Showing 63001 words to 66000 words out of 288773 words
Chapter 22 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
gama jefa zuciyata cikin ha'ula'in da bansan ta yadda zan futa ba! Bansan ta yadda zan cire sonka a raina ba, wayyoh Allah ni Saleema, hak'ik'a nayi nadama matuk'a na jefa rayuwata cikin tashin hankalin da Ina tunanin shi zai zamo ajalina......".
Shi kam khaleefa kasa fassara zancen ta yayi farat d'aya, tun jiya yake auna maganar wai bashi take kokawa ba kanta take kokawa, toh kanta take kokawa kamar yaya? Kuma akan me? Yaga abunda ya shafe shine shi kad'ai ita meye nata a ciki? Shin tana nufin labarin rayuwar shi zai kawo k'arshen alaqar sune..........". Sai yayi saurin girgiza kanshi da k'arfi da kuma k'araji yace, "noooop! Sam ba haka bane? Saleema ba zata rabuwa dani ba har abada, zamu rayu tare dake doleee! Baki da masoyin daya kaini Kuma ba zaki samu ba duk fad'in duniyar nan in aka d'auke iyayen da sukayi silar zuwan ki duniya........". Saleema kam cikin tsoro da razanin ganin yadda ya rikid'e mata lokaci guda yana maseefa kamar ba khaleefa data sani ba, tana tunanin gwara ta had'a ya nata ya nata tabar mishi d'akin tun kafun ya karairayata a banza, don ta fara zargin watak'ila yana da matsalar kwakwalwa bata sani bane, shiyasa ko a soyayyar su lokaci zuwa lokaci yake mata wasu kalar d'abi'u kamar ware kanshi daga cikin mutane na tsawon wasu mintuna.
Shi kuwa mik'ewa tsaye yayi ya soma nuna kanshi yana tunkararta, ita kuma ta fara jan jiki tana ja baya tana kuka mara sauti.
*Note👇*
_love romance wata haramtacciyar soyayyah ce da masoyan turawa suke gudanarwa, sun d'auke ta kamar ruwan sha tunda ba addinin islama a tare dasu, sai dai Kash! Wani abun tashin hankalin mutanen mu y'ay'an hausawa, hausa Fulani da aka haifa cikin addinin musulunci aka tarbiyyantar dasu da hanyoyin sanin Allah da yadda zasu bauta mishi, babu jahilci ko guda a tare dasu, amma wani abun al'ajab sun d'auki wannan d'abi'a sun rataya a wuyan su, a gurin wanda suke d'abbak'a wannan soyayyah akwai mutanen gaskiya da auren zasuyi a lokacin akwai kuma na banza da k'arya ce ta kaisu, in sun kai ki sun baro ko kyallin keyarsu ba zaki k'ara gani ba, wannan soyayyah takan jawo matsaloli da yawa ciki harda gurb'atar tarbiyyar yara matasa masu tasowa da wanda ma basu gama tasowar ba, yaudara ta shiga cikin soyayyah tayi kane kane duk ta sanadiyyar love romance, aure yana lalacewa duk akan love romance, shin masu gudanar da wannan soyayyah suna da tabbacin zasu auri juna ma da farko? A'a ko kuwa su sunsan rayuwarsu tun daga farko har k'arshe? Shin suna tunanin ya rayuwar auren su zai kasance bayan shallake wancan soyayyar ta banza? Dole zargi zai shiga cikin rayuwar auren su, daga ranar da namiji yasan mace a titi bata k'ara daraja ko k'ima a gurin shi, ko bayan auren ma haka zaita ganinta a banza, data d'aga hankalinta zata yi wata fuffuka zai iya yanke mata kowanne irin hukunci ciki hadda rabuwa da ita_.
_Abubuwa da dama dai duk gasu nan suna faruwa kuma wallahi ta silar wannan gurbatacciyar soyayya, Sannan abu na biyu daya kamata mu fahimta, shi bature mutum ne mai alk'awari, zai iya auren mace yayi ta rayuwa da ita tsawon lokaci da iya romance, basu d'auki sex dole ba kuma basu d'ora shi a k'ok'on ransu kamar mutanen Africa ba, shiyasa suke iya raba romance da sex. Wanda mu a k'asar mu ba'a iyawa. Zasu fara kamar gaske da option 1 kafun su farga sai kigan su tsumu tsumu cikin option 2 . Soo mind you Mutanen Africa ba zasu tab'a zama turawa ba. Da haka nake Jan kunnen mu don girman Allah Mata, mu kama kanmu da bawa ire iren wad'annan matasa fuska, da yak'i tuk'uru akan su. Don akwai abinda yake faruwa yanzu sam ba za'a kira shi da sakacin iyaye ba, iyayen mu suna iya yinsu wajen bamu tarbiyyah tun daga ranar da suka haife mu, toh mu kuma ya kamata mu d'ora daga lokacin da muka fara mallakar hankalin kanmu, har ma mu taimaka musu wajen kwabar k'annen mu. Mu sani fa cewa duk abinda San gaba ya taka......._
_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page eighteen 1️⃣8️⃣
"Wayyoh Alla kuzo ku taimake ni yau khaleefa zai kashe ni a gidan nan?". Ta k'arasa fad'a tana yin kuka mara sauti jikinta babu inda baya rawa, shikam bai masan abinda yake yiba saboda zaucewar tunani. Sai da yaga ta kai k'arshen bangon d'akin ya dakata da binta da yake, fuskar shi a had'e idanun shi a rine yayi magana cikin daka tsawa, "ki fad'a mun abinda kike nufi da cewa rayuwarki kike yiwa kuka Saleema?".
Saleema kam cike da tsoro wani tunani ya d'arsu a ranta take a gurin, ko ba komai ya kamata na kawo k'arshen alak'ar nan ko na samu na rabu da khaleefa da matsalolin shi gaba d'aya, ta tabbatar idan har baiji hukuncin data yanke ba to bazai kyale ta taji da kanta ba, idan kuma yaji zai yi zuciya ne ya barta har abada, abinda ita kuma tafi so kenan a halin da take ciki. Sai ta saisaita yanayinta ta aro jarumta da dakiyar zuciya tasa a ranta, sannan ta dube shi ido cikin ido ba ruwan hawaye a cikin nata idanun tace, "mu koma can mu zauna zan warware maka komai". Bai yi musu ba wajen komawa dandagaryar k'asa ya zauna itama ta mara mishi baya. Suna opposite d'in juna duk hankalin khaleefa d'ungurungum na kanta kamar ya shiga cikin zuciyarta yaji abinda zata fad'a.
Ganin tayi shiru tana ta ruwan hawayen da yau ko tasu khaleefa ba yayi kawai yaji matsayin soyayyar shi a gurinta yace, "ke nake sauraro Saleema".
Share hawayenta tayi da bayan hannunta, kafun ta fara mishi magana da disasshen murya, "a gaskiya bazan b'oye maka ba kamar yadda al'adun mu suka banbanta haka tsarin tafiyar da rayuwar muma ya banbanta, mahaifina ya kasance mutum mai tsanani da magana d'aya, shiyasa duk abinda ya fad'a bana ja dashi don wahala zanyi a banza kuma ba zai fasa abinda yayi niyyah ba, a dunk'ule Ina nufin ko zan had'iyi zuciya na mutu a gidan mu ba za'a tab'a bari na auri wanda bashi da cikakken asali ba......." Wani irin dum dum khaleefa yaji a k'irjin shi, sai ya rasa a yadda zai fassara koya fahimci zancenta, tana nufin shi shine bashi da cikakken asali?
Saleema kam saida ta had'iye wani abu mai d'aci a mak'ogwaro kafun ta ci gaba da maganar ta, "shiyasa na yanke alak'a ta dakai tun wuri ba sai lokaci ya k'ure kace na yaudare kaba, sannan na d'aura d'amarar koyar yadda zan cire sonka a zuciyata kwata kwata ko naji dad'in fuskantar karatuna inyi abinda ya kawo ni ........". Khaleefa bai bari takai k'arshen zancen ba ya tare ta da hanzari ta hanyar fad'in, "idan na fahimce ki kina son kice ni bani da cikakken asali kenan? Bayan ni dake na fad'a miki mahaifina rasuwa yayi tun kafun a haife mu? Taya kuma na zama marar tunshe Saleema?".
Duk da halin da take ciki saida tayi murmushin takaici mai ciwo, "kana nufin kace duk iya tsawon shekarun daka d'auka a duniya baka fahimci mahaifiyarka kawai y'an dabaru take muku akan mahaifin ku ba? Toh ni yau zan fad'a maka abinda wani bai tab'a yi maka warwara a kai ba, mahaifinka yana raye shiyasa tak'i yarda ku ga hoton shi, tunda duniya da fad'i kada wata rana ku had'u dashi ko mai kama dashi kubi diddigin shi, abinda take b'oyewa ya futa, shiyasa tace ya mutu a nufinta sai kuci gaba da rayuwa cikin rigar yara masu mutumci ku zam d'aya da y'ay'a na halak".
"Na biyu lallai akwai wani abu data rik'e game dashi shiyasa bata tab'a yarda tace muku komai a kanshi, na uku daga yadda mutanen anguwa suke yi muku gorin baku da uba mahaifiyar ku tazo da cikin ku ta sauka gidan iya ta haife ku? Shin me yasa tun da can bata tab'a neman iya a matsayin mahaifiyar taba saida ta samu cikin ku rana tsaka, su kuma mutanen anguwa da tazo akan idonsu suka fara goranta abinda suka sani game daku tunda Nigeria ai ba kamar k'asar Germany ba........akwai abubuwa da yawa daya kamata ka fahimta wanda cikin sauk'i zai tabbatar muku da asalin ku d'in suwaye ba sai anyi muku hasashe bama, da wannan nake rok'on ka don girman Allah kaje kayi rayuwarka nima ka barni inji da tawa, magana d'aya tak ta k'arshe kuwa itace, kun kasance baku da uba, bi ma'ana mahaifiyar ku bata halastacciyar hanya ta samar daku ba......…..". Wani irin guduma khaleefa yaji tayi mishi rotse tun da ga kanshi har zuwa gab'ob'in yatsun k'afar shi, tun da mutane suke cewa ana iya dukan mutum da magana bai tab'a yarda ba saida ta faru a kanshi yau, lallai ya yarda za'a iya kashe mutum ma da magana. Wacce irin banzar magana ce yau Saleema take mishi haka? Shin tasan wacece auntien su kuwa? Shin tasan yadda take da gudun duniya da tsoron maza ma kuwa? Toh taya mace kamar ta mai nutsuwa da cikakken Kamala zata fad'awa aikata haramci har ta Samar dasu ta hanyar haramun kuma ta dinga alfahari dasu, ai data kashe su tun suna yara ba sai sun girma ba? "Ya ilahi ka kawo mun haske na fahimci komai yadda yake a wannan duniyar?". Khaleefa ya fad'a yana mai rik'e kanshi da hannuwan shi biyu, ita kam Saleema Jan jiki tayi ta koma jikin bangon d'akin ta jingina ta rufe bakinta da hannunta duka biyu ta fashe da wani irin kuka mai tuk'uk'i da cin rai.
Sun d'auki lokaci mai tsayi ita tana kuka shi kuma ya kasa yin kukan ma sai ajiyar zuciya da yake saukewa akai akai, tsabar tashin hankali ya kasa yin kukan ma. Da kyar ma ya iya tattara y'ar sauran jarumtar data rage mishi ya ja k'afafun shi daga d'akin ya futa.
Ko daya komao nashi b'angaren sai ya kasa shiga ya zube nan k'asa rik'e da key a hannun shi, ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu. Gaba d'aya duniyar ta soma juya mishi ya fara ganin hazo hazo.
Wani mak'ocin shi d'an k'asar India mai suna khaleed daya dawo daga waje ko shopping ya danje rik'e dai da kwalin kanti, har ya huce shi saboda ba wani shiga harkar mutane khaleefan yake ba in aka d'auke gaisuwa in ya had'u dasu a hanya, amma ko irin yaga kwana biyu baya ganin mutum shi bai iya zuwa yaga ko lafiya ba, sai suyi ciwon su su gama bai sani ba gasu gashi, don haka yanzun ma daya ganshi baiyi niyyar kulawa yaji me yake faruwa dashi ba tunda shima ai haka yake musu, sai dai abunka da zuciyar musulunci me cike da Imani taf, ko da khaleed ya duba Allah sai ya dawo yana tambayar shi, "are you okay?". Bai iya ce mishi komai ba sai key daya d'anka mishi, ya karb'a ya bud'e mishi d'akin ya ajiye kwalin ya taimaka mishi suka shiga ciki, wayar shi ya jawo gefen bed d'in daya kwanta da kyar ya bud'e lock d'in jiki yace ma khaleed, "please call me Ahmad".
Khaleed ya karb'a yana nema mishi no, "Ahmad with emoji heart is he the one?". Khaleed ya tambaye shi, gyad'a mishi kai yayi, khaleed yayi dialing no, bata jima tana ringing ba yayi picking yana tambayar, "yeah man watts up? Nazo d'azu ma fa baka nan Ina ka tafi kuma kaida baka da lafiya?". Khaleed yace, "he's not the one, Ahmad it's khaleed his neighbor, he ask me to call you, I see like he's not feeling okay Soo please come to him now".
"Okay" kawai Ahmad yace sukayi sallama. Da yake yana cikin gidan ba jimawa sai gashi yazo, khaleed na ganin Ahmad yazo yayi musu sallama dama ya tafi.
Ahmad ne ya dinga jera mishi sannu da tambayar abinda yake damun shi, banda juya kai ba abinda yake yi, ya kasa zama ya kasa kwanciya ya kasa tsayuwa, gaba d'aya duniyar yaji tayi mishi zafi tana jujjuya mishi, shi kanshi Ahmad ganin yanayin da yake ciki hankalin shi tashi yayi, k'arshe kawai sai ya koma gefe ya zuba mishi ido yana kallon yadda yake kaiwa bangon d'akin duka cike da tausayawa. Har hannun shi ya fashe yana jini bai daina dukan bangon ba, hakan yasa Ahmad ya taho ya rik'e hannun yana mishi magana cikin d'aga murya, "so kake ka illata kanka khaleefa? Na tambayeka me yake damun ka kak'i fad'a mun saboda kana ganin ban isa nasan damuwarka ba, nace muje asibiti kak'i yanzun kuma ka fara neman hanyar da zaka illata kanka, well zan tafi in barka in yaso ma ka halaka kanka don banga amfanin zamana a tare dakai ba....... ". Kafun ya k'arasa fad'a khaleefa ya kwantar da kanshi jikin gwiwar shi ya fashe da wani irin kuka mai cin rai, kuka yake irin wanda ya kasa yi tun d'azu yake cin zuciyar shi, duk wannan abun yana yine don ya samu hawaye ya zuba ko yayane yaji sanyi a ranshi. Dafa kanshi Ahmad yayi cikin tausayin shi yace, "kayi hak'uri khaleefa komai yayi tsanani maganin shi Allah".
Sai a lokacin ya d'ago kanshi ya d'ora hannun shi saitin zuciyar shi, "ba zaka gane ba Ahmad, jina nake kamar ba niba da ace zan mutu ma a wannan lokacin sai nafi kowa farin ciki da dai in dinga ganin bak'in ciki da tashin hankali irin wanda nake gani a yanzun.......". "Subhanallah da hankalin ka kake fad'in haka da bakin ka khaleefa? Don Allah ka nutsu kasha ruwa mai sanyi zaka ji sanyi a ranka". Ya fad'a tare da tashi ya d'auko mishi ruwa mai maseefar sanyi da kofi, ya tsiyaya ruwan a cup ya kai mishi bakin shi, aikuwa daya fara Sha sai daya ga ya shanye tass sannan ya d'auke kai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali kuma ya ji sanyi na kwaranya ruhin shi har ya samu ya dawo hayyacin shi, "kaci wani abu kuwa?". Ahmad ya tambaye shi, girgiza kai yayi kurum, tashi Ahmad yayi ya had'a mishi ruwan tea ya soya mishi chips sama sama ya juye a plate ya kawo mishi, da kyar ya iya shanye tea d'in yaci chips d'in shima kamar zaiyi amai, da first aid box d'inshi Ahmad yayi amfani ya mishi treating d'in raunin shi na hannu, ya bashi maganin ciwon kai don yasan bazai rasa ciwon kan ba, ya taimaka mishi ya kwanta saman bed, bai nemi jin komai daga gare shiba don yasan har a yanzu bazai tab'a fad'a ba, amma akwai sauran lokaci indai matsalar soyayyah ce tasa mai k'arfi ma ya sunkuya, da sannu zai magantu da bakin shi.
Ba jimawa bacci yayi gaba dashi, Ahmad bai tafi ba saida ya gyare mishi d'akin fess ya sake dafa mishi d'an abinda zaici in ya tashi, ya futo mishi da kayan da zai sauya sannan yaje ya dawo.
Ko daya futa saida ya saci kallon apartment d'in Saleema, ita kanta ya fahimci kwana biyu bata da cikakkiyar lafiya haka bata da nutsuwa Sam, ya tabbatar akwai abinda ya had'a su yake wujijjiga zuciyoyin su. Sai kawai yayi murmushin gefen baki ya ci gaba da tafiya yana tunanin yadda soyayyah tasa khaleefa zubar da hawayen shi masu tsada daba kowa ke iya ganin suba, zai iya rantsewa da Allah tunda suke a k'asar Germany bai tab'a ganin hawayen khaleefa haka ba sai yau, sannan duk sammakon ka ba zaka tab'a samun khaleefa bai yi abu biyun nan ba, sallah da wanka, shiyasa ya saka ayar tambaya a kanshi tun daga ranar da yaga ya makara sallar asubah da shirin futa makaranta, ga gyaran gida tsabta ko mace albarka, kayanshi haka zaka gansu a killace a adane bayan wankewa a washing machine har ioning d'insu anyi sai zabga k'amshin turaren shi suke. Lallai soyayyah daban take, abinda Ahmad yake tunani a ranshi kenan har ya isa inda ya nufa a lokacin.
Toh khaleefa mai bacci da k'a'ida kuwa sai gashi yau yana bacci sama da hour biyu ba ko juyi babu balle alarm da zai tashe shi a lokacin.
Azahar da la'asar duk saida suka je daf da magriba da Ahmad yazo ya tashe shi ya d'aura alwala ya gabatar a gurguje, yana idar da sallah Ahmad ya had'a mishi ruwan wanka irin wanda yake so, saboda yanayin sanyi da aka shiga cikin k'asar yasa kafun ya futo ya kunna room heater. Kaya ya zura masu sauk'in nauyi ya shafa mai da kyar a jikin shi ya koma ya kwanta kanshi na kallon rufin d'akin, hannun shi d'aya saman goshin shi ya dafe kanshi dashi. "sannu ya kake jin jikin naka?". Ahmad ya tambaye shi, "ba ciwo" ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba. Shima Ahmad bai sake ce dashi komai ba yaci gaba da research cikin system d'inshi, babbar damuwar shi a ciwon nan na khaleefa shine suna gab da sanin makamar su? Nan da kwanaki k'alilan zasu yi interview dasu bakwai d'in da aka zab'a suyi aiki tare da general hospital orthopedic Berlin. Yanzu kuma gashi shi ya kwanta ciwo don ma Allah yasa sun gama exam d'insu tun last week da baisan ya khaleefa zai yi ba. Gashi nan Sam ba irin Nigeria ba da za'a iya ma mutum magud'i ko attendance in bai halarci lectures ba.
Toh har kasun