Showing 111001 words to 114000 words out of 270738 words

Chapter 38 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Kin kaini wata sabuwar duniya da ban, na gaisheki kuma na yaba da ?o?arinki, ya farantamun. Wani daWine ya lulluSe Hadiza irin daWin da ya kasa tsayawa iyakar zuchiyarta. Kallonta yake yi hankali a kwance. A zahirin gaskiya Iyabo ce ke mishi gizo a idanunshi, tare da tunano daren farkonsu, da irin romon soyayyar daya kwasa a jikin Iyabo. Gata mai ?iba jiki duk laushi da ?iba. Idanu ya lumshe kawai, ha?i?a bai taSa tunanin akwai abinda ka iya rabashi da Iyabo ba face mutuwa. Ashe ?addara tuni ta rubuta ?a?a ukune kacal a tsakaninsu. Domin kuwa yasan har abada aurenshi da Iyabo ya mutu bazai dawo ba. Tamkar yadda ba'a taSa mutuwa an dawo ba.
"Nace ba. Tunda matar abokinka sun tawo da yara. Me zai hana kawai su zauna ba sai ka sha wahalar zuwa Wakkosu daga baya ba?" Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Zamu tattauna dasu zuwa anjima inna samu kaina. Yanzu wanka nake so in yi, in fice dan yanzu zaki ga gidan ya kuma Winkewa da mata." Mi?ewa yayi ya soma shirin wanka. Hadiza ce ta zuba mishi ruwan wankan a bokitin ?arfe. Kafin ya fito ta ?arashe gyare_gyarenta. Yana fitowa yace.
"Zan shiga cikin gida. Sai zuwa dare zan shigo. Ki shirya zan haWaki da amaryarki." Fuskarta ya shafa yana murmushi, dan ya hango kishi kwance a idanun. Har ?ofar Waki ta rakashi, a madadin ya fita, kamar yadda yace da'ita. Sai ya faWa Wakin Amarya. Hadiza tayi murmushi kawai ta komawarta ciki.
Tana shirin shiga banWaki dan ta wanke. Sai ga Balaraba Wauke da tiren abincin kari.
"Amarya uwar gida kuma irin wannan Waukar wanka haka"
Murmushi Hadiza ta sake.
"Ke dai bari Balaraba. Tun Wazu nake jiran yara ma su shigo su samo mun gaushi a cikin gida, inason yin turaren wuta." Balaraba ta ajjiye tiran hannunta a gefe tace.
"Tunda zan sake dawowa kawo ma amaren gidan abinci. Bani kaskon ki yarinya in ciko miki da gaushi" Dariya Hadiza tayi, ta Wakko kaskonta mai murfi taba Balaraba ta fita. Ita kuma ta faWa banWaki ta wanke tas. Kamar an tsikareta ta faWa kitchen ta soma canja mishi fasali. A kitchen Win Balaraba ta sameta ta mi?a mata kaskon cike da gaushi.
Kafin kace me Hadiza ta bunke Wakinta da turaren wutan daya tashi kan amaren gidan, harma da ma?ota, wanda su kiya daga Najeriya a hannun Mrs Bukhari gidan ?amshi. ( Turarene mai tsada na isassun mata. Sau Waya zaki turara Wakin ki dashi amman zai kai sati yana ?amshi. In kika siya gidanki bai kai sati yana ?amshi ba. Ni Mrs Bukhari gidan ?amshi zan dawo miki da kuWinki) Shafa data jiyo wannan ?amshi na turaren wuta sai taji ta raina ?amshin turarukan wutanta da take tunanin zata ya?i matan Nijar dashi. Damma bata san daga asalin Wakin da yake fitowarba. Ji kake kawai ana wannan turare ba dai ?amshi ba.
Hadiza tana zaune tana shan farfesun rago sai ga Aminiyarta Luba ta shigo ri?e da hannun ?aramin yaronta, Wayan hannu ri?e da ?atuwar leda sha?e da kayayyakin Wa'a inji katsinawa, kayan mata inji Kanawa, maganin mata inji jasawa.
"Ashe wannan ?amshin daga Wakinnan yake fitowa Hadiza? A gaskiya ban taSa jin ?amshin turaren wuta irin wannan ba. Banga laifinki ba yanzu da kika nace ke sai kayan ?amshin MRS BUKHARI ba. Matar tasan aikinta. Amman dai ?ar maidugurice ko, wannan ?amshi ya gigitani" Dariya Hadiza tayi ta kamo hannun Luba.
"Zauna ?awata. In dai kayan Mrs Bukhari ne baki ji komai ba, tunda baki sha?i humrar matan aurenta ba" Zama tayi tana kallon Hadiza. Hannunta da Hadiza ta kama ta shinshina babu shiri ta lumshe idanunta, ?amshi mai ni'ima ta daki hancinta.
"Wannan humra kwai ?amshi Hadiza" Dariya Hadiza ta kuma sakawa tace.
"Kajita, ai humrorinta sunfi da nan. Wannan ?amshin turaren turara jikine mai ri?e fata kita ?amshin ?an kanuri.
Luba Mrs Bukhari Kanuri ce, kuma a kayanta babu ha'inci, shi yasa zaki ji kuWin kayanta ya bambanta gaskiya. Amman muddin kika siya zaki san yaci kuWinshi. Taso muje ciki in nuna miki humrorinta na jiki, dana gashi ki gani"
Ba shiri Luba ta biyo bayan Hadiza, harda sunkuto tiran kayan karin da Hadizan take yi. Gaban mudibi ta kaita.
"Kinga wannan humrar matan aurece, ko kishiyarki ba'aso ta sha?a domin humrace mai sirri" Zaro idanu Luba tayi.
"Kaddai kice mun ta asirice, yaushe kika zama haka Hadiza?" Hadiza ta dafa Luba.
"Bata asiri bace, ba,a yita da rubutu ba, ba'a yita da wasu surorin Qur'aniba, babu wani surkulle tattare da duk kayanta wallahi sai aiki. Domin ba da ka take haWa kayayyakinta ba. Sirrin itatuwan mallakar miji sai Kanuri tarihi yasan da hakan. Tasan me zata haWa da me ya bada kwanciyar hankali. ?amshi shi kaWai rahamane, kuma shi kaWai zai sa mai gidanki ya yarda dake. Kinga wannan kulaccam ce, wato man ?amshi me gyara fata tayi laushi tayi ?amshi. Ko zufa kika yi ?amshine zai dinga fita. Wannan humrorine masu sirrin ?amshi kin gansu. Wannan turaren turara Wakin kwanan Oga ne domin saukar masa da duk gajiyar daya Webo a waje, in ya fita kuma yaji bashi da wata nutsuwa data wuce ya ganshi a gidanshi. WaWannan turarukan wutane iri daban daban, kuma suna da lokutan kunnasu. Ga turaren gashi, ga kulaccam ta gashi, mai sa tsayin gashi, taushi, da ?amshin gaske. Ga turaren turara gashi, gana turara jiki. Wannan sunanshi gam. Turaren tsugunnone mai maida tsohuwa yarinya. Ga_ga_ga. Hadiza ta dinga jero mata bayani.
"Ya isa Hadiza yaushe zaki saka odar wasu kayan ni dai inaso da gaggawa, kuma zaki Wan samun dan Allah?"
"Kwantar da hankalinki zan sammiki. Oda kuma dama akwai kuWaWe a hannuna, ki kawo naki saimu tura mata kuWi ta nita, kayanmu zasu iso cikin aminci. Tana da kostomomi sosai a kasar Nijar sosai, kinsan ?an Nijar suna son kaya masu kyau da inganci. Tsadar abu in dai mai kyaune baya damun mu" Nan suka zauna zaman cin abinci kuma.
"Ga magungunan ki nan, tukuWinma an daka miki garinshi da dama, saiki dinga samun lafiyayyen Nono kina damawa ki sha. Gasu tsumi kala_kala harda maWi, akwai na matsi ma. Kinsan lamarin maza sai ka dage barinma ace kana da kishiya kuma budurwa. Sai fa ka dage sosai. A kwana bakwai da zaiyi a Sarayin Amarya kiyi ?o?arin tsuma kanki sosai. Kinga acan ya shiga sabuwar duniyane daban. Kema saiki sabunta baiwar da Allah yai miki. Ita mace tana son sabis lokaci zuwa lokaci inba haka ba, sai kiga injin Winta yayi tsatsa, shi kuma tsatsa kashe ?arfe yake yi duk kyansa, sai ana sabis ana zuba injin oyal."
Dariya suka saka dukkansu. A haka dai gidan ya Winke da jama'a. ?awayen Hadiza na makarantar da take koyarwa suma sai yau suka haWo kansu suka zo. Kuma suka tawo mata da goma sha taran arziki.
"Hadiza ya kamata ki shige gaba muje ki kaimu wajen amaryarki a matsayinki na Babba. Dan na sanki da Wan banzan kishi. Ya kamata ki watsar da zafin kishi ki bi hanyoyin dabaru na zamani, wanda babu cutarwa, baki da laifi har a wajen Allah " Cewar Madam Chima ?awa ga Hadiza kuma itace uwar gida a gidanta tana da kishiyoyi har uku. Amman kab cikinsu babu wacce bata sha gabanta ba a wajen miji. Kullum madam Chima mijinta ke goyota a moto ( mashin kenan suke nufi) ya kawota makaranta. Kuma duk abinda yake yi da zaran lokacin tashi yayi zai tawo ya mayar da'ita gida. Hadiza tace.
"Ni ai har wayewar garin yau bansan wacce kalace Amaryar ba. Ni ai tunanina ita ya dace tazo ta gaisheni tunda itace ?arama" Chima tayi shewa tace.
"Baki san takan duniya ba. Ai zuwan da zaki yi kankaro mutuncinki zaki yi a wajen mijinku. Ke dai she?a kwalliya kisa kaya tsadaddu muje kinji?" Akace mutum baya ?in ta mutum wai ance da Sarawo ya ruga. Duk wayonka da dabararka in kaga wani sai kace wannan malaminka ne a komai. Hadiza ta shirya tsab cikin ba?ar shadda wacce tasha surfani irinna al'adar ?asarsu, ta sanya Wan kunne da sar?ar zinaren da Malam ya basu, ta Wauko farin takalmi dake cikin akwatin da taima kanta ta saka. Tabi jikinta da humrar Mrs Bukhari, kana tabi kayan jikinta da turaren fesawa na tufafi mai sanyin ?amshi shima daga Mrs Bukhari ( kina so ?amshinki ya zam na daban a rasa da kalar turaren fesawan da kike amfani? Ko kuma kyauta kike so na musamman ki baiwa maigida na turare mai sanyaya ruhi kuma kin rasa wanne kikeso? To ina da turaruka na fesawa da nake haWawa masu sanyi da taushin ?amshi na mamaki. Hajiya daga yanzu babu ke babu siyan turare Designer babu ke babu zuwa kanti siyan turare. Zan haWa miki turare naki na karan kanki wanda in kasuwa za'a karaWe ba za a samu me irin ?amshin naki ba. Gashi da ri?e tufa????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
fi har ki wanke tufafinki bazai bar ?amshi ba.)
Gaba ta wuce ?awayenta suna biye da'ita a baya har zuwa Wakin Amarya. Da sallama suka shiga, kafin su ?arasa shiga falon har ?amshin Hadiza ya cika falon ya doke turaren wutan da aka turara Wakin Shafa, dama turaren cikin akwati da ita Shafar ta fesa. Hadiza da Shafa idanuwansu ya sar?e dana juna. Dukkansu sai suka tsinci kansu cikin damuwa da rashin ?arfin guiwa cikakke. A fakaice Hadiza cikin sakanni ta karance irin kayan alatun da aka dan?ara a Wakin Shafa. Muryar Ayashe ce ta dawo da Hadiza cikin doka da oda.
"Uwargidanmu ga waje ku zauna. Yanzu muke shirin mu kai Amaryar ma Wakinki sai gashi kin rigamu ma zuwa" Ya?e Hadiza tayi wanda ya gyara mata fuskarta cikin sakewar murya tace.
"Ai babu komai nasan sha'anin biki anata fama da jama'a. Ni Winma tun Wazu naso shigowar." Nan Wakin ya kacame da gaishe_gaishe a tsakanin dangin Shafa, da ?awayen Hadiza. A sanyaye Shafa tace.
"Yaya ina kwana, ya akaji da jama'a?" Hadiza taji wani abu ya daketa a zuchiyarta yadda taji Shafa na karya harshe wajen lafazi. Bama Gwadabe ba hatta ita salon muryar ta burgeta.
"Lafiya lau Amarya ya ba?unta" Wata tsohuwace ta katse maganar ta hanyar cewa da Hadiza.
"Dama yanzu zamu kawota wajenki, mu shiga da,ita cikin gidan surukan nata, da manyan gidan. Dan gobe asubar fari zamu kama hanya, anjima kuma zamu le?a kasuwa muga gari. ( Kunsan ?an ?auye akwai son shiga kasuwa ko ba zasu sayi komai ba zasu je suita zare ido) Mi?ewa Hadiza tayi tare da yi musu sallama. Shafa tabi Hadiza da idanu ta baya. Dirarriyar mace doguwa son kowa. Kanta ta sauke ?asa yayin da zuchiyarta taci gaba da harbawa. Ta bangaren Hadiza wannan yanayin ma yafi ?arfi dam ita sai da ?walla ta taru a idanunta. Basu jima da komawa Waki ba sai ga sallamar dangin Shafa sun tusota gaba.
Tana saye da riga da siket na atampa Winkin yan Abuja da wata sar?a da Wan kunne fashion me kalar atampar. Mayafinta da takalminta su kuma iri Waya amman ko kusa babu kalar a jikin atampar.
"To Hadiza ga Amanar Shafa mun dan?a a hannunku ke da Gwadabe. Dan Allah ku zauna lafiya ku rungumi mijinku banda tayar mishi da hankali. In kika ga Shafa tayi wani abun ba daidai ba a matsayinki ta babba wacce ta fita shekaru da hangen nesa sai ki nushetta. Ke kuma Shafa duk abinda zamu faWa mun riga da mun faWa miki. Kiyi musu biyayya, kinga a ?asarnan baki da kowa sai su, duk abinda abokiyar zamanki ta gyara miki ki gyara. Ni da Mahaifiyarki tsawon zaman kishi na shekara hamsin da mu ka yi a tsakanina da'ita girmamawane. Yaya sama, Yaya ?asa, kuma duk abinda Yaya ta sani shi nake yi. Mu kai zamanmu salamun_salamun dan Allah Shafa kiyi koyi da irin tarbiyyar gidanku" In wannan yayi sai ya cika, wannan sai ya kama. Haka dai sukaita yi. Hadiza tace.
"To Allah ya bamu ikon ri?e wannan amana. Allah ya bamu zaman lafiya da fahimta a zaman?" Nan su kai mata sallama kuma. Daga nan su ka kaita Wakin Yaya Tasi'u shima suka dan?ama Anty Badi'a amanar ta musu ido akan zamantakewar. Ita ta rakasu Wakin matar Jamilu. Sai gatsina take tana magana ciki ciki dai. Daga nan Anty Badi'a ta jagorancesu zuwa dukka Wakunan amaren gidan, daga nan suka shiga cikin gida shima suka zagaya du Wakuna huWun tas.



Cikin gidan Malam
Anata hada_hadar Waura girkin rana. Yayin da ba?in da suka taso daga nesa suketa haramar komawa garuruwansu tunda dai biki ya ?are.
Baba Suwaiba da Amaryar Malam suna dai cikin danginsu anata hada hadane. Amman zuchiyarsu a cike take tab da tsoro da fargabar Malam. Malam ya Wauki zafi sosai, hatta gaisuwarsu yau Malam ya?i amsawa abinda bai taSa yi ba kenan. Kuma ya sake jaddada musu lallai su zauna da zaman shirin dole zasu tafi gidajensu. Kafin ace abinci ya nuna tuni rabi da kwatan ba?in biki ko wacce ta kama gabanta, sai tsirarin ?an uwa da su kai ragowa su kuma sai zuwa gobe zasu watsr. A Wakin Baba Suwaiba duk ?an uwanta sun watse. Amaryar Malam kuma dama mutum ukune suka zo daga Sangarenta, sai ?awayenta na ma?ota, kasancewar ba ita ke aurarwa ba. ?akin Baba Fhatsima ma Altine da Balarabane kaWai su kai saura, sauran dangi su ana gama karin kumallo ma suka tattare yanasu yanasu suka kama gabansu. ?akin Baba Asshine yake cike da jama'a sosai dan su ko soma raguwa ma basuiba. ?an takai ma su Laila suna nan, sai su Ayashe, da dangin Amaryar gwadabe, da su Bara'u wanda su kuma gobe zasu kama hanyar suma.


DAKIN BABA FHATSIMA:.
Balaraba sai faman gyarama Baba Fhatsima Waki take yi, ko ina kaca_kaca shine take son ta gyara komai ta ajjiye a mazauninshi. Baba Fhatsima tana zaune sai ta dubi Balaraba tausayinta ya kamata. A ranta saita ?udurce zata tuntuSi Tasi'u da batun Balaraba ko Allah zaisa a dace yaji ya amince zai aureta a karo na biyu. Dan Balaraba yarinyace mai hankali sosai, kuma bata da wata makusa da za a ?ita dominta.
"Altine gobe Balaraba ba zata biki ba. In zaki tafi ita ki barmun ita. Akwai tunanin da nake yi ne. In hakan ya tabbata zaki ji, amman ki barmun ita gaskiya. Daga Balaraba har Altine wani daWine ya lulluSesu dukkansu sun gane inda ita Baba Fhatsiman ta dosa. Kuma shi kanshi Tasi'u ya nuna kamar har gobe yana jin Balaraba a ranshi.
"Shikenan Yaya Balaraba ai taki ce kumfi kusa, gata nan" Dariya Baba Fhatsima tayi tace.
"Balaraba ai zaki zauna tare dani ko? Duk da babu sa'anninki a gidan. In yaso dan kar kaWaici ya dameki ba sai ki koma islamiyya ba?" Balaraba tace.
"Zan zauna Baba ba komai ai nanma gidanmu ne" Tana gama faWar haka ta fice Wakko abin kwashe shara.
"Shikenan Yaya Wallahi naso in Wakkota in kawota wajenki ko wajen Yaya Dije. Acan gabana in banda kuka da damuwa babu abinda take yi. Kinga nan kuma birnice ai nima zanso tayi aurenta a birni. Inta koma islamiyya zata ?aru sosai. Sai dai bata Webo kata da yawa ba" Baba Fhatsima tace.
"To in banda abinki ai da kin kawota. Batun kaya kuma Yayansu zai siya mata a WiWWinka mata ta samu na cin zawarci. Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi. Kije ku duba abincinnan fa ko ya nuna. Kwanciya nake son inyi ko ina ciwo yake yi mun an sha kacaniyar biki. Da kuke_koken yara"

Ta bangaren Angwaye kuma, suna Wakinsu na samartaka suna zubar da zance gami da tsokanar juna.
Gwadabe dai Baya cewa uffan sai murmushi, jiya ya ?ara tabbatarwa cewar Iyabo na da wata baiwa da ba ko wacce mace bace zata iya samu ba. Rabuwarshi da Iyabo sai ya sake dawo mishi Wanye. Har ya gama haWa ?an kayanshi da basu shige kala shida, da jakar magungunanshi baice komai ba. Bara'u kuwa ya ?ura mishi idanu yana nazartarshi, tuni ya bugo kuwa jirgin nashi, abotar wasan ?asa ba abota bace ta wasa. ( Fatima Abdullahi Owuna zanso ace kina karatun littafin Hausa, da a daidai wajennan zaki tuno lokacin muna yara). Hannun Gwadabe Bara'u ya ja zuwa waje, Tamu dama baya Wakin yana wajen Ayashe suna tattaunawa dangane da maganar barin toye da kahinde da Gwadabe yayi musu.
"Gwadabe wai shin duk zu?a_zu?an matannan kana nufin basu isa sun maye maka gurbin Iyabo bane? Ya kai da kake da Amare kana tunanin matar da ba mallakin ka ba. Babu mamaki Iyabo tana gidan wannan wan nata Debisi tana aurenta cikin kwanciyar hankali tama rufe shafinka, ta shimfiWa sabuwar rayuwa. Matar da ko yaranta bata sake waiwaya ba shekara biyu fa."
"Sabida kasan na?i jinin Debisi shine ma dalilinka na danganta Iyabo da aurenshi" Da gaske sai gabaki Waya ya hautsine. Bara'u kuwa mai zaiyi ba Dariya ba. Dole shima Gwadaben ya dara, tare da dorawa da faWin.
"Kana ji. Aishi tunanin Iyabo tamkar numfashina yake. Zare tunaninta a gangar jikina daidai yake da zare numfashina. Bara'u Iyabo mutum ce harda Sari kai shaidane kan hakan, kuma ta cancanci a dauwama ana tunanin ta tare da binta da fatan alkhairi. Fatana shine Allah yasa iyakar ?arshen wahalar rayuwar Iyabo ya ?are a gidana. ina mata fatan samun mijin da zai kula da'ita fiye da kima. Kai dai mu ture batun Iyabo mu dawo batun yara. Bara'u."
"Dakata malam dallah. Nina faWa maka gaskiyar abinda yafi dacewa. Ka zauna da matanka a nutse ka gama gane kansu tukunna. Toye saiya gama firamare zai dawo hannunka zancan gaskiya kenan. Zuwa lokacin suma ko wacce da nata. Da yazo saiya faWa sakandare kai mun wannan alfarmar." Dariya Gwadabe yayi yace.
"To Shikenan hakan za ayi duk yadda kuka ce. Shi Tamu yama ?i yadda zai bani yaran. Naga Toye da Husna sunyi wani irin sha?uwar data haure misali, ko hakan hujjane. Babu komai in suma sai sun gama firamare Win za a bani su duk babu komai" Ana haka sai ga Tamu ya shigo Sarayin.
"Me ake tattaunawa aka wani ja gefe?" Cewar Tamu. Bara'u kuuwa yace.
"Maganar Iyabo muke yi daka ganmu" ?arasowa yayi kusa dasu yace.
"Baiwar Allah. Alkhairan Allah ya kai mata a dukkan inda take. Kai kuma Gwadabe Allah ya baka ha?urin rashinta. In sha Allah nan ba da jimawa ba Toye da Kahinde zasu maye maka gurbin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login