Showing 51001 words to 54000 words out of 270738 words

Chapter 18 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

dani taji amman ta ?i ya" Yaya Hamma ya dubi wannan matashin, ya dubi Daso wacce ta turSune fuskarta kamar bata dariya.
"To jeka zata zo yanzu. Kuma ni Hamma na baka damar zuwa zance wajen Daso Manga daga yau kuma yanzu. Daso tashi kije Manga zai yi magana dake" Nasan ganin rashin wasa gami da murtukewar fuskane yasa ta bishi ba dan ranta ya so hakan ba. Tafiyarta ke da wuya Yaya Hamma ya ce.
"Bani labarin abinda yake damun zuchiyarki. Nayi miki al?awarin magance miki matsalar duk girmanta"
A'a Yaya Hamma babu komai. Ni dai inaso gobe zan je garin Kano. Amman nayi maka al?awarin kwana biyu rak zanyi zan dawo." Da sauri ya kalleni har tsoron da yake son Soyewa ya kasa Soyuwa.
"Kano kuma, ba dai wajen tsohon mijinki kike son zuwa ba, ko ganin yaranki ba? Kinsan yin hakan a wannan halin da kike ciku ka iya fama miki ciwon dake zuchiyarki" Da sauri na katseshi da cewa.
Ko Waya ba abinda zai kaini Kano ba kenan. Akwai wani shiri da nake son in yi ne a can Kanon. In abun ya tabbata kaine mutum na biyu da zan faWa ma bayan Daso" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Au ashe Daso ta fini matsayi a wajenki? Sai ta sani kafin ma in sani ko. Nagode" Yanda ya turSune ?ar kyakkyawar fuskarshi sai ya bani dariya ainun.
Ba haka nake nufi ba. Sabida ita Wakunmu Waya da'itane. Amman kana da matsayi a wajena gaya. Ko tafiyar nan da zanyi gobe babu wanda na sanarma sai kai. Sai mun koma gida zan sanarma da Yafendo" DaWi yaji sosai, sai kuma naga damuwa ta maye gurbin daWin.
"Allah yasa ba ?auyenmu bane ya isheki kike son komawa maraya ba, sai da muka sha?u dake kike son ki gudu ki barmu da kewa." Daso ce ta dawo ta zauna jagwab a gefena tana rishin kuka.
"Ni Yaya Hamma bana son Manga. Bazan iya rayuwar aure da abokin ChubaWo ba, gani zanyi kamar naci amanar ChubaWo ne. Gashi kai kace ka bashi izinin zuwa zance, kuma kab garinnan waye baisan zafin kishin matar Manga ba. Ni ban shirya jefa rayuwata a cikin haWari ba gaskiya " Dubanta yayi ranshi a bace, ko me ya tuna oho sai ya shiga aikin rarrashinta gami da yi mata nasiha. Mijintane dai ta rasashi har abada, ya zame mata dole yin sabon aure ko ba dan sha'awa ba ko dan tsira da mutunci. Ya Waura da cewa.
"Kuma kinsan Baba ba zuba ido zaiyi ya barki kita zama a gabanshi babu aure ba ko. Lokacin da zai matsa miki da fito da miji nake jiye miki, dan in baki fitarba al'ada zata haWaki aure da wani Wan uwanki ko kina son hakan, ko bakya so. Ni abinda nake jiye miki kenan. Sannan Manga kab Rugar nan ansan mutumin kirki ne, gashi da yawan shanu, kuma jarumine sosai. Ko wacce bafulatana burinta auren jarumin namiji." Zaman dandalin dai haka muka ?areshi babu armashi, Yaya Hamma ya mayar damu gida. Muna shiga a daren na sanar ma Yafendo inaso zanje Kano in Allah ya kaimu gobe, kwana biyu zanyi. Sai da ta Wanyi jim kamar ba zata yarda ba, kamar tana son tambayata Allah ya soni bata tambayeni ba, sai cewa tayi dani.
"Allah ya kaimu goben cikin rayayyu, sai ki shirya da wuri tafiyace mai nisan gaske" Da tunanin tafiyar na kwana a raina harma da mafarkin wai naje amman ban samu Uwani ba sai Hafizu mijinta.
Washe gari tun asussuba nayi wanka. Ina yin sallah na fito da ?ar jakata ta hannu da kuWaWena a ciki. Kaya ko kala Waya ban Wauka ba, nayi musu sallama akan zan biya wajen Dada da BoWdo mu yi sallama. Daso ce ta fito domin yi mun rakiya. Muna fitowa muka ci karo da Yaya Hamma a zaune a bakin wata bishiyar darbejiya yana kallon ?ofar gida yaga yaushe zamu fito. Ba Daso ba ni kaina nayi mamakin ganinshi a wajen. Dan sai da nayi turus. Tasowa yayi ya nufo inda muke.
"Yaya Hamma kaine da sassafe haka a ?ofar gida, zaman me kake yi a wajen?" In ji Daso kenan. Dariya yayi mata kawai kafin yace.
"Tunda dai Allah ya ?addari ganawarmu ai shikenan. Babu gaisuwa sai tuhuma ko? Da fatan kun tashi lafiya" Muka amsa a tare, sannan mu ka gaisheshi cikin girmamawa. Gidansu Yaya hamma muka soma zuwa. A Wakin Yafendo muka zauna, a gurguje mu ka gaisa na sanar mata inaso zanje birni amman kwana biyu zanyi.
"To Allah ya dawo dake lafiya. Hamma sai ka kaita har tasha ka tabbatar motarsu ta tashi kafin ka dawo. Allah ya tsare. Hama da BoWWo suna garken shanu kuje ku samesu ko? Ke kuma Daso kizo in kin taso tallan Nono zamu yi magana muhimmiya dake" Kan Daso a sinne ta amsa da
"To Yafendo" A garken shanu muka yi sallama da Hama da BoWWo. Sai adda'a su ke yi miki, daga nan sai wajen Dada. Ni da Daso ne muka shiga, Yaya Hamma fur ya?i shiga yace Baffa faWane dashi bai fiye son ba?i suna shigar mishi gidanshi ba. Mu ma muna shiga ya taremu harda sanda kamar zai dokemu.
"Kai ku tsaya nan kar ku sake ko taku Waya a wajen" Ya faWa da fillanci, Daso ce ta fassaramun abinda yace. Wannan kalma daya faWa kamar ance Dada ta fito ta duba sai firit ta fito daga bukkarta. Su Cubu kuma da su Yusufu suna tsakar gidan, suna aikin dafa madara. Da sassarfa ta iso inda yake tsaye. Wallahi Waga sandar shi yayi kamar almara sai ya kwaWa mata a goshinta jini ya yayi tsartuwa har a hijabina" Cikin hargagi yake yi mata magana da fillanci. Hannunta ta dafe da goshinta ta yi saurin juyawa, na fahimci umarni ya bata. Yusufu da Cubu ne suka yi kanta Cubu ta riketa zuwa ?ofar bukkarta.
"Ku je Jabu. Zan dinga zuwa dubaki. Na mancene ban sanar miki ba ya kafa dokar kar ?afarki ta tako mishi gidanshi" Da yarbanci tayi mun Magana. Ajjiyar zuchiya na sauke ina hango irin yadda sandar ta sauka a goshinta, ba tare da wani babban daliliba, ko da dalili addini ya bada umarnin a daki mace har a zubar mata da jinine? Ko da ma suna da ?arancin ilimin addini, rayuwarsu a kiwo da tallar Nono take ?arewa. Ji nayi na sake jin ?arfin guiwar hukuncin dana yanke dan cire Dada a cikin wannan u?ubar. Hawayen daya zubomun nake shirin gogewa Baffa ya Waga sandarshi ya sauke mun a kafaWata, zafin ya ratsa dukkan ?asusuwan jikina kau,. Kafin in tantance tsakanin mamaki da tsoro naji Daso tayi ihu ta jani mun rufa waje a guje. A guje muka wuce Yaya Hamma. Sai biyo mu yayi da sauri yana tambayar ba'asin abinda ya haddasa gudun. Daso ce ta bashi labarin abinda muka tarar. Ni kam hawaye kawai nake sharewa ina kallon mayafina da jinin Dadana a jiki, sanadiyyar zuwa ganinta kawai aka zubar mata da jini.
"Jabu kiyi ha?uri. Mu kanmu mun rasa yanda zamu yi mu tsamo Dada daga cikin halin da take ciki a wannan gidan. Amman abinda nake so dake shine dan Allah ki taya ta da adda'a, kuma zan baki shawarar kada ki sake zuwar mishi gidanshi, Dada zata zo har inda kike ta dubaki. Kar hakan yasa in kika tafi ki ?i dawowa, hakan ka iya jefata a halin da yafi wanda take ciki yanzu. Zamanki tare damu zai iya kawo mata sau?i sosai, kece babba ke zaki dinga rarrashin ?annenki, kinga BoWWo kullum a cikin kuka da damuwar da Dada take ciki take." Ajjiyar zuchiya na sauke kawai nace.
Babu komai, nagode da shawara. Daso ku koma daga nan ni zan tafi"
"A'a ai kinji abinda Dadanmu tace dan haka har sai na tabbatar da fitar motarku a tasha. Daso ki koma gida ke" A wajen mu kai sallama da daso. Ni dai har muka gama wannan gwajab_gwajab Win fita zuwa gari hankalina baya ma tare dani. Wai duk haka Aure yake cike da ?alubale kowa da irin nashi? Oh ya Allah ka kawo mafita a zamantakewar aure, ya Allah ka ba ma mata mafita. Har muka shiga cikin babbar tashar Adamawa babu wanda yace da wani ?ala a tsakanin ni da Yaya Hamma, dukkanmu sai tubka da warwara kawai muke yi, tare da karanta wasi?ar jaki.
"Fullo Kano ne, ko Kaduna, ko Zaria ga motar HaWejiya?" Cewar ma'aikatan tashar da suka nufo kanmu har suna rige_ rige.
"Kano zata je, nawa ne kuWin motar?" Cewar Yaya Hamma, tare da cusa hannu a aljihunshi.
"Nera dubu da Wari biyu zata biya" KuWin ya zaro ya kirga ya basu, ni kuma ya mi?o mun dubu da Wari biyar. ?in karSa nayi, ya dubeni rai a Sace yace.
"In baki karSaba zaki barni cikin damuwa, da kokontan dawowarki rugar mu. Ni kuma dana tuna zaki iya ?in dawowa, ko zaman rugarmu ya isheki take sai inji fargaba ta dirarmun. Jiya Sarawon baccine ya Webeni shima cike da mafarkai akan tafiyar taki. Ungu kuWinnan ko tsaraba kya yi musu"
Nagode sosai Yaya Hamma, in sha Allah bazaan wuce kwana biyun ba. Kuma dan Allah ka je ka dubo Dada, ko a Soye ne ka kai mata magani, kai mata bayani kwana biyu zanyi" Yaya Hamma bai bar tasharnan ba har sai da ya ga fitar motarmu. Sai da motarmu ta yi nisa sosai na dena hango hannun Yaya Hamma a sama yana yi mun Adabo., ban dena waige ba har sai da na dena hango shudiyar rigarshi, Ajjiyar zuchiya na sauke na lumshe idanuna ina tunano yanda Baffa ya kabWama Dada sanda. Wannan dalilin ne yasa kullum in zanga Dada sai in ganta cikin rashin guzari da rashin walwala, kullum cike take da tunani. Ta haWu da azzalumin miji mai kafiya, tallar Nono ya cinye mata lafiyarta da kuzarinta. A shekarunta ya kamata ace tana zaune a nutse yaranta na hidinta mata, ba wai tai ta fita tallar nono, kuma mijinta na cin zarafinta harma da fitar mata da jini. Wallahi da Baffa zai iya amincewa in fanshi tallar Nonon Dada, da tuni na famsheta na zama ?ar tallar Nono kamar yadda ya zama al'adar matan fulani musamman mazauna rugage. Ya zame mun dole in yi duk abinda ya dace dan ganin na kawar ma da Dada ?wallar data daWe tana zuba a idanunta. Gaga_gaga haka mukaita cin hanya, azahar, la'asar sai dab magriba muka shiga garin Kano, a unguwa uku muka sauka, ina fitowa titi na samu Bus har ?ofar layinsu Uwani. Na ko yi sa'a tana gida, tana tsakar gida tana kwasar tuwo Hafizu kuma yana shanya kayan yara a igiya. Tana ganina ta sau marar hannunta ta mi?e a zabure.
"Iyabo kece haka afujajan?" Tana faWin haka na fashe mata da kuka a tsakar gidan kamar ?aramar yarinya.
"Uwani jata kuje ciki maza" Cewar Hafizu. Hannuna Uwani ta ja muka shiga ciki, wallahi na fi minti talatin ina kuka take zazzaSi mai azabar zafi ya rufeni. Uwani da Hafizu suka rufu a kaina suna ta rarrashina da ?yar na haWiye kukan nawa bakina na ambaton Allah. Ganin na Wan samu nutsuwane Hafizu ya fita ya bamu waje.
"Kawata lafiya kuwa kinga yanda ki kai ba?i kika rame kuwa? Gabaki Waya kin koma wata ?ar ?auye, meke faruwa haka?" Cikin shesshe?a nace.
Labarin da tsayi Uwani, amman bari in rama sallolina sai mu tattauna tunda abinda ya kawoni wajenki kenan" Ina gama faWar hakan na mi?e jiri na kwasheni na fito tsakar gidansu dan kama ruwa da alwala. Uwani kuma taci gaba da aikin tuwonta, ina kan yin alwala yaran Uwani suka shigo gidan da sallamarsu. Matar gidan buWar bakinta tace
"Wannan wacce iriyar rashin tarbiyyace zaku shigoma mutane gida da gudu, kalan ku zubar mun da miyar da ko kayan Wakin uwarku in an siyar bazai siya miyar ba?" Yaran su kai turus, ni dama nasan irin matsalolin da Uwani take fuskanta a gidannan shi yasa ban yi mamaki ba, gashi uwani ta kasance kamar zawayi wajen rashin ha?uri ai kuwa nan ta tanka.
"Maman Shamsu kenan. Ba?in cikin ki takashinki zai koma da izinin Allah. Ni Uwani nafi ?arfinki, kuma in mijinki yafi nawa mijin kuWi, ai ni na fiki more aure tunda mijina bai taSa zagin iyayena ba. Kuma bai taSa korata da watan azumin ramadana ba, dan haka ki iya bakin ki" A mugun zafafe Uwani tayi maganar cike da hargowa. Yaran na kaWa ciki dan gudun kar su kantamo kalmomin da suka shige shekarunsu. Da Uwani da maman Shamsu sun ci uwar sabada har sai da mazajensu suka dawo daga masallaci suka raba wannan ja'iba, dan wallahi na kasa ri?e Uwani sam, har zani Maman Shamsu ta fincike mata ya rage daga ita sai gwari na tsuma ( siket Win ciki). ?ayar matar gidance ta Waukoma Uwani zanin ta Waura. Baban Shamsu cikin son bin goyen matarshi ba tare da bin ba'asin abinda ya faru ba yace.
"A Wayan biyu ya kamata ko ku ku bar gidannan, ko kuma mu tashi mu bar muku gidan. Wannan bala'in yayi yawa dan watarana wannan jarababbiyar karyar matar taka zata iya illatamun mata'"
"Karya kace mata ?asimu? Uwani ba karya bace tunda bata le?en mazan mutane in sun shiga bayan gida. Uwani Iyabo ku shige ciki kar ku tanka musu" Shigewa mu ka yi mu ka barma
Hafizu faWan. Matan gida sai ihu suke yi. Nifa harna rama sallolina ba'a dena gwabza habaice_habaice ba. Wannan ta jefa ma wannan, waccan ta rama, Uwani na tsaye a bakin ?ofa ri?e da labule sai Sarin zance take ta faman yi. Yara kuma sai cin tuwonsu suke yi a yinwace."
Uwani dan Allah ki rabu da Maman Shamsu ki shigo mu tattauna matsaloli" labulen ta saki muka shige uwar Wakinta duk muka yada zango a kan katifa"
Wai Uwani me matarnan take nufi dake ne haka?"
"Sharri mana, ba?in ciki take yi mini. Jiya jiya fa na kamata tana barbaWa mun garin magani a ?ofar Wakina, kinga Wauki babu daWin da mu kaita yi kuwa? Mune har gidan mai unguwa fa. Amman kinga ta sake takaloni" Ajjiyar zuchiya na sauke . Labarin duk matsaloli na ba uwani, da ?udirina da dalilin zuwana wajenta"
"Lallai rayuwar mata cike take da ?alubale mai tarin yawa. Wata matsalarta uwar miji irinki, wata matsalar ta ?annen miji, wata jarabawarta ma?otane marasa ?aunarta irina. Wasu dangin mij, wasu matan ma?ota, wata ma abokin mijina, ko matar abokin mijinta sune matsalarta, banda kishiya da shegiya facala su ba'a lissafinsu ma. Na tausaya ma Dada aimun. Kuma ya kamata ku yaranta ku haWe kai lallai ku nema mata takaddarta. Iyabo amman ramar da kika yi da sauyawarki ta ban tsoro" Hawayena na share.
Uwani ?auyene fa sosai can inda na koma. Babu ruwan famfo, sai wata rijiya guda Waya jol anan ake Wiban ruwa, ba wutar lantarki, babu sabis Win waya, ba titi, amman suna da makaranta, sai dai al'ummar cikin ?auyen aikinsu kenan kiyo, matansu kuma tallar Nono, suna da ?arancin ilimin addini, ai dole ki ganni haka. Kuma jinya nayi magashiyyan sai an Waga sai an ?wantar"
Mun jima muna tattaunawa, sai da mu kai sallar isha mu ka ci abinci sannan Uwani ta zura mayafi muka nufi gidan Hajiya Salamatu.
"To naji bayaninku. Amman Uwani kin mata bayanin komai da komai dai ko?" Cewar Hajiya Salamatu tana hakimce taci gwala_gwalai kunne da wuya, da tsintsiyar hannu.
"E Hajiya na yi mata bayani. Sai dai itama bata da kuWi kamar dai ni. Amman Hajiya in muka je can za'a cire a kuWin aikinmu har mu gama biya. Mu ba ma daWewa zamu yi a can ba shekara uku ya ishemu, dan da ita Iyabo shekara biyu ma tace" Hajiya tayi dariya tare da girgiza kai.
MRS BUKHARI



3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundati
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm


NAMA YA DAHU
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

15
Kafin tace.
"Ba dai shekara biyu ba, dan a ?alla ba a ?asaru ba, zaku iya kaiwa shekara guda kuna biyan kuWin jirki da duk abinda aka kashe muku. Sai dai in babban gida kuka samu suke biyanku kuWi da kyau, amman in ba haka ba shekararnan sai kun yita. Babu rufa_rufa sai kun gama biyan kuWin jirgi zaku samu damar yin aikin hajji da umara baki Waya. Amman muddin kuka zama masu haza?a da kazar_kazar to gidan da za'a kaiku aiki zasu soku, kuma in dawowarku najeriya tayi, su hadoku da goma sha tara na arziki." A nan na fahimci Saudiyya zata turamu, sai naji hankalina ya ?ara kwantawa. Kafin mu baro gidannan mata da tsofaffi a ?alla mutane fin ishirin sai da suka shigo, duk akan batun tafiyar. Ni dai mun tsayar da magana akan gobe da safe in zo mu je hajj kam aimun fasfo kafin in koma garinmu, nan da wata Waya da kwana goma jirginmu zai Waga zuwa ?asa mai tsarki.
Muna tafe muna Wan tattaunawa har bus ta saukemu a unguwar su Uwani. Muna sauka muka ci karo da mijin Uwani yana zaune a wata majalisar maza ?an sa ido. Zumbur ya mi?e da ganinmu ya nufomu gadan_gadan.
"Ke Uwani daga ina kike?" Ya faWa a fusace. Tsaki uwani ta ja tace.
"Aikin banza aikin wofi, ka dai ji kunya ka kuma yar da zuchiyarka kare ya cinye. Maza majiya ?arfi masu zuchiya, ka gansu a titi suna aikin sufuri dan su rufa ma iyalinsu asiri. Banda kai Hafizu baka da aiki sai zaman majalisa, duk matar data wuce kuna ?arema surarta kallo, ka barni da buga_buga mata a layi duk sun rainani" A faWace take maganar tana yi tana kumfar baki. Shima zabura yayi ya ce.
"Duk macen da take fita dai ba da sanin mijinta ba mala'ikun Allah har taje ta dawo suna tsine mata. Shashasha kawai." Tsaki ta buga fuu ta wuce ta barmu a tsaye.
Hafizu ka ?ara ha?uri dan Allah. Dama har yanzu irin wannan zaman na rashin daraja kuke yi ma junanku? Ga yara sai sake girma da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login