Showing 33001 words to 36000 words out of 288773 words
Chapter 12 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
ta ce, "woww what a nice guy dear".
Murmushi kawai raihana tayi ta d'an kai mata naushi a kaikaice, ta dafe gefen cikinta tana fad'in, "ouch a gaban saurayin naki ma sai kin yiwa mutane mugunta in ban koma ba wallahi".
Da sauri raihana ta k'ara damke hannunta tace, "I'm sorry toh".
Sun k'arasa har inda Imran yake suka gaisa dashi cikin mutumci, shidai rabin hankalin shi duk na kan raihana, saboda a yau yake sake ganin wasu sirrikan kyau da take tattare dasu, wanda a baya duk baisan dasu ba.
Bayan sun gama gaisawa zasu tafi kud'i masu yawa ya basu amma suka k'i karb'a, sai da yayi da gaske sannan raheela ta amsa ya basu wata babbar leda ta shopping yace su tafi mata dashi, raheela ce ta sake karb'a suka yi mishi sallama bayan sun gama zuba godiya.
"Yae! Baby zamu k'arasa ne?".
Kallon shi raihana tayi galala sannan ta kalli inda yake nuna mata, "kana nufin mu shiga cikin motarka muyi hirar a ciki?".
"Eh to meye" ya fad'a yana wara idon shi a kanta. Sai tayi k'asa da kanta tace, "babu komai amma me zai hana mu zauna k'asan bishiyar can".
Ba musu ya amince tayi gaba yana bin bayanta yayinda yake sake k'arewa duk wani takunta kallo, kai yarinyar nan ta mishi to the extent, komai nata da sanyi abun kallo da burgewa, dole maman shi ta kyale shi akan maganar auren nan saboda shifa harga Allah yayi mata dai dai da ra'ayin shi irin wadda ya dad'e yana mafarkin samu".
Ita ta fara zama kan iccen sannan shima ya zauna gab da ita, sunso suyi kusanci da yawa, ta kuma yi niyyar yi mishi magana sai dai yayi mata kwarjini, sai ta kauda kanta gefe ta russuna tace, "Ina wuni ranka shi dad'e".
"Ranka shi dad'e kamar wani sarki, Wai raihana har yanzu bakiji ya kamata na samu wani matsayi koda gutsire ne a cikin zuciyar ki ba?".
Murmushi tayi tana wasa da tsinken hannunta tace, "akwai wani matsayi dama bayan na amincewa da aurenka?".
"Raihana" ya kira sunanta babu wasa, ta amsa a sanyaye ba tare data kalle shiba, "raihana d'ago idonki ki kalleni" ba musu ta d'ago ta zuba kwayar idanunta cikin nashi, sai dai bata iya yarda ta kalli kwayar idonshi da yawa ba ta maida idonta k'asa tana wasa da yatsun hannunta,
Dai dai lokacin motar Ayman ta Parker daga nesa da inda suke, zuba musu ido yayi gaban shi yana fad'uwa raihana ce tare da wani guy suke hira, "waye shi" ya fad'a a zahiri, sai kuma wani tunani ya fad'o mishi, "toh ko shine wanda jiya suna hira da iya take bashi labarin ya kawo kud'in auren raihana?".
"shin baki ga wani abu bayan matsayin matar da Zan aura cikin kwayar idanuna ba?".
Shiru tayi mishi still tak'i cewa komai, "raihana say something mana please shin ba kiga soyayyar ki fal kwayar idanu na ba?".
A hankali taji tunaninta yana tafiya wani waje, hancinta suka fara shako wani extra ordinary perfumes, ta lumshe idanunta a hankali ta bud'e kan k'afafun shi da suke zube cikin bak'in takalmin fata, tun daga k'afar ta soma kallonshi har zuwa kan kyakkyawar fuskarshi da bata rabo da murmushi mai k'ayatarwa amma fa a yau babu, kallonta yake da wani irin yanayi kamar ba shine Ayman ma'abocin faram faram da wasa ba.
_Comment and share_
24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page ten 🔟
"Laah Yaya Ayman! Kaine?". Raihana ta fad'a da mamaki, shi kuwa Ayman murmushi ya wanzar take a saman fuskarshi ya mik'awa Imran hannu tare dayi mishi sallama. Shima mik'a mishi hannun yayi sukayi musabiha irinta addinin islama. Ayman bai ko sake tsayuwa a gaban suba kota dede de second ya koma cikin motarshi ya zauna.
Imran ne yake tambayar raihana, "waye kuma wannan?".
Cikin basarwa don harga Allah ta tsorata da yanayin data gani da farko a tare da Ayman d'in tace, yayanta ne. Imran da bin diddigi sai ya sake tambayar ta, "the same father or the same mother?".
"Noop ba d'aya". Ganin tayi kici kicin alamun bata son maganar taci gaba saiya kyaleta. Sunci gaba da hirar su fiye da hour d'aya, ita dai raihana duk ta k'agu ya tafi taje taga Ayman, bata san dalili ba amma duk sai take jinta ba nutsuwa, kamar tayi wani abu ba dai dai ba, shi kuma Imran yak'i tafiya yana nazartar inda hankalinta yafi karkata, yana zargin akwai wata a k'asa tsakanin su ta wani raina mishi hankali da yayanta ne.
Ko daya tashi tafiya yaga tana shirin yin sallama dashi a nan gurin b'ata fuska yayi yace, "dear ba zaki rakani gurin mota ba?".
Duk'ar da kanta k'asa tayi tace, "okay to muje".
Tare suka jera Imran na zolayarta kasancewar shi gwanin barkwanci, sai data kaishi har gaban motar shi, ta jingina kanta jikin motar sannan tace, "sai ince ka gaida gida Allah ya tsare ka ya kare ka ya maida kai gida lpy, a gaishe da hajiya...."
"Ban gane me kike nufi ba y'an mata, kina nufin a nan zaki barni?".
Cikin rashin gane maganar shi raihana ta tsaya tana kallonshi galala, kashe mata ido d'aya yayi ya d'an matsa gabanta kad'an, "ta Ina ma na shigo nan gurin ne? In baki futar dani ba Zan b'ace fa, In kuma na b'ace keda hajiyata don sai taci tararki, zatace tun kafun ta bani ke d'ungurun gum har kin fara mata wasa dani"
Yanayin yadda yayi maganar dole yasa raihana ta murmusa. Shi kuwa a hankali ya bud'e mata front seat yace, "Bismillah". Yanzun ma dai da idon rashin fahimta ta kalle shi sai yayi saurin rik'e kunnuwanshi, "alfarma ce dai na nema iya bakin titi zaki futar dani sai ki dawo".
Kamar ta kyale shi saboda taga samun gurin nashi yayi yawa sai kuma zuciyarta ta tuna mata wani abu data manta, "shifa bak'on kine, kuma bak'on ka annabinka ne, kiyi mishi alfarmar nan koda iya ta yanzu ne ko don albarkacin son da yake nuna miki".
Ko kafun ta shiga motar saida ta saci kallon motar da Ayman ke ciki dake rufe ruf.
Murmushin cin nasara Imran yayi ya kewaya mazaunin driver.
Abun mamaki shida yace iya bakin titi sai gashi ya d'auki hanyar shiga cikin gari, ya sake bata wani hak'urin wai yana son ganin garin bichi da kyau.
Duk yadda Raihana taso tayi ja inja dashi game da hakan kasawa tayi, daga k'arshe sai kawai ta zubawa sarautar Allah ido, haka yayita shawagi da ita layi layi yana bata labarin daban daban game dashi da y'an uwanshi, wanda raihana sam bata ganewa. Sun d'auki lokaci me tsayi kafun ya d'auki hanyar maida ita inda ya d'auko ta, raihana kawai mazewa take Amma tuni ta cika tayi fam, a ranta abu d'aya kawai take jaddadawa, "kaida sake d'auka na a motar ka har abada". A bakin titi ya sauke ta shi kuma ya huce. Sam bata d'auka zata tarar da Ayman ba saboda lokacin data d'auka yaci ace ya gaji da jira yayi gaba abun shi, jiki a sanyaye ta k'arasa inda motar shi take, ta d'ora hannu da nufin bud'ewa ta shiga kawai ya mata key yayi reverse ya bar gurin. Duk inda hankalin raihana yake in yayi dubu yau ya b'aci, how on earth mutum zai taho tun daga guri mai nisa dominta su samu matsala irin wannan, dama ta fahimci kwana biyu kamar yayi fushi da ita ne shiyasa ba Kiran waya ba zuwa.
Ko data koma hostel guri d'aya ta samu ta nutsu tana ta tunane tunanen ta duk maganar dasu raheela suke da kod'a Imran sam hankalinta baya kai, bama ta fahimta k'ark'ari dai in akayi abu tayi murmushi.
Daga k'arshe ma sai kawai ta juya musu baya tayi kwanciyarta.
*********
Shikam Ayman ta b'angaren shi Sam bai fahimci a halinda yake ciki ba tun daga lokacin daya samu raihana tana hira da wani bashi ba a inda suka saba zama duk lokacin daya zo mata weekend, da farko yayi niyyar juyawa sai dai ya kasa tafiyar kuma, burin shi bai huce ya ga tafiyar guy ba saiya tafi, yana nan still sai yaga sun taho raihana ta shiga motarshi, koda wasa bai tab'a d'auka bayan shi raihana zata iya sakewa da wani namiji har ta shiga motarshi su futa ba, ko fad'a mishi akayi bazai yarda ba, amma sai gashi yau a gaban idon shi tabi wani saurayi bayan gashi yana jiranta ta sani kuma tana kallo.
Still kuma suka jima basu dawo ba, yana tunanin ma ta manta dashi, bai ji ranshi ya sake b'aci ba saida ta nufo inda yake tabbacin tana sane da wanzuwar shi a gurin yana jiranta, a wannan lokacin ne ya kasa hak'uri, toh in tazo me zata ce mishi ma, yasan raihana bata kasance ma'abociyar k'arya ba, ba zaiso kuma a kanshi garin kare kanta ta fara ba. Shiyasa tana zuwa yaja motar shi yayi gaba.
Wannan abu daya faru tsakanin raihana da Ayman shine ya zamo abu na farko daya fara tsoratata har tunanin ta yaje inda bai tab'a zuwa ba a kanshi. Shima kuma shine karo na farko da wani abu ya tab'a zuciyar shi, yana ganin tunda take yin samari bata tab'a irin wannan daya gansu tare ba, duk dashi mutum biyu ya tab'a gani a cikin biyar d'in da suka fasa aurenta, amma duk da haka yana ganin babu mai rawar Kai daya tsorata Ayman kamar Imran, ko don duk wad'an can masu aure ne sun huce shekarun yin abu na samar taka irin nashi sai wannan.
Da rana a kwance Auntie ta same shi kan carpet kamar wani mara galihu, ba bacci yake ba amma yana jin shigowarta ya maza ya rufe ido kamar me yin baccin, tasan Sarai ba baccin yake ba amma tunda ya nuna hakan yana nufin baya son takura ko magana da kowa a lokacin. Don haka saita juya a nutse ta fuce daga d'akin.
Daga baccin gujewa tambayoyin auntie sai gashi na gaske ya riske shi nan k'asa.
Da yamma bayan ya farka, wanka ya sake yi ya shirya cikin wasu kayan riga da wando na yadi d'inkin irin na matasa da suke yayi a lokacin, kayan sun amshe shi sosai yayi kyau kwarai, saida ya fara gabatar da sallar la'asar data kwace mishi sannan ya kira wayar Nur ya fad'a mata yana hanya ta had'a mishi abinci mai sauk'i da tasan in yazo zaici, lokacin daya kira Nur bacci take yi cikin magagi sukayi magana, amma tana jin abinda ya buk'ata take ta watstsake kuma ta tabbatar mishi da zatayi kamar yadda yaso, murmushi yayi bayan ya ajiye wayar.
Hannun shi rik'e da car key ya nufi parlon auntie. Bayan yayi knocking ta bashi izinin shiga tura k'ofar yayi ya shiga bakin shi d'auke da sallama, tana zaune tana aiki da system ya k'arasa gareta gently ya zauna kusa da ita yace, "Auntie barka da yammaci".
Kallo d'aya tayi mishi ta maida kanta ga abinda takeyi tace, "barkan ka dai, d'azu naje na tarar kana bacci, Ina fatan kaci abincin ka?".
D'an b'ata face yayi yace, "eh na d'an kwanta na huta ne, yanzu gidan su Nur zani nasan Zan samu abinda zanci a can".
"Anya kuwa har yanzu kana sakewa kaci wani abu a gidan mami?".
Murmushi yayi tare da mik'ewa tsaye yace, "noop but insha Allah yau zanci".
"Toh Allah yasa".
Daga haka sukayi sallama ya d'auki hanyar futa daga parlon.
Gidane babbah mai k'aton compound da parking lot a gefe, zaune suke kan brown kujerun katako gaban su well round table cike da flate flate da glass cups masu kyau da tsada.
Kyakkyawar yarinya ce fara, mai matsakaicin tsawo da k'iba, tayi kwalliyar ta sosai cikin riga da zani na lace maroon, ta yafa gyalenta match da kayanta a gefen kafad'ar ta, kallo d'aya zata fassara maka ita d'in asalin jinin sameera ce saboda kamannin da suke yi, gefenta Ayman ne zaune ya d'ora k'afar shi d'aya saman d'aya yana dariyar hira mai dad'i da Nur take yi mishi a lokacin.
"Allah sweetheart ya kamata kaci abincin nan kafun a jima kace mun kai tafiya zakayi sai wani lokacin". Nur ce meyin wannan magana cikin siririyar muryarta.
Ayman yana dariya still yace, "ai kece babie kika d'auko hanyar cika mun ciki da dad'ad'an labarun ki, shiyasa koda yaushe bani da burin daya huce nazo na ganki, ke ni kaina har mantawa nake da kaina a duk lokacin da muka kasance tare da ke balle wata yunwar cikina, Ina sonki da yawa matuk'a Nuriyyata".
Murmushi nuriyya tayi ta fara zuba mishi abincin data girka da hannunta domin shi a plate tana fad'in, "yau dai duk wayonka sai kaci abincin nan in ba so kake kuma mu b'ata ba....".
"Nina isa ai yau ba zan tab'a k'in cin abincin dana tashe ki a bacci nasa kika yiba". Sai ta tsaya da abinda take ta kalleshi, idanun shi ya lumshe mata yace, "duk da baki fad'a ba amma na sani, ai naji yanayin muryarki". Murmushi kawai tayi ta girgiza kai
Tura mishi plate d'in tayi gaban shi bayan ta gama had'a mishi komai tace, "Humm nifa ba bacci nake ba, in ma baccin nake aikin ka ai yafi shi muhimmanci".
Ayman yana kallonta yace, "Allah ko sweetheart?".
"Sosaima" ta fad'a da murya k'asa k'asa.
Sunci gaba da hira cikin happie ta b'angare guda Ayman yana cin daddad'an abincin data dafa mishi. Sai da yaci da yawa sannan yasha Ginger and lemon masu sugar baya baya, shima yayi dad'i cox Nur ta samu horo indai ta b'angaren aikin girki ne, sam sameera bata saba musu da sangartacciyar rayuwa ba, aiki suke kamar kowanne yara dan ita gidanta ma ba me aiki, suna tasawa ta sallame ta.
Ayman bai bar gidan su Nur ba ranar sai daf da magrib shima don ya yakice ne da sai yayi sallah a anguwar Nur zata barshi ya tafi.
Tuni ya manta da tension d'in wani raihana ko ya tunata baya jin irin wancen b'acin ran da tashin hankalin, tafiya yake slowly kamar ba shine ya futo daga gida a hargitse ba, shiyasa yake son ganin Nur kowanne lokaci saboda tana d'ebe mishi kewa, ba don kunya da take tsakanin shi da mamin suba da kullum sai yazo gidan.
_Wannan kenan_
Toh raihana kuwa duk cikin satittikan da suka biyo baya sukuku tayi su, ga Imran da takurar Kiran wayar shi, ga Ayman da ya juya mata baya, ko wayarta baya d'agawa, gashi ita kuma alk'awari ne saita kira shi da tunanin ko ya huce fushin nashi amma har tsyi ring ta gama baya d'agawa.
Ranar da sati ya cika cif da zuwan Imran, raihana tana shanya gama wankin innerwears d'inta kenan, taji wayarta tayi k'ara, kamar karta duba don tasan Imran ne shine baya gajiya da da kira da text, sai kuma tayi tunanin ko daga abban tane, don lokacin tana tsammanin shigar kud'in abincinta daya d'auko hanyar k'arewa. Tana dubawa kuwa taga kud'in ne aka saka amma ba daga abban taba daga Ayman.
Zama tayi gefen bed ko tsayawa saurarar surutun su raheela batayi ba ta dannawa no shi kira, dama a satin kwana biyu ne kad'ai bata tab'a shiba itama tayi zuciya, katsewa yayi ya mata text kamar haka, "Ina inda muka saba had'uwa".
Raihana ai da sauri ta mik'e tana duba shigar jikinta, a lokacin wata bubu ce a jikinta ta roba robar yadi ta kamata kad'an, ganin Ayman ne sai kawai ta zunbula hijab dogo ta fuce, "yana zaune kan iccen bishiya ya duk'ar da kanshi k'asa.
Raihana ta Isa da sallama, sai ya ajiye abinda yake ya sake gyara zaman shi donta samu gurin zama.
Raihana ta zauna tana gaishe shi, "Yaya Ayman Ina wuni".
"Lafiya Lou ya karatu". Raihana tace, "alhamdulillah, sai naga sak'o yanzun, nagode Allah ya k'ara rufa asiri"
"Ba komai gani dai banyi zuciya ba na sake dawowa. Kallon shi tayi narai narai da idanunta kamar zatayi kuka tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman don Allah... Ranar ne gaba d'aya kawai dai kayi hak'urin ma zance, tabbas na b'ata maka kuma nasan ban kyauta.....ba".
Murmushi kawai yayi ya sake maida cikakken duban shi gareta, "u are changing raihana, sauyawa kike a kullum safiyar Allah, sai dai bansan dalili ba, kinga da farko haka rannan munyi magana dake zan dawo dake makaranta sassafe, kikayi tahowar ki baki jira niba, na biyu ashe an kawo kud'in auren ki, shima nida ke baki fad'a mun ba, na uku ban tab'a zaton zaki iya amincewa da wani namiji har ki sake mishi irin yadda naga kin yiwa saurayin ki a waccen ranar ba, raihana ya kamata kiyi taka tsantsan da rayuwa da samarin yanzu ma kansu gaba d'aya".