Showing 9001 words to 12000 words out of 288773 words

Chapter 4 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt

29 Oct 2025

1045

yace, "yana gida a kwance yana bacci".
"Daga gidan kake kenan?". Ta sake tambayarshi cikin tsare shi da ido.
Kauda kanshi yayi kafun ya sake cewa, "a'a daga gidansu Ahmad nake mahaifin shi ya buk'aci ganina, yanzun kuma da naje kema yace yana son ganinki".
Take yanayin fuskarta ya sake d'inkewa ta dawo kicin kicin, ta kalle shi cikin b'acin rae sosai tace, "Wai khaleefa wane irin yaro ne kai, Ina ce tuntuni nayi cancelling tafiyar ka gantalin banza wata k'asa da sunan karatu nace a'a ba zaka je ba, toh tun wuri kaje ka shaida ma mahaifin Ahmad d'in da kanka kamar yadda ka amsa tayin su tun asali ba tare da shawara da kowa ba cewa mahaifiyar ka tace a'a ba zaka tafi ba suda suka ji zasu iya sai su tura d'an su can su k'arata matsalar su ce".
Cikin marairaita khaleefa yace, "please Auntie.....". Surayyah yanzun cikin daka tsawa tace, "wallahi summa tallahi yanzun nan ranka zaiyi mummunan b'aci".
D'akar da kanshi yayi k'asa shiru yana sauraron bambaminta har ta dire, Jakarta ta d'auka da car key ko tea plask d'inta bata tsaya d'auka ba ta nufi hanyar futa ranta bak'ik'irin, har ga Allah ita gaji da jin magana d'aya da sukeyi kullum kullum da khaleefa ba don Ahmad ya kasance yaron kirki ba da tace tayi nadamar had'uwar shi da khaleefa, tasan dashi ne suka shawarta duk wannan hark'allar, a sanyaye khaleefa ya tashi shima yabi bayanta, ta rufe offishinta suka d'auki hanya. Saida tayi sallama da lebura da suke aiki a yammacin sannan ta shiga mazaunin driver a motarta, shima gefenta ya shiga ya zauna shiru babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har ta fara driving, a hakasuka iso anguwar su.
A k'ofar gida Suka samu Ayman zaune kan dakali yana koyama wata yarinyar mak'otan su iya msi suna raihana karatu. Duk suka nufi inda surayyahn take har raihanatu ta durk'usa tana gaishe su, khaleefa bai amsa ba don ko kallonta baiyi ba sai auntie ce ta amsa mata har tana tambayar ta maman ta, Ayman bin bayan shi yayi ya cimmasa a soro ya dafa kafad'ar shi, da sauri ya janye hannun Ayman ya sa kai ya huce cikin gidan, sallamar raihanatu yayi ta hanyar mik'a mata littafinta ya bi bayan auntie da sauri.
"Wai meya faru ne Auntie Keda yaya khaleefa? why the sudden change? Nasan dai bazai huce a kan tafiyar shi Germany bane, toh don Allah Auntie ki barshi ya tafi mana indai hakan zai dawo masa da walwalarshi.....".
"Rabu dashi Ayman sai dai ya dawwama cikin bak'in ciki amma ni da izinina ba zai tab'a barin Nigeria zuwa wata k'asa da sunan karatu ba, Soo learn how to be with him a hakan".
K'arshen abinda ta fad'a kenan ta tashi tabar mysu gurin shida iya. Bin bayanta iya tayi ta tarar tana cire takalmin k'afarta da agogo, zama tayi gefenta ta fara tambayar ta, "surayyah meya had'a ki da magaji ya shigo fuska a d'inke? Nima ta bakin Ayman indai akan tafiyar nan ne kiyi hak'uri ki barshi ya tafi mana". Cikin d'inke fuska har lokacin tace, "iya mubar maganar nan don Allah, yanzun Ina fatan akwai ragowar abincin rana don yunwa nake ji"
"Eh akwai d'an wake na fulawa da rogo, nasan kina so shiyasa na ajiye miki dama, sannan akwai ragowar alkubus d'in dana yiwa malam da magaji kinsan har gobe ya kasa sabawa da d'an wake shi". Surayyah tace,
"Bar alkubus d'in nan iya ki kawo mun d'an waken zaifi mun dad'in ci".
"Toh y'ar albarka" iya ta fad'a tana nufar inda ta adana mata abincin,
Ayman ne ya sake biyo ta bayan iya ta futa ya zauna a kusa da ita yace, "mum sai yaushe zaki sa a kawo mana wayoyin mu gashi waec d'in da mukayi daga baya har ta futo tuni, kuma as we promise mun futo da good result bisa amincewar ubangiji".
Dafa kanshi tayi tace, "Sunday insha Allah son". Da farin ciki ya mik'e zaune yana fad'in, "really mum".
Gyad'a mishi kai tayi, rungume ta yayi tsam yace cikin farin ciki yace "I luv you mum bari naje na fad'a ma khaleefa nasan shima zaiyi farin ciki".

Ayman da gudu ya nufi d'akin da y'an biyun nashi yake, ita kuma ta bishi da kallo cike da farin cikin da ya wanke b'acin ran da khaleefa ya haifar mata.
Khaleefa yana kwance a d'aya daga d'akunan parlon iya (Wanda malam yasa aka basu da suka kai shekaru takwas a duniya, wanda kafun haka suna kwana ne tare da surayyahn har ma sai sun sata a tsakiyar su suke iya bacci, amma su da kansu suna girma suna sake ja baya da ita har aka basu d'aki sukayi zaman su)
Idon shi kan ceiling d'in d'akin Ayman ya shigo ya bama kanshi mazauni kusa da d'an uwan nashi, "we are sorry bro nida Auntie ne ko? Bama son muyi missing d'inka shiyasa bama son kayi nesa damu, but we are Soo sorry plzz".
Kallon d'an uwan nashi yayi cike da so da kulawa ya tashi zaune sosai yace, "kasan abinda yasa nake son tafiya Germany twin bro? Saboda a can ne zan fi samun kwarewa a kan physiotherapy da duk wani abu daya shafe shi, Ina son nayi karatu mai zurfi a kan ciwon ta yadda zan zama kwararren physiotherapist doctor" sai ya had'a hannuwan shi biyu, "don Allah Ayman ka fahimce ni a dai dai ka fahimtar da Auntie ma". Ayman yace,
"Kada ka damu zata fahimceka insha Allah, nima na amince ka tafi sai dai Ina son ka tafi bisa albarkar Auntie shine kad'ai zaka samu abinda zaka je nema, Ina yi maka fatan dukkan nasara".
Rungume juna sukayi kowanne idonshi na kawo ruwan hawaye.

Nan suka baje kolin hajar hirar su irinta y'an uwantaka, har Ayman na yiwa khaleefa albishir d'in wayar su da Auntie tace zata zo soon, khaleefa yayi farin ciki shima sosai.


#######


Toh a tak'aice an matuk'ar kai ruwa rana kafun Auntie ta amince suje gidan su Ahmad abokin khaleefa, daga yadda mahaifin Ahmad ya dabaibaye ta da maganganu na fahimta da k'arfafa gwiwa ya fad'a mata ko a ina d'anka yake addu'a zakayi mishi kawai amma ba wayonka ba davarar kace take tsarewa sai taji jikinta yayi sanyi har ta amince da tafiyar tashi a take, abinda bata tab'a tsammanin zatayi ba.
Mahaifin Ahmad shiya shige musu gaba kuma kud'in registration na makarantar kawai ya amsa sai na apartment da za'a kama musu, amma kud'in jirgi da sauran hidin dimu na makaranta tuni yayi musu komai shida d'an shi. Ya kuma tabbatar ma Doctor surayyah da kanshi zai rakasu har makarantar, idan tana son taje taga komai da idonta zata iya biyo su suje tare.
Ko kad'an ba zata iya wannan rashin karar ba, ta amince da mutumin kasancewar shi babban mutum mai nagarta, haka d'an shi ta yadda da tarbiyyar shi tunda kusan tare da y'an biyun nata yake wuni mafi yawan lokuta a nan gidan iya.
Ranar da khaleefa yaji wannan albishir kasa bacci yayi yana mik'a godiyar shi ga Allah, yayi farin ciki yayi murna har da kukan murna.

Kamar yadda tayi musu alk'awari ta sa an kawo musu waya mai kyau irin wadda ake yayi. Cikin kwana bakwai cif shirye shiryen tafiyar su ya kammala, duk da surayyah taso ya tsaya ya karb'i allon saukar su data rage kwana kad'an yanzun, amma hakan bai yiwu ba, saboda suna sake yin delay zasuyi missing komai nasu.
Ana i gobe zasu tafi iya malam da surayyah Suka sashi a tsakiya suka yita mishi nasiha da fad'a kan rayuwa. Alhamdulillah naseehar ta shiga jikin shi sosai, hakan yasa har washe garin ranar daya gama had'a Kaya jikinshi a sanyaye.
Ya yima su iya da malam sallama lafiya. Auntie da Ayman sukayi mishi rakiya zuwa airport.

AMINU KANO International airport
Surayyah data kasance matashiyar mace da kallo d'aya zaka musanta cewar itace ta haifi wad'an nan yara ma'abota kyau da cikar kamala kamanni sak da juna in aka d'auke wasu banbance banbance k'alilan da sai wanda ya zauna dasu zai iya gani, tana tsaye gefenta Ayman da khaleefa, komai na jikinsu iri d'aya hatta da agogo da takalmi da wayoyin hannunsu ba abinda ya banbanta, sai trolley dake rik'e a hannun khaleefa babu a hannun Ayman. Fuskokin su kad'ai zaka kalla kasan suna cikin tarin damuwa.
Surayyah ta kamo hannun khaleefa da hannun shi ke rik'e da jakar kayan shi, ta kira shi cikin kwantaccen sauti dake nuni da zallar damuwar da take ciki, "khaleefa".
D'ago kanshi yayi cikin ladabi ya amsa kiranta da, "na'am Auntie".
Hannuwan shi duka ta had'a ta rintse cikin juna tace, "toh khaleefa yau gaka ga cikar burinka ka samu, duk da nasan kafi kowa sanin kanka don Allah ka lura ka rik'e maraicinka da amanar kanka da zan baka yanzu, sannan ka maida hankali akan abinda ya kaika, a k'arshe Ina maiyi maka fatan samun dukkan nasara, Ina rok'on Allah ubangiji ya baka ilimi mai amfanni wanda zai amfaneka duniya da lahira".
Sai ta saki hannun shi tana share hawayenta da gefen gyalenta.
Shi kanshi saida hawaye ya taru a idonshi, amma kasancewar shi mai k'arfin hali da k'arfin zuciya, sai bai yadda hawayen sun samu damar futowa ba ya shanye. Cikin sake russunawa a gabanta yace, "insha Allah Auntie, zanyi yadda kike so".
Cikin jin dad'i ta shafa sumar kanshi tace, "Allah yayi muku albarka ya cika muku burikan ku my twins". Ya amsa da, "ameen yumma na da banda kamarta".
Surayyah ta shafa kanshi tana murmushi mai tafe da siraran hawaye, "Allah ya cika muku burikan ku kai na zama medical physiotherapy Doctor, shi kuma na engineer". Duk murmushi sukayi khaleefa ya leqa fuskar Ayman daya juya mishi baya, kuka yake yi sosae, dafa kafad'ar shi khaleefa yayi cikin kulawa yace, "Ayman kuka haka kamar mace?". Sake zagayowa gaban shi yayi ya rik'e duka shoulder shi yace, "as a man you have to be strong Ayman, idar har k'aramin abu zai iya assasa zubar hawayenka haka to taya zaka iya yak'i da k'addarorinka? Ya kamata tun daga yanzu ka fara sawa ranka hak'uri da juriya, shekaru shida zuwa bakwai zanyi na dad'e da yawa takwas ba shekaru dubu ba"

"kayi hak'uri khaleefa bansan ya zanyi da rayuwata ba idan ka tafi ka barni ni d'aya, dole nayi kukan nan don shine kad'ai zai rage mun d'acin bak'in cikin rashinka da zanyi, khaleefa kada ka manta mun saba yin komai tare, cin abinci, yawo cikin gari, tafiya school, da buga football duk k'arshen mako,idan ka tafi ka barni bana tunanin zan iya futa waje cikin mutane har nayi walwala, kayan mu da suke duk iri d'aya bansani ba ko zan iya sawa ni d'aya bayan ba ka nan, tabbas zanyi kewar fushinka, fara'arka, da miskilancin ka idan baka da lafiya, zanyi kewarka gaba d'ayan ka bro.......".
Ya k'arasa fad'a cikin kuka had'e da takawa da sassarfa ya rungume shi, ba tare daya juyo ba cikin sake danne zuciyar shi yace, "sorry man ai duk kaine ka raba tsakanin mu da kak'i amincewa mu tafi tare".
Girgiza mishi kai ya dinga yi, "bazan iya tafiya na bar Auntie ba shiyasa na zab'i da nayi karatuna a nan gida Nigeria, sai dai zanyi k'ok'ari na dinga biyo Auntie idan zata zo duba ka, a k'arshe ina yi maka fatan samun abinda zaka je nema twin bro, wish you oll de best of luck".
Khaleefa juyowa yayi ya rungume shi ya lumshe ido a hankali hawayen da suka taru cikin idonshi da yake ta yak'i da zubar su suka soma biyo kuncin shi, daga nan gurin Auntie yayi ya russuna a gabanta gwiwar shi biyu duka a k'asa "ki gafarceni mum nasan har yanzu ba da son ranki zan tafi karatun nan ba, toh amma Allah ya riga ya tsara hakan a cikin k'addarorin mu ba yadda zamuyi, sai dai ban sare ba haka banyi k'asa a gwiwa ba gani nazo gareki da kokon barar addu'ar ki domin na samu abinda zanje nema duk da kinyi Ina son ki k'ara mun wata a kan wata domin addu'ar ki itace zata zamo silar samun dukkan nasarar abinda zanje nema".
Itama cike da tausayin shi matuk'a ta d'ora hannun ta saman kanshi tace, "Allah yayi maka jagora son ya albarkace ka ya albarkaci karatun". "sai abinda zan sake jadadda maka a matsayin naseeha ta a gareka ta k'arshe, "don Allah ka kama kanka ka rik'e addinin ka ba tare da la'akari da rashin ingancin addinin mutanen da zaka shiga cikin su ba, kayi abinda yake halal, ka guji aikata Haram don gujewa fushin ubangiji".
He can no more hold his tears at that very moment, kuka yake irin wanda ya kan jima baiyi irin shiba, da kanta surayyah ta d'ago shi ta share mishi hawayen, su duka ta had'a ta rungume a k'irjin ta tana jin sabuwar k'aunar yaran a cikin zuciyar ta.
A haka y'an gidan su Ahmad da sukayo mishi rakiya suka same su, sun gaisa cikin mutumci kafun su sallamu yaran su soma tafiya inda za'ayi musu screening, tunda khaleefa ya had'a hannun Ayman da Auntie ya dank'e cikin na juna ya fara tafiya bai waiwayo ba.
Kuka yake har lokacin, suna tsaye a gurin har saida ya b'acewa idaniyar su.


Comment and share
24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyaert lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page four 4️⃣


Basu iya barin airport d'in ba har saida suka ga tashin jirgin su khaleefa,ko a cikin mota babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har suka k'arasa gidan k'awarta sameera.
Ayman bai shiga gidan ba ya kwantar da seat yayi kwanciyar shi a mota,
Ko data shiga gidan ta tarar sameeran tana shirin futa anguwa duk yaran sun tafi school sai baby heedaya da take bacci sab'e a kafad'ar ta hannunta rik'e da car key, komawa tayi suka zauna a parlon, sun gaisa cikin mutumci da mutunta juna inda take bata labarin tafiyar khaleefa Germany yau.
Ta taya ta dayi mishi addu'o'i sosai kafun su fad'a hirar business da lissafin shirye shiryen bud'e shagon boutique wanda Ayman da babban d'an sameera haydar zasu kula dashi a ranakun da basu da lectures, ko idan sun taso school haka tunda ita har lokacin tana futa aiki.
Sun tab'a hira mai yawa a kan business da k'ullalliyar alaqar da suke son su k'ulla na auratayya tsakanin yaran su don k'ara dankon zumunci. Ko data futo ita ta jasu har gida don Ayman zuwa lokacin yayi laga laga da zazzab'i da ciwon kai.
Suna shiga gida ko bi takan iya da take mishi magana bai yi ba ya dusa kanshi d'aki ya kwanta.
Da kyar auntie da iya suka shawo kanshi yaci wani abu yasha magani, wasa wasa saiga Ayman ya dangane da likita saboda zazzab'i ne yaci k'arfin shi karurus.

Ta b'angaren Khaleefa kuwa kwanan shi biyu a Berlin dake k'asar Germany ya siya sim card ya nemi no's d'insu sukayi magana, ba k'aramin tashi hankalin shi yayi da yaji ciwon Ayman ba, har saida Auntie ta dinga kwantar mishi da hankali sannan, shida Ahmad a wani plat house aka kama musu apartment sai dai kowa cikin su d'akin shi da ban ne, gida ne babbah sama da k'asa d'akuna iri d'aya a jejjere kusan guda ashirin, kowane d'aki da kitchen da toilet a ciki, haka akwai d'an gado k'arami da drower, khaleefa basu sha wahala wajen siyan duk abubuwan buk'ata irin wanda suke so ba, saboda gidan kusan mutum 6 cikin 20 y'an Nigeria ne da suka kwana biyu a garin, su sukayi musu jagora. khaleefa sun fara karatu ba tare da sun Samu matsala da kowa ba a babbar makarantar...... Dake birnin Berlin na k'asar Germany, a wasu lokutan idan basu da lectures yakan je gurin Ahmad su yini tare su jagwalgwola girkin abinda zasu ci wanda khaleefa ya zama jagora don yakan taya Auntie aikin magana wani lokacin a gida idan ta tuna da abincin k'asar su ta Egypt. wani lokacin kuma suje k'aramin eatery suci abinci dai dai da kud'in su.

******** ********

_Nigeria kuwa_

Anyi bikin saukar su Ayman cikin k'ayatarwa inda Auntie ta shirya musu lafiyayyen bikin walima, Ayman shiya wakilci khaleefa har ya karb'ar mishi allo, ranar yini Ayman yayi yana video call da khaleefa yana nuna mishi komai, ko da yamma a wajen walima shi bashi da wasu abokai sai kad'an daga y'an ajinsu da Suka zo mishi, daya sallamesu yaga akwai ragowar take aways sai ya kira raihanatu ya bata ragowar duka yace ta kaiwa y'an gidansu kawai don shi baisan ya zaiyi dasu ba. Da kyar ta karb'a saboda ganin yawan su kamar itace ta shirya walimar, raihanatu duk da kasancewar ta yarinya k'arama a lokacin amma tana da taka tsantsan da mutane, a anguwar ba kowa take kulawa ba sai Ayman d'in da tasu tazo d'aya har yake kiranta da k'awar shi, a mafi yawan lokuta shi yake yi mata assignment ya nuna mata abinda ya shige


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login