Showing 108001 words to 111000 words out of 288773 words

Chapter 37 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1096

da rintse ido mutane suka yo caa a kanta suna salati da sallallami.


_Shin kuna bibiyar littafan in-identical twins? Toh maza garzaya ki karanta DARAJAR HAK'URI na doctor fayeez m usmern. Kada a barki a baya. Da JARUMAR UWA na merhreeyeart lerwerl👉🏻don jin irin sak'on da suke d'auke dashi_

_Masu comment Ina godiya da jinjina 😍😍kune k'arfin gwiwa ta a koda yaushe,,,,,fatan muna tafe tare masoyan asali_


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page thirty one3️⃣1️⃣


Sam ta kasa bud'e idonta bare tasan ainahin abinda yake wakana a gurin har zuwa lokacin da hancinta ya soma shak'o mata wani k'amshin turare na daban, ba zatace batasan irin k'amshin ba amma wanda ta tab'a shak'ar irin k'amshin a tare dashi ya kwanta mata.
Shi kuwa cikin zafin rai da b'acin rai mai tsanani ya fara mata maseefa, ba don hakan ya kasance halin shi ba sai don zafin b'acin ran daya futo dashi tun daga gida ya rasa inda zai sauke Allah ya had'a shi da ita yanzun a dai dai, tunda ya ganta tsakiyar titi yake faman zabga mata horn da yink'urin kauce mata hakan bai yiwu ba har saida ya daki gefen k'afarta. "ke wacce irin mahaukaciya ce, bakya gani ne zaki hau tsakiyar titi kina tafiya....". Sai da ta sake rintse idonta a lokacin da mummunar kalmar hauka ta shiga kunnen ta, abu na k'arshe da take fad'awa wanda duk ya dameta da yawa a rayuwa, saboda a ganinta duk girman zagin da mutum zai mata in ta kira shi mahaukaci ta fanshe.
Idonta ko bud'ewa sosai baiyi ba amma a haka ta mik'e ko rad'ad'i da zugin da k'afarta take bata tsaya sauraro ba ta fara mayar mishi da amsa cikin zafi, "Kaine babban mahaukaci da baka iya ganin gaban ka idan kana tafiyaaaa". Ta k'arasa fad'a cikin maseefa tare da komawa ta zauna a gurin lokaci d'aya sakamakon wani mugun zafi da zugi da k'afarta ta k'ara. "wayyoh Allah na!!!" Ta fad'a k'asa k'asa tana jujjuya kanta cikin azaba. Duk da yaso fad'a mata bak'ak'en maganganun da saita raina kanta bisa gangancin dangantashi da kalmar hauka da tayi, amma ganin halin data shiga sai ya danni zuciyarshi ba don ya hak'ura ba,,,,, sai don tsoron abinda zai biyo bayan aika aikar da yayi a k'afar a sanadin tafiya ba kulawa da fad'awa dogon tunani a lokacin da bai kamata ba.
Ganin ya kasa d'aukar wani kwakkwaran mataki ga yarinya durk'ushe tana matagugun ciwo sai mutanen gurin da suke kallon komai suka fara yi mishi fad'a, "kada ka zama mara Imani mana dubi halin da yarinyar nan take ciki, dukkannin ku kunyi laifi, Kuna tafiya kuna tunani har bakusan inda kuke sa k'afar kuba.... Wanda hakan yake babban kuskure".
Wani tsoho ne meyin wannan magana, wata mace da take cikin adaidaita sahu itama kusan taga komai akan idonta ce ta futo da alama nurse ce ko likita, sanye dai da fararen kaya tazo ta d'ago raihana, "bud'e mana motar ka". Matar ta fad'a ba wasa. Shima ba annuri har lokacin a fuskarshi yace, "me zakuyi a motata".
"Ba kai ka bige taba? Asibiti zaka kaimu a duba mata k'afar ka biya duk abinda ya biyo baya". Ko kafun yace wani abu mutanen gurin sunce wannan haka yake, kuje dashi asibiti ya tsaya a tabbatar an duba ta yadda ya kamata.
Raihana kam a lokacin don bata da bakin magana ne amma data fad'a musu sam bata buk'atar taimakon wannan marar Imanin mutumin.
Shima baice komai ba, ya bud'e musu k'ofar aka shiga da ita cikin motar shima ya shiga ya fara tafiya.
"Wanne asibitin zamu". Ya tambayeta, matar tace, "city star". "can you locate please". A ranta tace ashe ma bak'o ne kai a garin, a fili kuma tace, "okay ba damuwa".
Suna tafe tana kwatanta mishi har suka isa, yanzun ma ita ta taimaka mata suka shiga har cikin asibitin, a wani empty room ta ajiye ta shi kuma ya samu gefe guda ya zauna ya ciro wayarshi a aljihu yana dubawa.

Ita kuma nurse d'in ta futa ta kawo kayan aiki, sai a lokacin raihana ta d'aga dogon hijab d'in jikinta ashe taji ciwo sosai a k'afar har yana jini, satar kallon shi tayi, bata ga fuskar shiba har yanzu saboda ya juya mata baya. Taso taga wannan shugaban marassa Imanin da bayan ya bige ta har yake da bakin kiranta mahaukaciya, mtsss! Taja dogon tsaki a fili tare da kauda kanta gefe. Ya jita sarai amma ya share ko motsi beyi ba. Ganin lokaci yana tafiya ga nurse d'in sai safa da marwa take tsakanin d'akin da reception zuwa office sai khaleefa ya mik'e yana tambayarta, "is there any problem". Dafe kanta tayi da hannunta tace, "Babu doctor da zai iya duba mata raunin cikin k'ashin a asibitin ne".
Sai yayi d'an jim kafun ya saci kallonta, duk data kauda kanta gefe amma kallo d'aya zakasan she's in pain, ga k'afar sai d'igar da jini take har ta fara jik'a gurin ma. Baice da nurse d'in komai ba ya k'arasa gaban gadon ya zauna ya tsurawa k'afar tata ido, har yanzu bata yarda ta sake kallon shiba duk da tarin k'amshin shi daya cika mata hanci.
Slowly ya saka socks ta hannu ya matso da kayan treatment kusa ya janye rigar jikinta zuwa gwiwar ta, ko kafun raihana tasan me yake ciki tuni ya soma jan k'afar yana mik'ar da ita had'e da d'an jijjigata kad'an, tsananin azabar daya kai mata har kwakwalwar kanta yasa ta rintse ido tare da d'ora hannunta kan hannun shi ta rik'e shi gam. Sai daya saci kallon fuskarta, sai jujjuya kai take.
Matar da take gefe kuwa cike da tsoro take faman jera mishi tambayoyi, "bawan Allah! Kada ka nakasa y'ar mutane saboda rashin fahimtar ka na banza da wofii fa!!! Malam! Malam!! Kai likita ne ko kuwaaaa, security malam kada ka illata yarinyar nan faaa!!". Duk wannan sambatun da take yi bai kulata ba har ya daidaita k'ashin gurin daya targad'e ya mayar dashi dai dai ya mata treatment d'in raunin saman fatar. Sake kallon fuskarta yayi har yanzu idonta a rufe yake ta datse lebenta na k'asa da hak'ori. Shikam ba don kada yayi k'arya ba sai yace yasan wannan yarinyar amma ya manta a ina.
Nurse d'in kam ajiyar zuciya ta sauke tana faman jera mata sannu, bata iya amsa mata ba, sai hannunta data d'auke daga saman nashi ta kife kanta jikin k'arfen gadon da take zaune, matar ce ta dawo da dubanta gare shi ya koma inda ya taso yana ci gaba da danne dannen shi a waya hankali kwance, cikin lokaci k'alilan yayi aikin da a asibitin su likita d'aya ne zai iya yi kuma bada sauri haka ba, sai taji ba zata iya hak'uri ba sai ta tambaye shi, don haka ta matsa gaban shi ta sake tambayarshi, "how do you help her? Are you a physiotherapist?". Murmushi kawai ya mata, zata sake yin magana wayarta ta d'auki ruri, "excuse me please" ta fad'a tare da fucewa. Ita kuwa raihana tuno da k'alubalen da yake gabanta sai taji hankalinta ya sake tashi, shin waya kamata ta fara kaiwa kukanta? Waye zai taimaketa ya shawo kan Imrana ya janye daga fasa aurenta? A duniya yanzu bata da buk'atar data huce taga ta auri Imrana komai wahalar da zata Sha bayan auren shi kuwa,,,, Tasan tabbas iyayenta suka ji abinda ke faruwa ba k'aramin tashin hankali zasu shiga ba, musamman ummie data fita damuwa akan fashe fashen auren nan nata, har ta fara tsoron ko haka zata k'are rayuwarta ba aure,,,, gefe guda ga umma salaha da taci mugun alwashi akan ta, ya kamata ayi auren nan ko don a k'aryata ta "Ya Salam! Allah ka gaggauta kawo mun d'auki". Ta fad'a a fili ba tare da tasan maganar ta futo ba.
Wani tunani ne ya fad'o mata saita duba wayarta da Allah yasa duk abun nan tana hannunta ta nemo no Ayman, gajeren sak'o ta sake tura mishi ba dogon tunani kafun aiwatarwa.
"Ka taimake ni ka ajiye duk wani kuskure nawa da yasa kake fushi dani a kanshi wanda bansan ma na aikata maka ba cikin ajizanci irin nawa,,,,kazo ka taimake ni na futa daga matsalar da nake ciki please.....". Tana tura sak'on ta ajiye wayar ta gefe a ranta tana jin dole ta bar gurin nan a yanzu yanzu, ta dire k'afarta d'aya me lafiyar zata ajiye me ciwon tsoro ya hana ta, shi kuwa motsin tane ya sa shi d'ago kai ya dube ta, ta sauko da k'afa d'aya kuma ta kasa komawa ga mazauninta.
Kamar yayi banza da ita tunda ba jaririya bace ita d'in sai kuma zuciyar Imani ta hane shi da aikata hakan. Sai ya mik'e ya k'arasa gaban gadon ya mik'a mata hannun shi, sai a lokacin ta d'ago ta kalle shi, "Yaya Ayman" ta kira sunan duk da tana iya ganin wannan ba irin Ayman d'in da ta sani bane, shima kamar ba zaice mata komai ba sai kuma ya wayar mata dakai, "Ni ba Ayman bane". Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta kira sunan shi da murya k'asa k'asa ba tare da tasan ma ta aikata hakan a fili ba, "khaleefa". Da mamaki ya sake kallon fuskarta "a Ina kika sanni". Bata bashi amsa ba sai k'ok'arin zama a gefen gadon da take amma ta kasa, kamar ya taimaka mata yanzun ma,,, sai kuma ya barta, ganin da gaske ba zata iya zama da kanta saman gadon ba saida taimakon shi, k'afar me lafiya ya d'age mata ta zauna da kyar bayan ta rintse idonta tsananin azaba na kai mata har cikin kwanyarta. Sai a lokacin kukan ta ya samu damar futowa fili, kuka take wanda ya zarta na zafin ciwon da yake jikinta...., khaleefa yayi imanin indai za'a gyara mata k'ashi ba tayi kuka ba lallai wannan kukan da take na wani abun ne daban. Sai ya koma gefe ya zauna yana sauraron yadda take kuka sadidan kamar an turo ta, kuka irin mai buk'atar ban baki da rarrashin nan. Tun khaleefa na iya sauraronta har ya gaza, Cox she mutum ne da baya son jin sautin kuka cikin kunnen shi sam, sai ya sake mik'ewa daga inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya zauna ya tsura mara ido yana kallonta, "baiwar Allah! Me nayi miki zaki hukunta ni da sautin kukan ki haka.....". Karo na farko da yayi magana da wani cikin tausasawa tun bayan daya dawo gida Nigeria.
Sai ta rage sautin kukan nata ta soma share hawayenta da tafin hannunta, farin hankie ya zaro a aljihu ya mik'a mata, ta karb'a bayan ta saci kallon shi da rinannun idanunta, bayan ta share hawayenta ajiyar zuciya ta fara saukewa a jejjere. Koba komai kuka rahama ne Shikam tsura mata ido yayi yana nazarin tarin damuwar data bayyana saman fuskarta, "a wasu lokutan saka abu a cikin rai kan assasa damuwowi da yawa masu tushe da marassa makama, kamar yadda futar da magana daga cikin ciki kan rage rad'ad'i da zugin dake cikin zuciya... Wani abu yana damun ki wanda kike jin ba zaki iya tattauna shi da kowa ba,, wata k'ila saboda gudun kar ya shiga kunnen mutane da yawa,,,, har yakai kunnen ma'assasa damuwar.....". Sai yaja ajiyar zuciya yana ci gaba da kallon targad'addiyar k'afarta da tasha nadi a gurin shi d'azu kafun ya d'ora da fad'in, "idan kin yarda da duk abinda na fad'a da gaske.... Toh ki tattauna damuwarki dani insha Allah sirrin ki zai zama safe a gurina......".
Kallon shi raihana tayi na y'an dak'ik'u tana nazarin shi, shima ita yake kallo haka kawai lokaci d'aya yaji ya aminta da yarinyar, nutsuwarta da kamalarta suna sanar dashi asalin wacece ita.
Itama kusan abinda taji a ranta kenan game dashi, tana iya ganin rib'anyar kyawawan halayen Ayman fiye da goma a tare da wannan giant d'in (Nikam nace ta ina😨). Sai taji ta aminta zata iya futar mishi da abinda bata tab'a fad'awa wani mahaluki ba, hatta Ayman da yake tare da ita tsawon shekaru kuwa. Yamutsa fuskarta tayi kad'an ta d'ago suka k'ara had'a ido, sai tayi mishi murmushin k'arfin hali. "Sannu ya kike jin k'afar". Ya tambaye ta da kulawa, Da disasshen muryarta ta amsa, "da sauk'i".
Ta jima shiru zuciyarta na kai komo kafun ta sake mishi wata maganar, "shin idan na fad'a maka matsala ta zaka nemo mun mafuta?". Direct ya bata amsa, "idar har ina da yadda zanyi na nemo mikin baa".
Sai ta tsura mishi ido zuciyarta na ingizata kan ta fad'a mishi damuwarta kawai, watak'ila zai iya taimaka mata wajen ganin ta samu mafuta ba tare data karya zuciyar iyayenta ba sun d'aga hankalin su, ita kad'anta tana neman zama matsala gare su. A hankali cikin nutsuwa ta fara mishi bayanin abinda yafi damunta a duk cikin matsalolin, "yau shekarata uku kan na hud'u ana saka ranar aurena ana fasawa sau kusan biyar, duk an yiwa k'annena da suke bina aure, haka sauran y'an matan familyn mu, duk da kasancewar Ina da burin yin zuzzurfan karatun likita amma na sadaukar da wannan buri nawa tuni ga wata kwallin mutum guda tal data ke iya sadaukar da komai domin mu,,, wato mahaifiyata da a kullum safiyar Allah dare da rana bata da addu'ar data huce Allah ya kawo mun miji na gari nayi aure kamar kowacce yarinya,,, hakan yasa nima na karkata hankalina ga abinda naga tafi so a tare dani wato nayi auren,,,, kamar yadda yake babban burin mahaifina shima yaga cewa sun aurar dani lafiyar Allah ko don sauke nauyin da Allah ya d'ora musu a kaina, sannan ta gefe guda akwai tarin k'alubalulluka akaina daga gurin wasu tsirarun mutane da suka kasa fahimtar ba laifina bane dana iyayena nakai har yanzu banyi aure ba, haka zasu zo su juye buhu buhun cin mutumcin su ga mahaifiyata da suka d'orawa karan tsana ba li bare la a duk lokacin da aka fasa aurena, sai kace itace ta hana ni yin auren, ta wani gefen kuma ga wata mata da taci alwashin indai tana numfashi bani da miji a duniyaaa tayi alk'awari....Wanda duka nida ummiena bamu san dalilinta ba". Ta k'arasa fad'a dakyar cikin muryar kuka, khaleefa girgiza kanshi kurum yayi yana al'ajabin halin mutanen mu na yau, baice mata kanzil ba har ta gama share hawayen ta ajiye mishi hankien shi gefen shi, taci gaba da magana da rawar murya mai cike da rauni. "a wannan karon na k'arshe na had'u da wani saurayi Imrana, ban tab'a tsayawa nayi soyayyah da wani mahaluki ba sai shi duk cikin samarina, tafiyar mu tayi nisa sosai har na fara tunanin me yiwuwa shine zai zamo mijina a wannan karon, su kansu y'an gidan mu tun suna d'ari d'ari har suka saki jiki suna shirye shiryen biki hankali kwance, har an kawo lefe an gama komai kwatsam! D'azu da yammaci Ina ninke kayana ya turo mun sak'o kamar haka.....". Hannunta har rawa yake ta nemo sak'on ta nuna mishi, taci gaba da maganar ta kuma "ko bayan ba duba dana kira shi sai yake bani hak'uri yace mun wai shima ya fasa aurenaaaa,,,,, na rasa wanda zan fad'awa damuwata shine na futo don na nemowa kaina mafuta ba tare da nasan inda nake nufa ba har Allah ya had'a ni da kai ka bugeni........".
Ajiye mata wayarta yayi a lokacin da ta kai aya a zancenta, ya mik'e tsaye ya fara safa da marwa cikin matuk'ar tausayinta, sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa d'azu ta hau titi tana tafiya kamar sabuwar mahaukaciya, bata jin horn bata ganin inda take jefa k'afarta ma gaba d'aya.
Sake dawowa yayi kusa da ita ya zauna yana kallon yanda take kuka bilhak'k'i da duka gaskiyarta, wato shi tunda yake ma rayuwar wani mutum bata tab'a bashi tausayi kamar tata ba in aka d'auke tasu damalmalalliyar rayuwar. Yarinya k'arama kamarta, daya kamata ace yanzu tana can wajen fafutukar Isa ga muradanta, amma gata a nan tana fad'a da k'addarorin ta! Babban abin bak'in cikin ma akan aure? Sai yaja tsaki a fili yana sake auna zantuttukan ta kafun wani tunani ya fad'o mishi, lallai k'addarar ta tayi shige da tasu ta wani b'angaren. Sai wani tunanin ya sake fad'o mishi from no where, Kuma ba tare da dogon nazari ko lissafi ba yayi na'am da shawarar zuciyarshi ta lokacin a take.
Sai ya kalleta yana tambayarta,
"Yanzu kwana nawa ya rage auren?".
"Kwana shida" ta bashi amsa a sanyaye, sai yayi jimm a ranshi, kafun ya k'ara kallonta yace, "toh nidai a halin yanzu bansan wata mafuta da zan kawo miki da zata sa saurayin ki ya dawo ya aureki dole ba, amma akwai wata shawara, shin zaki aureni?"
Da hanzari ta d'ago ta kalleshi ba tare ma da tasan ta aikata hakan ba, wannan wane irin mutum ne yana nufin ta aure shi daga had'uwa a yau d'azun nan, hakanan ba dogon tunani ko nazari, bare a kaiga tushen abinda ke had'a alak'ar aure.
Khaleefa ganin tana yi mishi wani irin kallo na rashin fahimta, sai ya fara k'ok'arin gyara zancen shi da fahimtar da ita ainahin abinda yake nufi, "yi hak'uri naga kina kallona a bai bai, kamar yadda kika bani labarin ki, nima zan baki labarin soyayyata bazan b'oye miki komai ba" sai yaja dogon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login