Showing 252001 words to 255000 words out of 288773 words

Chapter 85 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1067

kuma yana kallon duk wani motsinta ta k'asan ido, koda ta gama yaga tana shirin had'a tray hana ta yayi, sai tayi saving d'inshi a nan ya fara ci da basmala. Yaci da yawa kuwa kasancewar jikin shi akwai yunwa don tea ne kawai a cikin shi sai ruwan da yasha da safiyar yau.
Suna zaune opposite to each other sai dai sam ba abincin take ciba juya cokali kawai take, da gaske ta takura da zaman shi ga kwayar idon shi data mata nauyi aka, ko son d'agowa ba tayi bare su had'a ido.
Shima yana lura da ita that's why yana gamawa ya tashi, in less than 20 mint ya gama shirin futa office ya lek'a ya ajiye mata kud'i masu yawa da yakan bata lokaci bayan lokaci ko zatayi wani abu dasu. Tabi kud'in da kallo har ya futa ta kasa furta komai.

****Kamar yadda raihana ta fad'a mishi a rubuce haka ya yaudari Ayman suka shirya zasu had'u a garin Abuja cikin k'arshen satin, ya kuwa amince, ko neman hutu baiyi a gurin aikin shiba, ya tsara dai zai zo Friday Sunday da yamma ya koma.
Duk abinda akeyi bai fad'a ma auntie ba don baisan ta inda zai fara tunkararta da zancen ba, gashi twin yace kada ya kuskura tasan dashi zai had'u. Ana saura kwana biyu su tafi ya samu auntien a kitchen, da yake kwana biyu mama haleema bata da lafiya bata samun zuwa, shiyasa tana tashi office kai tsaye gida take zartowa ba wani uzuri da take yadda ya tsaida ita, albasar data yanka taga yasa hannu ya fara wankewa, sai ta tsaya kawai tana kallon shi don tasan lallai akwai magana a bakin shi. Ganin kamar bai fahimci kallon tuhumar da take mishi ba sai ta karb'e bowl d'in da albasar ke ciki, "nagode da tayin aiki, amma daka fad'a mun abinda ya kawo ka basai ka sawa hannun ka warin albasa mai wahalar futa ba....".
D'an b'ata fuska yayi ganin ta harbo jikin shi da wuri, da kuma garin neman gira yana neman rasa ido, sai ya had'e fuska yace, "nifa gani nayi aiki ya miki yawaa nazo na taimaka".
"Ni dai na yafe taimakon, d'auki morning fresh ka wanke hannun ka same ni a parlour na in na gama sai muyi magana".
Kujera yaja ya zauna yace, "ai maganar ba mai tsayi bace, dama tafiya ce ta kamani nassarawa, sai dai bazan huce kwana biyu ba".
"Toh Allah ya tsare hanya amma me zaka je yi nassarawa? Ko a can y'ar tawa take?".
"Ahm... ah... a'a...bikin wani abokin aikin mune".
"Allah ya sanya alkhairy bani invitation card d'in".
D'an dam yayi, daman yasan za'ayi haka, Cox duk d'aurin auren da sai anje wani gari tana karb'ar invitation card saboda address, "ai.... Aita....aita online ne aka turo catin, ni ban ma samu nawa ta no ta ba".
Ajiye cokalin hannunta tayi tana kallon shi da wannan uwar k'arya daya yanko mata, da yake ba sabawa yayi ba duk ya wani diririce tsabar yadda k'afar shi ta sage sai jingina yayi jikin drower.
Ita kuwa Murmushi tayi kafun tace, "Ina fatan kana sane da kai ba k'aramin yaro bane? Am sure da kayi aure akan k'a'ida da yanzun kana da yara biyu ko? Toh Alhamdulillah kasan abu mai kyau da akasin shi, kasan yadda zaka kula da kanka a duk inda ka tsinci kanta ko? Good and fine Allah ya tsare hanya....". Tana gama fad'in haka ta juya taci gaba da aikinta, Ayman kuwa jikin shine ya sake yin sanyi lakwas! Har ya fara tunanin fad'a mata gaskiya sai kuma k'ak'k'arfar gargad'in da khaleefa ya mishi ya dawo cikin kwanyar shi a take, sai kawai ya fuce a kitchen d'in, Auntie ta bishi da kallo tana girgiza kai.

****Da yammacin ranar tafe take sauri sauri don sunyi da doctor andal zasu had'u a gidanta, bata son kuma likitar tazo tayi ta jiranta. Kamar a tare suka taho sai gasu sun sauka kusan a tare. Ta bud'e gidan Suka shiga suka gaisa ta gabatar mata ruwa da tea tasha, sannan ta fad'a mata yadda komai zai kasance, ta d'aukar musu hutu ita da khaleefa na sati biyu yanzu visa kawai ya rage musu. Cikin jin dad'i raihana ta dinga murna, she's just imagining yadda khaleefa zaiyi a duk lokacin da akace gashi ga mahaifin shi, sai taji kamar ta jawo lokacin kusa ace su k'ifta ido su gansu a gaban Suraj Abdallah tofa.
Andal ta jima a gidan har sai dab da khaleefa zai dawo ta tafi.

****Da dare tana zaune kan darduma tana muraji'ar karatun al-qurani mai girma, da kwantaccen sauti irin wanda sai kana kusa da ita zaka ji.
Daga inda take ta dinga jiyo hirarrakin mutane a cikin gidan, tasan bazai huce Yasmine da mijinta ba shiyasa ta rufe qur-anin ta zura hijab dogo ta futo parlon. Sab'anin tunanin ta Muhammad ne da matarshi yau a gidan nasu.
Ta k'arasa da fara'a kan fuskarta suka gaisa dasu, kafun ta kawo musu abinci da ruwa. Basu ci abincin ba da yake ma a gurguje suke saboda dare suka musu sallama suka tafi, khaleefa ya raka su har waje ita kuma taci gaba da zama cikin parlon da takardun da andal ta bata ta ajiye mishi d'azu har ya dawo ya tadda ita. Ya zauna tare da kwantar da kanshi baya. Saita d'ora mishi takardun kan cinyarshi, ya bud'e idon shi da suka fara lumshewa saboda gajiya da bacci yana mata kallon neman k'arin bayani. Maimakon tayi kamar yadda yake so sai tayi k'asa da idon, shima kan papers d'in ya maida nashi idon yana bin komai daki daki har ya gama karantawa, ya sauke doguwar ajiyar zuciya, duk wani abu da yake tsarawa akan yadda zai had'u da mahaifin shi sai tunkaro shi yake gradually, lallai koma waye ya d'aukar mishi hutun nan yana kusa dashi.... Amma zaiga ko waye ranar da zasu tafi.
"D'auko mun passport d'inki". Ya baiwa raihana umarni.
Ta tashi ta shiga d'akinta mintuna k'alilan ta dawo dashi a hannu ta mik'a mishi. Bai karb'a ba saima bin yatsun hannunta da yayi da kallo, yana matuk'ar k'aunar kallon yatsun saboda yadda lallen jiki ya haska fatar ta, ya kuma dace da jikinta, ci gaba da kallonta yayi har zuwa kan fuskarta data nuna gajiyawa da tsaiwar da take, ya lumshe ido ya sake bud'ewa akan cute lips d'inta da suke ta glowing kamar tasa lip balm, wani irin yanayi ne ya fara taso mishi ata jinin jikin shi yana bin kowacce jijiya yana isar da sak'on da yake ta son gujewa cikin ranakun.
Raihana kam gajiya tayi da tsaiwa ta ajiye mishi a gefen shi ta juya zata bar gurin, sai dai cak ta tsaya jin ya sak'alo yatsunta, ko kafun ta gane takamaiman abinda yake shirin yi tuni ya jawo ta baya jikin shi, sai ganinta tayi daram a saman cinyarshi, ya rungume ta tsam a cikin jikin shi yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ita kuwa gabanta ne yayi wani irin luguden bugu, saita fara k'ok'arin sauka sai dai ya hana mata damar hakan ta hanyar nuna mata k'arfinta cikin cokali ne in aka had'a da nashi, ganin da gaske ita ba kowa bace saita fara marairaice mishi tana rok'on shi, "please ka bari manaa...". Taja kalmar k'arshe saboda yadda taji yana murza yatsun hannunta....
"Ka bari don Allah, bana....".
Sake yin shiru tayi jin hannun shi na yin gaba zuwa tsintsiyar hannayenta..... Ya kai bakin shi saitin kunnenta in a cool voice yace, "more complain...more.... Kissess". Ya k'are fad'a tare da sumbatar bayan hannunta.
Shiru tayi a jikin shi ta kasa kwakkwaran motsi, tana ganin kamar khaleefa baisan abinda yake shirin aikatawa gare taba, shi kuwa hannunta ya kamo ya d'ora saitin zuciyarshi, "kiji bugun zuciyata raihana....". Lumshe kwayar idonta tayi tana jin yadda zuciyarshi take bugu da k'arfi da sauri. Sun jima a haka kowa da abinda yake ayyanawa cikin zuciyarshi har zuwa lokacin da tunanin shi ya fara dawowa dai dai, kwakwalwar shi ta fara tuna mishi matsayinta gare shi, da kuskuren da zai haifar ta silar kusancin da yake son wanzarwa tsakanin su...., sai ya janye hannun shi daga jikinta ya bata dukkan dama.
Ta mik'e jiki a sanyaye ta shige d'akinta da sassarfa.

***** Sauran ranakun da suka biyo baya duk na shirye shiryen tafiyarsu Nigeria ne, da kusan komai yazo musu a dai dai itama raihana sun samu hutun kammala exams.....
Khaleefa bai samu nutsuwar fad'awa Ahmad halin da ake ciki ba sai saura kwana biyu jirgin su ya d'aga. Shima labari Ahmad d'in yaji a gurin Muhammad khaleefan ya d'auki hutu, shine ya kira shi a waya yake tambayar shi da son jin lafiya dai, bai fayyace mishi komai ba a lokacin yace sai in ya taso office ya same shi saboda maganar bata waya bace dama kuma yana son ganin shi shima.
Koda ya tashi office bai shiga gidan shiba ya samu khaleefan a gaban harabar gidan suka fara magana, bai b'oye mishi komai dangane da yadda yasan mahaifin shi yana raye har zuwa kan yadda komai yake tafiyar mishi a duk'unkune ta hannun raihana.
Doguwar ajiyar zuciya Ahmad ya sauke, ya taya shi murna sosai, duk da yaso ace khaleefan ya fad'a mishi komai akan lokaci, da dashi za'ayi tafiyar, amma ba komai tunda watarana zai had'u da Abban. Sai dai fa ya matuk'ar taya khaleefa murna, ranar basu rabu ba har sai bayan k'arfe tara na dare. Khaleefa ya rako shi suna sake yin sallama don ba lallai su sake had'uwa ba tunda jirgin su k'arfe uku na washe garin ranar zai tashi, sai a lokacin Ahmad ya samu damar kawo mishi maganar saleema, ta hanyar laluma da nuna mishi kuskuren watsi da lamarinta da yayi a kaikaice ta yadda zai fahimta bada zafi ba don yasan halin mutumin nashi. Shiru khaleefa yayi bayan gama sauraron maganar Ahmad da tayi kama data raihana sak. Har suka k'arasa sallama suka rabu khaleefa na tuna sunan saleema da yadda komai ya rikice tsakanin su har ya iya mantawa da ita da lamarinta gaba d'aya cikin rayuwarshi, a baya in akace zai iya rabuwa da ita ba zai tab'a yarda ba, sai gashi ta silar abu d'aya ya yakice ta da soyayyar ta cikin rayuwarshi, yakicewa irinta har abada. Saiya sauke kanshi k'asa sunan Raihana na fad'owa cikin tunanin shi, har zuci zuci yake ya had'u da Ayman su warware matsalar nauyinta yabar kanshi ko ya samu nutsuwa in tayi nesa dashi........
Ranar kusan kwakwalwar shi sake cinkushewa tayi, ta wani sashen kuma zuciyarshi na nutsawa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, har yanzu jin abun yake kamar tatsuniya, wai suma mahaifin su yana raye? Suna da uba kamar kowanne d'a har zai had'u dashi ma gobe? Kai wannan abu yana yi mishi dad'i sosai in ya tuna......

****Tun cikin dare kowa a cikin su ya gama had'a kayan shi jaka guda, duk daba dad'ewa zasuyi ba tana fatan khaleefa ya mata alfarma ta k'arasa gida taga iyayenta da take matuk'ar kewar su. So take ta musu bazata shiyasa duk wannan abun bata cewa ummie komai ba sai ranar da suka had'u a nutse ta labarta musu komai.
A cikin raihana da khaleefa bansan wanda yafi wani zumud'i da son ganin ya jawo gobe ba, don ranar haka suka kwana zuciya fal da farin cikin tafiyar su bacci ma rabi da rabi duk mafarkai ne......

Ko zuwa lokacin da agogon k'asar jamus ya buga k'arfe tara da mintuna na safe, tuni ta gama had'a karin kumallo ta futar da duk wani abun da tasan zai lalace koya bada matsala bayan tafiyarsu, tayi kwalliyarta cikin riga da skirt na lace milk da adon maroon, ta futo da jaka da takalmi da mayafinta matching colour ta d'ora saman jakar kayanta, so take ta shiga yiwa yasmine sallama don ta fara mata complain ta waya, wai wace irin tafiya ce zasuyi haka ba sallama da mak'ota.
Madaidaicin yalolon gyalen ta yafa ta futo rik'e da wayarta tana bin parlon da kallo, tabi food warmers data ajiye saman dinning taga komai yana nan yadda ta barshi tabbacin har yanzu bai futo a d'akin shi ba.
Tayi shiru tana nazarin mai yiwuwa har a k'arshe tayi tunanin mishi knocking sai kuma ta fasa, k'aramin sak'o ta tura mishi na neman izinin shi akan futar da zatayi, sai dai mintuna k'alilan da tura sak'on reply ya shigo na k'in amincewa, saita zauna kawai cikin parlon ranta a d'an dame.
Tana nan zaune ya futo cikin shigar marrocon jallabiyyah fara sol, gashin kanshi daya d'an taru a kwance bak'i sid'ik sai d'aukar ido yake, jikin shi na fudda k'amshin dawwamammen turaren shi, Koda idon shi ya sauka a kanta kasa d'auke idon yayi saboda wani maseefar kyau data mishi cikin shigar tata ta yau, a take kuma zuciyarshi tayi d'arrr gaban shi yayi mummunar fad'uwa da wani abu ya gifto cikin zuciyarshi.
Raihana kam tunda ya futo sassanyan k'amshin turaren shi ya sanar da ita zuwan shi, tana sane ta dake tamkar bata ganshi ba saboda haushin hanata futar da yayi. Ganin yau ko gaishe shi bata yiba shi sai yace mata, "Ina kwana Raihana!".
Abun sai yayi mata banbarakwai har yasa ta sauke k'afarta data d'ora d'aya kan d'aya tace, "In...Ina... kwana".
"Fatan kin tashi lafiya". Ya fad'a yana sake ci gaba da kallonta, "alhamdulillah" ta fad'a k'asa k'asa har lokacin bata yarda ta kalle shiba. Shima huceta yayi zuwa dinning.
Bayan ya gama karya kumallo komawa yayi cikin d'akin shi ya d'auko mukullin gidan da wayarshi ya sake futowa ya ganta inda ya barta.
"Bismillah muje ko?". Ya fad'a cikin bata umarni.
Ta mik'e kamar zata ce dashi wani abu sai kuma dai ta fasa suka d'auki hanyar futa a gidan gaba d'aya......

****Saleema kam abubuwa sun sake mata tsanani, gaba d'aya komai ya sake hautsine mata har ya kwantar da ita jinya sosai. Ba k'awa! Ba y'an uwa a kusa! Bare wani mutum da zai iya kawo mata taimakon gaggawa, tun tana iya jurewa da k'arfin hali har ta gaza, a k'arshe dai dole ta dangane da asibiti, ta shafe wasu kwanaki tana jinya har da fudda rai da rayuwar duniya, ciwon daya sabbaba mata bud'e waya don a samu hanyar da za'a sanar da y'an gidan su mutuwarta. Cikin ikon Allah sai gashi ta samu sauk'i ta warke har an sallame ta. Koda Amna taji labari tazo mata sannu bata ce mata komai ba, sai dai har yanzu tak'i sakewa da Amnan don tana son khaleefa har kwanan gobe a k'asan ranta, tana kuma jin zafin Amna da ganinta matsayin wadda tayi silar rabuwar su. Bisa nasiha da shawarwarin da take samu daga likitar da tayi jinyarta ta saki jiki ta komawa asalin rayuwarta, makaranta ce kawai bata koma ba shima cikin satin take shirin komawa in taji kwarin jikinta.
Yauma tana zaune bayan gama wayarta da Abban ta, tayi shiru cikin duniyar tunani tana sake nazarin yadda rayuwa ta koma mata, Wai kamar ba itace Saleema y'ar gayu da maza da yawa idon su yake kanta ba! Kamar ba itace khaleefa yake tsara kalaman soyayyah da alk'awari iri iri ba, Sam batasan lokacin da wasu hawaye masu d'umi suka silmiyo saman kuncinta ba saida ta shafa da hannunta taji laima a lokacin da ake kwankwasa k'ofar apartment d'in nata.

Ta tashi da sanyin jiki ta wanke fuskarta, ta yafa siririn gyale saman kanta sannan ta bud'e k'ofar.
Kamar a cikin irin mafarkan data saba yi haka taga Abdallah khaleefa, sai ta mutstsika idonta don ta sake tabbatar daba gizo idonta suke mata ba, shine dai tsaye a gabanta duka hannuwan shi zube cikin aljihun jallabiyyar da take jikin shi ya jingina da katangar dake kare gaban d'akunan kwanan d'aliban.
"Khaleeefaaahhh.....". Ta k'arasa fad'a a sanyaye hango raihana tsaye a gefen shi cikin shigar data sake nuna mata asalin banbancin da yake tsakanin da ita, cikakkiyar mace irin wadda maza da yawa ba zasuyi sakacin mata rik'on wasa ba.
Sai taji gabanta yayi mummunar fad'uwa, zuciyarta ta karye, idonta ya ciko fal da ruwan hawaye, jikinta ya sake sanyi lakwas!

_Ina godiya da addu'a fatan Allah ya bar zumunci, alhamdulillah naji sauk'i sosai kam sai dai uzururruka sun sha kaina, amma in shaa Allah ina saka ran next week zamu k'ark'are labarin nan gaba d'aya. inda zamu zo muku da wani sabon salon labari na daban nida Dr Fayeeza, masu comment Ina matuk'ar jinjina_


_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy two 7️⃣2️⃣


"Ina son magana da ke". Ya fad'a bayan ya d'auke kanshi ga barin kallonta. Itama cikin k'arfafawa kanta da kanta gwiwa don tana ganin a wannan karon ya kamata ta fuskance shi suyita ta k'are tace, "kazo magana dani amma ka taho da wannan?". Ta k'arasa fad'a tana nuna raihana, saita girgiza kai, "toh ni bazan iya magana da kai a gabanta ba, idan ka manta in tuna maka nice fa Saleema macen data fara bud'e zuciyarka, ta koyar da kai soyayyah har a yanzun wannan yarinyar ta samu gurbin zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login