Showing 147001 words to 150000 words out of 288773 words

Chapter 50 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1115

yayi ba. Duk da dama ba wai bud'e baki yayi sosai yadda zata ji ba.



_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty one4️⃣1️⃣


Gyaran murya yayi bayan ya ajiye k'atuwar jakar system d'inshi gefe, sai a lokacin raihana ta lura dashi, aikuwa ta kama kanta da sauri hadda gyara zamanta gabanta yana tsananta fad'uwa. K'arasawa yayi kujerar dake kusa da wadda take zaune ya zauna daga d'an nesa da ita yace, "barkan ki da gida Mrs khaleefa". . cikin diriricewa da inda inda tace, "ya Yaya Ayman an wuni lafiya....".
Wani abu mai d'aci ya had'iye yace, "kamar yadda kike,,,, koda yake halinda muke ciki ya banbanta, don ke ga dukkan alamu kina cikin k'oshin lafiya cikin nutsuwar zuciya data ruhi, sab'anin ni da nake a hargitse, nake kwana da ciwon Soo nake tashi dashi har yana neman hanyar da zaiyi ajalina,,,,,".
Ba tasan lokacin data juyo ta kalleshi ba har saida ta tsinci kwayar idanunta cikin nashi..
Saita d'auke idon da sauri ta dafe saitin zuciyarta da hannunta. Shima d'auke idon shi yayi yana korar shaid'an daga cikin zuciyarshi, ba tare daya kalleta ba yaci gaba da cewa, "a baya mun d'auki lokaci mai tsawo muna gaisuwar mutumci da sunan friendship wanda yake sam ba haka ba a cikin zuciyata, da farko na fara jin shigar wasu sababbin abubuwa cikin zuciyata sannu a hankali da bansan a yadda zan fassara suba lokacin, na d'auka Nur nake so bake ba shiyasa ban tab'a kallon ki da wata siga ta daban ba, a hankali wannan soyayyah ta dinga ginuwa a cikin zuciyata tana sake k'arfi, na dinga kishin ki ba tare da nasan dalilin aikata hakan ba, har takai na kasa jurar alak'a dake a lokacin da Imran yake dab da aure ki, Ina ganin kamar shi zai shiga tsakanina dake, ban k'ara tabbatar da matsayin kiba saida muka samu sab'ani da Nur, a lokacin na gane lallai ke nake so tsawon lokacin nan ba tare dana sani ba,,,, gashi a lokacin Ina gab da rasa ki gaba d'aya, anan hankalina ya sake tashi na sake shiga damuwa mara misali.
Na samu dama ta farko a lokacin da kika turo mun da text na rabuwar ku da Imran, nayi farin ciki nayi murna har na fara mafarki da tunanin watak'ila dama ke d'in mallakina ce, shiyasa maganar auren ki ta dinga lalacewa har karo shida,,,, na tambayi malam da zumud'i tunda a bakin su nake jin labarin duk wani rugujewar auren ki, sai dai a wannan karon su kansu basu sani ba, haka yasa na sake jinkirtawa har zuwa sanda zancen zai fasu sai in fad'a musu a nema mun auren ki.
Koda dare yayi na kasa bacci da hak'uri saina yanke shawarar fad'awa auntie kawai, sai dai wani tashin hankalin khaleefa ya riga ni kai maganar neman auren ki gabanta, wannan ya d'aga mun hankali ya sake dilmiya ni a damuwa, sai dai bani da yadda zanyi don khaleefa yafi k'arfin komai a gurina kamar yadda shima ba abinda bazai iya sadaukar mun a duniya ba, nayi kuka a fili nayi a zuci har bansan adadi ba, tun ina ciwo a tsaitsaye har takai na kwanta magashiyan, bikin ku yana k'aratowa ciwona yana dad'a tsananta, na kasa taimakon khaleefa da komai duk yadda na dinga dannar kaina da zuciyata kuwa saboda wutar kishi da take cin raina. A k'arshe na tattara na bar gidan zuwa gidan iya, amma duk da haka ban tsira ba, nayi alk'awari duk yadda zanji dani za'a d'aura auren nan, sai dai jarumtata ta gaza a lokacin da aka shafa fatiha na tabbatar na rasa ki kenan har abada...... Take naji wata hajijiya tana wujijjigani kafun na cewa Ahmad komai ganina da jina had'e da numfashina sun tsaya cak, sai bud'e ido nayi na tsinci kaina a gadon asibiti likitoci sun kewaye ni suna fafutukar ceto rayuwata, a lokacin da ni kuma nafi son na mutu ma nabar wannan rayuwar duniyar......".
Doguwar ajiyar zuciya yaja cikin dauriya yaci gaba da cewa, "tabbas Ina sonki raihana,,,, kwatankwacin son da zan iya yiwa rayuwata, Ina sonki fiye da yadda duk kalmomin bakina zasu fad'a,,,,, kuma har gobe bance zan daina sonki ba don bazan samu makwafin ki a rayuwa ba har na koma ga Allah..... Raihanatu ba wai Ina fad'a miki haka don ki soni ko don ina saran zan same kiba, a'a ina fad'a miki ne don na rage rad'ad'i da mikin da yake cikin zuciyata..... Duk dani bansan irin auren da kukayi da khaleefa da soyayyar gani da kallo d'aya data kama zuciyoyin ku ba, amma a zuciyata bana fatan wata rana ki futa daga rayuwar shi, domin a duk inda kike ke haske ce me yaye duhu.... Kuma zaki kasance haka a rayuwar khaleefa dama ta Auntie baki d'aya naji haka a jikina....".
Tunda ya fara magana raihana ta d'auke wutaa tana sauraron shi ko kwakkwaran motsi ta kasa yi har ya dire, inda bacci take data jima da farkawa don kunnuwanta sunji abune da bata tab'a zaton zasu jiba ko a cikin mafarkinta. Yaya Ayman yana sonta! Ta Yaya?, Saita dafe kanta da hannunta duka biyu tana kiran sunan Allah ya kawo mata d'auki.
Shikam mik'ewa yayi yana jinshi sakayau zuciyarshi babu wannan nauyin, jakar daya shigo da ita ya bud'e ya ciro wani abu a farin kwali yazo ya d'ora mata saman cinyarta, "your marriage gift".
Bata d'auki kyautar ba kamar yadda bata motsa daga yadda take ba har ya fara k'ok'arin barin parlon.
Kamar daga sama ya tsinkayi maganarta don bai tab'a tunanin zata bashi amsa ba.
"Ka keta iyakah! Kayi magana da matar wani! Magana irin wadda addinin mu ya haramta!!! sai dai watak'ila k'arshen matsalolin kane da nata zasu zo ta hanyar aikata wannan zunubin,,,,,".
Taku kad'an ta sake yi ta rage nisan dake tsakanin su taci gaba da fad'in, "aurena da khaleefa ya kasance wani b'oyeyyen sirrin mu da bai kamata ka sani ba, sai dai nayi alk'awari duk ranar da wa'adin auren mu ya cika.... nayi alk'awarin duk ranar dana bar rayuwar khaleefa....., bazan manta da soyayyar daka nuna a kaina da tarin sadaukarwa ba, zan kasance a rayuwarka koda ka auri wata bani ba indai har zaka soni a lokacin....".
Saita ajiye mishi kyautar shi k'asan k'afar shi tace, "na gode amma bazan iya karb'ar kyautar nan ba, iya d'awainiyar da kayi dani a baya ma Allah ya bada lada.....".
Jin kamar motsi a bakin k'ofar shigowa parlon yasa duk suka kalli gurin ba tare da sun shirya aikata hakan ba, iska ce kawai ta kad'a murfin, kudun kada wani ya same su a lokacinya zargi wani abu sai raihana ta d'auki hanya zata futa a d'akin, Ayman yayi saurin shan gabanta hannun shi rik'e da kwalin kyautar shi, cikin marairaicewa yace, "kada kice mun zaki futa daga rayuwar khaleefa don ki dawoo cikin tawa! Kin riga kin zama tashi mallakin shi watak'ila ma nan da lokaci k'alilan zaki haifi d'an shi ko y'arshi,,, beside matar khaleefa ma ta haramta a gareni har abada......". Ya kai k'arshen zancen yana jin wani tuk'uk'in bak'in ciki a zuciyarshi.
Girgiza mishi kai tayi tana sake ja baya tace, "ko ban futa daga rayuwar shiba shi zai futa daga tawa, raihanatu zata zama mallakinka da komai nata, bisa kyakkyawan albishir na cewa ko hannunta khaleefa bazai samu nasarar rik'ewa ba nasan shine tunanin ka".
Sai yanzu murmushi yayi escaping saman fuskarshi, "lallai akwai wani abu cikin auren ku tunda kika yimun irin wannan alk'awarin,,,, yadda kike haka khaleefa yake, baya wasa da alk'awari kamar yadda baya wasa da abinda yake so, zai bi kowanne mataki komai rintsi indai zai samu cikar burin shi,,,,, alhamdulillah bisa ga wannan kyauta da Allah yayi mun, raihanatu kece farin cikin rayuwata...". Murmushi tayi ta maida kanta k'asa itama tana jin wani tarin farin ciki a cikin zuciyarta.
(Ko'ina tunanin raihanaa da Ayman yayi?)
Ayman ya d'an kalleta na adadin wasu mintuna a ranshi yana raya kamar ma k'ara mata kyau akayi, kafun ya kori shaid'an da hanzari ta hanyar barin kallonta.
Kwalin kyautar daya mata ya soma k'ok'arin d'anka mata a hannunta yayinda ita kuma tak'i karb'a tana girgiza mishi kai, turo k'ofar parlon akayi shigo da sallama. Muryar auntie ce, hakan yasa duk suka juya da sauri,,,, daga bakin k'ofar ta tsaya nad'e da lafaya hannunta rik'e da Jakarta da Mukullin motar ta, kallon su take irin kallon tuhuma da zargi. Khaleefa kam da yake bayanta kallo d'aya yayi musu ya kewaye ta ya k'arasa shigowa cikin parlon ya nemi gefe d'aya ya zauna had'e da kwantar da kanshi saman kujera ya lumshe ido yana jin wata masifaffiyar yunwa na farmakar shi.
Ayman k'arasa zura mata kwalin yayi ya d'auki jakar shi ya tunkari k'ofar.
"Sannu da zuwa auntie". Ya fad'a bayan ya tsaya gefe guda, murmushi tayi tace, "Kai za'a yiwa sannu ya jikin ya aikin kuma".
Murmushi yayi shima yace, "ai na warke insha Allah naji sauk'i".
"Toh Allah yasa" auntie ta fad'a tana k'arasa shiga cikin d'akin shi kuma ya futa.
"Sannu da zuwa auntie". Raihana ma ta fad'a kanta a k'asa.
Har yanzu fuskar auntie fad'ad'e da fara'a tace, "yauwa raihanatu, baki iya yiwa mijin ki sannu da dawowa ba amma kin iya yiwa wata mata can a gefe...". Satar kallon inda yake tayi, cikin jin kunyar auntie kamar ta nutse a gurin tace, "kiyi hak'uri auntie insha Allah zan gyara". Dafa kanta tayi tace, "ba komai raihana, mama haleema tazo kuwa?".
Raihana tace, "nima ban dad'e da shigowa ba maybe tazo kafun nazo ta tafi".
Zama tayi a kujerar da khaleefa yake zaune tace, "Anya kuwa? Jiya tace mun bata jin dad'i watak'ila jikin ne har yanzu".
Raihana tace, "ayyah Allah ya bata lafiya". Auntie tace, "ameen".
Futa tayi zuwa kitchen donta sama musu abinda zasu ci taga kamar a gajiye suke, ita Kuma auntie ta dawo da dubanta ga khaleefa "khaleefa kana lafiya kuwa?". Ta tambaye shi da harshen Arab.
"Ana bikhair". Ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba.
"Allah yasa!". Ta fad'a tana d'aukar wayarta data fara ringing.
Raihana bata sha wahala wajen had'a musu tea mai kyau irin na k'asar Sudan ba saboda mama haleema tayi rannan a gabanta taga yadda ta had'a komai.
Shap shap ta shirya musu indomie iya wadda zasu ci su biyu ta d'auki trayn tayi parlour.
"sannu raihana mun saki wahala ko?". Auntie ta fad'a tana karb'ar trayn ta ajiye kan glass table k'arami dake gabanta.
Komawa tayi ta kawo musu ruwa da lemu ta had'a da kofuna.
Auntie sai jera mata sannu takeyi kamar wadda tayi wata uwar aiki, har tasa tana jin kunya. Ita ta zuba musu shayin a funjalai biyu ta bawa auntie nata ta kaiwa khaleefa ma nashi, "ga shayi" ta fad'a ganin baisan tazo gurin ba.
Sai a lokacin ya tashi zaune sosai, ya karb'i shayin yana bin yatsun hannunta da kallo, ganin jan lalle a yatsunta sai yaja k'aramin tsaki a ranshi yana ayyana, wai ita wannan kullum saita saka wannan abun a yatsunta, taji tsakin shi sarai auntie ma kuma taji, amma sai cikin su babu wanda ya nuna mishi ko yabi takai.
Auntie ta fara zuba ma indomien ta mik'a mata bayan tasa fork, ta d'auki wani tray zata zubawa khaleefa auntie ta dakatar da ita ta hanyar fad'in, "khaleefa baya cin indomie, in akwai ragowar dankali ki soya mishi chips". Da "toh" ta amsa ta tashi da hanzarinta ta tafi don cika umarnin auntie.
Bayan ta futa auntie gyara zamanta tayi ta kalle shi da kyau a lokacin da yake shan shayin hannun shi tace, "khaleefa me yasa ka yiwa raihana tsaki?".
Shiru yayi ya dakata da shan shayin, "kayi shiru Ina tambayarka? Yanzu tsakani da Allah ka kyauta kenan? Kana gani fa muna shigowa yarinyar nan da rawar jikinta ta tashi donta sama mana abinda zamu sa a cikin mu saboda taga yanayin kowa a cikin mu, tuntuni nake kwab'ar ka saboda tsaki mummunar dabi'a ce da take hana zaman lafiya tsakanin mutane, gashi yanzu matar ka da take iya k'ok'arin ta wajen ganin ta kyautata maka ita ka yima tsaki, gaskiya bana so kada ka kuma". Ba tare daya kalleta ba yace "insha Allah za'a kiyaye".
Auntie tace, "tom". Raihana bata d'au lokaci mai tsawo da yawa ba ta had'a mishi chips d'in ta kawo mishi, yanzun ma saida ya kalli yatsun hannunta yana d'arsa wani abu a cikin ranshi, kad'an ya rage yaja tsaki ya tuna da kashedin Auntie, madadin haka sai yace,
"Ki dawo ki d'auke ni bana ci". Ya fad'a bayan ya gama k'arewa abincin kallo.
Har ta juya zata d'auko kamar yadda yayi umarni muryar Auntie ta dakatar da ita, "raihana dawo ki zauna, domin shi kina gama wani aikin ko hutawa bakiyi ba na k'ara tashin ki, kuma sai yaci".
A d'arare raihana ta zauna gefenta tana wasa da gyalenta, shikam khaleefa banza yayi da plate d'in abincin ya d'auki wayarshi yana latsawa.
"Wad'an can kayan fa waya kawo su?". Auntie ta tambayi raihana tana nuna mata direction d'in data ajiye kayan data kawo d'azu.
Raihana da sanyin muryarta tace, "dama wanda kika ce na kawo akai d'inkin nan ne".
Auntie "Kai! Iya wad'annan kuma? Ai sunyi kad'an ki k'aro kamar biyun su yanzun nan".
Ba don karta yi mata musu ba da tace haka sun isa, duba da uban kayanta da aka kawo ta dasu, a haka ma ummie iya sababbin ciki tace a d'auka mata, ragowar duk ta bayar, wani ma sawarta d'aya ummie duk ta had'a dasu taba mutanen da suka fita buk'ata.
A nutse ta mik'e ta futa daga d'akin don cika umarnin auntien.
Futar ta yaba Auntie damar yiwa khaleefa magana a karo na biyu, "matar ka zaka nunawa ban isa da kai ba kenan?".
Ajiye wayar yayi tare da yamutsa fuska idon shi kan plate d'in yace, "kinsan matsalata fa Auntie".
Auntie tace, "matsalarka ta banza ta wofi,,, abinda zaka duba wannan ai umarnina ne, nasan da matsalar kuma nayi umarnin,,,".
Baice mata komai ba sai kanshi da yake k'asa, ta tab'e baki a lokacin data mik'e zata shiga bedroom d'inta tace, "khaleefa duk tsaftar kafa ba zaka kai raihana ba,,,, Soo ka daina kallon kanka wani abu daban,,, ka iya cin abincin restaurant da bakasan waya sarrafa shi bama, sai a nan zaka futo da wani fi'ilin banza.....".
Ta kai k'arshen maganar tare da shigewa d'akin baccinta. Shikam juya chips d'in ya dinga yi a plate kafun a d'arare ya d'auki d'aya ya saka a bakin shi.
Ba don ya kwanta mishi a rai ba ya dinga tutturawa har yaci da yawa, dama yunwa yake ji sosai tsabar iyayi ne ya hana shi ci.
Koda raihana ta shigo da sallama bai d'aga ido ya kalleta ba ya amsa, don yana ganin in ya kuskura ya kalleta abincin nan haramiyar shi.
A inda ta ajiye wad'an can ta ajiye wad'annan ma ta koma gefe ta zauna tana buga game a wayarta.
Da sallama aka turo k'ofar aka shigo, ta amsa ba tare data d'ago kanta ba, Ayman ne ya k'arasa kusa da inda khaleefa yake zaune sukayi shaking hands sannan ya zauna.
Lokacin khaleefa ya gama tuttura chips d'in dole kenan ya ajiye plate d'in gefe.
Ita kam raihana mik'ewa tayi a ranta tana tunanin ko tayi karambani ta d'ora musu abincin dare? Amma bari dai ta gwada. Sai ta ajiye wayarta a nan ta mik'e tsam ta futa daga parlon, Ayman yayi iya yinshi wajen ganin bai kalleta ba har ta futa.

Bata sha wahalar gano inda komai yake a store na gidan ba, ta soma tunanin me zata dafa musu da zasu iya ci, a irin abincin da ake aika mata ta fara laluben d'aya, sai dai kash duk irin abincin k'asar Sudan ne auntie take zama ta shirya da kanta, a k'arshe saita hak'ura ta dafa musu jallof rice da taji wadataccen kifi.

A parlour kuwa a haka auntie ta futo ta same su, ta tambayi "ina raihanan kuma?" Ayman yace, "ta futa". Kayan data dad'o ta d'auka ta shige d'akinta itama.
Sunci gaba zama har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib kowa ya tashi don sauke farali.

Bayan ta kammala girkin ta gyara kitchen d'in, ta adana komai a muhallin shi warmers din da ta zuba abincin ta d'auka ta kai dinning na parlon ta ajiye. Har lokacin khaleefa da Ayman suna zaune ba kuma hira sukeyi ba, hasalima football channel da Ayman ya kama duk suke kallo.
Ita kam so take ta tafi amma ba tayi sallama da auntie ba. Saita zab'i zama a parlon itama zuwa lokacin da auntien zata futo.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login