Showing 258001 words to 261000 words out of 270738 words

Chapter 87 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Usman ya shigo sai naga hannunshi duk datti ya nufi masaukina. Barin biyu nayi a wajen Luba nabi bayanshi. Ina shiga yana fitowa daga banWaki. Idanu muka zuba ma juna. Yana tsaye ya?i motsawa nima kuma na kasa ?arasawa gareshi. Hannunshi ya mi?o mun dole ?anwar na?i na bi hannun. Ina ?arasowa ya fisgoni duk girmana ya Waura kaina a ?irjinshi. Idanuna na lumshe kawai inajin yana wasa da inda yafi Waukar hankalinshi. Banyi yin?urin hanashi ba sai taimaka mishi ma da nayi. Abu fa tun daga tsaye sai gamu a zube a ?asa. Ku dai kunsan komai.
Sallamar Luba ce tasa ya zare bakinshi a nawa yana sauke ajjiyar zuchiya. In tashi tsaye ya hanani tashi. In amsa sallamar ni kuma harshena yayi mun nauyi. Da taji shiru dole ta juya ina jiyo kukan biyu.
"Kin susutani haka doguwar riga take zama miki a baya? To daga yau kar in kuma ganinki da zani, doguwar riga kawai nake so, so samu irin waWannan masu santsin. Ki shirya yau zaki tare dan jiya na ?waru"
Ni wallahi matanka tsoro suke bani"
Saida ya shafi wuyana yana wasa da sar?ar dake wuyan yace.
"Ki sha kuruminki ai na dawo dake gidana dake jikin wannan, yanzu haka jera miki kayanki akeyi ma"
Idanu na zaro, inason tambayar dalili ya hanani wannan damar.
"Ki bani abinci inci zan koma inga aikin. Su Alhaji Baba suna hanya fa yau zasu dawo.
Abinci naje na kawo mishi yaci ya ?oshi ya koma can gidan tare da sake jaddadamun yau da ?irjinshi zanyi matashin kai. Ni kuma har ga Allah nafi son yaje ga matanshi ni maci amarcin namu a can.
Ai kuwa da daddare sai ga su Alhaji Baba. Nan na gabatar musu da abinci suna ci harda Usman suna hira, ni dai nayi shiru .Da dai Alhaji Baba yaga dare yayi sai ya dubi Usman yace.
"Ya kamata ka Wauki haramar tafiya kaga dare na yi. ?ata kema ya kamata kije ki kwanta gobe zaki tashi da shirye_shiryen tafiya"
Ai zuruf na mi?e nayi musu sai da safe, Usman kuma sai kashe mun ido yake yi nayi kamar ban gani ba.
Sun jima ina jiyo muryarsu kafin daga bisani ya fice ya tafi can wajen matanshi.
Washegari na tashi da shirye_shiryen tafiya. Zuwa taran safe Anty Sumayya tazo muka fita, sai a mota take faWamun da ?ar mai aikinta zamu tafi zata dinga yi mun renon ?an biyu kuma ta Webe mun kewa in Usman zai yi aikin kwana. Ai kuwa naji daWi sosai. Shagon dogayen riguna Anty Sumayya ta kaini ta dinga zaSamun masu kyau kalar ?an gayu. Daga nan muka shiga shagon rigunan bacci nanma ta siya mun masu bayyana sura ni dai duk kunya ta kamani.
Anty Sumayya inaso in sai kaji inaso in yi dambun namane"
"To Shikenan akwai mai kajin su Hajiya sai a sa ya kawo"
Ai kuwa muna dawowa na samu mai kaji ya kawo guda shida. Ni da Luba muka yi aikin dambun mune har taran dare bamu gama ba. Da daddare sai ga Mus'ab ?anin Usman da wata ?ar yarinya da bata wuce shekaru sha uku ba da jakar kayanta. Luba ta kirani muka gaisa da Mus'ab yace.
"Anty Sumayya ce tace in kawo miki Halima ta kwana sabida gobe sassafe zaku wuce"
Allah sarki to nagode sosai ka gaida iyalan"
"Zasu ji. Ohh su Halima an zama ?an India iye iye"
Ya shiga tsokanarta ita kuma ta shiga murna.
A wannan daren na kai kusan biyun dare ina haWa kaya. Inayi muna waya da Usman da duk ya dameni da zantukan sake layi. Ni dai sai dariya kawai nake yi mishi.
Washegari sassafe Mus'ab yazo shi da Usman shi zai kaimu Airport. Alhaji Baba ya jima yana mun nasiha haka Hajiya ma. Nan nayi sallama da Luba muka kama hanyar Airport. Muna zuwa muka soma bin layin shiga Bus Win da zata ?arasa damu wajen jirgi. Usman na rungume da Hassan ga akwatin kaya. Ni kuma ina ri?e da kayayyaki Halima na goye da usaini.
Gaga gaga sai ga jirginmu a Abuja. Hotel ya kama mana a Abuja dan sai dare jirginmu ya Waga zuwa India da misalin ?arfe takwas na dare. Allahu Akbar Allah shi ke da iko akan komai.
Tafiyar awa goma sha uku da minti goma a sama.
Karfe taran safe jirginmu ya sauka a filin jirgin Rajiv gandhi international airport.
Ni dai sai zazzare idanuna nake yi, ina biye da Usman har zuwa fitowarma daga cikin Airport ni?i_ni?i da kaya ga biyu ga Halima. Mota mai ?afa uku muka shiga wanda a wannan lokacin ban taSa ganinta ba har ga Allah. A filin jirgin ?asa motarnan mai ?afa uku ta sauke mu muka shiga, a wani dogon benci da masu jiran tashin jirgi suke zaune Usman ya zaunar damu.
"Ku zauna ina zuwa, zan kawo muku abinci kuci, sai in siyo mana tikiti jirginma da halama ya kusan cika"
Ni dai sai zazzare idanu nake yi ina kallo indiyawa maza da mata da yadda suke magana suna motsi da kayukansu. Wasu suna zaune suna cin abinci, duk masu cin abinci abun mamaki da hannu suke ci. Muma Usman ya kawo mana wata shinkafa da kaza, da wasu miyoyi dil_Wil daban daban kusan kala shida kuma a ganye aka zuba abinci sai aka Waura a tire.
Ruwa ya zuba mun na wanke bakina da hannayena na soma cin abincin shi yana ri?e da biyu. Halima ma sai zuba loma take yi ta shawo yunwa duk da mun cicci abinci a jirgi amman dangin fulawane kuma ?an kaWan kaWan ne a cikin kwalin. Sai da na ?oshi na ba biyu suka ci Usman dai yace shi bazai ci ba.
Sai da mu ka yi sallar azahar aka soma sanarwa a shiga jirgi. Duk muka shiga muka zazzauna jirgin akwai girma sosai tarago_tarago. Tafiya mabuWin ilimi muna tafe Usman yana yi mun bayanin garuruwan da muke ta wuwwucewa, abubuwan gwanin sha'awa sai gamu a garin Rajasthan garine mai matu?ar girma da yawan jama'a yana daga cikin manyan birene a India a ?ar?ashin Rajasthan akwai birane masu yawa. Daga nan muka hau wata doguwar bus zuwa Udaipur city.
A wannan gari Usman yake zaune. Bamu muka shiga gida ba sai dare, iyakar galabaita nayi sosai abinka da ba'a sababa. Da ?yar na daure na tashi na yima biyu wanka suka sha nono sai bacci suma sun galabaita sosai. Usman na fitowa daga wanka nima na shiga na watsa ruwa na gargass jikina sosai. A zaune a kan teburi na fito na sameshi yana cin cake da dambun nama da tea. Murmushi ya sakarmun yanata ?aremun kallo ganina Waure da tawul. Ni kuma duk sai naji na takura rigar baccina na dau?a na koma bayan gida na saka, na shafe jikina da Humrar matan aure.
Na fito na sameshi sai dariya yake yi mun ni kuwa na basar na je na ja kujera na zauna na soma shan tean da ya haWa mun.
"Iyakar abinda zaka ci kenan ko in shiga kitchen in dafa maka wani abun?"
Idanu ya lumshe yace.
"Ya'isheni yau ba daren cika ciki bane yau ni dake ne a wannan daren. Na kai ?an biyu can Wakin Halima in muka gama abinda zamu yi sai in dawo dasu, gobe zamu shiga kasuwa mu siyo musu gadon yara"
Gaga_gaga a wannan daren abubbuwa da dama sun faru na farin ciki masu tsaiwa a zuchia.
Allahu Akbar bawa bai isa tsallake ?addara ba, face adda'a dake rage karfin ?addara koma ta canjata baki Waya. A hakanma nayi imanin adda'ata ita tasa Allah ya taimakeni.
Usman ya zame mun uwa ya zame mun uba. Ya haWani da yara ya rungumemu. Gaga_gaga rayuwa taci gaba da shurawa cikin farin ciki. Cikin watanni dani da ?an biyu duk muka canja jin daWi da hutu ya soma sauka sossi a jikinmu.
Rayuwar tayi daWi ci gaba ya sameni na komawa makaranta.

Bayan wasu shekaru:.

MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


ramlex266: Ina mata da suka amsa sunan su ba Muna mata ba....

Ina macen da take so ta zamo tauraruwa a gidan mijinta,itace uwargida itace amarya...
ramlex266: Uwargida ko Amarya shin minene matsalar ki a wajen miji?

Rashin dandano ko ni'ima?
Bushewar farji qayau kamar busashen ciyawa?
Rashin samun gamsuwa a wajen maigida ko rashin sha'awar ce ga baki d'aya?
Budewar farji kamar kofar wambai ko qarni/wari ke damunki
ramlex266: Kina so ki zama tauraura kuma sarauniya a wajen oga a rasa gane sirrin naki? Ki zamo yar gaban goshi sai yanda kika ce wato kin mayar da oga mijin kafin ta ce? Ba boka ba malam gyaran shimfida kawai Hajiya to ki nemi hjy ramlex domin qarin bayani
ramlex266: 07069722234 ko 08064421211


Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801


Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU....
ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA HU?U

17

INDIA

IYABO:.

A kwance nake a Waki idanuna a lumshe, bayana kamar zai dare gida biyu dan azaba. Tun cikin dare ciwon bayannan ya tashi mun dan ko runtsawa ban ba. Ban kira Usman na sanar mishi ba gudun kar ya baro aikinshi na dare ya dawo gida.
Hassan ne ya shigo da gudu ya faWo kaina.
"Umma kinga Alhaji ?arami yana mun gwalo ko?"
Da ?yar na buWe idanuna na dubeshi.
Wai baka ga Rumaisa'u na bacci bane so kake ka tasheta kai da baka da girma, yanzu Alhaji ?aramin ka kawo ?ara, ina Halima ta barku kuna wasan banza?"
Kafin ya bani amsa Nana ta shigo hannunta ri?e da kofin tea yarinyace ?ar hekara uku ?anwar Alhaji ?aramice, yayar Rumaisa'u kuma.
"Umma abinci zanci"
Hassan yi maza ka kirawo mun Halima yanzu."
Na dubi Nana nace.
Bari Halima tazo ta baki abincin, ku da in ba makaranta kuka tafi ba bakwa barin mutum ya huta
Kafin in rufe bakina sai ga Halima ita da Usaini da Hassan"
"Anty gani. Naga har yanzu baki fito ba. Kuma Abba ya kusan dawowa."
Agogon dake manne a bangon Wakin na kalla ?arfe takwas na safe.
Kiba Nana abinci, ki Wauki Rumaisa'u da su Hassan kuje can Wakinku ku Zauna bana jin daWine zasui ta damuna."
Ina gama faWa mata hakan na mi?e da dabara na shiga kitchen. Dankalin turawa Halima ta fere ta tsane a kwalanda shine abincin mu na karyawa yau dake manne a taswurar girkin gidana.
Mai na Waura a wuta na zuba dankalin. Na sake Waura ?aramar tukunya na haWa kayan chai tea na jama'ar india.
Na gama zuba komai a kula kenan na jiyo sallamar Abban yara a falo, tare da hayaniyar yaran sunata mishi oyoyo.
Ni dai ina tsugunne bayana ya kage nama kasa Wagowa balle har in fito.
A haka ya shigo ya sameni yana sanye da lap kot Winshi ta likitoci.
"Subhanallaah Habibty lafiya na ganki a haka?"
Ya faWa cike da kulawa da tsantsar damuwa.
Tallafoni yayi jikinshi da ?yar muka karasa ciki. Baku tambayeni ?iba ba hahaha ?iba sai abinda ya ?aru akan na da hutu da gogewar rayuwa yasa na zama kyakkyawa sosai. A bakin gadon Wakinshi ya zaunar dani.
"Meke damunku haka, ai ni na Wauka ma zamu haWu a asibiti har ward Winku na je ?awarki Sabitri tace mun baki zo ba, kuma ta kira wayarki a kashe. Ba morning kike dashi bane?"
Duk wannan maganar da yake yi mun hidima yake yi dani, ya kwantar dani, ya samun fullo ta bayana kamar yadda yake yi mini a duk sanda wannan ?addara ta ciwon baya ta tasanmu. Duk bincike, da kwarewa ta likitocin india, da irin kayan aikin da suke dashi wallahi sun kasa samo maganin ciwon bayannan nawa, hoto babu irin wanda ba'ayiba ba'a ganin komai, magani ko nasha sai dai ya lafar da ciwon. In kuwa cikine dani bana iya moruwa wannan dalilinne yasa Usman yasa aka juya mun mahaifar tunda muna da yara biyar ai sun ishemu.
"Sannu kinji, amman me yasa baki kirani ba, kuma kika wani shiga kitchen kina haWa kayan kari. Ai da kin barshi ko tea inna dawo sai in dafa mana ba, ko girkin kike so ba inayi muku ba?."
Mi?ewa yayi ya Wakko man zafin da in ciwon ya tashi ake mun masach dashi ya shiga yi mun masach Winnan. A kife fuskata take kafin ya gama mun na ji?e fulo sharab da hawaye. Azabar tana da yawa ainun.
Wayata ce tayi ruri a gefen gado.
"Ga Hajja Mama na kiranki, bari in Wauka nasan ba lallai ki iya magana ba"
Kai kawai na Waga mishi.
"Hello Hajja Mama barka da safiya"
Daga cikin wayar tace.
"Likita bokan turai. Ya gida, ya jikokin nawa?"
Murmushi yayi yace.
"Suna can Sarayinsu ai da suna jin na ambaci sunanki zasu soma ihu dake uwar ba lafiya wallahi nima yanzu dawowata daga aiki kenan, ita ko aikin ma ba zata samu zuwa ba"
"Assha wannan ciwon baya sai adda'a kawai. Anyi na asibitin, anyi na hausan abu ya?i ci ya?i cinyewa. Sai dai muce Allah ya dubeta ya bata lafiya kawai. Kai wannan yarinya tana ibadar Allah. Dama tsintsiyar ?amshine (turaren wuta Wan tsinke) masu shaguna suka soma sanarwa yayi ?asa shine nace bari in kira in sanar mata, to ashe ita babu lafiya ma."
Usman yace.
"Babu damuwa ai ko Halima sai ta je ta saro tunda tare suke zuwa. Kin turo sunayen waWanda kuke sonne?"
"Na turo likita bokan turai. Muna godiya sosai da irin gudunmawar da kake bama Iyabo, dama mu kanmu mungode ?warai Allah ya barku tare har ?arshen rsyuwarku. Jiya take sanar dani zaku sake zuwa Umara nace baka gajiya ne?"
Dariya kawai yayi yace.
"Sabida ciwon bayannan nata ne shi yasa nake yawan kaita ka'aba tana ro?on Allah ya yaye mata, in kuma bana warkewa bane Allah yasa shine silar shiganta aljanna. Irin na mata mai farfadiya da ma'aikin Allah ya shaida mata wannan ciwon shine silar shiganta aljanna"
Sun Wan jima suna tattaunawa. Kafin su kai sallama ya ajjiye wayar.
Idanuna a lumshe suke amman ba bacci nake yi ba.
Ji nayi ya fita, bai jima ba ya dawo da abinci da tea.
"Taso kici abinci sai ki sha magani ki kwanta. Zan kira asibitin da kaina in sanar musu baki da lafiya."
Sai da ya taimaka mun na samu na iya zama na jingina bayana a kan gadon. A hankali nake cin abincin mu na Wan taSa hira, duk da rabi da kwatan hirar ?orafine akan ban kirashi a waya na sanar mishi ba.
Matarshi data kirashi a waya ne ta ceceni ya fita amsa wayar. Sabida karamcinshi baya iya amsa wayar matarshi a gaban Wayar matar tashi.
Asma'u uwar kishi da raina Wan adam kenan. Na rasa dalilin da yasa matan Usman suke kishina haka. Akan zamana tare dashi a nan da komawata makaranta an sha artabu dasu sosai da sosai, Alhaji Baba ne yake taka musu birki. Dan a baya babu irin magiya da rarrashin da bai yi musu ba akan su bishi su dukka su dawo can da zama sabida suntirin yayi yawa. Ko wacce ta nuna ita tafi son aikinta ba zata iya tafiya ta bar aikinta ba. Ko zuwan da suke yi in anzo da Waya azo da Waya da ?ar suka yarda shima a cikin Sacin rai suke yi. Ni sai daga baya ne yake bani labarin komai da zama yayi zama, ya kuma bani labarinshi tun daga ?uruciya har girmanshi, da rasuwar mahaifiyarsu. Alhaji Baba ma yace duk su tawo Indian tare da yaran nasu. Sai suka nuna su sai dai ni in dawo duk mu hadu mu zauna shine abinda suke so. Irin muguntarnan ta mata na Wabi'ar kowa ya rasa. Shi kuma Usman ya nuna baisan wannan ba. Shikenan al'amuran gidanshi suka rincaSe. Duk haihuwa biyu da nayi a can Gombe nake yin wankan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login