Showing 237001 words to 240000 words out of 288773 words

Chapter 80 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1099

zuwa lokacin da zaka gama bawa patient d'inka kulawa ta musamman ya samu lafiya sosai.... Ina fatan ka fahimci abinda nake nufi?".
Ahmad cikin ladabi yace, "eh! Insha Allah khaleefa ba zaiji komai daga abinda na sani ba har sai bayan komai da kika tsara ya kammala yadda kike so".
Tace, "gud! nagode sai ka jini".
Daga haka kuma sukayi sallama ya futa a office d'in ita kuma ta fara had'a yanata yanata.

Hannunta rik'e da car key nata da Jakarta ta k'arasa ofishin khaleefan, yana kwance a resting chair ya lula duniyar tunani ko lissafin tafiya gida ma ba yayi lokacin data mishi knocking k'ofar.
Bai bud'e ba haka bai bada izinin shiga ba ya tashi yana had'a duk abinda yasan zai tafi dashi gida, rataye da jakar computer shi, hannun shi kuma rik'e da labcourt da tea plask k'arami ya bud'e k'ofar ya futo.
B'oyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi kafun tace, "har na fara tunanin ko ka tafi ma".
"Ai munyi magana bazan tafi ban jira kiba".
"Hakane! Toh amma kasan neman me nake maka ne?".
"A'a" ya bata amsa.
"Gidan ka nake son muje".
Da sauri ya d'ago ya kalleta sai suka had'a idanu, wani kwarjinin ta ya cika shi. Baisan ma'anarta ta binshi gidan ba, amma koma meye ba matsala, shiyasa baiyi mata musu ba suka tafi tare har inda ta Parker motarta.

****** Raihana kuwa tana can cikin laluben hanyar da zata shawo kan matsalolin khaleefa da yadda zata fara fuskantar su, gaba d'aya kwanakin da suka biyo baya tunaninta kenan.

Tana zaune a parlonta tana nazarin littattafan makarantarta wayarta ta fara ringing, koda ta duba taga no ummie bata d'auka ba don tasan maybe su hibbatullah ne suke son magana da ita ta watsapp.
Tana bud'e data taga rututun missed call daga gurin su, tana shirin kiran su suka riga ta, tayi picking ta saka su a handsfree tana fad'in, "Ni na mayi fushi kwana biyu kun manta dani babu wanda ya kira ni cikin ku, Ni in na kira kuma bakwa d'auka.....".
Daga chan b'angaren muryar ummie taji cikin wayar tana farawa da mata sallama, saita nutsu suka fara gaisawa da ummien taji lafiyar kowa cikin mutanen gidan dama y'an uwa duk da tana yawan gaisawa da kowa musamman ta watsaapp.
"Ina son kiran mijin ki na kasa, don Allah ki mik'a sak'on godiyarmu gare shi...".
"Ummie Yaya khaleefan ya muku wani abu ne?".
"babba ma", Nan ummie ta bata labarin duk abubuwan daya aikawa su al'ameen, abun ma mamaki ya bata saboda ita dai ba tasan lokacin daya bawa auntie kayan ba.
Bata b'oyewa ummie ba ta fad'a mata ita bata sani ba amma zata mik'a sak'on su gare shi inshaa Allah.
Basu jima suna tattaunawa ba sukayi sallama bayan raihana ta gama complain na rashin magana dasu hibba kwana biyu, ummie ta mata bayanin sun fara exams ne Abba yace a daina basu wayar har sai sun gama dom sufi maida hankali, raihana ta musu addu'ar samun nasara da fatan alkhairy.
Littattafanta ta had'e guri d'aya ta dawo da nufin kwanciya aka tab'a k'ofar.
Koda ta bud'e yasmine ta gani, sai ta bata hanya ta shigo ta maida k'ofar ta rufe. A nan parlon suka zauna raihana tana mata sannu.
Ko amsawa bata iya ba saida ta kwanta ta huta sannan.
"Wai har yanzu jikin ne?" Raihana ta tambayeta.
Yasmine cikin shagwob'ewa ta fara kuka tana fad'in, "Ni wallahi na gaji gidan mu zan tafi haka kurum ciwo yana son kashe ni a hana ni yin bankwana da iyayena".
Cikin nuna damuwa raihana ta sake dawowa kusa da ita tana sake tambayarta, "wani abun ya sake faruwa ne?".
"Meye ma bai faru ba bayan nace a cire cikin nan Ahmad yak'i, kullum fa sai nayi amai, kuma komai ma bana ci naji dad'in shi, ga yawan bacci kamar y'ar syrup.. Allah in na fara baki labarin abubuwan da nake ji a jikina sai mun yini ban gama fad'in komai ba".
Raihana dafe kanta tayi a zuciyarta tace, ohh yasmine rigima!
A zahiri kuwa gyara zamanta tayi tace, "haba yasmine kada ki bada mata mana tun kafun aje ko'ina! Ke bakya son ganin d'anki ne a duniya kike son kora shi kwata? Sannan taya ma Allah zai haramta abu ke ki hallata shi, kowacce mace ba da haka ta Zama uwa ba? Shin iyayen mu suna kwance ba tashin zuciya suka haife mu? Me yasa su suka hak'ura suka jure komai? in da sun kasa jurewa za'a gan mu a duniya? Amai! Tashin zuciya! Da yawan barci sune kacal matsalar ki? Toh in kika ji matsalar wata ta ninka taki, kuma a haka munna take tana godewa Allah bisa babbar kyautar da yayi mata, wadda babu wanda ya Isa maka ita a duniya sai shi.... Shin mutum dubu nawa ne suke neman haihuwar ruwa a jallo basu samu ba?, ko kinsan akwai wadda ko ana suma ana mutuwa tun daga wata d'aya har tara zata jure? Don haka tun wuri kiyi istigfari kada ma ki kuskura mijin ki yaji don duk sonda yake miki sai ranshi ya b'aci".
Cikin sanyin jiki yasmine ta gama sauraron naseehar raihanan, sosai maganar ta shige ta har taji nadamar duk abubuwan data yiwa Ahmad a safiyar yau daya kaisu har da rigima ya futa yana fushi da ita.
"Aikuwa na fad'a mishi har munyi fad'a dashi ma d'azu".
"Raihana cikin kulawa kanta tace, "ohf! Amma Kinyi kuskure duk da kina da sauran lokacin gyarawa, yanzu dai ki fara K'arfafa jikin ki yadda zai dawo anjima ya ganki kamar sabuwar amarya ni kuma zan Miki dilke da halawa na musamman".
Murmushi tayi ita kuma raihanan tayi dariya.
Haka ta dinga janta da hira tana mata nasiha cikim hikima har ta sake sakin jikinta da kyau, gyaran jiki mai kyau ta mata hadda turaren jiki dana gashi, nan da nan kuwa ta d'au sirrin k'amshi.
Bata bar gidan ba sai yamma lis, shima raihana ce tace tayi maza kada ya dawo gidan yaga bata nan ranshi ya sake b'aci.

Koda yasmine ta futa raihana bata zauna ba saida ta gama girkin abincinta na dare gudun kada khaleefa yau ma ya dawo da yunwa irin rannan.
Tayi kwalliyarta cikin doguwar riga irin mai kama da laffayar nan in aka nad'a gyalenta, ta nad'e gyalen a jikinta bayan ta shafa powder da lip balm a lab'b'anta, tayi sihirtaccen kyau mai fizgar hankali sai baza k'amshi take duk inda ta motsa.
Tana futowa d'akin zata shiga kitchen taji ana murza key na gidan, tsayawa tayi chak ba tayi gaba ba bata yi baya ba har ya shigo doctor andal na biye dashi rataye da Jakarta.

"Sannun ki da zuwa". Ta fad'a cikin harshen turanci tana nufar inda khaleefa yake tsaye.....
Andal ta zubawa yarinyar idanu tana kallonta da nazarin inda ta tab'a ganinta ko saninta.

_kuyi hak'uri wanda basu ga uzurin dana bayar ba, masu comment ina sake godiya da jinjina👍👍_

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page sixty seven6️⃣7️⃣


Har ta karb'i jakar hannun khaleefa suna tsaye a inda suke basu motsa ba, sai ta koma gefe ta sake ce musu "Bismillah". Sai a lokacin duk suka dawo daga d'an k'aramin tunanin da suka fara tafiya andal ta k'arasa cikin parlon ta zauna, khaleefa kuma ya nufi kitchen.
Raihana kuma d'akin shi ta nufa da jakar computer shi ta ajiye mishi ita gefen drower.
Koda ta futo har khaleefa ya gabatar mata ruwa da tea, daga kujerar da yake zaune ta zauna suka gaisa da bak'uwar tata da bata san daga inda take ba. Ta dai k'ok'arta sun gaisa da Arab.
Sai bayan sunyi shiru andal ta gane ashe ba inda ta tab'a saninta kawai yanayin dressing d'inta da k'amshin gidan da taji ne take tunanin ko itama asalin ta Sudanese ce, hakan ya k'ara mata k'arfin gwiwar tambayarta, "ke y'ar wace k'asa ce?".
"Nigeria" ta bata amsa bayan gama dogon nazarin fahimtar kalamanta da kyar.
"Baki da kowa a Sudan?".
Wannan karon khaleefa ne ya bata amsa, "hausa fulani ce bata had'a komai da Arab ba".
Shiru tayi tana nazari kafun can ta sake cewa, "Amma zanso sanin yadda ta samu sirrin matan mu har ta rik'e shi da kyau haka?".
Khaleefa saida yayi shiru sannan ya bata amsa, "mamana ce!".
Wani abu ya sokawa andal a k'ahon zuci, kamar tace surayyah ko? Sai kuma ta sake danne zuciyarta gudun kada ta fallasa kanta da gaggawa ta ba khaleefa damar gano manufarta tun kafun aje ko'ina.
Raihana tashi tayi ta zuba ma matar abincin data dafa ta kawo mata. Ganin zata ci abincin sai duk suka tashi don su bata guri.
"Ya zaku tafi Kuma! Mrs Abdallah ina son magana dake fa". Ta fad'a da harshen turanci yadda raihanan zata jiyo ta.
Komawa tayi ta zauna shi kuma khaleefa ya shige d'akin shi.
Taci abincin bada yawa ba tasha tea kafun ta fuskanci raihana da kyau, "sunana andal.... Ni abokiyar aikin khaleefa ce, nazo ne don sanin gundarin abinda yake damun mijin ki har yasa baya maida hankali kan aikin shi idan ba zaki damu ba?".
Shiru raihana tayi tana tunanin abinda maganganun matar suka k'unsa, sai kuma sunanta ya sake dawowa cikin kunnenta, "andal" ta fad'a da sauri bayan ta d'ago ido ta sake kallon matar.
Itama kallonta take yi, hakan yasa ta maida idanunta k'asa tana ci gaba da maimaita sunan a zuciyarta.
"Ke nake saurare meye sunan ki?".
Ba tare data d'ago ba tace, "Raihana".
Andal tace, "Masha Allah! Sai dai ince kiyi hak'uri raihana watak'ila nayi miki shishshigi cikin al'amuran ki ko? To amma tunda farko na fad'a miki dalilin zuwana, sai dai tunda kin zab'i sakaya sirrin mijin ki ina ganin zan baki wasu y'an shawarwari, a rayuwar auren ki kada ki tab'a yadda ace mijin ki ya samu matsalar da ke baki San da ita ba, ya kamata ace duk abinda ya samu mijin ki ke ya sama ta yadda zaki fishi damuwa da son ganin kin magance mishi duk wata matsalar shi".
Still kanta yana k'asa tana wasa da yatsun hannunta.
Andal tayi murmushi kawai kunyar yarinyar sai ta shiga ranta har taji ta burge ta, jakarta ta d'auka ta duba lokaci taga ana gab da kiran sallar magrib.
"Shawara ta k'arshe kuma mijin ki yana buk'atar kulawa ta musamman daga gare ki ko bai fad'a ba ya kamata ki gane hakan ta hanyar amfani da baiwar da Allah ya baki". Ta k'are fad'a tana mik'ewa tsaye, "Ni zan tafi ina fatan zakiyi nazari akan takaitacciyar shawarata".

Itama raihanan mik'ewa tayi tace, "na gode in shaa Allah zanyi kamar yadda kika ce, bari na kira miki shi kuyi sallama ko?".
"A'a barshi yana buk'atar hutu don ya wuni aiki na zuci dana zahiri".
Raihana tayi murmushi ta raka matar har bakin k'ofa inda zata futa, tana ta son tambayarta wani abu daya shafi Auntie sai dai tana gargad'in kanta, don suna da k'asa sunzo d'aya sai ya zamana itace ake nufi?. Tana wannan tunanin har likitan ta bud'e k'ofa zata tafi.
Kamar wadda aka zabura haka maganar ta sub'uce daga bakinta ba tare da tasan ma zancen ya futo ba, "Ni fa gani nake kamar na tab'a jin labarin ki.....".
Itama andal kamar jira take aikuwa ta tsaya da hanzari ta juyo tana sake kallon yarinyar.
"A gurin wa kika tab'a jin labarina?".
"A gurin auntie maman khaleefa".
Andal batasan lokacin data k'arasa shigowa cikin parlon ba, cikin gigita take tambayar raihana, "surayyah?".
Raihana ta gyad'a mata kai.
Ai saita maida k'ofar ta rufe tace, "Zan iya ganin hoton ta?".
"Eh" ta fad'a tare da nufar d'akin gadonta, andal ma bayanta tabi ba tare data san ma ta aikata hakan ba, har Saida raihana ta nuno mata pic d'in a wayarta sannan ta fahimci kuskuren da tayi ta juya zata fuce. "Sorry na shigo miki d'aki ba izinin ki, amma tabbas wannan k'awata ce tun ta k'uruciya".
Raihana ta yiwa Allah hamdala a zuciyarta sannan tace, "zaki iya zama a nan ba matsala, saboda indai da gaske kece k'awar da auntie tayi rubutu mai yawa a kanta toh ina buk'atar taimakon ki".
Komawa tayi ta zauna k'asan carpet ta tankwashe k'afafunta ta tallafi hab'arta da hannuwanta, Anya da gaske ne yau itace take jinta kusa da surayyah? Ko dai cikin irin mafarkan data saba yi ne? "Ohh ya Allah! Alhamdulillah Allah na gode maka....." Sai kuma ta hau girgiza kanta duk da son ganin ta tabbatar ba mafarki take ba.
Raihana dai tayi shiru tana kallon yadda matar take abu kamar zautacciya, magana take ita d'aya bata san ma tana yi ba.
Kiran sallah da akayi yasa duk sukayi haramar sallah.
Sai bayan sun idar da sallah andal ta samu sukunin zama ta fuskanci raihana, "kince kina neman taimakona, sai dai nima Ina son sanin abubuwa da yawa game da k'awata".
Raihana tace, "kada ki damu da wannan saboda tayi rayuwa cikin kariyar ubangiji bata samu wata matsala ba, sati biyu da suka huce ma ta kawo mana ziyara nan k'asar.....". Shiru tayi kanta a k'asa tana nazarin abinda zata fad'a kafun taci gaba da cewa, "sai dai ta tafi ta barni cikin tunani da taraddadi....". Nan ta fad'a mata kad'an daga tarihin yadda su khaleefa suka rayu da ita a anguwarsu da yadda akayi ta mata bahagon kallo game da asalin yaran, har a k'arshe ta k'are da bata labarin yadda ta bar mata aikin had'a khaleefa da mahaifin shi data bar address d'inshi a k'arshen rubutun ta.....
Andal tayi shiru kafun tace, "Allah mai iko? Komai yana shirin warwarewa cikin sauk'i, shin Abdallah zai iya barin ki futa in kika tambaya ba tare da yabi diddigin inda zaki ba?".
"Ehhh toh gaskiya bani da tabbaci saina tambaye shi d'in naji?".
"Koma dai yayane Ina son ki same ni a office gobe da misalin sha biyu zuwa biyu na rana akwai muhimmin abinda nake son mu tattauna".
Raihana tace, "insha Allah sai dai lokacin da kika fad'a ba lallai na samu zuwa ba saboda zan shiga karatu".
"Kina zuwa makaranta kenan?".
"Eh"
"Toh Allah yayi jagora, Zan ajiye miki no ta da address na asibitin mu,,,,, lallai Ina son ganin ki a asibitin nan jibi koda safe koda yamma...".
Cikin gamsuwa ta amsa mata sukayi exchange phone no ta tura mata addreshin.
Sun futo raihana zata rakata, khaleefa ma ya futo cikin fararen kaya da alamu sabon wanka ya sake. "kin futo" ya tambaye ta yana satar kallon raihana da take daga bayanta.
"Eh zan tafi naji dad'in had'uwa da matarka, munyi magana mai yawa wadda nake fatan ta silarta duk matsalolin ka suzo k'arshe".
Khaleefa ya maimaita kalmar -matsalolin ka suzo k'arshe- a zuciyarshi a zahiri kuma yayi murmushi.
Kusan a tare suka d'ago suka saci kallon juna kafun su d'auke kansu cikin sakannin da basu huce uku ba. Doctor andal da take tsakiya tayi kamar bata ga komai ba.
"Ina muku fatan alkhairy da addu'ar Allah ya bar ku tare abadannn".
Duk cikin su aka rasa mai amsawa sai sanyi da jikin su ya sake yi, har ta k'arasa musu sallama khaleefa ya rakata jikin su a sanyaye yake.
Suna futa kan layin Ahmad na futowa zasu futa anguwa da yasmine, da sauri ya k'araso gurin suka gaisa ya gabatar mata da Yasmine ma, itama suka gaisa cikin mutumci da girmama juna, har Ahmad ya buk'aci tazo tare dasu ya sauketa sai yaga motar ta kuma......

Lokacin da khaleefa ya shigo gidan raihana tana tsaye hannunta dafe da kujerar da take tsaye bayanta. Ya zauna cikin kujerun parlon ya kwantar da kanshi baya yana yamutsa sumar kanshi da duka hannuwan shi kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login