Showing 39001 words to 42000 words out of 288773 words

Chapter 14 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1048

mata doguwar riga, kayan sunyi mata kyau sosai.
Tana ninkewa su hapser suka dawo daga gantalin nemo k'osai a anguwa. Su duka hud'u suna dariya suka shigo suna fad'a ma raihana ai basu samu k'osai ba sai wata jagwalgwalalliyar awara a idoma idan ka ganta kamar ayi amai. Dariya raihana ta dinga yi musu, "ai na fad'a muku ba zaku samu k'osai a anguwar nan ba kuka k'i, nima wanda naci kuna bacci iya ce tayi ta aiko mun, tunda Yaya Ayman ya fad'a mata Ina son k'osai toh kuwa indai tayi Ina gida saita aiko mun dashi".
Xee ce ta balla mata harara tace, "gaskiya raihana bakiyi ba, amma ko guda baku rage mana ba kika bammu da jin k'amshi".
Salma da take parlour tana jiyo su tace, "toh sarakan son banza ni kaina da nake jego bata ajiye mun ba bare wasu ku".
Duk waje sukayo gurinta dama a k'iris suke sukayi mata caaa suna fad'in, "ai ke wannan ke kika so, muka ga da mijin ki da komai kika wani tattaro kika barshi wai kinzo kwanan biki". Hapser tace, "fad'a mata dai xee aini ko baki raihana tazo zatayi saina hana haka kurum".
Ido bud'e Salma ta kalle su, "au hakane ma abun?".
Ameena da bata ce komai ba ta samu kan kujerar dake kusa da Salma ta zauna tana fad'in, "yanzu saboda Allah Salma ke kin yarda mijin ki duk safiya yazo nan ganin ki da dare kuma ki ajiye mana samha ku tafi yawon barbad'ar cin abinci restaurant".
Raihana ma futowa tayi rik'e da wayarta tana replying text d'in Imran, Zama tayi bayan gama abinda take cikin k'asa da murya tace, "ba sai in ma gidan cin abincin suke zuwa ba.....".
Duk a gurin kowa zaro ido yayi, xee da k'arin abun haushi hadda tafa hannuwa, "kice wani gurin da ban sukeyi?".
Salma tayi narai narai da ido tace, "kiji tsoron Allah dai Auntie raihana".
Raihana tace, "toh da tsoron ki zanji keda yuseep d'in ai duk manyan y'an iska ne, abun daya fi wanda na fad'a ma zaku iya yi, in kuma ba tsoro ba ki k'aryata ni yanzu in bud'e miki aiki, kinsan dai....?"
Kamo hannunta Salma tayi tana dariya tace, "haba auntie na kar mu fara yin haka dake mana, kinga gasu zee da ameena nan sun zubo mana ido"
Dariya raihana tayi, ameena tace, "don Allah Salma ki k'aryata raihana muji abinda yake b'oye". Mak'e musu kafad'a tayi tace, "umm umm ai ba kyau ma k'aryata wanda ya girme ka koda second uku ya baka a duniya kuwa balle Auntiena data bani kusan shekara".
Wata irin dariyar shak'iyanci duk sukayi a d'akin zee tace, "Allah raihana kece maganin Salma".
Ameena kuma tace, "ai ba Salma kad'ai ba raihana maganin kowa ce don dai tana shiru ne".
Haka sukayi ta hirar su irinta y'an matan da suke ganiyar k'uruciyar su, a tsokani wannan a tsokani waccen, Salma dai da taga zasu tire ta k'arshe sai tabar musu d'akin. Har amarya ta dawo daga gidan gyaran jiki.

Washe gari suka tashi da kamu, a wani k'aton kango da Abba ya siya aka gudanar da walimar kamun, anci ansha anyi wa'azi mai shiga jiki da sanyaya gab'ob'i, amarya tayi kyau cikin lafaya milk and brown data haska ta sosai, su raihana kuma cikin d'inkin doguwar rigar kamfala mai kyau da tsada, tsabar bak'in ciki dangin abbanta duk wanda suka had'a ido saiya zabga mata harara, kamar kowanne lokaci in ana biki ko suna sukan yi k'ananun maganganu da yada habaici wannan karon ma ba'a barsu a baya ba, ita dai ummie tuni ta saba da halayyarsu y'an uwanta kawai ta jaddadawa duk abinda zasuyi don Allah suyi hak'uri karsu kulasu, da an gama bikine zasu kama gabansu kowa tayi nata guri.
Alhamdulillah an tashi kamu lafiya kowa yasan inda ya nufa.
A daren ranar kusan kwana su raihana sukayi suna hira saboda k'aruwa da sukayi da kusan mutum 6 sa'o'insu masu aure da y'an mata. (Tunda su familyn su na wajen uwa ba masu matsala da takura bane, y'ay'an su basa aure har sai sunyi NCE ma, wasu ma suna tsaka da karatu a university Allah yake kawo musu miji suyi aure ba k'aramar magana bare gajiyawa da y'ay'a)
Ranar Saturday ango ya shirya k'asaitaccen dinner party a d'aya daga mafiya kyau da sauk'in kud'in event center.
Amarya tasha kyau cikin blue black net da yaji d'inkin gown mai kyau irinta amare. Fuskarta tasha make-up mai kyau da tsari.
Raihana yau ankon lace d'insu tasa wanda akayi mata d'inkin riga da skirt dai dai jiki, d'inkin ya zauna mata dass gwanin burgewa, ita yau tayi make-up amma light ko eye lashes bata yarda an saka mata ba.
Anyi biki dangin amarya da dangin ango y'an mata sunsha rawa samari na musu lik'i, ita dai raihana tana gefe, Sam bata da rawar kai irin na y'an mata, ko d'an zirga zirgar kula da bak'i batayi kamar y'ar gayyata.
Bayan an tashi biki gidan su ya cika fal da mutane saboda d'aurin auren gobe, sai ya zamana sun rasa inda zasu kwana ma, d'akunan su tuni dangi sun gaje, gashi su ba wani huld'a suke da mutanen anguwa sosai ba in aka d'auke gidan iya babu gidan da take shiga a layin bare su shiga suyi dabdala.
Wani tunani ne yazo ranta a lokacin da suke zaune a parlour jigum suna tunanin abinyi ita dasu xee. Sai ta nufi d'akin ummie direct, suna zaune ita da mammie (yayarta kenan) sun saka khausar a tsakiyar su suna maganar da raihana bata san kota meye ba, da sauri raihana tayi baya tace, "kuyi hak'uri na shigo muku ba excuse".
"Ba komai ki shigo dama ruqayya yanzun ta gama cigiyar ki". Mammie ce keyin wannan magana. K'arasa shiga raihana tayi ta jingina da closet.
"Kun samu inda zaku kwanta kuwa?". Ummie ta tambayeta.
Da sauri raihana tace, "a'a ummie amma dani cewa nayi ko zamu tafi gidan iya kawai mu kwana a can kona iya yau ne".
D'an jim ummie tayi don ita har ga Allah bata fiye son wannan had'in hark'allar ba, "Ina ne gidan iyan?". Mamie ta tambaya.
Kafun raihana tace wani abu Auntie tace, "gidan limamin masallacin anguwar nan ne, shine wanda kuka amshi cooler d'azu a gidan".
Mammie tace, "Okay to suje can mana idan babu damuwa?"
"Kuna da yawa ai kuje" ummie ta fad'a sannan ta dubi raihana da muryar gargad'i tace, "ki kula". Raihana tace, "insha Allah ummie".

Raihana tana zuwa kayansu ta had'a kawai tace kuzo muje. Kusan su takwas suka nufi gidan iya.
Har malam ya sakaya kyaure da tuni ma ya rufe tafiyar Ayman kawai suke jira ya tafi, shi kuma Ayman tunda ya samu hirar zamantakewar mutan da sai ya kasa tashi a gurin yana ta sauraron labarin abun gwanin burgewa a gurin shi.
A haka su raihana suka shigo da sallama. Iya da Ayman muryar raihana suka gane duk a ciki saboda itace suka fi sani, amma tunanin abinda zai futo da raihana cikin wannan lokacin yasa tace, "kamar muryar raihana ko?".
Raihana Zama tayi gefenta kan tabarmar da suke zaune tace, "eh nice iya munzo ne mu kwana a nan idan babu damuwa saboda gidan mu ya cika taf da y'an biki"
Iya cikin jin dad'i tace, "laaaah babu laifi sannun ku da zuwa, ki shigar da k'awayen naki ciki mana, koda yake kuzo muje na kaiku don wannan indai donta itane".
Murmushi raihana tayi, iya tayi gaba su kuma suka bi bayanta. Littafin da yake gaban Ayman ta d'auka sai kuma ta d'ago ta kalle shi, ya zuba mata ido yana kallonta, marairaice fuska tayi tace, "Yaya Ayman kallon fa?".
"Uhm Ai dole na kalle ki raihanatu tunda kika shiga hidimar biki gaba d'aya kin manta dani, wayarki switch up oll the time".
"Ayyah Yaya Ayman bafa mantawa nayi dakai ba, kawai dai nayi busy, toh wai zaman me kake yi anan goma fa ta huce".
Shiru Ayman yayi kafun ya sake d'agowa yana mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa farat d'aya. Itama shiru tayi tana kallonshi kawai, doguwar ajiyar zuciya yayi yace, "yanzu fa shikenan raihanatu kina yin aure mun rabu?".
B'ata face tayi tace, "Toh meya kawo wannan maganar kuma don Allah, nidai a'a ko nayi aure ba abinda zai raba mu har gidana ma zaka dinga zuwa lokaci bayan lokaci muna gaisawa". Wani irin murmushi Ayman yayi ya shafi gashin kanshi yace, "Anya raihanatu?, da hakan zai yiwu da nafi kowa jin dad'i da farin ciki ai".
Murmushi itama raihana tayi tana tuna gaskiyar maganar shi, abinda ya fad'a haka yake, duk inda suka kai da shak'uwa da kusanci yanzun tana yin aure sun rabu, k'arshen tama ita da sake wata doguwar hira dashi har abada.
Wani abu taji ya caki k'ahon zuciyarta, sai kawai tayi k'asa da kanta tana tuna yadda farkon soyayyar shi da Nur taso raba tsakanin su, ta tashi hankalinta kullum cikin rigima dashi, shi kuma yak'i rabuwa da ita, a cewar shi ai ba ita ta had'a suba, hasalima tun kafun ya nuna yana sonta suke tare da raihanatu, idan tayi hak'uri in lokacin su rabu yazo zasu rabu da kansu ma, gashi kuwa lokacin daya fad'a Yana gab da zuwa.
Lallai Ayman ya cika aboki na kwarai kuma cikakken mutum mai magana guda, yanzu gashi da kanta Nur data fahimci gaskiya take neman had'a alaqa da ita.
Iya ce ta katse musu tunanin da suke ta hanyar fad'in, "ya kamata kazo ka tafi ganan mamanka tana tambayar ko anan zaka kwana ne? Tace tana ta kiranka baka d'agawa".
Shafa idon shi yayi da hannun shi ya zura hannu cikin aljihun wandon shi ya zaro wayar, tun d'azu yake jin vibration amma ya kasa ciro wayar ya duba har kiran ya katse.
Mik'ewa raihana tayi tace, "Yaya Ayman ka gaida gida ka gaishe da auntie".
Bai ce da ita komai ba ya mik'e hannun shi rik'e da mukullin mota, ya yiwa iya sallama ya tafi. Sai bayan futar shi raihana tace, "iya wane d'aki kika zab'a mun ne? Ina fatan an kunna mun air-conditioner yadda zanfi jin dad'in bacci kinsan kishiyar farko saida kulawa, in ba haka ba kuma yanzu tayi out data ciki".
Iya tace, "ke tafi can y'ar son jin dad'i wato ke har wata AC kike nema a gurin matar da zaki yiwa kwacen miji, toh Ina laifi ma dana baki d'aki jikin nawa koda yake dana sani ma na kusa da kwata na ajiye ki"
Raihana tana dariya tace, "ai baku da d'aki kusa da kwata iya indai ba toilet d'inki zaki kaini ba, kuma kinsan mai ran k'arfe yana zuwa zaici tarar ki".
Dariya iya tayi a lokacin da raihana ta gama maganarta ta shige cikin parlon.
Yau bata yarda tayi magana da kowa ba tayi kwanciyarta bacci Cox ta gaji over.
Washe garin d'aurin aure raihana tunda tayi sallah da asuba ta sake komawa ta kwanta har 10 bata tashi ba, duk su hapser sukayi budurin su suka gama, har me make-up tazo tayi musu, iya tayi musu break suka karya aka ajiye mata nata.
Iya ce ta sake lek'owa d'akin nasu tace, "Wai har yanzu bata tashi baccin ba?".
Zainab tace, "eh iya yanzu nake son na tashe ta dai saboda me make-up d'in zata tafi".
"Ya kamata kam gashi ba abinda taci ma".
Saita k'arasa shiga d'akin tana d'an bubbuga k'afarta da hannunta, a hankali raihana ta bud'e ido tana karanta addu'ar tashi daga bacci, "tashi raihana kada a d'aura auren ke kina nan".
Mik'ewa tayi zaune tana bin y'an matan d'akin da kallo d'aya bayan d'aya. Duk sunci kwalliya cikin shaddar d'aurin aure.
"Tashi maza na had'a miki ruwa me zafi kiyi wanka".
Mik'ewa tayi ta zari zanin da maama ta cire already da k'aramin hijab jikinta ta bi bayan iya, har toilet iya ta rakata sannan.
Da soap tayi wankan da ruwa ta d'auraye bakinta da toothpaste ta d'auro alwala ta futo.

Sad'af sad'af ta wuce d'akin iya da gudu saboda Jin muryar Ayman da tayi suna magana da malam a sitting room.
Shap shap ta shirya su ameena sunata azalzalarta wai make-up artist d'in zatayi tafiyarta in bata zoba, ko breakfast batayi ba ta zauna bayan ta gama shard'anta mata dokokin kar a cika mata fuska kamar tasu. Shaddar pitch colour ce an mata adon aiki da zare milk and dark blue. Sosai tayi kyau kamar itace amaryar. Duk sai yaba mata sukeyi, nan suka shiga hotuna suka cika parlon iya da hira, da kuwa tsit dasu kamar basu ba. Iyace da ta shigo ta tsaya tana kallon raihana kafun tace, "a'a a'a kece nan aka ranbad'a miki jan baki da kwalli haka?". Duk sukayi dariya Salma da take feeding baby samha a lokacin tace, "ai bata yarda anyi mata yadda ya kamata bama iya" iya na zaro ido tace, "a hakan? toh Ina fatan dai ta karya ko in aka maka wad'annan kayan ja ido da ja hancin ba'a cin komai?".
Raihana ta bud'e baki zatayi magana karaf idonta ya fad'a bakin k'ofa, saita kasa cewa komai sai zaro ido da tayi tana kallon k'ofar.

_A gaskiya Ina jin dad'in comment d'inku, ta hakane nake gane asalin yadda muke tafiya tare, sorry 4 de late update naje bikin k'awata ne, Aysha aleeyu Ina yi mata fatan zaman lafiya mai dorewa a gidan mijinta da zuri'a d'ayyiba_

*Ku muje zuwa my fans*


_Comment and share_
24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page twelve 1️⃣2️⃣


Da sauri ta daka tsalle taje ta rungeme su. Su kansu cikin farin ciki suka rungume raihanar suna murnar had'uwa da juna kamar wanda sukayi shekara basu had'u ba. Cikin parlon iya ta k'arasar dasu. Sun gaisa da mutanen cikin d'akin har iya don basu manta ta ba tun a waccen ranar. Ai tuni raihana ta ware anan sunata hira tuni ta manta ma da wani karin kumallo. Salma ce ta kawo musu ruwa da lemuka, hadda tuwon safe da akayi.
Iya ganin raihana zata ci gaba da zama da yunwa don bata cin miyar taushe, sai ta kamo hannunta bayan ta kai mata abincin sitting room inda su malam suka tashi. A tsakar gidan suka tsaya.

Raihana kam murmushi tayi tace, "iya bamu gaisa ba fa dake kema ko?!". Saita d'an russuna a gaban ta, "iya Ina kwana".
Iya tace, "lafiya tashi muje ni ki karya". Kamo hannun ta iya tayi, bata sake hannunta ba kuma har saida ta dangane ta da sitting room d'in, tayi tunanin zata tarar da Ayman sai kuma taga ashe babu kowa ma a ciki, Zama tayi kan tum tum iya ta ajiye mata abincin a gabanta. Tana futa Ayman na shigowa kare da waya a kunne yana murmushi kai da gani babu tambaya kasan da Nur yake magana.
Zama yayi kan kujerar da take fuskantar ta yana ci gaba da maganar shi, raihana kallo d'aya tayi mishi ta maida hankalinta kan abincin ta, Ayman kuwa kamar television haka ya zuba mata ido yana kallonta, da yanayin yadda take cin abincinta gwanin burgewa, ya dad'e da fahimtar komai nata tana yin shi ne with passion.
Tak'aita hirar da suke da Nur yayi sukayi sallama ya ajiye wayar, sai a lokacin tace, "Yaya Ayman Ina kwana?".
"Ina kwana ko Ina wuni? Kina can kina bacci har aka d'aura auren aka gama, sai yanzu kin tashi kusan 11,30 kina breakfast a makare zaki wani cemun Ina kwana". Ayman ne me yin wannan maganar yana kallonta ko cikakken k'iftawar ido babu. Murmushi kawai tayi ba tare da ta sake ce dashi komai ba, sake gyara Zama yayi yace, "kin je kin wani ciko fuska da powder to ni dai Zan baki shawara kar ki sake ki futa waje a haka, don zaki sha dariya gurin mutane y'an biki".
Sai a lokacin ta kalle shi, "bafa tsoron ki zanji ba, so kibar ma zare mun ido".
D'auke idonta tayi k'asa k'asa da murya tace, "toh aini dama ba don su nayi ba, shiyasa ko futa waje su ganni bazan yi ba ma". Yadda tayi maganar da iya gaskiyarta sai abun ya bashi dariya, amma dai baiyi ba ya gimtse.
"Toh kenan don wa kikayi? Wannan saurayin naki me idon...... Umm bari dai nayi shiru zaifi". Ya k'arasa fad'a yana rik'e bakin shi. Sai a lokacin raihana ta fahimci so yake yau ya kaita geji kawai, don haka ture abincin tayi daga gabanta tace, "shima ba don shi nayi ba, ni yanzu ina ma zan ganshi".
Tab'e baki Ayman yayi yace, "tom nidai koma don me kikayi bari na yaba miki ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login