Showing 252001 words to 255000 words out of 270738 words

Chapter 85 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

yace.
"Gwadabe kayi ha?uri mu bar maganar zuwa ka samu lafiya. Likita yace mun kar ayi wata maganar da zata Sata maka rai kayi ha?uri kayi shiru ga Shafa.
Ni bara in kira likita yazo"
Yana gama faWar haka ya mi?e ya fita.
Shafa ta dawo bakin gadon ta zauna suna fuskantar juna.
"Haba Baban Abba in banda abinka ai adda'a ya kamata ka dage mata dashi domin babu abinda yafi ?arfin Allah. Ita kuma adda'a bata faWuwa ?asa banza. Hakika na tausayama Anti Iyabo sosai, na kuma tausaya ma danginta dan Satan rai uku bafa wasa bane.
Abinda zamu yi shine tunda Yaya Bara'u yasan ?auyen da take sai mu Wunguma muje ayi musu jaje ko babu komai ai ta haifa maka yara har uku, kuma sune kan gidan tunda sune manya"
Shafa ta dinga kwantar ma da Gwadabe hankalinshi har sai da Bara'u da Likita suka shigo tayi shiru.
"Yanzu meke maka ciwo Gwadabe yaya kake jin jikin naka?"
Likita ya jefo mishi tambayar.
"Ina jin jiri sosai daga kwancen da nake, sai matsanancin ciwon kai, ga faWuwar gaba"
"Assha sannu Allah ya sauwa?e. Dan Allah duk abinda ke zuchiyarka ka daure ka cire ko dan ?oshin lafiyarka jininka ne ya hau sosai a ta?aice ka kamu da ciwon hawan jini na farat Waya a sakamakon jin mummunan labari. Zamu Wan ri?e ka mu kula da kai tukunna sannan zamu Wauraka bisa magunguna.
Ku kuma da kuke tare dashi ku kula wajen tausarshi da rarrashin shi."
Likitan dai ya Wanyi gwaje_gwajenshi yace a samu abinci a ba Gwadabe yaci zai sha magani.
Ai kuwa likitan na fita Sakina ta shigo kici_kici da kayan abinci. Shafa ce ta zuba mishi kokko da lafiyayyen ?osai. Bara'u ya taimaka mishi ya jingina da gadon. Nan aka shiga tata Surza dashi, shi yana ya ?oshi, su suna ya daure ko babu yawa yaci. ?osai biyu da kokko rabin kofi yasha da ?yar, sai maganinshi da yasha, bai jima ba bacci ya sureshi.
"Wallahi jiya ban rintsa ba. Bara'u ai ya kamata mu je mu can ?auyen da abin ya faru ko?"
Cewar Sakina kenan. Shafa tace.
"Nima nace mishi muje ayi musu jaje sannan a jiyo ko akwai wani labari. Yanzu dai da zaran ya samu lafiya ai sai mu rankaya mu je tunda kai kasan garin.
Kamar dai wasa sai da Gwadabe ya kwana uku a asibiti kafin aka bashi sallama
Meeting Win da bai samu halarta ba kenan. A ranar da za'a sallameshi Chairman da kansila Zul?i suka zo dubiya asibitin
Shigowarsu kenan Da'u da Yaya Halima ma sun shigo duba Gwadaben kuma Babala ce taji labarin a gari shine ta wakiltasu suje su duboshi.
Mamakine ya kashe su ganin yadda Chairman da kanshi shi ya biya kuWin sallama. Sun dai san Zul?i abokin ?uruciyar Gwadabe ne, amman basusan meye ala?ar Gwadabe da Chairman Win ba.
Basu samu ganawa da Gwadaben ba dan basu samu kallon arziki ba ya dai amsa musu gaisuwarsu baya ga haka baice komai ba. Da shirun yayi yawa ne sai Halima tace.
"Da'u mu je gida hakanan. Gwadabe Allah ya ?ara sau?i"
"Ameen nagode, ku gaisa gida"
Jiki a mace suka fita. KuWi ya zaro ya ba Shafa yace ta kai musu
Ta fita ta samu Yaya Halima na share hawaye.
"Yaya wai gashi Baban Abba yace in baku"
Da sauri harda rige_rige wajen karSar kuWin Da'u ne yayi nasarar warce kudin. Kwana uku cib basu Waura tukunya ba, sai dai abinda aka dafa a gidan aka basu.
"Shafa kice mishi mun gode. Me sunan ?ar tamu ne?"
Murmusawa Shafa tayi tace.
"Sunanta Iyabo"
Tare suka sake maimaita sunan.
"Iyabo?"
Sai suka shiga karkaWa kai kawai. A wajen dai Shafa ta koma ta barsu.
To ana sallamar Gwadabe suka rankaya gidan Bara'u. Gwadabe ya mugun matsantama kanshi sosai.
"Gwadabe abinka ya soma zama fa iskanci. Shin ka mance wai Iyabo da mijinta ne? Kafa sauwa?ama kan ka.
Ka daure kaci abincin kaga kayi ma Chairman al?awarin zaka je ku tattauna zuwa bayan isha a gidanshi. Yanzu dai ga abincinnan ka daure kaci sai mu tafi sallah."
Ganin ran Bara'u ya Saci da yawa ne yasa Gwadabe yayi saurin jawo abincin gabanshi ya soma ci.
"Yauwa tsuntsun soyayya ko kaifa. Amman naga jikin naka babu ?arfi zamu iya tafiya mai nisa gobe kuwa garin fa da bala'in nisa. Ko dai mu bari ka warware da kyau ne?"
"A_a Bara'u jikin fa babu laifi. Jirinma ai kaga da sau?i"
Ya faWa da sauri, tare da ?ara ?warara kanshi. Alwala suka yi suka fice masallaci sallar magriba.
Ai kuwa ga Gwadabe a sahu ga Da'u. Gabansu kuwa Sukairajune, shi bai ga shigowar Gwadabe ba har sai da aka idar da sallah. Juyowar da zaiyi carab idanunsu ya sar?e dana juna. Sukairaju yayi tsamo_tsamo sai kallon Gwadabe yake yi ?aunar ?an uwantaka na ratsashi. Ha?i?a suna jin matsananciyar kunyar Gwadabe domin sun san abinda suka yi mishi babu daWi sun sashi a cikin tsaka mai wuyar fita. Amman dake Allah al hakim ne yau jibi Gwadabe cikin rigar mutunci, su kuwa babu sana'a babu dukiya yanzu ne suka soma daga farko, a yayin da shi kuma Gwadabe likkafarshi taci gaba.
Sum_sum Sukairaju ya fice daga Masallacin ba tare daya kula Gwadaben ba. Shima da idanu kaWai ya bishi har ya fice yana mamakin ramarshi.
Da'u dai da zai fita sai da ya sake gaishe da Gwadabe da jiki tare da yin godiyar kuWin da Shafa ta kawo musu Wazu kafin ya fita.
Zul?i ne ya matso kusa dasu sukaita hirarsu a ?o?arinsu na kawarma da Gwadabe tunaninshi.
Suna sallacewa suka nufi gidan Chairman dan tattaunawa.
Taron daya haWa da masu jiran kujerar kansilolin ragowar gundumomin kamar dai Gwadabe suka ga junansu aka gaggaisa nan taron ya soma.
"To mu dai fatanmu shine kamar yadda gwamna yace mu zaSo waWanda suka cancanta, a namu tunanin mun zaSo ku. Ya kuma rage naku ku yi abinda har abada tarihi bazai manta daku ba. Ku sani wata amanace ta talakawa zata dawo hannunku. In kuka hau kujerar mulkinnan ku ji tsoron Allah ku yi tsaiwar daka dan ganin kun wakilci Takai wakilci mai kyau"
Charman ya jima sosai yana bayaninshi. Kafin Ways bayan Waya ?an takarar gundumomin suka soma nasu jawabin dalla_dallah. Taron bai watse ba sai da suka yi liyafar cin abinci tukunna. Bara'u dai shi kaWaine Wan rakiya yau gashi dalili yayi dalili gashi ga Chairman a zaune a inuwa Waya harma yana cin abincin gidanshi. Allah mai iko"
Washegari suka Wauki hanyar Adamawa amman Bara'u ya ba da shawarar Shafa ta zauna ita da Sakina su dai su tafi, dan tafiyar bata rago bace.
Suna ta casar tafiya a hanya amman Gwadabe hankalinshi da tunaninshi ma basa jikinshi yayi zurfi sosai.



Ina godiya da addu,o'inku a gareni, waWanda suka kirani a waya ina godiya. WaWanda suka turo mun sa?o suma ina godiya sosai. Ha?i?a naga soyayya daga wajen masoyana masu bibiyar rubutana sosai
Ubangiji Allah ya bar mana zumuncinmu.

Kuyi ha?uri posting zai dawo na dare bana safe ba.
Ba wannan tafiyar kaWaiba duk wata fitowa da zanyi da daddare zan dinga posting kafinnan mata duk sun gama kwaramniyar gida sai su washe ?wa?walensu da karatu ko ya kuka ce masoyana.
Nagode sosai.

MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI



**Anty Ramlex Me kayan Da'a,ingantattu,fitattu,kuma shahararru*
Na zo muku da albishir na Promo Promo Promo=؃?
Abun da kuka Dade Kuna nema....,hakika dogon Jira ya kare.....Ga abunda kuke bege gaba gare ku=؃??+?=? ?

Ina Uwargida me son sabunta martabarta a wurin Oga,Ina amaren bana masu son su mallaki zuciyar ango,Ina zawarawa da suka shirya gyaran abun cikin buje,domin farfado da mutuntakarsu........ku matso kusa......

Hajiya ta sauke farashi,me kike jira........

Babban set na promo
~#20k~#15k=?L? <د? _dambun zabuwa
<د?tsumin bugenta shakaf
<د?Gumbar Madara me Sanya megida Santi da dalalar yawu
<د?Hadin dabino da cukwui hadin basarakiya
<د?Tsugunno me sirri_

*Karamin set*~#15k~#10k=؃? =???Herbal for vaginal infection
=???Tsimin bujenta shakaf
=???Gumbar Madara da hadin dabino.
=???Hadin dabino da cukwui (manta uwa)
=???Tsugunno me sirri


=ؚ?Muna aika kaya ko Ina a fadin Nigeria da kewaye.
=???Ku tuntubeni a wnn numbern 07069722234
Anty Ramlex taku ce>?p?
MAMA YA DAHU..
ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

LITTAFI NA HU?U

(13)

TABALBALIN

Uwani na turare Wakinta da turarukan wuta Laure tayo sallama ta shigo da tiran abinci ni?i_ni?i.
"Hajiya ga abinci inji Hajiya Babba ta kuma ce tana gaisheki."
"Allah sarki kice mata ina amsawa zan shigo inna yi Sallah mu gaisa in ga yaran ma"
Laure tace.
"Za'a faWa mata in sha Allah"
Ta saka kai ta fita.
Bayan Uwani ta bi sa?o da lungun gidanta ta turare ko ina. Sai ta yi sallar magriba kana ta nufi daining table domin cin abincinta kuma.
Da Uwani ta buWe abincin wallahi take ta raina kanta. Tun daga ?amshin, kama da kyanshi a ido, uwa uba daWi a baki.
Tuwone na semobita da wata iriyar miya wanda Uwani ta rasa gane wacce iriyar miya ce wannan dan ba irin miyar tuwon Arewa bane. Ga wasu irin kifaye sama da kala bakwai a cikin miyar gunduma_gunduma. A baki dai uwani ta gane akwai albasa sosai a miyar, ta ji ?amshin ni?a??iyar gyada ma. ( Miyar duniya ce wallahi) ?ayar kular kuma farfesun ?afar saniyace tayi mugun dan?o sosai ta dahu har kashin ya rabu da nama.
Uwani na cin abincinnan tana girgiza kai. Sai da ta ?oshi ta yi ?as ta wanke hannu tukunna. Sai ta soma tunanin da sakel ya zame mata dole ta sake zage damtse wajen fito da kalolin girki na ?asashe daban_daban ba iyakar abinda akeyi a Najeriya ba najeriyar ma Arewa.
Murmushi tayi ta mi?e da ?arfin guiwa data tuno da nau'ikan abincin larabawa da abubbuwan shan su.
Mayafi ta zara ta fice duk inda ta gilma sai ?amshin turaren turara kaya take yi ?amshin yana tsayawa a duk inda uwani ta ratsa.
A matattakalar benen sauka suka ci karo da Hajiya Sa'a suna haurowa ita da ?an yaranta mata su biyu.
Tun daga dai nesa data hango uwani sai ta turSune rai.
Itako Uwani da fara,a tace.
"Hajiya Sa'a barka da gidan. Sai naji kamar tsayuwar motar Alhaji Sama'ila ko?"
Da mamaki ta dubi Uwanin dan ba'a kiran sunanshi da Abba kab yara da su matanshi suke kiranshi harma da masu gadinshi."
"E shine"
Tana faWar haka ta yi wucewarta. Uwani tayi murmushi tare da yin ?wafa.
"Dani kike zancan wallahi in dai nice zuchiyarki ma na dab da bugawa ne. Ni bana Waukar iskanci Allah ma ya sani. Mata sai shegen ba?in hali, nifa miji bai dameni ba balle kishiya wallahi "
Tana sauka harabar gidan ta hango babbar yarinyar Hajiya Mansa mai suna Mabaruka ta amshi jakar uban. ?annenta suna biye da'ita yayin da uban ya take musu baya. Uwargida Hajiya Mansa kuwa tana bakin barandar shashenta tana jiran isowarsu. Tayi ado da wata jar atampa dinkin doguwar rigar daya shanye ?ibarta ya Soye tumbinta tayi kyau sosai kamar ba itace uwar zagada zagadan ?an mata da samarin ba. Murmushi ta sakarma mijinta shima murmushin yayi mata suka shige ciki.
Uwani na harWe tanaa kallonsu cikin sha'awa. Hajiya Sa'a na daga barandar sama itama kallon nasu take yi.
Uwani na Waga kai ta hangota ita kuma sai karkaWa kai take tana bin shashen Hajiya Mansa da kallo.
Murmusawa Uwani tayi kawai ta nufi shashen Hajiya babba.
Da sallama ta shiga du suna falo a baje a ?asa Alhaji Sama'ila yanata ciro kayayyaki a leda.
Ita kuma uwargidan tana Sarayin daining tana zuba mishi abinci.
Tana ganin Uwani ta saki murmushi.
"Hajiya Uwani kece? Mu da muke shirin haurowa da yaran duka?
Samira ga Antynku ku gaisheta."
Murmushi Uwani ta mayar mata ta nemi waje ta zauna, cikin mutunci da girmamawa suka gaishe da Uwani. Alhaji Sama'ila ya sallami ko wannensu da tsaraba kana ya dawo da kallonshi wajen Uwani.
"Amarya ba kya laifi. Dama kuwa nayi tunanin in haura wajenki dangane da batun shagonki na kasuwa. Yaran da aka saka aiki sun gama jera komai. Zuwa gobe zan Waukeki in kai ki, kiga wajen."
Hajiya Mansa ce ta karaso suka gaisa da Uwani tare da yi mata Allah ya sanya alkhairi batun shago.
Uwani dai bata jima ba ta mi?e
Ai kuwa Hajiya mansa ta ciko mata leda da cincin da alkali na bikin ?aninta da suka yi.
Tayi musu sallama ta fita.
Washegari da sassafe ta gama aikinta ta ci ado sosai na kece sara ta sakko ?asa Alhaji Sama'ila na jiranta su fita.
A bakin motarshi ta samu Hajiya Sa'a a tsaye suna magana, da dukkan halamu ?orafi take yi mishi ko akan menene dai oho. Ganin isowar Uwani ne yasa tayi shiru tare da sake tamke fuskarta. HaWe rai Uwani tayi bata tankata ba ta ratse ta bayanta. Ita kuma tayi ?abe_?abe a gaban motar.
"Baiwar Allah Wan matsa ko inaso zan shiga motarr."
Uwani ta faWa rai a haWe.
BuWar bakin Hajiya Sa'a sai tace.
"Tunda ni kika zo kika samu ai sai ki jira in gama abinda ya kawonu ko tunda ba kwana zanyi ba. Sannan ko da kika zo kinyi sallamane balle gaisuwa?"
Ta yi maganar cike da wula?anci.
Uwani ta kalleta ta sake kallonta har ?asa. Sai kawai tayi dariya tace.
"Hajiya Sa'a ni dinnan da kika ganni bana neman faWa, amman fa bana barin ta kwana balle tayi tsami. Na fahimci baki samu tarbiyya ba, ko girman kaine yayi miki yawa, ko kishi ke mu?ir?usarki ohon miki dai. Ai tunda nazo gidannan baki taSa buWe baki kin gaisheni ba. Kinga kuwa ai ba zamanki nake yi ba da zanta binki da sa?on gaisuwa sai kace wata ?ar iska ba"
Wani dogon tsaki Uwani ta saki tare da jan kafaWar Hajiya Sa'a zuwa gefe tayi shigewarta mota. Hajiya Sa'a kasa magana tayi dan mamaki. Shi ko Alhaji Sama'ila baice musu komai ba. Ya fahimci Uwani dama zata yi mishi maganin rashin mutuncin Hajiya Sa'a. Ta saba cunkusama Hajiya Mansa ba?a?en maganganu yau gashi ita ake mayarma.
Uwani ba tai aune ba Hajiya Sa'a ta bude murfin motar sai ji kake tas ta mari Uwani tare da karkaWa yatsunta tace.
"Ruwa ba sa'an kwando bane. Iyayena sun fi ?arfin ki zagesu marar tarbiyya wacce ta je saudiyya ta gama iskancinta da mazan larabawa.
Wata uwar tsawa Alhaji Sama'ila ya daka ma Hajiya Sa'a.
Uwani ta yinkura zata fita ya ri?eta.
"A_a Uwani kinga gidannan cike yake da masu aiki. Ki yi haquri in na dawo da daddare sai muyi magana"
Ai bai ?arasa magana ba Uwani ta fice jikinta har rawa yake yi ta dira a wuyan Hajiya Sa'a.
Ba sai dambe ya kaure ba. Uwani ta zage ta dinga jibgar Hajiya Sa'a kamar Allah ne ya aikota.
Hajiya Mansa da yaranta da Laure ne suka tawo a guje, suna ?o?arin SanSare Uwani a wuyan Hajiya Sa'a. Uwani ta ma?al?ale mata wuya sai gula take mata a ciki da dundu a baya.
"Alhaji Sama'ila ka fito ka raba wannan faWan dan Allah, jini ne yake fita fa. Ku Mabaruka maza kuje direba ya kai ku makaranta "
Da sauri yaran suka tafi dan basu taSa ganin tashin hankali haka ba.
Alhaji Sama'ila ne yasa hannu ya SanSare Uwani daga wuyan Hajiya Sa'a, yana tsakiyarsu.
"Ke shiga mota mu wuce, ke kuma ki haura sama inna dawo zamu yi magana"
"Iyakar abinda zaka ce kenan Alhaji. Jibi abinda mahaukaciyar matarka tayi mun."
Ta nuna mishi wuyanta da Uwani duk ta yakushe mata yana jini, ga cikinta a ?ulle.
"Mekike so ince dan Allah Hajiya Sa'a. Ba dai juninki bane faWa da masifa ba. To dama watarana sai ka samu daidai da kai."
Hajiya Mansa tace.
"A dai yi ha?uri ai Sa'a da hakuri kika yi. Uwani yaushe ta zo gidan da har za'a soma irin wannan abun?"
"Dallah malama ki rufa mana baki...."
Kafin ta ?arashe Uwani tayi wuf ta matsar da Alhaji Sama'ila ta sake rarumar Hajiya Sa'a suke tafi taga_taga suka faWi yib a cikin ciyayi. Uwani ta Wale ruwan cikin Hajiya Sa'a.
An yi abu sosai dan kayan jikinsu duk yayyagewa yayi.
Nono Uwani ta ri?e ma Hajiya Sa'a carab, sai ihun azsba take yi. Alhaji Sama'ila ya kama hannun Uwani ya haura da'ita sama ya kulle Wakin nata.
Ya sakko ya koma wajen su Hajiya Sa'a da take ta kumfar bakin ita wallahi ba zata yarda ba.
"Kin kyauta Sa'a. Na kuma gode da wula?antani da kika yi a gidana. Hajiya Mansa cikata nace"
Da sauri Hajiya Mansa ta saketa. Keyn Wakin Uwani ya bata yace.
"Gashi zuwa anjima ki buWeta. Ke kuma in direba ya dawo daga kai su Samira ya Kai ki asibiti."
Ya ja motarshi ya fice.
Uwani dan jaraba ta window ta zuro kanta ta nuna su Hajiya Sa'a tace.
"Zaki san kin ce mun karuwa. FaWannan wallahi bai kareba kinsan Allah saina zaneki ciki da waje sannan hankalina zai kwanta. Zan nuna miki ni cikakkiyar ?ar bariki ce"
Hajiya Sa'a tace.
"Ni an faWa miki ?yaleku zanyi ki karyani? Wawuya da?i?iya ashe mahaukaciya Alhaji Sama'ila ya auro bamu sani ba"
Uwani ta dinga aiko guma_guman zagi ji take yi kamar ta diro daga sama. Hatta ma?ota sai da suka shigo. Da ?yar uwani tayi shiru, shima sai da Hajiya Sa'a ta shiga mota direba ya kaita asibiti bayan ta sake kayane.
Uwani ta kai mari ta kai gwauro a falonta sai naushin hannunta take yi tsabar masifa hancinta sai bubbuWewa yake yi.
"Hahaha ai na rantse da Allah saina Warsa miki tsorona a zuchiyarki ta yadda ko waje nazo sai dai ki gudu. Bura uba ni kishiya zata yima wannan cin kashin a gaban miji in ?yaleta? Ai wallahi bata isaba da dai iyabo ce itace lusara matsoraciya."
Uwani ta jima sosai tana kai kawo. Sai da tayi wanka ta Wauro alwala ta dinga nafila kafin jikinta ya dena rawa.
Wajajen azahar Hajiya Mansa ta buWe barayin Uwani Laure ta shigar mata da abincin ranarta.
Har zuwa la'asar babu Hajiya Sa'a babu labarinta.
Hajiya Mansa ce ta kwankwasa ?ofar falon Uwani.
Uwani tazo ta buWe mata tare da tarbarta da fara 'a.
Waje ta samu ta zauna.
"Hajiya Uwani ashe kema babu damane wajen faWa?"
Ta ?arashe zancen da dariya. Uwanin ma dariya kawai tayi mata.
"To ayi ha?uri dan Allah abun ya wuce kuma dan Allah kar a sake maimaita hakan dan hankalin mai gidan in ya kai dubu nayi imanin a tashe yake. Gamu da ?an aiki gamu da ma?ota. Dan Allah kar ki sake biye mata dan in Hajiya Sa'a ce zata kuma"
Kai Uwani ta gyaWa a zuchiyarta tace.
"Ai ni nafi son ta kuma in koya mata hankali tukunna in yaso daga baya a sasanta. A fili kuma ta ja ajjiyar zuchiya tace
"Babu komai Hajiya Mansa komai ya wuce na gode da shawara"
Sallama Hajiya Mansa tayi ma Uwani ta fita.
Ita dai Uwani har washegari bata fito tsakar gidan ba da daddare Alhaji


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login