Showing 60001 words to 63000 words out of 288773 words

Chapter 21 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1087

Shiyasa yanzun ya dage da sallolin dare yana kai kukan shi ga Allah subhanahu wata'ala akan Allah ya d'ora shi kan auntien su ta amince idan tazo.
Yana nan yanata lissafin zuwanta ita kuma tana wasu lissafe lissafen nata daban, a lokacin da ta samu hutun shekarar akwai tafiyarta ta kasuwanci Egypt da Dubai sannan ga khaleefa a Germany tana son je mishi shima, tayi tunanin cikin wata d'aya zata iya yin duk wannan abubuwa sai gashi Kuma abun ya faskara, at the end sai kawai ta bashi hak'uri akan sai dai daf da dahowar shi zata yi k'ok'ari maybe lokacin Ayman ya samu hutun k'arshen shekara ma sai suzo tare.
Khaleefa bai ji dad'in hakan ba sam, toh amma babu laifi idan har zata zo k'asar kafun su suje can Nigeria.

Toh akace tafiya sannu sannu kwana nesa, da sannu dai gashi yanzu saura 1month su kammala karatun su gaba d'aya.
Kansu ya d'auki chargy shiyasa kwana kusan uku rabon shi da Saleema, kuma dama da zarar yayi busy ko suna tare sad'ad'ewa yake ya barta yaje yaji da al'amuran shi.
Yau ma tun safe daya fuce bai samu kanshi ba sai kusan gab da magrib, saboda har meeting sukayi da doctor raazi, Su bakwai aka yiwa tayin aikin Soo su 7 d'inne ake jin aji ta bakin kowanne d'aya daga cikin su.
Alhamdulillah duk sun suna amincewar su, sai dai kowanne ya buk'aci da'a barshi ya nemi dama daga manyan shi idan sun koma gida bayan kammala wannan course d'in.
Tafe suke shida Ahmad suna tattaunawa a tsakanin su har suka k'araso gida, bai nufi apartment d'in shi ba yabi Ahmad. Saida sukayi sallah yaci abinci sannan ya tattara komatsan shi yayi mishi sallama ya tafi. Yana tafe yana jin yadda temperature jikin shi take high, da yadda kanshi yake bala'in sara mishi, kamar zazzab'i yana shirin kama shi haka.
Yana zuwa a k'ofar shi yaci karo da Saleema rungume da wasu uban tulin littattafai, rataye da y'ar k'aramar jaka sai wayarta a hannu.
Tana ganin shi ta shagwob'e tana fad'in, "Wai Ina ka shiga ne tun ranar Friday ko nema na bakayi ma". Murmushi yayi mai kyau da k'ayatarwa ya k'araso gabanta ya kama kunnen shi, "apologize madame kinsan one month ya rage mana mu yanzu". Saleema tace, "ayyah Allah yayi jagora". Bud'e musu d'akin yayi suka shiga tare, a k'asa ta zube tulin littafan da jakar ta fad'a bathroom da hanzari ta d'auro alwala ta futo.
Shikam khaleefa Zama yayi kan sofa yana kallonta da matuk'ar mamaki, yayi tunanin idan suka had'u zai tarar tayi mugun fushi dashi sai ya had'a da rarrashi amma........ Saiya saki murmushi, shi tunda yake ma tare da Saleema sun tab'a yin fad'a ko cacar baki irin na masoya kuwa?
Tana sallar yana y'an tunane tunanen shi har ta idar, tayi tasbihi ga Allah sannan ta juyo ta fuskance shi, "kasan ina sallar nan kuwa na tuna da wani abu? Labarin familyn ka da kace zaka bani wata d'aya kafun barin ka Berlin".
Tsare ta yayi da ido kafun yaja gwauron numfashi ya mik'e, "am let's get you something to eat nasan kina jin yunwa kam".

_happie juma'at Mubarak, may all our dreams come true🤲🤲🤲_



_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page 1️⃣7️⃣


Had'e fuskarta tayi kamar zatayi kuka tace, "noop ni ai bance maka Ina jin yunwa ba". Yanayin yadda tayi maganar saida ta bashi dariya amma dai ya gimtse. Kusa da ita ya dawo ya tankwashe k'afa ya zauna yana kallonta, "ta Ina zamu fara ne?". Saleema tace, "Ni duk ta inda ka fara ma".
Sai yayi gyaran murya ya fara magana da fad'in, "Toh nidai sunana Abdallah Suraj Abdallah kamar yadda kika sani, sai k'anina twins d'ina Adam Suraj Abdallah, tare aka haife mu rana d'aya a lokaci guda, kawai ki kwatanta yadda so da shak'uwar mu zata kasance, mahaifiyata, surayyah Adam akwai kyakkyawar zamantakewa tsakanin mu da cikakkiyar kulawa, mun taso duka tare a gidan iyayenta malam da iya. Auntie ta fad'a mana mahaifin mu ya jima da rasuwa kuma ya tafi bai bar ko hoton shi guda d'aya ba, hakan yasa bamu tab'a sanin yadda kamannin shi suke ba, nan yaci gaba da bata labarin cikakken tarihin shi da yadda suke rayuwar su tare da auntie da gorin da y'an anguwa suke yi musu wani lokacin suna Kiran su da shegu, khaleefa yaci gaba da ba Saleema tarihin shi yayin da take kallon shi da fuskar tausayawa har yazo kan inda ya taho karatu Germany bayan an matuk'ar kai ruwa raana. Ya d'ora da fad'in, "babban abinda yafi d'aure mun kai guda biyu shine, mahaifina ya rasu mun rayu bamu San shiba kuma Auntie bata so ayi mata hirar shi koda wasa, bare ta bamu koda labarin shine muji sanyi a ranmu, na biyu dangin mahaifina tunda muke rayuwa basu tab'a zuwa don su gan mu ba Auntie ce kad'ai take wahala damu da abinda take samu a kasuwancin ta da aikinta" sai ya soma girgiza kanshi, "wannan abubuwa biyu da su nake rayuwa a kowanne dare Saleema, abun yana cin raina da zuciyata, gashi har Alk'awari mun d'aukar ma auntie lokacin muna yara cike da k'uruciya cewa ba zamu k'ara tambayarta wani abu game da mahaifin mu ko dangin shiba......".

Saleema data zuba mishi ido tana kallon shi da wani bak'on yanayi kan fuskarta mai wuyar fassaruwa farat d'aya, hawayen idonta daya taru ta soma sharewa kafun ta mik'e tsam ta tattare duk wani shirgi data shigo masa d'aki dashi ta d'auki hanyar futa, da mamaki khaleefa ya tashi ya bi bayanta yana kiran sunanta, "Saleema". Tsayawa tayi tana kallon shi da idanunta da hawaye suka fara sintiri.
Hannu yasa yana share mata hawayen, shi kanshi ji yake kamar yayi kuka a lokacin, ba don yana da kyau tasan waye shiba daba abinda zaisa ya fara bata cakwalkwalallen labarin rayuwar shi mai cike da hargitsi da zargi a gurin mutane, gashi ba mutum ma'abocin k'arya ba bare ya k'irk'iri wani k'agaggen labarin ya mak'ala. Cikin sanyin jiki dana murya yace, "I'm sorry Saleema, kiyi hak'uri ki daina kuka akan abinda kika ji game dani yanzun.... Duk da nasan dole zaki yi kuka wa rayuwa ta da......" Da sauri ta d'aga mishi hannu ba tare data bari ya kai aya ba, "labarinka yafi k'arfin a koka mishi ta wannan hanyar, wannan ba kukan komai nake ba khaleefa saina rayuwata, rayuwata nake koka ma a yanzun ba kai ba....." .
Tana gama fad'in haka ta fuce da gudu tana kuka mai sauti.
Zama yayi a k'asa jiki ba kwari yana harhad'a maganganun saleeman da tunanin yadda zai fassara kowanne a ciki. Ganin yana wahalar da kanshi a banza bayan ba gane komai yake a halin yanzun ba sai ya fad'a kan gadon shi kamar wani kayan wanki ya haska madubi a zuciyar shi yana kallon rayuwar shi tun daga lokacin daya zama matashi yafara mallakar hankalin kanshi har kawo yau.
Da kyar ya iya yin sallar isha'i ranar, ko daya sake kwanciya kasa bacci yayi sai tunane tunane cinkushe cikin ranshi. Sai da b'arawon gwanin iya sata yazo yayi wuff dashi tsakiyar dare.

Yau na fari khaleefa ya kwana da kayan daba na bacci ba a jikin shi, na biyu ya makara sallar asubah har lokacin futar su yayi har ya huce bai tashi ba, saida Ahmad ya gaji da kiran wayar shi yazo ya dinga buga mishi k'ofa da k'arfi sannan ya farka. K'ofar ya fara bud'ewa sannan ya dawo ciki yana kallon yadda gari yayi haske.
Ahmad zama yayi kan k'aramin table yace, "I cannot believe kaine yau kake bacci har rana baka yi sallah ba".
Bai ce dashi komai ba shi dai ya shige bathroom. Shap shap yayi wanka ya d'auro alwala, sai daya zura kaya sannan yayi sallar, suka gaisa da Ahmad yaso had'a musu abinda zasuyi break sai dai lokaci ba zai basu damar hakan ba, sai ya d'auki briefcase da wayar shi da jakar system suka futo tare.
Yana rufe k'ofa Saleema na rufe tata itama, "minti biyu please" yace da Ahmad sannan ya nufi inda take takowa itama da fuskarta kumburarriya, ya bud'e baki zaiyi mata magana tayi saurin d'aga mishi hannu, kamar walk'iya kuma tayi sif ta hucewarta ta barshi nan tsaye. Ahmad da komai ya faru gaban idon shi d'auke kanshi yayi a lokacin da khaleefa ya fara dawowa don su huce.
Ko a clinic yana lura da yadda yake gaba d'aya a dame, ko abinci bai ciba ranar through out. Haka suna tashi bai k'ara jira ba ko dede da second ba yayi gida abun shi.
Wulli yayi da komai ya kwanta a k'asa yana sauke numfashi. Ahmad ne ganin yanayin yadda ya futa kamar bashi da lafiya cikakke ya biyo bayan shi, yau ko d'akin bai rufe ba yana zuwa ya shiga, ganin shi a k'asa sai ya k'arasa kusa dashi da hanzari yana kiran sunan shi, bud'e idon shi yayi ya kalli Ahmad da yake durk'ushe gefen shi, "Wai yau me yake faruwa da kai ne khaleefa? Ko baka da lafiya?". Da kyar ya yink'ura ya tashi zaune ya d'ora kanshi jikin gwiwar k'afar shi. "ko mu je nearest clinic a duba ka?". Cikin dakiya da kuma basarwa khaleefa yace, "ba abinda yake damuna Ahmad just help me with something to eat".
Bai yi musu ba ya tashi da hanzari ya zari waya da master card d'inshi ya futa, in less than 20 minute yaje ya dawo mishi da abincin da zai iya ci mai sauk'i, yana yadda yake har yanzun. A gurguje ya d'auko plate bayan ya had'a mishi tea mai mugun zafi ya juye a mug.
"Ka fara shan tea khaleefa in yaso sai kaci abincin".
Girgiza kanshi kawai yake yaja jiki da kyar ya nufi jikin bed ya jingina. Ahmad sai faman jera mishi sannu yake, shi ya taimaka mishi yasha tean sannan abincin ma, ba laifi yaci da d'an yawa, sai gashi har ya samu kuzarin shi ya d'an dawo, dama yunwa ce ta sake galabaitar dashi. Ahmad ya had'a mishi ruwa ya shiga yayi wanka ya d'auro alwala, ya zura wasu riga da wandon parkistan na maza, yayi sallolin da suka huce shi bai samu yayi ba. Yana idarwa ya samu kan sofa ya kwanta, Ahmad na gefen shi cike da damuwa yana mishi sannu, da ka kawai yake amsawa, wayar shi yasa Ahmad d'in ya bashi, da yake a silent take anyi mishi kira rututu bai sani ba, ko dubawa bai tsaya yiba ya shiga kiran Saleema, sai dai har ta katse bata d'aga ba, hakan yasa ya k'ara mata wani kiran, shima bata d'aga ba. Sai kawai ya ajiye wayar gefe yaci gaba da tsurawa guri d'aya ido yana tunanin abinda zaisa Saleema ta d'auke mishi wuta daga jin labarin shi, meyasa zata jefa kanta cikin damuwa shima ta jefa shi bayan tasani sarai babu abinda ya tsana kamar ganin damuwarta ko tashin hankalinta, shin idan ma tana taya shi bak'in ciki ne me yasa ba zata saurare shi tazo suyi alhinin tare ba, balle ma yana ganin wannan k'addarar shice abinda ya shafe shi shi kad'ai bai shafi wani ba.
Yana Wannan y'an tunane tunanen Ahmad ya dinga yi mishi magana bai jiba har saida ya tab'a shi sannan ya dawo hayyacin shi, "auntie tana kiran ka a waya" Ahmad ya fad'a yana mik'a mishi wayar, kauda kanshi yayi gefe yace, "ka barshi kawai ahmad". Ba musu Ahmad ya ajiye wayar a gefe, ranar bai bar gurin shiba har dare bayan ya tabbatar yaci abinci ya kwanta bacci.
Ko daya futa sai da yayi tunanin ya tsaya ya yima Saleema magana don ya tabbatar tana da masaniya akan halin da khaleefa ya riski kanshi a ciki, toh amma da yayi wani tunani sai ya ga bari ya kyale su ya zuba musu ido kawai watak'ila sun samu d'an rashin fahimta ne ba wani abu mai zafi ba, kuma dama a kowacce soyayyah ba za'a rasa cin karo da matsaloli iri iri ba, toh amma shi abinda yafi bashi mamaki shine yadda khaleefa ya d'auki abun da zafi har yake son kwantar dashi, yasan halin khaleefa ciki da bai sai dai yaba wani labarin shi, mutum ne murd'ad'd'e mai matuk'ar k'arfin hali dana zuciya, ko ciwo yake sai yaci k'arfin shi wani yake iya sani, haka zurfin cikin shi baya ma bari aji damuwar shi har sai yayi maganinta da kanshi, in tafi k'arfin shine makusantan shi zasu iya ji, sannan abu na k'arshe baya d'aukar komai da wasa musamman abinda yake so kamar ita saleeman.
Da wannan tunane tunanen Ahmad ya isa apartment d'in shi ya bud'e ya shiga.


★★★★★★★


Saleema kuwa tana can cikin tashin hankali da muguwar damuwa, labarin khaleefa ya tab'a ta ba kad'an ba, kuma ya shiga cikin alak'ar soyayyar su matuk'a, hakan yasa ta kwana tana kuka ranar bata runtsa ba, sai tsakiyar dare, da kyar kuma ta iya tashi asubar fari jikinta duk yayi weak kamar mara lafiya, ta dai daure ta lallab'a ta shirya, bata da lectures da sassafe amma tana son tabar gidan kota samu sauk'i in ta had'u da course mate d'inta, gashi ita ba wata k'awa ba da zata tattauna damuwarta da ita, Amna ce kuma sun rabu tun farkon haduwarta da khaleefa.
Ta futo shima ya futo shine yaje don yayi mata maganar nan, ita kuma a halin da take ciki lokacin bata buk'atar sake sauraron duk wani abu da zai futo daga bakin shi, ya barta taji da kanta ma. Shiyasa yana fara magana ta dakatar dashi tayi hucewarta. Haka ta wuni kamar marar lafiya, lokaci bayan lokaci takan tuno da wani abu, sai zuciyarta ta karye ta fara share hawaye.
Bata yarda ta koma apartment ba sai yamma lis ta shiga ta kulle dama already ta taho da abinda zata ci ba girki zata yi ba.
Tana cin abincin ta kora maganin headache ta kwanta a nan k'asa sai bacci, ba ita ta farka ba saida garin Allah ya waye don ma Allah ya taimake ta ba sallah zatayi ba, kuma bata da lectures. A gurguje ta shirya kanta a d'akin wankan ta futo ta zura wata y'ar k'aramar doguwar riga data sake fudda ainahin sirantar ta. Bata buk'atar cin komai ga cikinta da yake uban ciwo har yana neman kayar da ita ga miki a zuciya. Wayarta dama tun jiya da taga khaleefa ne yake kira ta wurga cikin jaka bata sake yarda sun k'ara ido hud'u ba har yau. Haka ta gama murk'ususunta ba wanda yasan tana yima bare ya kawo mata d'auki.
Sai zuwa can cikin ya lafa ta d'an sha hot milk da magani ta sake kwanciya, ba jimawa wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin ne kuma taji ana faman Danna mata door bell at the same time ana mata knocking, cikin magagin bacci ta tashi zaune ta dubi kayan jikinta, hijab d'in sallarta ta zura don bata san wa zata tarar a wajen ba.
Ko data bud'e khaleefa ta gani tsaye hard'e da hannu yana kallonta kamar wanda ya shekara yana jinya. Saleema take zuciyarta ta karye, tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka, cikin d'an saurin kuzarin daya rage mata ta tura k'ofar zata rufe, duk da shima ba kuzari a jikin shi amma ya fita k'arfi ba zama a had'a ba nesa ba kusa ba, cikin k'arfin hali ya ture k'ofar ya shiga kanshi tsaye ya mayar da k'ofar ya rufe hadda murza key. Cikin b'acin rai Saleema ta fara masifa tana fad'in, "malam waye kai da zaka shigo mun d'aki just like that?". Khaleefa yana nuna kanshi yace, "Saleema ni kike tambaya waye ni?". Cikin sake had'e gira tace, "yeah I say who the hell are you? toh nasan kane?".
Wani irin karyewa zuciyar shi yayi ya zuba mata ido yana kallonta cikin mabayyanin tashin hankali, da yafi k'arfin miskilancin shi ya b'oye. Itama kallon shi take idonta cike da hawaye, burinta d'aya ya futa ta samu tayi kukan nan ko taji sanyi a ranta. Shi kuwa tun yana iya tsayuwa da k'afafun shi sai gashi k'afafun sun gagara d'aukar shi, sai ya zube nan k'asa ya had'a hannu da kai da gwiwa. "innalillahi wainna ilaihi rajiun! Saleema me yasa kike son ganin baya na lokaci guda? Me yasa kike yin duk wannan abun? Akan wani dalilin ki marar tushe kike son azabtar da zuciyarmu akan me? Ni da abun ya shafa ma ban tab'a yin irin abunda kika yi ba balle ke da labari kad'ai na baki.......".
Da wani irin zafin rai mai cakud'e da muryar kuka tace, "sau nawa kake son na fad'a maka ni ba kai nake kokawa ba? Naji tausayin ka tabbas, amma nafi tausayin kaina da fad'awa soyayyar da nayi da kai har nake mafarkin auren ka mu rayu tare, dolee nayi kuka Abdallah! Dolee! Saboda ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login