Showing 222001 words to 225000 words out of 288773 words
Chapter 75 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
wanda iyayen su suka toshe kunnuwan su daga sauraron zagin mutanen gari, yaci jarrabawar common entrance a ajin k'arshe na firamare, sai ya tafi boarding school dake gwarzo.
Ya kammala secondary a k'arshe ya samu gurbin karatu a A.B.U Zaria.... Yana cikin karatun aka bashi auren wata matashiyar yarinya da ba zata huce shekaru sha uku a duniya ba mai suna Maryam..... Da auren ta yaci gaba da karatun shi tun daga matakin degree har izuwa master's, yayin da itama bai barta haka nan ba, ya maida ita makaranta ta k'arasa had'a karatunta na sakandire tsab.
A lokacin suna da yara uku duka maza, salis! Mukhtar!! Abubakar!!!
Abdallah ya fara lecturing a makarantar da yayi karatu kafun ya fad'a harkokin siyasa, ya rik'e muk'amai da dama tun daga k'anana har zuwa manya, kafun a k'arshe ya k'are da samun babban matsayi na zama ambassador Nigeria a k'asar turkey. A lokacin matarshi da suke kira maryam ta k'ara haihuwar yara uku, sooraj sai Aysha da Fatima! Duk da kasancewar mijinta rik'ak'k'en d'an boko da yake rayuwa a cikin turawan larabawa basu d'auki tsarin yahudu na k'aiyade haihuwa ba, suka haifi yaran su tamkar asalin Nigerians suke kuma kula dasu da kyakkyawar kula da tarbiyyah ingantacciya don matarshi normal house wife ce, ba irin matan da kullum suke gantali akan hanya makaranta ko aiki ba.
Tun asalin sooraj ya tashi wani irin bahagon yaro mai murd'ad'd'iyar fahimta, yana da matuk'ar kaifin kwakwalwa da basirar data zarce ta duka y'an uwan shi, sun fara karatun su a turkey mataki mataki kafun su tattara su dawo Nigeria gidan mahaifin su dake garki....
A hankali rayuwa taci gaba da tafiyar musu har kusan matasan biyu suka kammala karatun su suka samu aiki d'aya a B. U. K Kano d'aya kuma yake aiki matsayin babban likita a garin Zaria...
Taufeeq da sooraj kuma suna gab da kammala degree na biyu.
Shekaru sunyi nauyi wa Abdallah, ya daina harkokin siyasa tuni, yanda shekarun shi sukayi nauyi saiya daina tunanin komai don adadin abinda ya tara yasan zai ishe shi ya k'arasa kula da rayuwar iyalan shi har bayan ranshi.
Taufeeq ma ya samu aiki a babban bankin Abuja sai dai sooraj ya nuna sam bashi da sha'awar aikin gwamnati ko zama k'ark'ashin wani company.
Yayyen shi sunso ja dashi sai dai basu samu goyon baya daga mahaifin su daya kasance mutum mai ra'ayi da magana d'aya ba.
Ya dunk'uli kud'i masu yawa ya bashi yace ya fara business, ya fara harkar kasuwancin shi da kad'an kad'an har Allah yasa mishi albarka cikin k'aramin lokaci ya mallaki company nashi na k'ashin kanshi.
Koda aka zo maganar aure, maman su taso shima tayi mishi zab'in d'aya cikin yaran family had'in auren zumunci kamar yadda ta yiwa sauran y'an uwan shi daga mazan har mata da tuni dama su tuni akayi musu aure, kowa ya karb'a banda sooraj da akazo kanshi ya nuna sam bashi da ra'ayi akan aure yanzu.
Yayan shi saddik tuni yayi auren shi matar ta tare a gidan tunda babban gida ne da aka gina shi da tsarin had'a extended family.....".
Nannauyar ajiyar zuciya raihana ta sauƙe ta mik'e donta gabatar da sallah, tayi girki tunda khaleefa yana gida yau ba futa zaiyi ba.....
Cikin zak'uwa da son jin k'arashen labarin ta shiga d'akin wankanta ta futo ta shimfid'a darduma ta kabbara sallarta.
Tana idarwa ta b'oye littafin k'asan pillow ta futo daga d'akin.
Dai dai lokacin da khaleefa ya shigo gidan shima.... Duk suka kalli juna lokaci d'aya kuma suka d'auke kansu.....
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty three 6️⃣3️⃣
A parlon ya zauna ita kuma ta shige kitchen. Har ta gama aikin ta futo yana inda ta barshi a kwance yana kallo.
A k'aramin table na gaban shi ta had'a mishi komai ita kuma ta koma kitchen taci nata, tana cin abincin ta kira yasmine suka gaisa taji lafiyarta, ba laifi yadda taji muryarta kad'ai ma tasan da sauk'i sosai, tayi mata tayin abinci tace bata cinye wanda ta kawo mata na safe bama. Sunci gaba da tab'a hira kan wahalar da take sha na laulayi, kafun suyi sallama kowa ta ajiye wayarta.
Har ta ajiye wayar zata wanke hannunta ta futo wayarta ta bada k'arar sautin shigowar sak'o.
Da sauri ta wanke hannun tazo ta duba, daga Ayman ne, "Assalam! Mrs Abdallah fatan kina lafiya?", murmushi tayi ta mayar mishi da reply kamar haka, "lafiya k'alou nake fatan kaima? Ya fushi damu?"
"Fushi na huce tunda auntien munyi waya kun saketa tana umrah".
Dariya tayi kad'an lokacin data gama karanta sak'on shi, ta sake mayar mishi da amsa, "toh Allah ya k'ara hutar zuciyarka".
"Ke kad'ai kika iya wannan addu'ar banda mijin ki".
"Shima ina baka hak'uri a madadin shi".
"Ai hak'urin ki ya wadatar tunda keda khaleefa a gurina duk abu d'aya ne, ki mik'a sak'on godiyata ga twin bro na, kice in ya gama fushin ya kira ni ina son naji muryarshi kada abun ya taru yayi mun yawa....".
"(😸😸) Insha Allah zan isar mishi da sak'on ka fatan alkhairy".
"Thanks matar bro..... Fatan alkhairy gare ku baki d'aya".
Murmushi tayi bayan gama hira dashi ta text message ta mik'e da sauri ta futo a kitchen d'in.
Khaleefa yana zaune ko yaci abincin da aka kawo mishi ma? Ita dai ta ganshi ya had'a kai da gwiwa. Har zata huce d'akinta sai ta dawo da baya don isar dashi sak'on Ayman, "amm Yaya Ayman yana son magana da kai da alama yana ta kiran ka wayar bata kusa shiyasa baya samun ka, a k'arshe yana maka fatan alkhairy yace yana sauraron kiran ka...".
Tana gama maganar tayi hucewarta, shi kuma yabi bayanta da kallo kafun ya mik'e don wayar ma cikin d'akin shi ya barta".
Raihana koda ta shiga d'akinta gyare gyaren ta tayi har zuwa lokacin da akayi sallar la'asar, dama tana idar da sallah ta koma kitchen don girkinta zai iya kaiwa dare inta zauna.
Duk abinda take yi zuciyarta tana kan gab'ar labarinta data bari ne, burinta tayi ta gama ta k'arasa jin yadda zata k'are,,,,,
A tak'aice bata sake samun damar zama ba sai yamma, ko abinci bata tsaya ciba, ta dai ajiyewa khaleefa nashi a dinning, ta bud'e diaryn zata ci gaba da karatu taji ana tab'a kararrawar k'ofa, ba tayi saurin tashi ba saboda tana zaton khaleefa zai bud'e k'ofar, sai dai jin ana ci gaba da danna kararrawar had'e da dukan k'ofar saita mik'e ta zura dogon hijab ta nufi k'ofar.
Koda ta murza key ta bud'e Ahmad ta gani kamar a gigice yana tambayarta, "Ina man d'in? Ya jikin nashi?".
Ita da batasan ma bashi da lafiya ba, bashi hanya kawai tayi ya shiga ita kuma ta rufe k'ofar, ganin Ahmad bai shiga d'akin khaleefan ba sai tace mishi, "yana ciki ai".
"Noop! Ba saina shiga ba ki bashi wannan magugunan, amma ki tabbatar yaci abincin shi kafun.....".
Ta karb'a tare da gyad'a mishi kai, daga nan ya fuce a gidan ita kuma ta rufe k'ofar.
Ta jima tana knocking k'ofar d'akin baccin shi amma babu alamun za'a bata izinin shiga, har tayi nufin tafiyarta sai kuma taga rashin dacewar hakan, toh amma taya zata iya kutsa kanta d'akin shi kai tsaye?
Tayi ta tunane tunanen ta kafun tayi kasada ta tura k'ofar ta shiga a d'arare.
Yana kwance fuskarshi na kallon ceiling ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, hankalinta a kanshi ta k'arasa tana mishi sannu, bai iya amsa taba saida ya jima da kyar ya tashi zaune ya zauna har lokacin dafe da kanshi, raihana ta sake mishi sannu cikin tausayin halin da yake ciki, wannan karon ma bai amsa ba sai hannu daya mik'a mata, ta gane sak'on shi da Ahmad ya kawo mishi yake so.
Bata bashi ba saida ta fara gabatar mishi da abinci, da kyar da taimakonta yayi cokali hud'u zuwa biyar ya kora magungunan shi da ruwa ya koma ya kwanta, ba jimawa bacci ya kwashe shi mai nauyi.
Bata iya barin shiba kamar me gadi har yayi baccin ya tashi kan nashi da sauk'i.
Cikin kulawa itama ta sake matsawa kusa tana mishi sannu da tambayar ya yake jin jikin nashi?
Ya zuba kwayar idon shi a kanta ya lumshe ya motsa bakin shi da kyar yace, "da sauk'i".
"Allah ya k'ara sauk'i". Ta fad'a,
Wannan karon a zuciyarshi ya amsa.
Sun jima shiru kafun tayi tunanin had'a mishi ruwan wanka, ya shiga wankan kafun ya futo tayi karambani ta ciro mishi fararen kayan bacci kamar yadda ta lura yana yawan sawa.
Yana futowa d'aure da bathrobe ta futa d'akin da sauri, yabi bayanta da kallo har ta futa sannan ya k'arasa gaban mirrow yaja stool ya zauna yana kallon kanshi da sauraron yadda har yanzu yake sara mishi kad'an kad'an cikin shi kuma yana kiran yunwa.....
Har ya gama shiryawa bata dawo d'akin ba, hakan yasa ya futo daga d'akin shi.
K'amshin girki daya buso daga kitchen yasa shi lumshe idanun shi cikin shi na nuna tsananin buk'atar shi da abinda hancin shi ya shak'o.
Ya fara takawa a nutse har zuwa kitchen d'in ya tsaya daga bakin k'ofa yana kallonta tana ta hidimar juye abinci a plate, ita kuma wannan yarinyar bata gajiya da girki? Ya tambayi kanshi, a plate ta juye mishi abincin zata futo idanunta suka sauka a kanshi, saita tambaye shi, "akwai abinda kake buk'ata ne?".
Numfashi ya sauke yaci gaba da takawa ya d'ibi ruwa a glass cup yasha.
Kusan tare suka futo ya zauna a parlour, sai ta ajiye mishi abincin a gaban shi ya fara ci itama tayi gefe d'aya tana cin abincin gaba d'aya zuciyarta da tunaninta yana kan jin k'arashen labarin auntie. Saboda jikin khaleefa kad'ai ta zauna a gurin amma da tuni ta k'arasa karance labarin. Gashi har yanzu taga kamar jikin nashi sai a hankali, don abincin ma bai iya cin na kirki ba ya barshi ya jingina kanshi ya lumshe ido.
Har dare ya fara nisa suna zaune a gurin, sai sannu da take yi mishi a duk motsin shi, tana tsoron barin shi ciwon ya mishi zafi, ganin lokaci na tafiya gashi ta gaji ga parlon da sanyi saita shiga d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci masu kauri ta k'ara hijab ta d'auko pillow, a d'auko pillown ne taga littafin data ajiye a k'asan shi, saita had'a har littafin ta dawo parlon.
Yana kwance yanzun amma hannun shi dafe a goshin shi.
Itama kwanciyar tayi ta soma neman shafukan data tsaya ta d'ora.
"Na had'u da Suraj a ranar wata juma'ah da bazan tab'a mantawa ba, a lokacin mun samu hutu a makaranta zan tafi Sudan gurin y'an uwan iyayena da k'awata d'aya tilo da muke rayuwa da buri iri d'aya duk da muna zaune a mabanbantan gurare, a rayuwa bana gajiya da zuwa Sudan don haka kurum nake tsintar kaina cikin shauk'i na musamman in naje k'asar, shiyasa bana mantawa da zuwa musu duk bayan shekara d'aya ko biyu,
Tun a airport Suraj ya ganni amma ko a fuska bai nuna komai ba har saida muka shiga cikin jirgi da Allah yasa tafiyarmu tazo d'aya.
Koda ya tashi sauka P.A d'inshi yasa yabi bayana har gidan k'anin babana (da yake can na fara sauka).
Kwana na uku da sauka a k'asar Sudan Suraj ya gama abinda ya kawo shi zai tafi yasa aka rako shi gidan mu kafun ya huce, direct yayi magana da k'anin mahaifina yana son a bashi izini ya nemi aurena, k'anin mahaifina ya nuna mishi sam aurena baya hannun shi yanzun tunda ina zaune garin Abuja tare da yayana, a nan Suraj yake fad'a mishi ai shima garin da yake zaune kenan, sun tattauna sosai kan muhimman abubuwan da ya kamata a sani a kanshi, a k'arshe aka bashi adreshin sauban da shawarar ya fara yin magana dani kafun ya isa ga sauban d'in.
A haka suka bar matsaya Suraj ya jirani cikin d'akin bak'in da suka gama tattaunawa a ciki.
Muna zaune cikin gida muna hirar mu nida andal da bama rabuwa da juna tunda nazo, hira muke kan rayuwar makaranta da irin yadda ake challenging d'inta akan karatunta, yayinda nake K'arfafa mata gwiwa da kwantar mata da hankali had'e da bata shawarwari masu kyau.
Koda uncle ya fad'a mun ina da bak'o nayi mamaki sosai tunda nasan ba saurayi gare niba.
Tare da andal muka same shi. Da kallo d'aya Suraj ya tafi da hankalina da duk wani tunanina tun kafun ya kaiga furta komai a gare ni, Cox ya kasance d'an gayun matashin daya fara huce shekarun rawar kai. Mun gaisa dashi gaba d'aya kafun muyi shiru muna sauraron muji da wadda yazo.
Shi kuwa da murmushi kan fuskarshi ya fara da tambayata, "surrayah ko?" Banyi magana ba sai andal ce ta amsa shi. Ya sake cewa, "toh surayyah Ni dai sunana Suraj Abdallah tofa, d'an asalin k'asar Nigeria garin Abuja, na ganki tun ranar da muka shiga jirgi d'aya, Ina fatan zaki iya aurena?".
Da mamaki duk muka kalle shi, mun d'auka kowanne saurayi da soyayyah yake fara magana har a kaiga batun aure, amma sai gashi karo na farko munga mai neman aure ba tare daya nemi soyayyah ba.
Haka Suraj ya dinga zayyano abinda yake ranshi kai tsaye, duk da naga baud'ad'd'en hali a tare dashi amma a haka nayi na'am dashi har na bashi full address na gidan yayana Sauban a karo na biyu. Bai tafi ba saida ya bar mana kud'i masu yawa.
Muka shiga gida muna al'ajabin halayen shi nida andal.
Sati na uku cif a Sudan na koma Nigeria da dashen soyayyar Suraj da tunda na ganshi sau d'aya ban sake sanyashi a kwayar idanu naba sai tunanin shi da nake kwana da tashi dashi.
Ina dawowa na tarar da sabon tashin hankali a gurin yayana, fad'a yake ta inda ya shiga ba tanan yake futa ba, Wai tunda na zab'i aure saina hak'ura da karatu, sannan ko auren nema shi yana da wanda ya zab'a mun matsayin mijin aure na.
Nan fa hankalina ya tashi na dinga bashi hak'uri nida aunti Sarah har muka samu ya hak'ura sai daifa cikin satin ya turo mun wani abokin shi d'an asalin k'asar mu daya dad'e yana sona ya nemi soyayyata dana dad'e da bada kyautar ta ga mutumin da baisan ma ina yiba, bansan yadda sukayi da sauban ba tun zuwan farko gurin shi, watak'ila korar shi yayi shi kuma ya hak'ura.
Ina cikin wannan tsaka mai wuyar na koma makaranta naci gaba da karatuna cikin sabuwar damuwar data fara ginuwa cikin zuciyata.
Ta b'angaren Suraj ma kai tsaye maman shi da duka y'an gidan su suka k'alubalan ce shi akan maganar auren, a cewar su bayan ya dad'e baiyi aure ba shine zai d'auko musu yarinyar wata k'asa da al'adarsu ta banbanta da ita,,,, Sam basu amince ba.
Ko kad'an hankalin Suraj bai tashi ba saboda shi bai tab'a jin ba zai same niba koda wasa, sannan yasan indai mahaifin shi yana raye ba zai barsu su zama katanga ga abinda yake matuk'ar so ba.
Haka kuwa akayi mahaifin shi yayi futu futu ya hana aci gaba da maganar ba'a sona a gidan, yayinda ya kafa musu hujja da komai yana faruwa da dalili, shi Suraj yaga nashi dalilin har ya fara sonta, su Ina nasu na k'inta?
Duk sukayi shiru, yayi fad'a sosai musamman akan momy hapsert data ke babba amma ba tayi tunani ba.
Da haka ya toshe bakin kowa babu wanda ya sake magana gidan, daga yayyen Suraj har k'annen shi.
Suraj yaci gaba da bibiyata har Allah yasa soyayyah ta k'ara k'arfi a tsakanin mu, ranar da yayana ya gane muna tare nan ma ya dinga masifa hadda rantsuwar ba zai tab'a bari na auri wanda basu san muhimmancin aure bare har su iya rik'e shi da kyau ba.
Haka akayita rigima, bazan manta ba mahaifin Suraj da kanshi ya taka yayi ma Sauban nasiha da kwantar mishi da hankali had'e da alk'awarin zasu kula mishi da k'anwarshi ba tare da wata matsala ba.
Saboda ganin dattakon mutumin daya kasance babban mutum mai kud'i da iko yazo takanas gurin shi yana bashi hak'uri