki, ki taimaka ba don niba, ba don halina ba ki amince a maida auren mu a karo na biyu..... Nayi miki alk'awarin ko zaki kashe ni bazan tab'a sakin kiba....". Ya k'are da kifa kanshi jikin gwiwar k'afar shi.
Ita kuwa takardar hannunta take ta dubawa kafun tsam ta mik'e ta futa daga d'akin, a kitchen ta tarar da mama haleema da raihana, duk suka yi shiru musamman raihana da take zaton ganin fushi ko b'acin ranta bisa ga k'aton kuskuren da sukayi mata, sab'anin tunanin ta sai ji tayi ta kalleta da cewa, "Raihana kina nufin har yanzu kina nan a zaune? Ya kamata ki nemi yaran nan masu share share kuje dasu side d'inku su gyara miki abinda ya kamata". Kanta a k'asa tace, "toh auntie". Saita mik'e ta d'auki jakarta kawai ta fuce. Ita kuwa mama haleema ta maidawa hankalinta, "kin gama had'a komai ne?". Mama haleema tace, "a'a saura kad'an dai".
"Ina so ki zuba abinda ya sauwak'a ki kaiwa bak'o a parloun k'asa".
Mama haleema tace, "toh ba damuwa".
Daga haka itama futa tayi har lokacin jikinta a sanyaye, mama haleema kuma ta fara k'ok'arin cika umarninta.
Lokacin da raihana ta shiga b'angaren su bata samu kowa a ciki ba, ita ta zage tare da yaran suka gyare sashen gaba d'aya, tayi wanka ta sauya kayan jikinta cikin wanda ta bari a gidan. Sai a lokacin ta nutsu ta fara cin abincin da mama haleema ta kawo musu.
Khaleefa kuwa bayan ya futo a gidan kai tsaye anguwar su iya ya nufa, yaci sa'a ya samu malam a k'ofar gida yana karatu da wasu magidanta da sukan zo gurin shi d'aukar darasi duk yammaci, tunda ya futo daga mota yake kallon shi cikin son tantance wanda idanun shi suke gani har yazo gaban shi ya durk'usa yana gaisawa da mutanen gurin.
"Ba don kar ace idanun tsufa ba da nace wannan Abdallah ne ba Adam ba.....".
Murmushi khaleefa yayi yace, "ka fad'a kanka tsaye malam".
Malam da k'arin mamaki yace, "toh Ina fatan dai lafiya? Ko kuma ka biyo jirgi ne kawai don ka gan mu ka koma?".
Murmushi ya sake yi yace, "ehh to kusan haka dai, zan shiga gurin iya idan kun gama sai muyi magana".
Malam yace, "toh madallah! Masha Allah ba matsala".
Iya tana zaune kan tabarma tare da wata y'ar dattijuwar mak'ociyar ta data shigo mata suna ta tattauna hirarrakin su irin nada, rik'e da hab'a iya ta tsaya tana kallon shi har ya k'arasa shigowa, "Kai kuma da baki kamar gonar auduga, da zuwa ba sanarwa ai saika fad'a mun abinda ta haifa tun kafun ka zauna ko?". Dariya yayi ba tare daya shirya ba, ya k'arasa kan tabarmar ya zauna ya fara gaishe da bak'uwar ta. "yau naga shegantaka irinta yaran zamani, yanzu kai ko y'ar kunyar nan da karar yaran fari baka iya ba? Dubi fa yadda yake dariya hajiya rabi matar sa tayi haihuwar fari".
Matar data kira da hajiya rabi tace, "to ai shi mai kunya nema cikin yaran zamanin nan tunda dai har a iya fuskarshi ake ganin farin cikin nashi".
"Allah ko hajiya?". Iya ta tambaya.
"Kwarai kuwa" ta bata amsa da tabbaci.
Shi dai khaleefa yana gefe yana ta kallon rikici iyakar shi. "malam baka fad'a mun abinda aka samu ba?". Iya ta fad'a tana kallon shi.
"Wai waye yace miki raihana ciki.... Cikine da ita, daga zuwan mutum ko jira ya zauna a gaisa ma baki yiba kin tsare shi da wasu zantuttuka da bansan inda kika samo suba".
"Kaci gidan ku! Ai tunda naga hak'orin ka a waje nasan zancen gizo ba zai huce na k'ok'i ba".
"Toh ni ba abinda ya kawo niba kenan". Ya fad'a yana mik'ewa zai shige d'akinta.
"Kar ka shigar mun d'aki kana bincike mun madafi".
Bai kula taba yayi shigewar shi ya kwanta saman doguwar kujerar ta.
_Bayan wasu awowi_
**** Malam da iya da suke gaban shi shiru duk sukayi suna sauraron shi har ya dire....
"Masha Allah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Hak'ik'a wannan abu yayi kyau yazo yadda ake saka ranshi, tabbas magaji kayi babban aiki ba abinda zamu ce sai Allah yayi maka albarka, yasa ka gama da duniya lafiya, kayi abinda ya kamata a gab'ar daya dace kam sosai.....". Malam ne mai yin wannan dogon bayani.
"Yanzu shi Abban naku yana can gidan ku?". Iya ta tambaya.
"Eh! So nake da malam ya gama cin abincin nan ma muje ku ganshi, duk da nasan auntie baza tak'i gabatar dashi a gurin kuba".
"Ai abinci bazai k'arasa shiga ba, Ina ganin abinda za'ayi zamu je mu ganshi don kamar yadda ka fad'a da gaske auren su bai k'are ba nima na gani a jikin takardar sakin farkon zuwanta gidan nan".
Kusan a tare motoci biyu suka Parker a k'ofar gidan, d'aya su khaleefa ne, d'aya kuma likita andal ce, momma da babban yayan su Suraj, sai suhaana da Ayman. Khaleefa ne ya musu jagora har cikin parlon k'asa inda aka gyara ma Abban su. Duk suka zauna a ciki har su malam da iya da suka zo tare dashi. Sun gaisa kafun Ayman yabi bayan shi su huce sama gurin Auntien, sun sameta tare da mama haleema, ba hira suke ba amma sun zauna ne jigum kowa da tunanin da yake tsakanin su. Shigowar su a tare yasa duk suka d'aga ido suna kallon su, "a'a saukar yaushe kuma Ayman?". Mama haleema ta tambaye shi, Ayman yace, "Eh wallahi yanzun nan na shigo tare da bak'i".
Auntie ce ta mishi wani irin kallo tace, "Kai kuma suwa ka d'ebo ka kawo mun gida".
Da sauri mama haleema ta katse ta, "duk wannan maganar fa ba taki bace uwar d'akina, tunda an gama magana meye kuma na dawo da hannun agogo baya".
Sai tayi k'asa da kanta ta dafe da hannunta d'aya, Ayman dai k'arasawa yayi gabanta ya durk'usa ya d'ora hannun shi kan k'afarta yace, "ki yafe mana Auntie in mun bak'anta miki rai cikin abinda mukayi da sunan gyara, amma bak'in da suka zo yanzun ba irin mahaifin mu suke a gurin kiba, bak'i ne da kuka rabu ba don kunso ba, bak'i ne da kika dinga rayuwa da tunanin su da musu fatan alkhairy tsawon lokaci a duk Inda suke sab'anin Abban mu.....".
Da sauri ta d'ago tana kallon shi kwakwalwarta na tuna mata wasu abubuwa da hankalinta ya fara zuwa kai tsakanin d'azu da yamma zuwa yanzun..... Saita mik'e tsaye kamar wadda aka zabura tana rarraba ido tsakanin shi da khaleefa tace, "yayana Sauban....".
Khaleefa da yake tsaye daga gefe har lokacin yace, "ba namiji bane macece wannan".
Saita kalle shi tsawon wasu mintuna kafun ta sauke ajiyar zuciya ta nufi hanyar futa a parlon sauri don tabbatar da zarginta. Duk suka bita da kallo cike da tausayinta.....
Mama haleema ce data tashi zata futa tace, "kunyi abu mai kyau y'an biyu....".
Ayman yana murmushi yace, "fiye da kaso 90 cikin d'ari na k'ok'arin khaleefa ne, don shi ya binciko komai nima bai fad'a mun ba sai kaini yayi kawai naga ni da idona".
Cikin jinjinawa mama haleema ta kalle shi, shima murmushin yayi yace, "nima bani nayi komai ba, raihana ce ta had'a komai da taimakon wata k'awar auntien y'ar k'asar su".
Mama haleema tace, "Allah sarki Allah yayi mata albarka, ai yarinyar nan macen arzik'in kace khaleefa, don Allah kada wani abu na zamani ya rud'e ka watarana kace zaka rabu da ita, don zakayi asara irin wadda ba zaka tab'a maye gurbinta ba, a k'arshe ka k'are da cizon yatsa.....". Kanshi a k'asa yace, "insha Allahu mama haleema zan ci gaba da rik'e ta bisa gaskiya da Amana". Tace, "Toh alhamdulillah Allah yayi muku albarka gaba d'aya kaida d'an uwan ka yaci gaba da haskaka rayuwarku". Suka amsa da ameen ta futa su kuma suka zauna cikin parlon.
*****Kamar a mafarki haka doctor surayyah taja tunga ta tsaya tana kallon mutanen da aka kira da suna bak'inta. Ita kanta k'awartata kallon ta take kafun ta tafi da hanzari su rungume juna suka fashe da kuka kusan a tare. Tsit parlon ya sake dawowa baka jin motsin komai saina sautin kukan su, zuciyoyi kuwa sun cika fal da tausayin su musamman ga wad'an da sukasan tarihin k'awancen su da shak'uwar da take tsakanin su.
Sai bayan sun gama koke koken surayyah ta durk'usa kanta a k'asa suka fara gaisawa da momma, itama kuka ta b'arke dashi ta durk'usa gabanta tana neman yafiyarta. Surayyah cikin jin nauyin matar tace komai ya huce a gurinta tuntuni ma.
Abubuwan da suka biyo bayan wannan had'uwa masu girma ne da ban al'ajabi, don surayyah taga k'auna a gurin mahaifiyar Suraj wadda bata tab'a zaton gani ba ko a mafarkinta. Suhaana dai sai raba ido take tsakanin k'ofofin parlon tana neman inda zata ga raihana tabar cikin wad'annan masu kukan.
Surayyah ta gabatarwa malam da iya kowa cikin Suraj da dangin shi harma da k'awarta da y'arta, suma ta gabatar da malam a gurinta, ta k'ara da basu labarin halaccin daya musu a rayuwa ita da yaranta. Duka suka yabawa dattijon taka irin ta mutanen, Suraj kam marking sunan malam yayi a zuciyarshi ya fara laluben tafkeken alkhairin da zaiyi mishi.
Bayan an nutsu malam ya kawo shawarar data kawo shi, duk shiru sukayi musamman Auntie dashi kanshi uban gayyar.
"Kuma fa abinda ka fad'a haka yake malam yusha'u, ina ganin tunda ga.... Nan sai ya zama wakilin shi Suraj, kai kuma ka zama na surayyah, don yanzu surayyah d'iya take a gurin ka".
Fuska ba annuri sam ta mik'e ta d'auki jakar kayan su andal tasa su biyo ta su tafi.
Bayan sun futa akaci gaba da tattaunawa tsakanin su malam har daga k'arshe akaci nasarar gyara wannan bantararren aure.
*Alhamdulillah! Burin mu ya cika an maida auren surayyah da Suraj*.
Khaleefa kuwa bayan futar mama haleema sun d'auki lokaci shiru kafun Ayman yace, "bansan me yasa mutane suke son ganin ka da raihana ba, bansan kuma me suke gani a kanku ba har suke yawan muku addu'ar kasancewa tare har abada bayan munfi dacewa ni da ita.....".
Wani mugun kallo khaleefa ya dinga wurga mishi ba tare da yasan ma yana yiba. Cikin basarwa Ayman yace, "meye kake kallona haka don na fad'i gaskiya".
Mik'ewa yayi ba tare da yace mishi komai ba zai futa a d'akin don maganar bakin shi ba zatayi dad'in ji ga Ayman ba. Da sauri Ayman ya mik'e shima yasha gaban shi yana dariya k'asa k'asa yace, "Wai meye duk hakane? Bayan munyi magana da kai ita matar ma dukanta tawa ce? Takardar sakinta kawai nake jira