Showing 57001 words to 60000 words out of 270738 words

Chapter 20 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Fhatsima tace.
"Ohh naji naji, shine haka ya zama babban mutum haka? Oh Gwadabe rabona da saka ga idanuna shekara talatin baya, kana yaro kyatunarka na yawan kawo mana ziyara a lokacin kana goye a bambunta" Gwadabe sai murmushi kawai yake yi yana sinne kanshi ?asa. Wata budurwace doguwa itama mai jiki ta shigo hannunta da kwanon abinci ta dire mishi a gabanshi.
"Wannan ?aunarka ce Habi kenan. Ashirin ga wanga wata za'a Wamra amrensu su bakwai cib. Habi wannan wankine Gwadabe." Gaisheshi Hari tayi da ladabi, ya amsa cike da fara'a, ta saka kai ta fita.
"To Fhatsima ga Gwadabe na dam?a amanarshi gareki, ki zame mishi uwa tunda kece babba a cikin gidannan. Rigingimu ne na dangi su kai yawa shine na yanke hukuncin tawo dashi in gameshi da su Auwala suna tafiya ha?an zinariya. Sauran bayanin in kwananki ya zagayo zan zaunar dake mu tattauna. Labulen Wakin aka Waga. Wata ba?ar dattijuwa mai zanzana ce tsaye Wayan hannunta ri?e da faranin silba sha?e da kwanonin silba a kai. ?ayan hannun kuma ri?e da labulen Wakin. Dukkansu suka Wago suna kallonta.
"Abincin Wakin Yaya zaka ci, ko in kai shi turaka?" Babu yabo babu fallasa tayi maganar. Sai da malam ya girgiza kai, Baba Fhatsima kuma tayi murmushi tace.
"In banda abinki kema kinsan ai a turaka zaici. Me zai sa yaci abinci a Wakina ke da ranarki" Guntun murmushi tayi tace.
"To wa ya sani abu a dubu Yaya."
"Ki kai mun turakata gani nan zuwa" Malam ya bata amsa da kaurin murya da halamun Sacin rai tattare da shi. Tana sakin labulen ya mi?e ya fita. Baba Fhatsima tace.
"Kaci abincin, sai a nuna maka shashen samarin gidan ko?"
"To Baba Nagode " Gwadabe ya bata amsa a dalabce.
MRS BUKHARI B4B GIDAN


3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundation gidauniyar da muka buWe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaWanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE)
300 kacal zasu iya kuWin karatu

*?ar uwa ina fatan baki mance da kayan ?amshin Mrs Bukhari gidan ?amshi ba ko? ?ar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ?amshi. Matso kusa ?ar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ?amshi ya ri?e miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake sa?awa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ?amshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haWe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ?ara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ?amshin kifi Wanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ?amshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ?amshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ?ar mutan Maiduguri kin samu ?amshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai Wauke da abubuwa huWu manya kuma a kan kuWi ?alilan karki bari garaSasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*



NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI CE

16
Kwanon da aka ajjiye mishi ya jawo. Tuwon Sula ya gani da miyar bushasshiyar karkashi. A tsanake ya soma ci, wannan tuwo ya bashi mamaki matu?a dan a ido bashi da kyan gani, amman a baki akwai daWi sosai. Zama ya gyara yaci gaba da kantara loma. Wannan budurwar dake kwance a gadon bono ce ta yi mi?a ta tashi zaune tana salati. Wankar tarwaWace kyakkyawa ma'abociyar siririyar fuska da siririn hanci, laSSanta suna da Wan girma kuma a Wane suke, ha?orinta biyu manya na gaba a waje suke ko da bakinta a rufe yake. Masu irin wannan ha?orin ana ce musu masu ha?orin zomo. LeSenta ba?ine wukul duk da ya fahimci duk mata da yaran gidan bakinsu duk ba?a?ene kuma kamar wani abun suke yi dan leSen ya zama haka. Bata da idanu manya ?anana ne idanunta kamar an huda sakwara, ga gashin ido da yaima idanun rumfa, in ba zaro idanun tayi ba ma baka isa ka ga ?wayar idanun ba." Ganin Gwadabe a zaune yasa ta rarami mayafi ta rufe jikinta ruf.
"Kayi ha?uri bansan kana ciki ba" Ta yi magana muryarta na rawa. A gaggauce ta gaisheshi ta fita. Itama doguwace mai kauri yar duma_duma fatar jikinta luwai_luwai dashi gwanin ban sha'awa, ga mazaunai Saka_ba?a. Iyabo ce ta dawo mishi rai, da irin yanda in ta yi walliyar Winkin buba da zani take burgeshi, da yanda in ya kallli tudun mazaunanta ta bata yake Wimaucewa. Ajjiyar zuchiya ya sauke a fili yace.
"Ina miki fatan samun namiji lafiyye wanda zai kula dake, ki huta a gidan mijinki irin hutawar da kika rasa a gidana. Allah ka sa jin daWi da nutsuwa a rayuwar Iyabo ta gaba. " Gabaki Waya abincin sai ya fice mishi a kanshi ma, rufe kwanon tuwon yayi ya sha ruwa. Yana zaune ?walam wannan basamudiyar budurwar ta sake shigowa dan doguwace ingarma.
"Baba tace in ka gama in raka ka shashen samarin gidan ka je ka yi wanka ka huta" Ledar Wan kayanshi kala biyu ya cacuma ya soke a hammata, baice mata komai ba ya biyo bayanta suka fito. Iyayen gidan basa tsakar gidan, sai tsirarin yara matasa masu wasa kawai. Tiryan_tiryan yana biye da'ita har zuwa wata ?ofa da suka shiga yaga Wakuna kusan bakwai a jere, da ba haya mara ?ofa sai labulen buhu yana kallosu, sai durom biyu na ruwa, da ?an butoci, da bokiti.
Wani Waki ta tura ta shiga.
"Bismillahi ka shigo" Bayanta yabi zuwa cikin Wakin. Katifun yayi ne guda huWu a jere, sai akwatunan ?arfe suma guda huWunne, ginine na jar laka, ba fulasta ba komai, ?asan Wakin ma ba daSe ba komai, rairayin ?asa ne takota ina sai ?ar tabarma da ke shimfiWe, saman Wakin kuma jinka ce, sai ?wan lantarki guda Waya jol.
"To bayan gida yana waje, akwai botiki, da ruwa zaka iya watsa ruwa. Lokacin sallah ma yayi sai ka sami malam a waje"
"Nagode sosai, sai dai bansan sunanki ba har yanzu." Ya faWa yana ?ar dariya.
"Sunana Hadiza"
"Ke yar Ine ce?" Ya tambayeta.
"E yarta ce ni" Sallama tayi mishi ta fita. Shi kuma ya shiga kewaye yayi wanka tare da Wauro alwala. Farin yadi ya saka, wanda ya cire kuma ya saka a botiki ya zuba ruwa, kafin ya fita waje wajen Malam. A ?ofar gidan Malam yai musu limanci. Bayan an idar da sallah almajirai sai suka soma karatu.
"Gwadabe ga allo da tawada ka iya rubutu ko?" Sai da Gwadabe ya amshi allo da tawada da al?alami yace.
"E na iya Baba, a can Takai ma makarantar allon mu ka yi, sai dai karatun baiyi zurfi ba, banfi izifi huWu ba"
"Hakane na sani Gwadabe. To yanzu daga farkon izifi huWun zamu soma. Yau ka bar rubutun kayi muraja'a yau da gobe, jibi kuma sai ka soma rubutun allo. Bana son wasa da karatu. Sannan ka zama jajirtacce sai Allah ya dafa maka. Na sani mahaifiyarka bata da daWi, iyayenmu kansu sun sha yin kuka da'ita. In banda fitina ta Babala ina ita ina kafewa sai Wanta ya auri Sarauniya sabida Allah fa?" Ana cikin haka sai ga su Auwala, da Mammada. Baba Magaji ya gabatar musu da Gwadabe, sannan ya mikashi ga Auwala akan zuwa gobe zai soma fita tare dasu. Su Auwala suka karSeshi hannu bibbiyu, kuma su kai maraba da shi. Baba Magaji yaranshi maza su rai goma sha Waya ne ras. Uku daga ciki sun yi aure, suna cikin gidan tare da iyalansu, tara kuma kowanne yana neman kudi, amman shida a ciki kowanne da budurwarshi da tsayayyar magana. Ukun yarane.
Washe gari Gwadabe yabi zugar su Auwala zuwa can garin ?an Issa inda anan ya ga dandazon dubban al'umma masu ha?an zinariya. Tun daga nesa dai ya hango tudun laka kawai, sai da suka isa wajen ya ga dubban al'umma. Da rijiyoin ha?on zinariya sama da Wari.
Mammada ne ya ja hannun Gwadabe ya kaishi ga shugaba mai kula da ?an ?wadagon wajen ya sanar dashi malam ne yace a kawo shi ya dinga ganin aiki kafin a hankali kuma ya shiga ayari.
To Alhamdulillah haka rayuwar Gwadabe taci gaba da tafiya, da safe su hau abun hawa zuwa Wan Issa, da yamma su dawo gida, su Wau karatu daga magriba zuwa taran dare, da asuba bayan sun yi sallah kuma zasu yi muraji'a kafin kuma su karya su tafi nema. Duk dabdala a Wakin Baba Fhatsima Gwadabe yake yinta. Mace mai kawaici da son jama'a kenan. A cikin sati guda da Gwadabe yayi a gidan Baba Magaji, ya fahimci ana buga kishi sosai da sosai tsakanin matan Baba Magaji, yaran ma suna taSawa dan ko wacce ta jaye yaranta, sun haWe kawunansu isu_isu. Ko wani abune ya faru da Wan wani Wakin, sai aita rurrufewa sai dai in na alkhairi ne, ko dan fahari a fito tsakar gida a faWeshi. Baba Suwaiba da Amaryar Malam sune suka fi gwabza kishi a tsakankaninsu, kasancewar sunfi Baba Fhatsima da Baba Asshi karancin shekaru, sune Baba Magaji ya aura a baya_baya. Dan Amaryar malam yarinyace da bata wuce shekarun Hadiza ba. Yaranta uku duk maza, sune ?ananu sosai a gidan. Fitinarta tafi ta kowa a cikin matan Baba Magaji, sabida tana ganin ai itace Amarya. Su kuma sauran matan kishinsu yafi tsananta akan Baba Fhatsima da yaran Wakinta da suka kasance manya, masu jam ragamar komai a gidan. Yaya Tasi'u shine Babban yaron Baba Magaji, babban Wan kasuwane da yake harkar riWi da gero, kuma yana kiwon tsuntsaye masu darajar gaske, dangin su Wawusu, da gigs, da Aku, da dai manyan tsuntsaye na ?asashe da dama. Kasancewar shine Babba shike ciyar da iyalan gidan baki Waya, kuma shi ke yi ma yaran gidan Aure, da duk abinda uba yake yi ma ?a?anshi. To kasancewar Yaya Tasi'u ya fito a Wakin Baba Fhatsima sai yaran Wakin Baba Fhatsima suka zama yara daban a cikin gidan, yana basu kulawa ta musamman, Baba Fhatsima kullum a cikin shigar daraja take. Kuma matar Yaya Tasi'u mai Suna Badi'a tana yawan yin dabgen kaza ta ciko kwano ta kawo ma Baba Fhatsima. Ko Shi Yaya Tasi'un yasa ayo mata miyar kaji cikin tukunya, sai dai su dinga ci, dan ko abincin Sarayin bata ci, daga can barayin Yaya Tasi'u ake kawo mata ishasshen lafiyayyen abinci. Ko da Sallah Yaya Tasi'u shi ke ma su malam da iyayen nashi mata layya. To ko akan ragon layyar duk shekara sai an samu yamutsi kan na Baba Fhatsima yafi na saurn matan gidan girma da ?oshi. Haka dai ake wannan rayuwa a wannan gida.
Ranar da Gwadabe ya cika sati guda bayan sun tashi daga karatun dare sai Malam ya zaunar dashi.
"Gwadabe banyi maka batun mace bane dama nace bari in bari ka nitsa. To kaga akwai ?an mata a gidana da yawa, duk da bakwai daga ciki am sa lokacin bikinsu. To shine nace ga Hadiza nan ina ganin kamar tafi sauran yaran hankali kasancewar bazawarace ita. Wata biyar kenan da mutuwar auren nata. A halin yanzu dai bata soma fita zance ba, in dai kana ganin tayi maka sai kayi ?o?ari ku sasanta kanku. In kuma batayi ba, kar kaji nauyi ka faWamun wacce tayi ma kai ko wacce tayi ma tana cikin waWanda za'a aurar ne, zan iya baka ita, shi wancan yayi ha?uri. In kuma dukka basu yi maka ba to Shikenan sai in taya ka da adda'ar Allah ya kawo maka wacce zata zame maka alkhairi. Duk da dai mun soma maganar da Fhatsima, Tasi'u da kanshi sai yayi sha'awar maka Hadiza tunda dukkanku Zaurawane. Amman kaje kayi tunani. Gwadabe take zufa ta keto mishi, zuchiyarshi ta shiga harbawa da ?arfi. Shi a halinnan da yake ciki na alhini da damuwar rashin Iyabo. Ina shi ina wata soyayya? Ta ina ma zai soma wata soyayya, baya jin akwai wata mace da zai iya bata zuchiyarshi harta samu gurbi. To taya zai kuSutar da kanshi daga wannan tayi na Baba Magaji? Kuma ko yaya ya nuna baya son ko Waya daga cikin yaranshi tabbas bazai ji daWi ba. Kuma shima nauyi da kunyar Baba Fhatsima zata iya hanashi zaman ?asar. Gashi har ya soma sakewa, ya soma jin daWin sabon wajen aikinshi, kuma Alhamdulillah shima harya soma shiga rijiyar tono, duk da yanda akaita tsoratashi, da irin yanda ake samun haWarin Waruruwan mutane su rasa ransu ta dalilin rubtawar ?asa, amman yasa a ranshi tunda anayi, shima zaiyi in sha Allah sai yayi kuWi. Tunda yanzu zumuncin ma sai kana da hannu da shuni akeyi da kai.
"Gwadabe kar ka damu, na baka sati Waya kaje ka yi tunani da kyau. Kuma ka kalli yaran da kyau ka zaSi ka darje, in yaso shekara mai zuwa sai a haWa auren naku dana su Mammada ayita ta ?are. Akwai babban filina gashi can, a cikin filin almajiraina suke wanki, da duk wasu harkoki. To anan zaku zauna dukkanku, Tasi'u zai gina ma kowa ciki da falo_falo"
Da haka Gwadabe ya tafi ya bar Baba Magaji akan zasu haWu nan da sati mai zuwa yaji wacce ya zaSa.
Jikinshi a mace ya shiga cikin gidan. ?akin Baba Fhatsima kai tsaye ya shiga. Anan ya tarar da Auwala da Mammada suna zaune da abinci a gabansu, da dukkan halama shi suke jira su ci abinci, dan tun zuwansu suke cin abinci a tare. Hadiza, da Ine suma abincin suke cii daga can kusa da gadonsu na bono.
"Yaya Gwadabe ya aikin?" Cewar Ine kenan. Sai da ya gaishe da Baba Fhatsima kana ya amsa Ine. Hadiza ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace.
"Yaya Gwadabe da safe naje nemanka Sarayinku ban sameku ba yau kun fita da wuri ko?"
"Sa hannu Malam muna ci kana amsa musu tambayoyinsu. In wanna yaranne sai mu kai sha Wayan dare ba mu ci abinci ba" Dariya duka suka yi, dan Auwala baya wasa da harkar cin abinci. Baba Fhatsima tace.
"Ato da gaskiyarshi ai. Maza kuci ku samu ku yi wanka sai ku kwanta. Allah dai ya sama nema albarka." Suna cin abincin ana hira baki Wayansu a haka dai suka ?are cin abincin. Sai ga Yaya Tasi'u ya shigo.
"Kuna nan ba? Anzo a cinye ma Baba Wan naman nata ba? Baba Yarannan ya kamata a matso da maganar aurensu, a samu suma su mallaki iyalansu, su dena zuwa suna cinye miki kayan daWi" ?an darawa su ka yi, duk suka mi?e suka gaggaisa, Yaya Tasi'u yace.
"Gwadabe ya ciwon jikin? Mammada ya faWa mun ranar daka shiga rijiyar ha?on zinariya kasa bacci kayi, jikinka yaita ciwo?" Kai Gwadabe ya sosa yace.
"Wallahu Yaya Tasi'u ai naji jiki sosai. Amman dai yanzu ina Wan taSa aikin, ciwon jikin yana ja baya"
"E dama a hankali zai bi jikinka. Kama yi ?o?ari ni naga jarumtarka sosai, dan wannan aikin bana malalata bane." Baba Fhatsima tace.
"Ni kaina na ga juriyarshi sosai. Allah ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yayi muku albarka dukanku Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira" Da
"Ameen" Suka amsa dukkansu. Hadiza tace.
"Yaya maganar kuWin angon baka bamu ba, kar mu rasa Winkin" tsaki Yaya Tasi'u yayi yace.
"Ana maganar kayan gado dasu katifa yayi kuWi. Ku ta ango ma kuke yi ko? To kuje dai wajen Antynku Badi'a zata baku atampopin ta siya muku, dan ni ban bata ko sisi ba. Kunga ni an hutasheni, sai in yima Mamana" Nan suka yi mishi godiya. Baba Fhatsima tace
"Ai Babannan ( haka Take kiranshi, kasancewarshi Wan fari kuma mai sunan Mahaifinta) Babu abunda zamu ce da Badi'a sai dai muce Allah ya saka mata da Alkhairi. Tana yi mun abinda ko su Hadiza iyaka kenan. Yarinyace adala. Ina ma su Auwala fatan Allah yasa yaran da zasu auro mana su kasance masu hankali. Sai kaga zumunci ya sake ?arfi sosai. Kuma naji daWin yadda Malam ya yanke hukuncin ware su wadannan yaran a gida daban. ?ila suma kansu su Sabitu su daure ayi zumuncin duka tare da matansu. Kuma kuyi ?o?arin haWe kawunan yaranku waje guda, kar ku sake a raba muku kan yara. Ni bana jin daWin irin yanda kowa yake jaye Wanshi jikinshi kaWai." Auwala yace.
"Tabb ni kuma Baba gani nake yi wannan haWemu da za'yi waje guda ba zai haifar da Wa mai ido ba. Sabitu da baya ko iya gaishe da mutane cikin daWin rai. In fa zai gaishemu kamar zai haWiyi zuchiya haka yake yi, dan ?aniyarshi dan yasan kashi zan bashi in baiyi gaisuwar bane. Ni wallahi bana son wannn haWemun da za'ayi" Yaya Tasi'u yace.
"Gaskiya ne za'a iya samun rikici sosai, musamman dag Sangaren su matan da za'a auro bare. Mun tattauna da Malam sosai akan matalolin da ka iya faruwa. Mum kuma yi magana akan irin nasarorin da zasu iya faruwa. Dan a wannan karon Malam ya shirya Satawa da duk wanda ya nemi ?etare umarnin abinda zai gindaya. I zuwa yanzu ya kamata ace an watsar da duk abinda ya shige, a fuskanci rayuwa. Malam bashi da wani buri daya wuce yaga kan iyakanshi a haWe. To matsalar Baba Asshi itace zata fi kawo matsala acikin lamarin. Amman Baba shi fa malam so yake filin ?an Abhuja dake jikin filin da malam ya bayar a gina, ya siya a faWaWa harni da Usman, da Jamilu duk mu koma can, sai ya ware ku kuma daban, muma daban. Ni a matsayina na babba sai in kula dasu baki Waya" Cikin damuwa da tunanin rashin yiyuwar haWin kai ga iyalan Malam Baba Fhatsima tace.
"Tab aikin da Malam ya Webo babbane sosai. Kuma abun zai yi matu?ar wahala asamu abinda akeso. Sai dai zamui ta adda'a kamar yadda muka kwashe shekaru sama da hamsin muna yi. Malam ya matsantama kanshi da damuwa, da tunanin abinda zai dawo mishi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login