Showing 255001 words to 258000 words out of 288773 words

Chapter 86 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1068

a muhallin daba nata ba" ta k'are tana nuna raihana da hannunta, dogon numfashi taja ta sauke ajiyar zuciya taci gaba da danne zuciyarta don kallon raihana ma kad'ai gabanta tsaye khaleefa rik'e da hannunta raise her blood soo high, tayi imanin khaleefa ya barta kenan har abada ko yanzun data kalli kwayar idon shi k'iyayyarta ta gani fal, shiyasa zatayi amfani da wannan damar ta bud'e mishi aiki ta yadda ita kanta yarinyar zata gane shi din kura ce da fatar akuya, tasan babu wani namiji da zaije neman aure ya ya bawa budurwa labarin irin soyayyar da sukayi dashi, lallai kuwa in hakane khaleefa yasan wata ne baisan wata,
Shi kuwa ganin tayi shiru saiya hard'e duka hannun shi a k'irji yace, "magana nazo yi dake ba neman fitina ba". Ya rik'e k'afad'un raihana duka biyu, suka kalli juna na wasu sakanni sannan yaci gaba da cewa, "wannan da kike gani saboda shawara da jajircewarta nazo gurin ki muyi magana ta fahimta, sai dai Ina ganin idan hakan ba zai yiwu ba babu lallai babu dole".
Sai ya juya da baya ya kamo hannun raihana da nufin tafiya.
Jikin raihana a sanyaye matuk'a ta zame hannunta ta tsaya tana kallon shi tace, "kayi hak'uri amma tana akan gaskiyarta ne, komai yana buk'atar sirri a rayuwa... Soo kar ka damu ni zan jira ka a waje". Ta k'arasa fad'a tana jin wani abu na sukar zuciyarta, tun farko da tasan nan zai zo ba zata tab'a yarda ta biyo shiba bare har budurwarshi taji haushinta a banza, saita fara k'ok'arin barin gurin. Sake rik'o hannunta yayi, "Ni dake duk abu d'aya ne raihana! Bazan iya magana da ita muddin ya zamana babu ke ba,,,, kinfi kowa sanin saboda ke da Ahmad nazo gurin ta". Saleema ganin da gaske khaleefa juyawa zaiyi ya tafi saita shanye b'acin ranta, takaicinta, had'e da ruwan hawayen ta tace, "khaleefa yanzu kana nufin wannan tafi ni? Da gaske zaka iya barina har abada saboda kaa same ta? Shin dama haka soyayyah take? Shin wannan shine alk'awarin da kayi mun?.....". Ta gama jera tambayoyin tana fashewa da wani irin kuka. Shi kuwa juyowa yayi yana kallonta, "ga zahiri ma kin gani, in kin manta na tuna miki komai na duniya yana da deadline, Sam a soyayyar da nake miki babu wani abu mai kama da k'arya ko yaudara, ke kika juya komai kika samun k'iyayyar ki cikin zuciya da abinda idanuna suka gani zahiri, sannan ke in banda son zuciyarki taya kike tunanin zanci gaba da sonki bayan na ganki da idona kina..... Wallahi kin bani mamaki, Ashe duk kallon da nake miki ungulu ce ke da kan zabo....". Ya k'are zancen da wani tuk'uk'uk'in bak'in cikin da yake taso mishi a duk lokacin daya tuna irin rayuwar da sukayi a baya. Sai yaci gaba, "duk da haka zan fara da miki godiya, ta silarki gashi na samu mahaifina, a waccen ranar da bamu samu sab'anin nan dake ba, da bazan tab'a tunanin nemo wani daya danganci dangin mahaifina har abun ya kai ga samun babbah jigo da yafi kowa a cikin familyn su muhimmanci ba wato mahaifina! Abu na gaba na janye duk wani alk'awarin aure na a kanki, soo ki saki ranki, kiyi abinda ya kawo ki.... A alak'armu kema kinsan ba cuta ba yaudara, komai ya k'are Ina fatan zaki yafe mun keta iyakar daba tawa ba da nayi.... Wannan shine ainahin abinda ya kawo ni".
Saleema da take kallon shi kuka takeyi sosai, ta kasa cewa komai sai kallon shi kawai take shida matar shi, matar data nuna tamkar bata gurin yake duk wad'annan maganganun.
Khaleefa kam sake rik'e hannun raihana yayi, ta rintse ido tana jin zuciyarta kamar ta futo, tayi k'asa da muryarta ta yadda saida ya d'an rankwafo kad'an yaji abinda take fad'a, "don Allah ka sake mun hannuuu...na". Wani miskilin murmushi yayi yana kallon kwayar idonta yace, "ko?". Ta gyad'a mishi kai. Tsayawa yayi kawai yana kallonta, yadda gaba d'aya ta kasa sakewa duk jikinta sai rawa yake ya matuk'ar bashi dariya amma baiyi ba ya dake, ga wani kyau na musamman data sakeyi mishi kamar ya saceta ya gudu (toh sace ta mana Ina ruwan wani🤣). Yadda ya shagala da kallon raihana sam sai ya manta da kanshi bare wata Saleema karan kad'a miya da take tare dasu a lokacin. Wadda ita kuma bak'in ciki ne ya sake turnike ta ta sake tunzira tace, "bazan tab'a yafe maka ba kuwa khaleefa don ka matuk'ar cutar dani,,,, tunda har kasan ba zaka aure niba amma ka dinga amfani da soyayyar da nake ma kana rayuwar data keta k'a'ida, khaleefa har ciki kayi mun fa in ka manta in tuna maka... Macuci! Mayaudari!! Mahainci!!!".
Kusan a tare raihana da khaleefa suka rintse ido suna jin saukar zancen kamar ruwan dalma me k'arfin narka zuciya, khaleefa kam hannun raihana yaja sukayi gaba don muddin yaci gaba da sauraron kalaman bakinta masalahar da yazo don a samar ba zata samu ba. Sunyi tafiya mai nisa yana rik'e da hannunta, tsabar yanayin da yake ciki yasa baya ganin inda yake d'ora k'afar shi sam. Unexpected yaci karo da wani dutse ya dake shi kuwa, ya saki hannun raihana da take bayan shi da sauri ya durk'usa a gurin yana kallon inda dutsen ya daka har jini ya taru ga k'afar sai zugi take mishi. A nutse raihana ta k'araso gaban shi ta durk'usa itama kamar yadda tayi tana kallon ciwon da yaji da fuskar tausayawa, hannunta ta kai gurin ta d'an matsa, aikuwa khaleefa baisan ya mik'e ba sai ganin shi yayi kawai a tsaye, itama ja baya tayi tace, "sorry". Bai kula taba yaci gaba da tafiya tabi bayan shi. Duk da tazarar dake tsakanin su bai damu ba haka ya dinga tafiya a k'afa bashi da niyyar tare musu motar haya, tun tana kawaici har ta gaza saboda takalmin k'afarta bazai iya d'aukar ta har zuwa inda yake so ba ga tafiyarshi da sauri. Bai fahimci shi kad'ai yake tafiya ba har saida ya daina jin sahunta a bayan shi, Koda ya waiga tana can baya a zaune kan wata kujera ta dafe kanta da hannunta. Sai a sannan ya gano girman kuskuren da yake son aikata mata. Taxi ya nema ya mishi bayanin inda zai kaisu suka k'arasa inda take ta shiga suka huce gaba d'aya.

**** Suna komawa ya shige d'aki raihana bata sake ganin shiba saida ta futo janye da trolley waya kare a kunnenta suna magana da likitar. A lokacin shima ya futo cikin sabuwar shiga ta wasu expensive English wears, fuskarshi a d'inke tamkar bai tab'a dariya ba, hakan yasa raihana sake kama kanta ta dakata da wayar sai dai idonta na kan k'afar shi tana kallon yadda yatsu uku suka kumbura, Koda ta d'ago ta kalli fuskarshi ido suka had'a, ta maida kanta gefe da sauri ta nufi hanyar futa.
Tsaye tayi a wajen ta k'urawa gidan Ahmad ido, tana fatan yasmine ta lek'o suyi sallama tunda khaleefa ya hanata shiga.
Har ya gama rufe gidan ya k'araso gidan take kallo, shima gidan ya kalla sannan ya maida duban shi gareta, "kije kuyi sallama, amma kada ki huce minti uku...". Kamar ta share shi sai kuma taga rashin dacewar hakan, koba komai ba shi zata kalla ba, hak'k'in mak'otaka da mutumcin yasmine d'in zata duba. A nan tabar duka jakunkunan ta ta nufi hanyar shiga gidan. Khaleefa yabi bayanta da kallo yana jin wani irin tashin hankali na musamman na kawo mishi ziyara, "bansan wanda yafi buk'atar kiba nida Ayman! Duk dani tarin laifuffukana zasu iya mun katangar k'arfe da samun soyayyar ki, tabbas zan kasance cikin tarihin mazan da soyayyah tayi wasan kura dasu...... Saleema!". Ya k'are fad'a yana jin sabuwar tsanar ta a ranshi.
"Wace irin tafiya kuma a irin wannan lokacin? Ina fatan ba wani mummunan abune ya faru a can Nigeria ba".
"Ko d'aya, duk da nima bazan ce komai ba tunda ba nice dalilin tafiyarba khaleefa ne". K'asa tayi da kanta idonta yana cikowa da hawaye, "zamu tafi Yasmine watak'ila ni ba lallai na dawo ba, Ina fatan zaki yafe mun abinda nayi miki na k'untatawa cikin ajizanci da kowanne d'an Adam baya rabo dashi, Allah ya raba ki da abinda ke cikin ki lafiya ya k'addara saduwarmu da alkhairi". Yadda ta k'arasa fad'a tana wiping tears haka yasmine ma ta fara magana cikin kuka, "haba mana ya zaki ce ba zaki dawo ba, so kike nima zaman k'asar ya gagare ni kenan? Raihana don Allah kada ki k'i dawowa, in kuma ba haka ba in bar Ahmad na biyo bayan ki....".
Duk yadda raihana take cikin k'unci saida murmushi ya sub'uce kan fuskarta, haka duk suka hau dariya suna share hawaye kafun su rungume juna. Sam Yasmine hana ta futa tayi tana ta karanta mata sak'onnin gaskiya da rok'on ta dawo bada jimawa ba, suna haka khaleefa ya kira wayar raihana, ta k'arasa sallama da Yasmine da sauri ta fuce, har ya tare musu mota ya shigar da kayan ciki.

***** Tafiya suke cikin babban filin tashi da saukar jiragen kowa rik'e da jakar kayan shi, suna tafe raihana nata waigen inda zata hango likitar sai dai basu had'u ba, ta d'ora k'afarta kan matakalar shiga cikin jirgin taji kamar an dake ta har tana neman fad'uwa, koda ta juya wata kyakkyawar matashiyar yarinya budurwa ce, da tafi kama da Arab a fuska ma kamar ta santa, kafun tace wani abu yarinyar ta riga ta da cewa, "am sorry please". Ta gyad'a mata kai taci gaba da tafiyarta har yarinyar na bin bayanta tana ta magana a waya.
Kusan a cikin jirgi ma haka ta gama bulayin kalle kallenta amma ba inda taga doctor andal bare mai kama da ita.

*After some hours*
Jirgin su yayi landing a Abuja lafiyar Allah, passengers duk sun fara sauka, suna tafe ita da khaleefa yanzun ma dav da dab sai bin takun shi raihana take har Allah yasa suka isa inda wata mota ke jiran su, shi ya bud'e mata back seat ta shiga shi kuma ya shiga mazaunin gefen driver. "U are welcome matar big bro" Ayman ya fad'a ba tare daya kalleta ba. Murmushi ta k'ak'alo ta fara gaishe shi, ya amsa a tak'aice ya maida akalar hirar shi ga d'an uwan shi. Haka sukayi ta hirar su har Allah yasa suka k'arasa hotel d'in da ya musu booking d'aki. Suka shiga har Ayman daya taimaka wajen shigar musu da jakunkunan kayan su. Room and parlour ne sai toilet a parlour bathroom a bedroom. Bata zauna a parlon ba tayi bedroom don gabatar da uzururrukanta.
Khaleefa ke tambayar Ayman ina ya samu mota? Ya fad'a mishi gidan su abokin shi daya sauka. Daga nan duk sukayi shiru, yana son shiga gurin kayan shi baya son shiga hak'k'inta, k'arshe dai ya hak'ura yayi amfani da toilet na parlon ya d'auro alwala ya futo nan ya sauke faralin sallolin da suka huce shi.
Ayman bai yarda sunci abincin hotel d'in ba yaje da kanshi gidan abinci mafi kusa ya musu oder abincin Nigeria irin wanda yasan sun jima basu ciba.
Yana tahowa zai shiga ita kuma tana tahowa zata futa, waya ce kare a kunnenta tana magana cikin matuk'ar zafi but a sanyaye, tana yi tana duba bayanta kamar tana tsoron wani yaji abinda take fad'a, tunda ya d'ora idon shi a kanta ya kasa d'aukewa, so yake ya takaita abinda yake ji a kanta amma ya kasa, har tazo dab dashi a lokacin itama idonta ya fad'a kanshi, ta d'auke kanta tana son tuna inda taga fuskar a dai dai lokacin da take k'arasa wayarta cikin harshen Arab, "Eh! To ammie ce taje had'a wasu y'ay'an k'awarta da mahaifin su, Ni kuma ban Isa masauki ba saida na nemi sim card na kira ki don kawai na fad'a miki yadda mukayi dashi, da yadda zamu kawo k'arshen komai ba tare da mun gogawa ammie laifi ba okay". Iya abinda kunnuwan shi suka ji kenan ya gifta ta itama ta giftashi ta huce. Kusa da d'akin daya kamawa su khaleefa wata mata ta futo me dattako da matuk'ar nutsuwa. Har zai huce ta sai kuma yaga tana ta kallon shi, hakan yasa yace mata "sannu". Murmushi tayi da yaren da tasan yafi fahimta tace, "kaga mun had'u a k'asa d'aya ko khaleefa?". Ayman shima murmushin yayi yace, "I'm sorry amma... Ba khaleefan bane Ayman ne".
"So he's your twin?". Ta tambaye shi, ya gyad'a mata kai, murmushi ta sakeyi, ya tsaya yana knocking k'ofa, few minute khaleefa yazo ya bud'e mishi ya shiga ciki. Yana zama cikin parlon yana fad'in, "yanzu wata ta ganni ta kira sunan ka, bansan sai zuwa yaushe mutane zasu fara banbance muba". Khaleefa tattare mishi hankalin shi yayi gaba d'aya yace, "a nan Abuja kuma? Cikin hotel d'in nan?".
Ayman ya gyad'a mishi kai cikin tabbatarwa kafun ya fara warware mishi yadda sukayi, bayan ya nisa ya sake tambayarshi, "how does she looks like". Ayman ya mishi kwatancenta, a take tunanin shi ya bashi andal ce, toh amma ba zaiyi saurin yanke hukunci aje kuma ba hakan bane.
Khaleefa ya mik'awa raihana abincinta, Ayman kuma suka ci tare da d'an uwan shi, bayan sun nutsu yake tambayar shi dalilin wannan zuwan bazatan daya gayyato shi. Murmushi khaleefa yayi don shi kanshi in za'a kashe shi baisan amfanin zaman da zasuyi a hotel d'in ba, abu d'aya daya sani raihana ta tabbatar mishi zai had'u da mahaifin shi that's all he know, shiyasa koda Ayman ya jefa mishi tambayar ya d'auke wuta, bai damu da lallai sai yaji ta bakin shiba shima ya mik'e yana mishi sallama kafun ya tafi.
Kamar wanda ake umarta haka ya dinga waigen k'ofar d'akin da yaga budurwar nan ta futo d'azu, hoton fuskarta na gilmawa ta cikin tunanin shi, take wani sabon tunani kuma ya fad'o mishi, saiya tsaya cak gaban shi na fad'uwa da sauri, lallai kam akwai abun dubawa cikin abinda zai kawo ta hotel ita kad'ai ta kama d'aki indai ba tare da mijinta tazo ko wani muharraminta ba? tunda dai nan Nigeria ne, k'asar da y'an k'asa suke kama d'akin hotel ba don sun rasa gidan zama ko sun kasance bak'i ba, a'a sai don kawai suna da harkokin banza da suka maida hotel d'in muhallin aikatawa, to ya kenan idan ya kasance da saurayi tazo? Koda yake ba y'ar k'asa bace, toh ko dai da mijinta tazo?...... Sai ya waiga yana sake kallon hanyar data bullo d'azu, kamar wanda aka umarta kuma yaci gaba da tafiya da sassarfa har ya fuce.

****A daren ranar khaleefa yana da tambayoyi da yawa da yake son yiwa raihana, sai dai bai samu damar hakan daga gare taba, already tayi bacci lokacin daya lek'a ya d'auko jakar kayan shi d'ungurungum zuwa inda ya zab'a ma kanshi matsayin gurin kwana wato parlour.

****A washe garin bayan sun karya kumallo da lafiyayyen breakfast da khaleefa yayi order, raihana tayi shirinta mai kyau cikin kayan da suka dace da jikinta, tana son magana da doctor andal amma batasan ko ta Yaya ba, tana zaune a gefen bed shiru khaleefa yayi knocking yana neman izinin shigowa, ta jawo gyalenta kamar bak'on mutum shi d'in a gareta ta yafa sannan ta tafi donta bud'e mishi k'ofar.........

Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu, wallahi abubuwa da yawa sun sha kaina, amma insha Allah cikin satin nan zanyi k'ok'ari mu rufe littafin gaba d'aya, inda zamu zo muku da sababbin littattafan mu masu d'auke da sabon salo........ Kada ku manta👇
Doctor ferhyeezz m usmern ce, and merhreeyaert lerwerl as in-identical twins


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy three 7️⃣3️⃣


A tsaye yake hannun shi duka biyu zube cikin aljihun wandon shi, yanayin fuskarshi kadaran kadahan ya tsaya yana kallon yadda ta wani rik'e handle, baiyi niyyar shiga ba amma yadda tayi d'in ya sashi nufar ciki direct. Saita kauce ta bashi guri ya shiga ya maida k'ofar ya rufe. "Ina... yin... Ina kwana". Ta harhad'a zancen da kyar, Yace, "lafiya lou fatan kin tashi lafiya".
Bata amsa ba, Shiru duk sukayi shi yana ta aikin k'are mata kallo irin wanda ya sata jin matuk'ar nauyin shi, ya kuma kasa d'auke idon shi a kanta duk yadda ya kai ga son aikata hakan. Tuna abinda ya shigo dashi ya sashi mik'a mata farar takardar hannun shi, "doctor andal ta turo wannan a baki". Karb'a tayi ta fara duba takardar mai d'auke da gajeren sak'o kamar haka. "ki zama ready k'arfe uku dot mu had'u a reception" ta d'ago ta kalli khaleefa da yake kallon rufin d'akin, "ita ce ta baka da kanta?".
Ya tsaya still yana kallonta da karantar yanayin da take ciki k'arara a kwayar idonta, sai yayi murmushi don ya tabbatar da hasashen shi tun kafun aje da nisa. Baice mata komai ba yasa kanshi ya fuce bayan ya dannawa Ayman kira ya mishi bayani kamar yadda aka yiwa raihana, sai dai ya buk'aci da yazo da wuri kafun lokacin.
Haka kuwa akayi Ayman ya tak'aita duk wani abu da zaiyi ya taho da wuri kamar yadda khaleefa ya buk'ata duk da dama bawai yana da abubuwan yi da yawa a garin ba, babban mak'asudin zuwan shi khaleefa ne, kuma yazo da tarin tambayoyi fal a bakin shi, sai dai yana ta hak'uri da dannar zuciyarshi kada ya nuna rashin hak'uri tun kafun aje da nisa.
Suna zaune kusa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login