Showing 183001 words to 186000 words out of 270738 words

Chapter 62 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

maganin muji me zaice mai kuma zai bamu. Kinga tashi kawai muje gidan matar abokin Hamman kawai mu wuce."
Ko abinci Uwani bata ci ba, ta dai sha ruwa. Allah yasa abincin dana dafa tazarce nayi har dare na cika babbar kula na dare. Sallama naima Yafendo nayi mata ?aryar zamu je gidan Cubu Uwani ta gano Wakin.
Muna fita sai gidansu BaWejo, dama matarshi a shirye take goyo kawai tayi muka wuce wani ?auye gaba damu sosai, munyi tafiya a mashin mai nisa kafin muka iso. Malamine sak ba boka ba, dama Yaya Hamma yayi mun bayani. Sai naga zahiri harda almajirai gasu a gabanshi. Amman layi ma ake bi ga mata da maza anata layi. Mun daWe sosai kafin ma layin yazo kanmu. Ni kaWai na isa wajen nai masa bayanin dalilin zuwan nawa tsab, da duk yadda nake ji, harda furucin da Hama tayi a kaina. Kai ya girgiza da lalatacciyar hausarshi yace.
"A lalle haukatakin taso tayi, tunda ko runtsawa bakya yi, ?arfin adda'ar da kike yi ne yasa burinta bai cika ba a kanki ba. Amman Allah ya fita. Yarinya ni ba boka bane, bana ba da laya. Sai dai zan rubuta miki ayoyin Alkur'ani in rubuta a allo in wanke miki. Sannan zan miki tofi da zaki dinga shafe jikinki, da habbatus sauda da zaki dinga turare Wakin ki dashi. Ba asiri ba ko sammu akayi miki da izinin Allah saiya karye. Amman sai zuwa gobe zaki dawo, sannan ki dena kwanciya da janaba, ki dinga alwala kafin ki kwanta. Allah ya ?ara sau?i gobe uwar haka sai ki dawo"
To Malam Nagode sosai. Nawa zan bayar abun sadaka?" Murmushi yayi yace
Sadaka bata kaWan bata yawa, abinda Allah ya hore miki ajjiye ki tafi, inma baki dashi zanyi miki dolena."
Nera dubu guda na ajjiye ina godiya na samu su Uwani muka kama hanya. Sai la'asar sakaliya muka shigo, a lokacin matan gidan duk sun daddawo anata aikace_aikace. A Wakin BaWWo duk muka zube, muka yi Sallah. BaWWo suka gaggaisa da Uwani ta fita ta bamu waje
"Iyabo wani tunanine ya faWo mun. Kin tuno da wannan adda'ar ta karya sihiri wadda na baki akayi yima Gwadabe mai ganyen magarya? To yau ba sai gobe ba kiyi" Idanuna na lumshe tare da yin hamdala ga Allah. Na mance da wannan maganin karya sihirin in banda yanzu da Uwani ta faWamun. Ai babu wata wata na aiki BaWWo ta Webo mun ganyen magarya a Wakina guda bakwai, ta kawo mun ruwa a bokiti na tottofa duk ayoyin ban mance komai ba. Na adana bokitin anan Wakin.
Uwani wallahi na sha'afa da wannan magani na karya sihiri, daga yanzu in Allah yaso ya yarda bazan sake rabuwa dashi ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga wanka da sha, tunda jarabawar gidannan ta kishiya mai asirice."
"Wannan shi ake kira nama ya dahi romo Wanye. Uwar miji a gidan auren fari ta hanaki sa?at. Wannan gidan kuma kishiya na neman rayuwarki. Ga kaya duk na siyo miki komai tashin hankali ya hanamu maganar kayan ma" Dariya nayi mata nace.
Ke dai bari ana takai wa yake ta kaya? Bari inje in samu in watsa ruwa me gidan yana hanya. Ga kiraye_kirayen sallar magriba anayi."
A Wakin Yafendo nayi Sallah, kana na fito na raba abinci, ina kan rabawa Yusufu yazo karSa musu na zuba musu nasu da nasu Dada.
"Adda ance in faWa muku Cubu bata da lafiya tana kwance a gida" Da sauri na Wago na kalleshi.
Meke damunta Yusufu?" Yace.
"Ban sani ba dai, amman ance ciwon sosai ne" kwanukan abincin na mi?a mishi.
Allah ya bata lafiya, gobe zanje in dubata. Ku kara ha?uri kunji ko Yusufu? Kaine babban kanka a yanzu kayi ?o?arin kulawa da kan ka. Duk abinda kuke bu?ata kazo ka sanar mun kaji ko?"
"To Adda, bari in tafi sai da safe" Yai mun sallama ya tafi. Ina fitowa Yaya Hamma na shigowa. Da sauri na ?arasa na karSi ledar hannunshi nayi mishi barka da dawowa. Daga Wakin Yafendo kai tsaye masallaci ya wuce. Duk muna tsakar gida kowa na sha'anin gabanshi. Sai da naga wucewar Yaya Hamma ya nufi Wakina na bishi Wauke da tiren abinci.
Saida na jima ina addu'a kafin nasa kai na shiga Wakin. Wannan tashin tsigar jikin dai saida naji, kuma sai inji anyi tsaye a kaina.
Shiru nazo na samu yaya Hamma ba dai yadda na saba ganinshi ba, kamar akwai damuwa a fuskarshi.
Yaya Hamma lafiya kuwa na ganka a cikin damuwa?" Ajjiyar zuchiya ya sauke ya dubeni yana dariyar ya?e.
"Babu komai halin rayuwane, yau da gobe kinsan sai Allah. Ya jikin naki, kunje wajen maganin?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Munje harda Uwani ma, da rana sai gata tazo" Ya yi dariya yace.
"Uwani ?awar amana kenan. Allah sarki. To yaya kuka yi da mai maganin?"
Na labarta mishi yadda muka yi, yana saurare yana cin abincinshi. Abincin loma biyu yayo ya ajjiye. Furarma kurSa biyu yayi kawai ya rufeta. Ni gabaki Waya na kasa gane mishi. Na tambayeshi yace babu komai. Bana son in matsa mishi dole in barshi, sai dai in naga damuwar tafi haka yawa dole in kuma tambayarshi.
"Zanje wajen BaWejo ba daWewa zanyi ba. Kema nasan Walibanki suna tsakar gida suna jiranki."
Tare muka fito, shi yayi waje ni kuma na ?arasa wajen Walibaina mu kai karatun dai babu armashi yanayin yadda naga Yaya Hamma zahiri a cikin damuwa yake. Bamu kai lokacin tashi ba na sallamesu, na faWa musu na kawo kayayyakin mata gobe kowacce ta kullo kudinta zan buWe haja. Suna cikin murna Yaya Hamma yazo ya wuce mu. Da idanu na bishi jikinshi duk a sanyaye ba laka. Jikina a mace nabi bayanshi a kwance naje na sameshi yana kallon sama. ?ur na ?ura mushi idanu ina nazarinshi.
Yaya Hamma dan Allah menene matsalarka ya kamata ka sanar dani damuwarka karka sani a wata sabuwar damuwar" Tunda nake magana yake kallona, hannayenshi ya mi?o mun halamun inje. Banyi musuba nabi umarninshi.
"Babu komai Jabu. Ki dena damun kanki bana jin daWin jikin nawane yau shiyasa tun Wazu a wajen aiki nake jina wani iri. Magani naje BaWejo ya bani nasha." Nan na shiga aikin yi mishi sannu. Wannan dare ya bamu wuya sosai dan har ji nayi kamar ana kiran sunana. Sassafe na yi amfani da wannan tofi, na sha na shafe jikina dashi tas. Abun da yafi komai bani mamaki a madadin Yaya Hamma ya tafi wajen aiki sai kawai na ganshi ya koro shanu ina du?e ina wanke kayan yaranshi da nashi. Tsayawa yayi suka gaisa faram_faram da Uwani ya dubeni da sandarshi a wuya yace.
"Ni zan tafi kiwo ki mun addu'a Murmushi nayi nace.
Ubangiji Allah ya kareka da kai da shanun a shiga jeji lafiya a fito lafiya" Kallona naga yanata yi, ni dai saina tsinci gabana da faWuwa. Harya fice a gidan na wanke hannuna na bishi.
Uwani ina zuwa"
Ina fita na sameshi a ?ofar gida yayi shiru yana kallon shanun, suma duk sun tsaya suna jiran shugabansu ya kirasu su soma tafiya.
Yaya Hamma yau baka da aikine zaka tafi kiwo?" ?agowa yayi ya kalleni. A madadin ya bani amsar tambayata sai yace dani.
"Ina sonki ina ?aunarki duk runtsi. Wannan halin lalurar da kike ciki yana tayar mun da hankali tunda a gidana kika samu wannan lalura, ga rasa idanunki da kika yi sanadiyyar dukan da ni Hamma nayi miki kaicona, ina tsoron ranar da zaki gaji da wannan auren ki nemi barin rayuwata Jabu, ina tsoro da fargabar wannan rana. Akwai wani mai magani da aka kwatanta mun in an gwada na malamin da kika je wajenshi baiyi ba, zan Waukeki in Kai ki can wajen wancan. Kiyi ha?uri Jabu, kinsan dai ina sonki kuma lalurar ta dameni ko?" Ga murmushi a fuskata ga hawaye inayi. Ina bala'in son Yaya Hamma ku kunsan komai, kuma duk sanadiyyar aurenshi ne nake samun wannan matsalolin, inajin auren ya fice a raina, inajin ?auyen ma ya isheni ?arfin sonshi da nake yi ke ri?e dani a ?auyen da ?arfin adda'a. Amman a kullum sai in dinga ji kamar in zunduma ihu ko in fice a guje. Da zaran naji hakan ya bijiromun sai inta karanta la'ilaha'illah anta subhanaka inni kuntu minal zalumin, hasbunallahu wa'ni'imal wakil, la haula wala ?uuwata illabillah. Sai inji dama dama.
Duk rintsi ina tare dakai Yaya Hamma. Bana fatan zuwan ranar da zan gujeka kasa a ranka zamu kasance har izuwa ?arshen rayuwarmu. Soyayya ba ?arya bace ina maka son so domin Allah ka yarda dani ka dena fargabar zuwan ranar da zan gaji da aurenka. Babu wannan ranar, bakasan girman matsayinka a zuchiyata bane."
Murmushi yayi mun, nima na mayar mishi da murmushin ina share hawayena.
"Nagode Jabu yanzu kin ?aramun kuzari, nutsuwata ta dawo jikina ni zan tafi kiwo"
To Allah ya tsare mun kai ya kareka. Inaso inna gama aikace_aikace zani gidan Cubu ance bata jin daWin jikinta"
"Assha to Shikenan sai kin dawo, kya gaisheta"
Da haka mu kai sallama na koma cikin gidan. ?an tsurko sai kallona suke yi, ni ko bansan ma suna yi ba. Nazo na tarar Uwani ta gama wankin Wauraya take yi. Tare mu kai shanya muka je Wakin Yafendo muka karya.
"Jabu kwanannan ina lure dake bakya komawa Waki har sai wannan yaron ya dawo ko ?arfe nawa zai kai. Ga rama kinata yi, inna tambayeki Jabu sai kice babu komai. Amman ni ko a fuskarki inna kalla sai inga damuwa ?arara. Ki sanar dani abinda ke damunki Jabu, ni Mamanku ce baki da wacce zaki sanar ma matsalarki daya wuce ni, ko dai rasa idanunki guda da kika yi ne kika saka abun a zuchiyarki yake ta nu?ur?usarki? Ki sani bawa baya wuce ?addarar da Allah ya ?adarto mishi. Kuma har gobe bamu cire rai ba anata neman magani in da rabo sai kiga idon ya dawo kinci gaba da gani dashi.
Murmushi nayi kamar yadda na saba, kaina na ?asa gudun karta gane ?arya nayi mata nace.
Babu komai Yafendo. Wannan ramar ta canjin yanayi ne kawai, sai Wan zazzaSi dake damuna a tsaitsaye kuma ina shan magani. Rashin shiga Waki zafine kawai yayi yawa dake a cikin zafin muke.
Sai naga tana murna ?ila tana tunanin ko ciki ne dani. Au ai kuwa makon jiya ya kamata inyi jinin al'ada kuwa amman banyi ba. Na faWa a raina"
"To masha Allah. Muga hannunki " Saina mi?a mata, ta duba tafin hannuna sai tayi dariya tace.
"Sai ki dinga yin komai a hankali. Girkinma ki dena yi BaWWo in tayi ta zuba miki, ke dai kiji da kanki, wannan yaron abinci ba damunshi yayi ba dama" Duk sai kunya ta lulluSe na fahimci dai Yafendo taga ciki ne dani. Sai naji wani farin ciki marar musaltuwa nake jina kamar wannan cikin shine cikin fari. Allah ya bani mai albarka, wanda zasu ji tausayina. A nan Yafendo ta fita ta barmu anyi haihuwa a ma?ota zata shigar musu barka. Na sanar mata zamu shiga muma gidan barkan, daga nan kuma zamu je gidan matar BaWejo.
"Ke baki san ma kina da ciki ba? Ni ko kinga ina ganinki ki kai mun kama da masu sabon ciki sabida naga kinyi haske. Amman da banji kince kina da cikin ba sai nake ganin ?ila sabida ramar da kika yine yasa kika yi fari. Nifa na mance ban faWa miki ba Gwadabe yaje gidan Hajiyarmu nema na fa"
Take gabana ya tattake ya faWi, zuchiyata ta tsinke jin an ambaci Gwadabe. Na yi jim ina tuno Gwadabe na, da irin rayuwar da muka gudanar duniya kenan. A duniya banyi tunanin ko a mafarki aurena da Gwadabe zai ?are ba. Bayan ya ?aren banyi zato ko tsammanin zan so wani Wa namiji rabin yadda nake son Gwadabe ba. Ashe ba haka bane so da ?aunar Yaya Hamma a zuchiyata ya dakushe tauraruwar Gwadabe a zuchiyata ta yanda ba'a iya hango ?yallinta ko mis?ala zarratan. Sai dai ina gani girma Gwadabe fiye da kowa, ina girmama ?o?arinshi a kaina. Yarana suka faWo mun ai sai hawaye."
"Au harda kuka Iyabo dan kawai na ambaci sunan tsohon mijinki?"
Gwadabe yafi ?arfin kawai Uwani kema kin sani. Kar kiyi tunanin da SirSishin son Gwadabe a zuchiyata alhalin da aure a kaina. Wallahi ko Waya, kuma nasan yin hakan laifine. Sunanshi da kika ambatane ya tuno mun da irin zaman da muka yi. Kukan da nayi kuma yarana na tuno kawai. Neman me Gwadabe yake miki, neman jin labarin inda nake ko? Gwadabe manya. Ina mishi adda'ar Allah yasa yana cikin aminci tare da yarana, ina mishi fatan samun macen da zata soshi fiye dani "
"Kamar kuwa kin sani. Har lambata yaso karSa Hajiya ta hana tana gudun kar Hafizu ya zargi wani abun. Kinsan tunda na soma kasuwanci Hafizu ya soma mun ba?in ciki, da yaga maza sai ya koresu a shagona. Na kulle gidan na koma gida satina daya yaita sintiri kinsan ba zuchiya gareshi ba, ga talauci na damunshi a gidan nawane yake samun abinci me kyau ya kwanta a lallausan zanin gado. Nifa Allah auren Hafizu ya fita raina. Kuma a yanzu haka ciki gareni, amman inaga ko wata Waya baiyi ba ma To Hajiya dai ta faWa mishi kina aure a garin da mahaifiyarki take. To sai dai tace ta mance bata tambayeshi yayi aure ko baiyi ba. Ta dai tambayi yaran yace suna cikin aminci sunata karatu"
Allah sarki Gwadabe nagode sosai. Inason ganin ?a?ana in sha Allah inna shigo Kano zan Waukeki mu shiga takai ko tsirenine Babala sai dai tayi"
"A'a ki rufa ma kanki asiri. Mijinki kishinshi da yawa kiyi zamanki ni zanje in dubo miki su da izinin Allah. In kuma sun girma babu mamaki Gwadabe ya dinga kawo miki su su kwana biyu. Amman ki samu matsalolin da kike ciki su warware. Wato Iyabo idon naki ya mutu da guda Waya kike gani? Allah mai iko mata muna ganin jarabawa iri da kala a gidajen aure, sai dai muce Allah ya bamu mafita. Tashi mu je mu dubo Cubu, daga nan muje gidan Dada ko?"
Sai da mu kai wanka, Uwani ta shiga Waki ta Wakko mun kaya nasa. Mu ka je Wakin BaWWo ta tayani muka buWe dila sabida ta cika ma BaWWo Waki, inaso in raga mu kai gidan Dada. Kayane gangariya na yara, mis dana jarirai masu kyau. Na jariran muka ware waje guda basu da yawa sai kawai nace ni da uwani mu raba tunda cikine damu.
"Aa ni na tara kayan jira jirai da yawa kin mance na saida dilar kayan yara? Ki ajjiye dai zasu miki amfani, tunda basu da yawa sai kawai ki Soyesu kinga in aka baki kuWin kya yi wani abun dasu."
Muka ware kayan kashi kashi. Muka Waubi ?unshi biyu wanda zamu tafi dashi gidan Dada na ware ma yaran Hamma, da yaran BaWWo, da yaran Amaduyal, Safiya ma na Waukarma yaronta guda Waya, matar BaWejo ma haka. Me jego da zamu shiga mata barka ma zanzo in duba mata kala Waya ranar suna in bata dan muna mutunci sosai ta kanyo zuwa na musamman wajena mu yi hira duk ranar da bata je tallar Nono ba.
Da muka fita gidan Dada muka soma zuwa sabida kaya da muka doro a ka ni da Uwani ni?i_ni?i muma muka saje da matan ruga. Daga gidan Dada ne bayan mun yi azahar sai muka tafi, na ba Dada Wari biyar nace ta yi musu girki ga yaran Jatau ma suna gidan suna wasa.
Da Sallama muka shiga gidan Cubu. Kishiyoyinta suna tsakar gida ko wacce na aikin gabanta. Gidan a share yake ?al suna da tsafta sosai ko bokatan gidansu babu kazanta a jikinsu labulayen bukkokinsu kuwa tas'tas haka jikkunansu ma tas.
"Sannunku Jabu anzo duba marar lafiya kenan?" Cewar kishiyar Cubu wacce acewarsu ita akaima kishiya tunda kafin zuwan Cubu itace Amarya, mata ta uku kenan. Na fahimci kamar tafi sauran guzumayen sau?i dansu sunci sun ?oshi suna da manyan yara gaisuwar arziki basa amsawa ni shi yasa ko kallonsu banyi ba. Na amsa ma kishiyar Cubu da cewar.
Wallahi kuwa nace dai bari inzo in dubata. Ina wuninku?"
In kun tanka sun tanka mu dai muka shige bukkar Cubu tana kwance ba yadda take duk ta bushe ta komaWe, ga zafi amman tana ?unshe a Waki tana fifita. Ganinmu ne ma yasa taji daWi.
Cubu kina zaune ke kaWai a wannan zafin ga matan gida a waje kowa na shan iska ba zaki fita rumfarki ki sha iska ba?" Cikin rawar murya tace.
"Adda inna fita sai suita zubar da habaici suna zagina wai Dadana ma ta?i zaman aure da girmanta amman aurenta ya mutu, mu bamu da tarbiyya muna ma kishiyoyin Dada rashin kunya. Dake kishiyata ta biyun ?awar Baba Dije ce, ko Wazu Baba Dije tazo wajenta. To Adda sai suita azabtar dani, kuma ranar girkina babu wanda yake taimakamun, ko da bani da lafiyannan basu Wauke mun komai ba, kuma ina jin ?aurin kara zanta hararwa"
?uri muka zuba mata ido ni da Uwani. Kafin muyi magana sai ga kishiyarta da nono cikin ?warya yaji sikari da dambu ta ajjiye mana.
Cubu har wannan kishiyar taki da naga kamar tafi manyan kirki bata taimaka miki?" Sai Cubu ta Wanyi murmushin da yafi kuka ciwo.
"Adda wannan matar muguwar makirace tunda nazo gidannan take ?ullamun makirci a wajen mai gidan. Bata so taga ya ambaci ko sunana" Uwani tace.
"Amman yaya tsakaninki dashi kuna zaune lafiya baya cutar dake?" Cikin kunya tace.
"Baya cutata, yana bani ha?uri kullum akan halayen matanshi shima sunfi ?arfinshi ne. Kuma yana kawo mun nama da lemun kwalba a Soye, shi kaWai nake iya ci"
Ajjiyar zuchiya muka sauke dukkanmu. Uwani tace.
"Komai zai zo miki da sau?i tunda mai gidan baki da matsala dashi. Shawarata anan shine ki zage ki ?waci ?ancinki babu wanda zaizo ya ?watar miki ?anci. Karki bari habaicinsu ya hanaki fita ki wataya, yadda kowa yake a zube a tsakar gida yana shan iska kema ki dinga fita. Yanzu lallaSa ki fita mu gyaggyara miki Wakin naga duk tarkace, in kin samu lafiya ki ro?i mijinki ya saki a makarantar dare da Iyabo take koyarwa kema ki samu ilimi."
A darare Cubu ta fita, kai kawai na girgiza ina mamakin wannan rayuwa. Tas muka gyare mata Wakin nata kayan wankinta Uwani ta haWa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login