Showing 141001 words to 144000 words out of 270738 words

Chapter 48 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

kika sani zubar da hawayen farin ciki. Rayuwarki zata yi albarka. Allah ya ji?an Adetoye da rahama."
Ameen Dada nagode sosai mu shiga ga Wakinki nan. Wancan nasu Cubu ne, sai na su Yusufu gashi can." ?akin muka shiga daga gado sai wata kujera doguwa guda Waya, sai kafet malale a ?asan Wakin da labule, sai akwatin kayanta guda Waya. Kayan ciki sababbi nasa aka Winko mata da hijabinta biyu da takalma biyu sai dadduma. Kan kace me labarin sallamomu ya kareWe ?auyen nan mata suka cika gidan ana ma Dada Yaya jiki ana mata barka da arziki.
To nima anan nake cewa mu tara gobe in Allah ya kaimu....
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanya????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? r tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801


Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667

*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE


BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

LITTAFI NA UKU (2)



Ni da uwani kuma muna madafa na hura kara ina kiciniyar Waura girki ta dubeni tace.
"Iyabo yanzu kema da karar zaki dinga girki in kunyi auren ko? Ni wallahi Iyabo ba wai ?in Hamma nake yi ba, ba kuma ?yamatar rayuwarsu nake yi ba.
Ke nake jiye ma, kece baki saba da irin wannan rayuwarba, su fes suke jin kansu ba wata matsala, ta ina ke zaki soma Iyabo?"
Murmushi nayi mata ko a jikina nace.
Nifa babbar nasara shine in zama mallakin Hamma kawai, kuma inason in zauna da Dada, aurenta fa ya mutu faWa miki ne banyi ba uwani. Uwani zuchiyata tayi nisa da sonshi, idanuna ya rufe bana hango komai. Bini da adda'a ?awata kawai, ki dena damun kanki. Da birni da ?auye duk rayuwar Wayace, ita mace kwanciyar hankali take bu?ata a gidan aure ba birni ko ?auyeba, sannan inason in koya ma ?annena yadda zasu bautama Allah. Hatta Dada daga iya alwalarta akwai gyara ina ga karatun Sallah kuma."
Dariya tayi kafin tayi Magana kawai sai muka jiyo guWar su BoWWo da su Cubu, harda Yafendo Jabu. Kuma wajenmu suke nufowa. Suna shigowa BaWWo tace.
"Adda yau dai kin zama matar Yaya Hamma an Waura aurenku babu jimawa" Farin cikine, a'a ruWewace sai kawai naji gudawa ta kamani. Kafin in mi?e sai Yafendona tace.
"Munyi farin ciki da wannan Aure. Muna fatan mutuwace zata rabaku. Adda Daso sai kukan farin ciki take yi"
Ni dai da jin wannan labarin saida nayi gudawa sau biyar cikin awa guda.
Ina cikin wannan zuruftu saiga Hamma da abokanshi biyu sun kutso kai gidan. Nayi maza na shige kitchen dan yafi kusa dani. Idanu na lumshe inajin wani farin ciki na cikar buri na lulluSeni. Amman sun sammaceni, babu shakka wannan shine dalilin zuwansu Baffa Musa da safe asibiti, kuma shine dalilin Dada na cewa za'ayita ta ?are, ashe tana nufin auren za'a Waura kowa ya huta. Uwani ce ta dafani nayi saurin buWe idanuna.
Sun tafine uwani?" Na tambayeta ina dariya. Itama dariyar take yi tace dani.
"Sun tafi, dake da Hamma bansan wanda yafi wani farin ciki ba. Bakiga bakinshi ba ya?i rufuwa sam. Ina miki fatan alkhairi Allah yasa ki samu farin ciki Worarre na zubar da makaman ya?ina iyabo, Allah ya ?adarto miki rayuwa a rugga"
Ameen Uwani ko ke fa. Yanzu dai me ake ciki dangane da kayan Waki? Ni a kano naso sayen gado da kayan kujeruna gaskiya, to yanzu ba lallai lokaci ya bamu damar hakan ba"
BaWWo ce ta shigo tace.
"Adda kizo Baffa na son magana dake"
Uwani ki dinga duba girkinnan kafin inzo'
Nasa kai na shiga Wakin Dada da sallama. Dukka ?an uwan Dada suna ciki. Yafendo KaSoji tace.
"Tawo ki zauna a kusa dani ?ata"
Cike da kunya na ?arasa na zauna a gefen ?afarta. Baffa yace dani.
"Ungo nan Jabu sadakinkine nera dubu biyar. ?azu aka Waura aurenki a ?ofar gidan mai gari ke da Hamma. Amman kasancewar auren yazo babu wani shiri, inda zai saki ma bai gina ba tukunna zaki zauna a gida kamar na sati biyu kafinnan ya gama ginin ya kuma gama haWa lefe sai ki tare"
Hannu nasa na amshi sadakin. Na kuma ji daWi sosai da akace mun sai nanda sati biyu zan tare. Har zan shiga Kano inje inyi gyaran jiki in kuma siyi kayan Waki irin wanda raina yake so" Yafendo KaSoji tace.
"A'a Yaya sati biyu yayi yawa. Ginin yau zasu soma da abokanshi zasu iya gamawa yau. A bar dai tariyar rana ita yau zaifi" Dada tace.
"Allah ya nuna mana rana ita yau Win. Amman ita Jabu gobe zata koma kano kamar yadda na sanar daku, acan za'aje a Wakko Amarya a wajen dangin mahaifinta suna da hakki. Da ace lafiya nake da ni da kaina zan kaita inyi ma Toyosi Win bayani a nitse dan gudun kar suga kamar anyi musu fin ?arfine." Baffa Musa yace.
"Hakanma yayi, babu damuwa ku zaku tsara yadda tafiya Wakko Amaryar zai kaya. Allah ya sanya alkhairi. Jabu zaki iya tafiya sai ki kwana da shirin tafiya kanon gobe. Duk abinda zaki kintsa saiki kintsa rana itayau za'a zo Waukar taki, ki sanar musu suma acan.
To Baffa "
Iyakar abinda na iya cewa kenan. Na fita na samu Uwani na labarta mata duk yadda mukayi.
Haka dai muka wuni tarbar ba?i masu zuwa dubiya. Su Yusufu duk suna gidan sun shige Wakinsu da abokansu. Sai da daddare Hamma ya samu zuwa muna tsakar gida mun gama cin abinci munyi sallar isha anata hira ina jin daWin kasancewata tare da ?annena, sai gashi ya shigo da sallamarshi.
"Ango kasha ?amshi lale da zuwa"
Cewar Uwani kenan tana tsokanarshi. Hannunshi ri?e da ledoji biyu. Sai ya mi?a ma Cubu leda Waya yace ta kaima Dada. ?ayar kuma yace ta Uwani ce, na karSa na mi?a mata.
Watsewa sukayi suka barmu mu mu biyu a tsakar gidan. Ni ina kan tabarma shi kuma yana kan jarkar ruwa yana fuskantata.
Ina wuni Yaya Hamma?
Na faWa a sanyaye da sabuwar muryar da baisan na mallaketaba. Wata iriyar muryace mai kama da busar sarewa." Sai da ya sauke ajjiyar zuchiya nannauya kana ya dubeni muka haWa idanu sai yace.
"FaWa ya ?are Hamma yayi nasarar samun Jabu na kayar da mutan birni."
Dariya ya bani sosai.
Yaya Hamma kenan. To Allah ya bamu zaman lafiya. Allah ya baka ikon yi mana adalci a tsakaninmu"
"Ameen nagode da wannan adda'ar taki. Sai batun tarewa Dada tace an tsayar da maganar tarewa sati me zuwa. Kuma a Kano za'aje a dakkoki ko?"
Kai na gyaWa mishi. Sai yace.
"Maganar kayan lefe zan baki kuWinne ki siyo abinda kikeso a Kano harda fantimoti ko yaya kike ganin za'ayi?"
Duk yadda kayi daidaine na baka wu?a da nama"
Kai ya girgiza yace.
"Ni kinga bansan kalaba. Sannan Hama ma ba sanin kala tayi ba bare in bata ta haWo komai"
To ka tuntuSi su Dada ko su zasu haWa ni basai na haWa lefe ba"
"To Shikenan Amarya yadda kikace haka za'ayi. Zan tuntuSi matar ogana na birni naga kamar kayayyaki take siyarwa in yaso sai in bata ta haWamun duk abinda ya dace. Yanzu nawa kike bu?ata na gyare_gyarenku na Amaren birni?" Dariya nayi mishi. Shima dariyar yayi.
To kuWin gyaran jiki, sai kuWin ?unshi, da kuWin kayan fitar biki Shikenan abinda nake bu?ata"
Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu goma sha biyar Murtala _murtala ya mi?o mun, nasa hannu na karSa nasa musu albarka."
"Gobe zanzo in kai ku tasha, dama inason zan sai fenti a birni mun gama gina miki Wakinki. Duk da dai ban samu yadda nake so ba lamarin yazo mun babu shiri"
Zamu rabu kamar ba zamu rabu ba a wannan dare mai cike da ni'ima iska sai kaWawa take yi hadari na rugugi a sararin samaniya. Ganin an soma yayyafi yif_yif yasa ba dan rai ya so ba muka rabu da juna cike da shau?in junanmu.
Washe gari sassafe muka shirya tsab Yaya Hamma yazo ya kaimu tasha har sai da motarmu ta bar tasha suka tafi shi da aminanshi.
Bayan la'asar sakaliya muka shiga gida. Su Iya duk suna tsakar gida suna murnar haihuwar Bose muka tarar dasu. Nan murna ta zama bibbiyu.
Sai da muka nutsa muka rama sallolin da aka boyomu, Uwani tai ma Iyaa bayanin duk abinda ke a kwai.
Da jin wannan bayani sai Iyaa ta mi?e tsaye tana buga cinyoyinta tana faWin.
"Mo ti pari mo ti pari ah ah ahh.. ( na gama yawo, na gama yawo) Iyabo aure a ?auye a wannan garin zaki zauna kiyi zaman aure? Kin kashe rayuwarki, kin kashe kanki"
Kafin kwabo Sai gasu Iyaa Beji da su Iyaa Kokodeen sun shigo. Bata sauya zane ba. Ita dasu duk kanwar ja ce, sukaita kwakwazo har sai da Alfa ya shigo shine ya tsawatar musu. Iyaa kuwa du hannuwanta aka ta Worasu tana jijjiga harda hawaye shaSe_shaSe tana ta ambaton
Ah ah ah...." Wanda indai kaji beyerabiya nata maimaita wannan kalma to fa abu yayi abu. Alfa ya tambayi Iyaa Kokodeen meke faruwa. Kafin tayi magana Iyaa Debisi ta soma magana da yare ta bashi labarin abinda Uwani tace mata. Jimm yayi sai halamun tsoro suka bayyana a fuskarshi muraratan.
"Je otito Iyabo?" ( Da gaske ne Iyabo) Ya tambayeni idanunshi kakkafe a kaina.
Beeni ( Eh)"
Itace kalmar dana furta a sanyaye. Shima jikinshine ya kuma mutuwa mus. Gwauron numfashi ya sauke yace.
"To Allah ya sanya alkhairi. Tunda rayuwar da kika zaSama kanki kenan mu bamu da abinda zamu ce dake. Toyosi kiyi ha?uri ki bita da adda'a a wannan karon kar ku juya mata baya."
Da ?yar ya rarrashi Iyaa ta ha?ura. Ni da Uwani dai duk mun takure, Uwani taso tafiya ma, amman ganin irin faWan da Iyaa ta dinga yi mun yasa dole muka kwana tare.
Washe gari ragowar samari da magidanta gidanmu duk labarin aurena ya ruskesu. Kowa sai jimantamun yake yi. Burodami Debisi kuwa kamar zai yi hauka da yazo gidan yaji labarin abinda ake ciki. ?asa zaman gidan yayi ya fice. Nan Iyaa ta sake saka Wambar faWa tana faWin.
"Ai duk Debisi ne ya ja wannan abun. Tunda tun farko dashi ya auri yarinyarnan da sai dai mutuwace zata rabasu. Gashi yanzu ta kashe rayuwarta a banza, wawuyar yarinya wadda batasan meke mata ciwo ba. Ko da yake Daso ce ta zuga ta shi yasa ta jayeta su je su sha wahalar tare"
Iyaa ta dinga jero zance babu arziki muka shirya tsab muka bar gidan. Da gidan Bose muka soma, sai muka nufi gidan Uwani data siya. Hafizu yana zaune a kan benci a ?ofar gidan sai gamu.
"A'ah Alaja Iyabo rakiyarce kuma har Kano? Lallai wannan ?awance naku da girma yake" Ya ?arashe yana dariya sai kace wanda yaga wawan zama. Uwani kuwa girar sama ta haWe data ?asa, ta buWe gidanta tayi shigewarta ta barmu muna gaisawa dashi.
A tsakar gida na sameta tana kiciniyar buWe ?ofar Waki.
"Taho ki soma ganin dilolin kayan. Da mun gama hidimar biki zan buWe dila amman nafi son in gyare shagona tsab."
Ta buWe Wakin muka shiga, ga dilolinan masha Allah, wani kan wani dukiya akwai daWi ganin dilolinnan sai ya sharemun ?uncin da su Iyaa suka dasamun a raina. ?akin uwani muka koma, Waki masha Allah har kayan kallo Uwani ta saka ga firjinta ?atoto.
Kinyi gyara gaskiya Uwani. Kuma gidan yayi kyau babu laifi"
"Wallahi kinga ga wani gida na jikin nawannan daga hannun hagu, shima da shago babbane dan yafi nawannan girma. Ni dai da zaki siya ko haya sai ki zuba Iyabo, ki Wan dinga karSar kuWinki, kuma ko babu komai kin ajjiye kadara. Gidan a hannun dillalin dana siya wannan gidan ta hanyarshi yake. Yana ta mun tayi gidanma akan in siya in haWe da nawa. Ni dai ki siya Iyabo. Ina da kuWin siya amman ke naima sha'awar gidan "
To Uwani naji shawararki zan siya babu matsala, dan dama shanu naso in siya ayimun kiwo. Ammam bazai gagaraba zan sai gidan"
Uwani bata ?yaleni ba har saida ta kaini ofishin dillalinta muka tsayar da magana harda rabin kuWi na ajjiye mishi mun tsaya akan gobe inzo da shaiduna insa hannu a takadda a mayar da sunan gida nawa a bani takadduna, in cika kuWi a bani Wan makulli.
Hakan kuwa akayi Burodami Kokodeen da Lekan sai Uwani su su kaimun shaida akayi aka gama komai aka bani takaddun gidana da Wan makulli.
?akuna shida ne falle falle, sai ban Waki da kitchen, da shago a waje kamar dai gidan Uwani.
Daga haka muka shiga sha'anin gyaran jiki, magungunan mata daga wajen Anty Ramlex, shiga kasuwa, kai dinki. Kafin dai sati guda duk abinda zan siya na siya na jibge a gida har dilolin kayana nasa mota ta Waukarmun ta kaimun gida. Na buWe jakar tsaraba naba duk wanda ya dace.
Ranar laraba sai ga mutanen Banyo da yamma sakaliya mota Waya duk mata, sai direba namiji.
Sun samu tarba ta girmamawa sosai dan ni banyi tunanin hakanba ma. Sun tawo harda akwatinsu mai taya guda biyu. Kayan ciki babu yabo babu fallasa ga bazawara kamata dai. Wasu a Wakin Iyaa Debisi suka kwana, wasu kuma a Wakin Iyaa Kokodeen suka kwana. Ni da Uwani muka kwanta a Wakin su Lekan.
Washe gari sassafe muka Wauki hanya. Motar da suka tawo da'ita Waukar Amarya muka shiga mu biyar. Ni da Uwani, sai Anty Ramata, da Iyaa Kokodeen. A gaban mota kuma Burodami Kokodeen ne sai direba. Motar kaya kuma aka lode kayayyakina hardasu dilar kayana aka rufe da tampol dan hadarine ba?i ?irin a garin motar kayan ta daWe da kama hanya ita kafin mu. Muka kama hanyar Adamawa. Tun kafin mu fita daga cikin garin Kano aka soma yayyafi sama_sama. Da muka soma shaga ?auyuka ruwan yanata ?aruwa, duk ?auyan da aka wuce ruwa akeyi sosai. Sai tafiyar ta zama me daWi babu zafin rana sam sai sanyi dake ratsawo ta ?asan motar. Su Iyaa Kokodeen tuni sukai baccinsu sai gwara kai suke yi. Idanu na lumshe inata tunani, tare da adda'ar Allah yasa kada Yaya Hamma ya bani kunya ya tozarta zumuncinmu.
Yanzu Shikenan rayuwata ta koma ?auye nima zan zama ba?auya kenan?
Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna wanda ni kaina bansan na meye ba.
Haka mukaita gudu har muka isa Adamawa ruwa akeyi sai tsurarun ?auyuka da basu wuce uku ba da muka wucesu ba'a ruwa. A Girai motocinnan suka tsaya gashi ruwa akeyi sosai. Haka dole muka fita daga cikin motar muka fake a ?asan wata bishiya mai yalwar ganye. Maza da mata duk muna fake mota ake jira. Munfi awa guda ana zabga ruwa daga bisani ruwan ya tsagaita mota ta tawo duk ta kwashemu. Kowa a takure yake sanyi ga jikewa da mukayi amman ba sosai ba. Hanyar tafi ta kullum muni, ko ina ruwa camSal a kwance, ga laka sai ri?e motar take yi a haka dai har muka iso masauki. Daga nan muka tari mashina suka shigar damu. Gidan Dada kai tsaye nace su wuce dani dan ina bu?atar in sake kayan jikina, ba a kai amarya a jike sharab ba. Dada da Yusufu ne kaWai a gidan tana ganin su Iyaa Kokodeen ta soma murna tana musu yare.
"Daso ciwo kikayi haka naga duk kin ?are sai wuya?"
Dada ta dubi Iyaa Kokodeen tace.
"Zauna tukunna manyan ba?i nayi farin ciki da ganinki. Yau gaku a garinmu."
Zazzaunawa sukayi Jikkunansu duk a mace. Sai jimantamun suke yi.
"Ni ina mamakin abinda Iyabo ta gani da har ta amince da rayuwar ?ungurmin ?auyen nan. Rayuwar ?auye a wajen Wan birni takota ina cutarwace. Jibi nisa da wuyar da muka shawo. Ohh ke kuma haka kikeson kaddararki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login