Showing 195001 words to 198000 words out of 288773 words
Chapter 66 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
ba amma tunda ya fad'i haka saita barshi da yadda ya fad'a d'in.
Direct tsohon apartment d'insu ya nufa bayan ya baro office, kai tsaye ya nufi sashen Amna, yana d'ora hannu zai buga tana bud'e k'ofar cikin shiri zata futa, ja da baya tayi tana kallon shi, bai shiga ba duk daya gane nufinta yaci gaba da tsayuwa a inda yake, "ka shigo mana".
Juyar da kanshi yayi yace, "ba futa zakiyi ba?".
"Noop ai futar ba mai zafi bace, zanje cin abinci ne".
"Alright toh mu k'arasa can sai muyi magana". Haka kuwa akayi suka tafi tare har zuwa gidan cin abinci mafi kusa. Baici komai ba baice komai ba har saida ta gama cin abincin da aka kawo mata.
Yana ta buga game a waya ta goge bakinta da tissue ta fara mishi magana, "Ina sauraron ka".
Ajiye wayar yayi kan table ya fuskanceta da kyau ya fara mata magana cikin nutsuwa, "Amna ki fad'a mun gaskiya a gurin wa kika samu labarin aurena?".
"Me yasa kake son sanin abinda bashi da wani muhimmanci, na d'auka zaka fi damuwa da son sanin shin Saleema tasan kayi aure ko kuwa?".
"Hakane?". Ya tambayeta kai tsaye cikin tsare ta da ido.
Murmushi tayi bayan ta kawar da kanta don ba iya jure kallon kwayar idonshi zatayi ba, "Eh s ganina ba".
"Ni kuma sai nake ganin ba yadda za'ayi kisan wani abu a kaina ace Saleema bata sani ba, hakane?".
"Ehhh! Toh kusan hakan, Amma kuma a wannan gab'ar batasan komai ba, saboda a ranar daka dawo na ganka tare da wata yarinya, koda nabi diddigi don nasan ba harkar mata kake ba sai na gano cewar matar kace daka auro a Nigeria komawarka hutu, a gaskiya bazan b'oye maka ba banji dad'in auren da kayi ba saboda Saleema har gobe tana sonka duk da zuciyarta ta fara hak'ura da kai, ba kuma da bakinta ta fad'an haka ba a ayyukanta na fara fuskantar hakan,,,, bazan b'oye maka ba a ranar da naje zan fad'a mata ka dawo da wata matar daka auro, sai tak'i saurarata gaba d'aya tak'i fahimtata ma saboda na tafi da zancen da son dakatar da ita ga barin aikata wani abu da takeyi da bana so. So a ranar mukayi fad'an da har yanzu bama tare".
Numfashi taja mai tsayi kafun taci gaba da cewa, "a gaskiya khaleefa duk ranar da Saleema ta fahimci gaskiyar magana a kanka ba zata tab'a yafe maka ba, saboda babu yadda za'ayi kana sonta har ka iya auren wata (duk da dama alak'ar ku ta samu tangard'a kafun faruwar komai bisa jagorancin rashin yin cikakken tunani kafun aiwatar da abu daga ku duka biyun)".
Shiru yayi yana kasafta kowanne zance daki daki, "kina nufin na yaudari Saleema?".
"Ba yaudararta kayi ba, yaudarar juna kukayi, duk da a halin yanzu ba zaka gane komai da zance ba har sai lokacin dana kawo muku maslaha da kyakkyawar fahimtar da zata sa kowa a cikin ku ya daina wahalar dakon soyayyar d'an uwanshi, zuwa yanzu ya kamata zuciyoyin ku su huta ta hanyar fahimtar gaskiya,,,, idan Allah ya kaimu gobe, da misalin k'arfe biyar na yamma, kazo garden na apartment d'inmu, nida Saleema zamu kasance a gurin muna jiran ka".
Khaleefa ko kad'an bai gane abinda Amna take son cewa ba, toh amma tunda har zata had'a shi da Saleema ta kawo musu gyara yana ganin ba laifi gwara ya fuskanceta ayi wadda za'ayi kawai, don yayi imanin yana yiwa Saleema bayani don ita yayi komai zata fahimce shi bi'izinillah.
Saida ya biya kud'in abincin da taci sannan sukayi sallama ya tafi gida ita Kuma ta koma cikin makaranta.
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page fifty five 5️⃣5️⃣
*Nigeria*
Shirye shiryen tafiya Germany Auntie take ba tare data fad'awa kowa a cikin raihana ko khaleefa ba, shi kanshi Ahmad sai kamar saura kwana biyu ta taho da sukayi waya take sanar dashi, amma ta nuna bata son khaleefa su sani saboda zata musu bazata ne.
A daren ranar da zata tafi suka zauna da Ayman, hak'uri take bashi da lallab'a shi da kalamai masu taushi da kwantar da hankali don tasan har yanzu baya son tafiyar a zuciyarshi, Saida taga ya sake ta fara zolayarshi da cewa, "soon zan maka aure saima sai kaje can ka dingawa matarka kullen". Murmushi yayi tare da kwantar da kanshi jikin k'afarta cikin jin kunya yace, "I will much miss you Auntie,,, don Allah kada ki dad'e tunda kinga ni kad'ai zaki bari a nan".
Dafa kanshi tayi tausayinshi na ratsa jikinta da ruhinta, ba don akwai wata manufa a tafiyar tata ba da ba zata fara k'ok'arin barin shi a wannan halin ba, so take bada jimawa ba ta kawo mishi gyara a rayuwarshi kamar yadda take k'ok'arin ganin ta kawowa d'an uwanshi khaleefa,,,,, duk da har yanzu akwai sauran rina a kaba amma zatace alhamdulillah komai ya fara lafawa, tasan zuwa yanzu khaleefa ya fara saduda.
Wannan kenan.
_ina labarin shaheeda ne?_
Imran tun bayan titsiyen da maman shi ta mishi akan komawar shaheeda makaranta yaje ya mata fad'a bai sake ganin fuskarta ba saida ta kammala exam d'inta suka shiga hutu, itama bata bi takan zancen ba saboda a lokacin ta tara hankalinta ne guri d'aya wajen ganin ta samu abinda take so kamar kowanne jajirtaccen d'alibi.
Sosai ta sauya salon rayuwarta a gidan cikin hutun, don wanka take d'auka na jan magana da haddasa fitina, yayinda ta dinga shiryawa Imran tarko kala kala bisa jagorancin shawarar k'awarta feena, tun yana iya kauce mata a dalilin shi na rik'e abinda ta mishi farkon auren su ya kasa mantawa, har ya bada kai bori ya hau🤪. Rayuwa suke zubawa ta zallar soyayyah, Imran har hutun sati ya d'auka a gurin aiki saboda tarairayar da yake samu daga shaheeda, bai tab'a d'aukar zai samu farin ciki a tare da ita ba, haka itama bata d'auka zata samu kanshi cikin sauk'i yadda taga yana daddaure fuskar nan ba.
Basu yaudari kansu da cewa suna son juna ba, amma suna matuk'ar begen juna, Cox dukkannin su shekarun su sunkai shiyasa ba zasu iya cewa a'a ga abinda zuk'atansu da gangar jikin su ke soba.
Ba laifi mamanta ta huce don Imran da kanshi ya kaita gidan a wani dare, sunji dad'in ganinta sun nuna kuma don rasa abinda zasu bata da zai burgeta k'arshe sukayi.
Data tashi tafiya mamie ta sake mata nasiha mai narkar da zuciya musamman akan uwar mijinta, ta sake gargad'inta daja mata kunne sosai akanta (duk da har yanzu bata k'ara kai k'arar shaheedan ba tun bayan na lokacin da aka kawo ta). Ta gaban kunne ta shiga ba tare data rab'i ko fatar kunnen ba bare ta shiga ta zauna a ciki. Da zasu tafi Imran ya bawa k'annenta kudi masu yawa yace su sha ice cream. Suna godiya suka karb'a ta musu sallama suka tafi.
Daga futar su har dawowar su akan idon masu tsegumin mom ne, sun kuma kai mata labari dai dai da abinda suka gani, kafun su shiga sashen su Imran ya tambayeta ba zata zo su k'arasa ta gaisa da mom ba tunda d'azu basu shiga ba, babu ko kara bare kawaici tace ita ta gaji bacci take ji gaskiya, bai takura mata ba ya barta ta tafi shi kuma ya nufi parlon mom d'in.
wannan karon kasa hak'uri mom tayi don hak'urin ta ya k'are akan abinda yarinyar nan take yi shi kuma yana goya mata baya.
Da kyar ta iya amsa gaisuwar shi ta fara da masifa akan rashin mutumcin matarshi, saida ta wanke shi tas a cewarta ai duk da sanin shi take aikata komai, shi yake goya mata baya.
Hak'uri ya bata don bashi data cewa, tunda shi har ga Allah bai d'auka shaheeda bata zuwa gaisheta ba, tunda yaga dai yarinyar zab'in tace, y'ar hannun damarta, ita tasan yadda ta shiga ta futa ta rabata da duk samarinta kamar yadda ta raba shi da RAIHANA ta had'a su aure, shiyasa yake tunanin ba yadda yarinyar zata kasa girmamata.
Lokacin daya shiga tana kitchen tana k'ok'arin had'a mishi abinda zaici don ita taci tare da y'an uwanta, shi kuma fafur yak'i cin komai saboda kunyar su da yake ji.
Tsaye yayi k'ofar kitchen ya zuba mata ido yana kallonta duk data juya baya bata san da zuwan shi ba, kallonta yake da kallon duk wani motsinta cikin fingilgilar riga armless iya cinya ,ba laifi yarinyar kyakkyawa ce ba k'arya, sai dai baisan matsalarta da mom ba, duk da yasan mom da d'aukar maganar mutane fiye da komai.
K'arasa shiga kitchen d'in yayi ya d'auki ruwa ya tsiyaya a cup yasha, fuskantar ta yayi da kyau kafun ya tambayeta, "da gaske tunda kike a gidan nan baki tab'a zuwa kun gaisa da mom ba?". Kallon shi tayi kai tsaye ta bashi amsa, "Eh".
"Meyasa?" Ya sake jeho mata tambaya.
"Saboda ba zamanta nake ba". Ta k'ara bashi amsa direct.
"Amma kina sane da cewar ni da kike zaman nawa neman albarkarta nake? Ko bakisan sab'a mata zai iya silar rugujewar rayuwata ba".
B'ata rai tayi tace, "Kai da kake d'anta kenan? Ni kuma da nake matar kafa?".
"Dole zaki bita matsayin kina wadda take k'ark'ashina".
Banza tayi dashi don in taci gaba da ja abun zai iya zama musu fad'a.
Shima sai baice mata ba don in yaja abinda sukayi fad'a bazai samu abinda yake so a gurinta anjima kad'an ba.
Da haka ya futa a kitchen d'in ita kuma taci gaba da aikinta.
_(Note: a rayuwa kada ka tab'a k'in hana b'arna saboda wani abu na samun cikar burinka ba, komai sonda kakewa mutum ka nuna mishi kuskuren shi a lokacin da yayi ba dai dai ba donka takawa abun burki, koda zaka shiga d'aki kayi kuka bayan kayi tsawatarwar kuwa,,,,,, wannan yana daga major problem da yake d'awainiya da al'ummar mu, musamman iyayen mu mata in akazo ta b'angaren yara, da yawan iyaye y'ay'an su suna aikata ba dai dai ba a gaban idon su, amma saboda kada ran yaran ya b'aci suyi kuka sai su zuba ido suna kallon su, wasu ma in akayi magana har suce yarane ai basu da hankali basu isa kwab'a ba, sun manta icce tun yana d'anye ake tankwarashi, wannan k'aramin abun da muke gani ba komai ba shi yake girma ya zama babba nan gaba har yafi k'arfin mu, wannan b'acin ran nasu da bama so shi yake zama namu b'acin ran a gaba... yana da kyau mu dinga tuna cewa y'ay'a Amana ce a gare mu, kuma Allah zai tambaye mu yadda muka tafi da ita ranar gobe alk'iyama... Allah yasa mu gyara)_
Da wannan kuskure Imran ya kyale shaheeda take abinda ranta yake so musamman a gurin hajiya tafeeda, Sam baya tsawatar mata duk dashi yana binta sau da k'afa a matsayinta na mahaifiyar da tayi silar zuwan shi duniya.
**********
Zaune take cikin filin tashi da saukar jirage na Aminu Kano international airport, ita kad'ai ce a gurin kare da waya a kunnenta ga dukkan alamu kira take, ana picking kuwa ta isar da gajeran sak'on da take son isarwa ta ajiye wayarta. Sake waiwaya hanyar da Ayman yabi tayi, ko alamun shi babu hakan na nufin yayi nisan da ba zata iya ganin shiba.
A hankali ta soma share hawayenta da hankie a ranta tana addu'ar Allah ya bata aron rai da lafiya ya bata ikon kawo gyara a rayuwarshi, ta kyautata mishi kamar yadda kullum yake da burin kyautata mata shima. A duniya tashin hankalin Ayman ya ganta cikin damuwa ko halin rashin lafiya, yana nuna kulawar shi gareta a zahiri koda yaushe.
@@@@@@
Tunda ya tashi yau yake jin jikin shi a sanyaye kamar wanda aka zarewa laka, yasan hakan baya rasa nasaba da had'uwar shi da Saleema da kwantacciyar rigimar da zai tarar.
Har ya gama shirin shi ya futa a gidan ya isa office bai daina jin fad'uwar gaba lokaci bayan lokaci ba.
******A mugun gajiye ta shigo gidan, Jakarta da wayarta ta ajiye kan table k'arami da yake parlon ta shiga kitchen da hanzari ta tsiyaya tea a cup ta had'a shap shap ta fara sipping tana sauke ajiyar zuciya, a zuciyarta take fad'in, lallai yunwa zata iya haukata mutum yau ta sake tabbatarwa data futa bata karya ba.
Tana gama shan tean ta gyara gurin, ta k'ara tattare parlon ta kammale komai a guri d'aya ta saka turare gidan ya d'au k'amshi.
Sannan ta samu sukunin yin sabon wanka ta shirya cikin doguwar rigarta maroon irin mai kamawa daga saman nan ta bud'e daga k'asa. Ta nad'e gashinta ta turare jikinta da turare kala kala, ta yane kanta da k'aramin gyale ta futo. Kitchen taje ta d'ora apron ta fara simple girki cin mutum biyu don tana son anjima ta kaiwa yasmine idan khaleefa ya dawo ta nemi izini.
Tana aikin tana bin suratul Maryam cikin jin dad'i da farin ciki mara iyaka, don yau jinta take kamar sabon mutum zero tension.
@@@@@@
Ahmad da yake aiki yana duba time, da wuri ya tashi office gudun kada ta sauka ta yita faman jiran shi.
Khaleefa ma dai da lokacin da Amna ta bashi yayi amfani ya tashi at exactly 4:50pm. Ko jakar system d'in a nan ya barta ya d'auko iya wayar shi da LC ya futo.
Saida ya tsaya ya siya colour flower da yasan tafi so, sannan ya d'auki hanyar apartment na d'aliban gaban shi yana tsananta fad'uwa.
Bai shiga ba saida ya gama karanto addu'o'in samun nasara a kanta da kyakkyawar fahimta.
Da Amna ya fara cin karo tsaye a farkon lambun, fuskarta d'auke da murmushi mai cike da ma'anoni, ba tare da dogon tunani a kanta ba khaleefa ya k'arasa suka gaisa.
Wayarta ta bashi, "sorry samun no ka a nan first".
Baiyi musu ba wajen karb'an wayan da zuba mata digit d'in ya sake mik'a mata wayarta. Tayi saving ta mayar cikin aljihun kayan jikinta tace, "muje ko?".
"Na ganki ke d'aya, Ina saleeeman?". Ya tambayeta yana kallonta.
"Me kake ci na baka na zuba, mu k'arasa ciki mana".
Bai mata musu ba yabi bayanta yayinda idon shi ke kallon inda yake takawa da takun Amna cikin tsanaki.
Turus! Yaga k'afarta ta tsaya daga tafiya, sai shima ya ajiye tashi sannan ya d'ago a hankali ya sauke idon shi a gurin da suke fuskanta,,,, Saleema ce gaban shi don ko shekara dubu yayi bai ganta ba baza ta tab'a b'ace mishi a kwayar idon shi ba.
Da wani irin zafin nama ya ture Amna da rabin jikinta ya shige mishi gaba baya iya ganin komai yadda ya kamata, ta tafi kamar zata fad'i Allah yasa ta rik'e jikin bishiya tana rarraba idanu kamar wadda ta yiwa sarki k'arya.
Khaleefa baisan lokacin daya saki flower hannun shi da wayarshi suka fad'i k'asa ba, k'arar fad'uwar wayar ce ta d'auki hankalin Saleema har ya kai inda suke tsaye shida Amna.
Gaba d'aya jikin khaleefa babu inda baya fudda gumi na zallar razani da shiga tashin hankali, bai tab'a zato ba, bai tab'a tsammani ba ko a mafarki da tunanin shi. Lokaci d'aya ya mugun fusata har jijiyoyin kanshi na futowa, nan da nan idon shi ya sauya launi kallo d'aya ba zaka so mishi gani na biyu ba.
Da wani fusataccen yanayi ya juya inda Amna take ya watsa mata wani mugun kallon daya kad'a hanjin cikinta yayi taku uku zuwa gaban ta ya had'a ta da jikin bishiyar data ke jingine har saida ta rirrik'e hannun shi gam ba tare da tasan ma ta aikata hakan ba.
"Daman kin kira nine saboda ki nuna mun adadin nisan da k'awar ki tayi mun?????". Yadda yayi maganar da k'arfi ba alamun sassauci a muryarshi ya sake d'ugunzuma hankalin Amna, gashi guri ba maceci bare tasa ran wani zai iya kwatar ta, yadda ta raina kanta farat d'aya haka Saleema data ke gefe ma ta raina kan nata,