Showing 171001 words to 174000 words out of 270738 words

Chapter 58 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

gidan Sakina ki wuni tare da Hadiza, itace ba?uwa a garin" Nan sukai mata sallama, kai tsaye masallaci suka nufa suka sallaci magriba. Sai gasu a majalisar abokai nan akaita hira zuwa isha, da sukai isha suka shiga gida da ?umshin nama, Bara'u ya aiki yaro ya kaima Shafa nata kason. Gwadabe fa tun haWuwar da yayi dasu Babala har yanzu ita ke yawo a kanshi. Sukuku haka ya shiga gidan ya tarar da su Sakina da Hadiza da yaran duk anata cin abinci. Shinkafa da miya harda latas suke ci.
"Gwadabe wannan nisan kiwo haka. Tun fitar sassafe ko abincin ranar ma baku shigo kunci ba. Kai ku ba iyayenku waje, ku dawo tanan" Yaran suka dawo inda Sakina ta nuna musu, iyayen kuma suka zauna a wajen. Hadiza dai taga mijinta duk ya canja abunka da mace mai shegen kishi sai zuchiyarta take raya mata dan yaga Shafa da Abbane, shine ita da ummi ya sharesu. Tunda tace mai sannu da zuwa bata kuma tankawaba. Gwadabe kuwa da ?yar yaci abinci loma biyar, a hakanma Bara'u ke ta janshi da hira.
"Gwadabe nace naga kayan da Anty Badi'a ta aiko mun dashi. Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Hadiza ma ta gwangwajeni da kayan mutan nijar, Allah dai ya bar wannan zumunci har gidan aljanna"
"Ameen Sakina babu komai. Wata rana haka zamu zama surukan juna kinga an sake curewa an zama abu Waya" ?an darawa akayi Hadiza tana zaune kamar dutse ummi harta soma kuka ta?i kulata ga yarinyar a cinyarta, sai cin abincinta take. Gwadabe da dama a hasale yake wajen saukewa yake nema yace.
"Kinaji yarinya duk ta cika mana kunnuwa da kuka ki bata Mama mana ta tsotsa" Da fishi Hadiza tace
"Nima fa abincin nake ci kana gani. Yarinyarnan yanzu tasha ni babu wani nono da zan bata" Dama Hadiza tayi ne akan ramuwa, batasan kura ta kwanto ma kanta ba. Duk da bai kulata ba face mi?ewa da yayi idandunanshi suka kaWe.
"Sakina zanje in kwanta kaina ciwo yake yi. Gashi gobe zamu shiga Kano"
A razane Hadiza ta kalleshi ya daka mata harara yayi ficewarshi ya Waura mata tention shi kanshi yaga hakan.
Sanyin bishiyoyi masu kaWawa da ?amshin korayen ganyayyaki ne yasa Gwadabe wani lafiyayyen bacci, duk da ranshi da zuchiyarshi a jagule suke.
Washe gari sassafe su ka yi wanka. Suka karya da alala da kunu mai zafi Gwadabe ya mike yace.
"To Hadiza, Sakina mu kam zamu Wau hanyar Kano sai in Allah yayi dawowarmu. Shafa zata zo ta wuni tare daku anan. Dan Allah Sakina ki shiga dasu gidan Zul?i. Ko kuma su jira inna dawo sai in gaisu in gabatar dasu"
Har sun fito ?ofar gida ya jiyo muryar Hadiza.
"Gwadabe dan Allah bani minti biyu" Murmushi yayi yasan za'a rina. Yana zuwa ta sauke murya tayi kalar tausayi.
"Jikina yana bani gidan tsohuwar matarka zaka je. Wai dan Allah sai yaushe Iyabo zata barmu mu mori mijinmu ne? Jiya na kasa runtsawa sabida tunani, duk da ba yau Iyabo ta taSa sani nai asarar darena ba. Amman abun ya haWemun harda canjin dana gani jiya a wajenka sabida kana zumuWin ganin Shafa da Abba"
Kallonta yake tayi tun sanda ta soma Magana. Da dariya ya fashe da yaga kuka take ?o?arin yi.
"Hadiza Matata ta kaina. Iyayen kishi su da kansu. Yafa kamata ki dena yadda da duk abinda zuchiyarki zata rayo miki gudun faWawa tarkon dana sani. Iyabo ta tsone miki idanu da yawa naga ko Shafa dake ainihin kishiyarki abokiyar gurzawa bakya kishinta rabin yadda kike kishin Iyabo, ya kamata ki kama muguncinki, karki bari ki sire mun. Mu zamu tafi karmu makara"
A tsaye a ?war gidan ya barta bata shige ciki ba har saida suka ?ule ta ja jiki a sanyaye ta shige hantar cikinta sai kadawa take yi"

Kano:.
Saukarsu Gwadabe ke da wuya a garin Kano suka wuce unguwarsu Iyabo gidansu Uwani. Mahaifiyar Uwani Hajiya ce ta fito.
"Au Gwadabe shine kuka tsaya a waje sai kace ba?i bismillah ku shigo"
Dole haka suka kutsa cikin gidan. Hajiya ta shinfiWa musu tabarma suka zauna aka gaisa a nitse.
"Dama Hajiya gidan Uwani muke son yaro ya rakamu." Hajiya tace.
"Allah sarki ai kuwa kunyi saSani Uwani ta tafi JaSiSi wajen Aminiyar tata Iyabo acan take aure, to tafiyar ta gaggawace ma dai. Kuma tunda ta tafi ba mu yi waya ba, yaranta ma suna nan tare dani"
Tashi Waya Gwadabe ya koma kalar tausayi. Ba ba?in ciki yake da auren Iyabo ba. Ba kuma baiji daWin jin tana gidan aure bane. Kishine na zahiri wanda bashi da masarrafarshi. Sai yaji ?irjinshi yayi mishi nauyi.
"To Hajiya ko zan iya samun lambar wayar Uwanin ko ita Iyabo Win?"
"To gaskiya ni babu waya a hannuna. Yara da zasu baku lambar gashi duk kowa ya fice. Sai dai in gobe zaku dawo sai in sa yara su rubuta lambobin a takadda" Bara'u yayi carab yace.
"A'a ki barshi Hajiya. Nanda sati Waya ma dawo kafin lokacin Uwanin ta dawo sai muzo a kaimu" Hajiya tayi jim tace.
"Amman Allah dai yasa lafiya ba wani abun bane ba ko? Naga kamar kun matsa lallai sai kunga Uwanin" murmushi Gwadabe yayi yace.
"Babu komai wallahi Hajiya. Dama dai labarin Iyabo muke son ji a bakin Uwani. Baya ga wannan babu komai" Dariya Hajiya tayi irin ta manya tace.
"Allah sarki. Ai indan wannan ne ba dole sai kun nemi Uwani ba. Iyabo dai tayi aure a dangin mahaifiyarta. Dan kamar Uwani tace mun da gyatumar yaron da ita Iyabo ta aura. Da gyatumar Iyabo ya da ?anwa suke. Sun jima suna son junansu tun su Uwanin da IYABO suna Saudiyya. Auren bai jima ba da akayi shi."
Sai kallon kallo tsakanin Bara'u da Gwadabe. Gashi babu damar su matsama Hajiya da tambayoyi. Saidai abubuwa da yawa sun cunkushe kan gwadawa. Na farko shine Saudiyya da yaji Hajiya tace tun suna can. Na biyu jin a irin dajin da Iyabo taje tayi aure. Yasan labarin ?auyen a bakinta amma bai san komai baya ga labarin bakinta ba."
"To Shikenan Hajiya mun gode. Mu zamu koma, a isar mana da sa?on gaisuwarmu wajen Uwani dama Iyabon." Cewar Bara'u kenan. Shi kam Gwadabe yana cikin dabaibayi.
"Zasu ji. Ya yaran duk suna cikin ?oshin lafiya dai ko?" Bara'u yace.
"Suna lafiya. Suna karatunsu arabi da boko. Hajiya mu zamu wuce to" Bara'u ya zaro jaka biyar ya ajjiye ma Hajiya. Sukai mata sallama suka fito.
Suna zaune a motar Takai Bara'u yace.
"Wannan shirun yayi yawa Gwadabe me kake nufi ne. So kake IYABO ta zauna babu aure ko me? Naga kai mata biyu ka aura rana Waya" A fusace yace.
"Na auresu ne a bisa tayin aurensu da akayi mun. WaWanda sukaimun tayin sun fi ?arfin komai a wajena. Iyabo itace rayuwata Bara'u "
"To itama saika Wauka umarnin mahaifiyarta tabi tunda ai kaji ance Wan uwanta ne ta aura. Ni na Wauka ma Debisi ne zai aureta wallahi"
"Hakane Bara'u. Ina tayata farin ciki da auren data yi. Sai dai ina tayata jimamin zaman ?auye. Dan a yadda take bani labarin ?auyan ?auyene ?ayau, gasu da ?auyanci da ?arancin addini. Ko asibiti babu fa, balle wutar lantarki, kaga babu ruwa babu kwalta, babu makarantu." Jim Bara'u yayi yace.
"Sanin da ba. Kasani ko sun samu tallafin gwamnati. Ita kanta sau Waya fa kace ta taSa zuwa tun tana yarinya. Inka lissafa daga lokacin da taje zuwa yanzu ?ila sun samu ci gaba. Ko shekara biyar baya ka kalli takai ai kasan an samu gagarumin ci gaba ko? Ni batun zuwansu Saudiyya ita da Uwani shi nayi tunanin zaka yi nazari akai ma" Kai Gwadabe ya dafe tare da lumshe idanunshi. Baice komai ba, tunani da lissafe lissafe yake ta faman yi har Allah ya dawo dasu Takai lafiya.
Cikin gidan ma daya shiga wani tarin tulin takaici ya tarar. Hadiza sai kumbura take yi kamar kwaSin gurasa. Sakina da Shafa su kuma sunata faman hirarsu da nishaWi. Gefe guda Gwadabe ya zauna jigum.
"Bara'u Gwadabe ba lafiya ne?" Bara'u ya amsa ma Hadiza da cewar.
"Kanshi ke ciwo ga hanya mun shawo" Shafa sai tabar abinda take yi ta koma wajen mijinta ta kai musu abincinsu. Lamarin daya sake zugunWuma fishin Hadiza ta sakei hawayen da take ri?ewa kenan. Ta kullace wannan wula?ancin da Gwadabe yake yi mata dan yaga ya kawota garinsu.
Da yamma li?is suka dunguma gidan Zul?i sun ko yi saSani Zul?i da iyalanshi basa nan sun tafi wani taro na masu kujeru a hannu a Abuja. Gwadabe ya kwashi su Hadiza harda Bara'u da Sakina suka je. Kwanansu biyu a gidan Tamu. Ayashe itama ta tarbesu tarba me kyau sosai. Nan da aka haWu dole saida labarin Iyabo ya ratso ta cikin zancan. Hadiza tana mamakin irin tasirin Iyabo a cikin rayuwar Gwadabe da duk makusantanshi. Wai shin wanne irin kirkine da Iyabo, wannan irin kawaici da juriyane da'ita? Hadiza taima kanta tambaya. Kishi na rugurguza zuchiyarta d gangar jikinta. Saita tsinci kanta cikin son zama kamar Iyabo badan komai ba sai dan kishin mijnta da son mantar da Gwadabe Iyabo. Wannan dalilin nata yasa ta cakaloma Ayashe da Sakina zancan Iyabo. Sai dai me da suka soma zana mata Iyabo sai taji e lallai takai macen da dole ta tsaya a zuchiyar Wa namiji. Sai taji a madadin ta zauna kishin Iyabo ya hanata jituwa da Gwadabe ai gara ta ari rigar Iyabo ta yafa. Amman me a daren ranar Hadiza ko runtsawa takasa yi. Sai jujjuya al'amura take yi a zuchiyarta wata zuchiyar tace da'ita.
"Ashe baki cika mace ba in har sai kinyi koyi da halayen tsuhuwar matar mijinki. Kenan ke ba zaki iya juyarma da mijinki hankali ba sai kin zama irin matarshi? Ai kamata yayi kema ki Sullo mishi da sabon salon tarairaya da tattalin daya doke na beyerabiyar matarshi ba ki tsaya kina bin diddigin halayenta ba" Ai sai ta hau kan shawarar zuchiyarta tayi Ware_Ware.
Haka dai suka gama kwanakin da zasu yi suka tarkato suka baro Takai da tarin tulin tsarabobin da Sakina da Bara'u sukai musu ?unshi_?unshi. Motarsu tana gudu a hanya. Hadiza zuchiyarta na gudu da tunanin mafitarta itafa tana ji tana gani ba zata bari Gwadabe ya sauya mata ba ta zama itace ma bare ba. Jibi Shafa tun shigowarsu motar take ta janshi da hira ya sake sai amsata yake yi sunata nishaWinsu. Ajjiyar zuchiya ta sauke ha?i?a ta fahimci Gwadabe ya gundura da ?orafinta da saurin fishinta. Ta daWe tana lura ita Shafa irin matannanne da kamar basu san ciwon kansu ba, kuma ba komai ke Sata musu raiba. Da ire_iren wannan tunanin bacci yai awon gaba da Hadiza Wiyarta na rungume a jikinta itama baccin take yi.
Juyowa Gwadabe yayi ya kalleta ya lumshe idanu. Hadiza tana da wani matsayi mai girma a zuchiyarshi yana sonta. Sai dai Wabi'unta na ?orafi, yawan fishi sun kaishi ma?ura shi yasa a wannan karon shima yayi watsi da lamarinta. Ummi ya zare a hannunta hakan yasa ta farka da sauri tare da sake cabke Wiyarta.
"Nine ba wani ba. Kawota ki samu kiyi baccinki"
Mi?ata tayi ta koma baccinta ba tare da tace dashi komai ba.
Sai dare suka isa gidan sosai. Sun jima sosai suna buga ?ofar gidan kafin Mammada yazo ya buWe musu.
"Sannunku da dawowa mutanen najeriya kune da tsohon darennan Gwadabe?" Matan ciki suka yi, Gwadabe ya tsaya suka gaisa da Mammada kafin ya ?ule Wakin Shafa.
Hadiza tana kwance sai juyi take yi fitowarta daga wanka kenan. Tayi tsammanin Gwadabe ko babu komai zai le?o yai musu sallama ai. Amman sai taji shi shiru a Wakin Matarshi.
Washe gari ma ta jima sosai tana jiran ya shigo su gaisa da taji shirun yayi yawa dole ta goya ummi ta fito ta nufi Wakin Shafa dan a ?ofar Wakinta aka jibge tsarabar.
"Shafa Gwadabe yana ciki kuwa?" A kitchen ta samu Shafa tana zuba abincin da zata ci. Ita sai lokacin ma ta tuno ashe ko karyawar batai ba. Sai da Shafa ta gaisheta tace.
"Da wurwuri ya fita zaije cin kasuwar Damagaram. Ko ya shiga Wakinki kina bacci ?ila" Wannan abu ya daki Hadiza sosai, sai dariyar ya?e tayi tace.
"Babu mamaki kam dan ban jima da tashi ba. Bari in kunce tsarabar zan shiga ma da su Baba nasu'
"To Yaya gasu nan. Nima inna gama karyawa zam shigo cikin gidan "
Hadiza dai zuchiyarta na tafasa ta yi cikin gida da tsaraba. Saida ta mikawa matan malam nasu tsarabar kafin ta nufi Sarayin Baba Fhatsima.
"Zafine a garinne Hadiza naga dul kin rame, ga ?uraje duk sun feso miki?" Cewar Baba Asshi dake du?e tana dauraya. Baba Suwaiba tace.
"Takai fa ?auyene sosai. Ni nasan ?auyan da jimawa dole su rame ai" Hadiza dai bata ce komai ba tayi murmushi tasan abune mai wuya ?an gidan su canja halinsu. Tana shiga ta samu Baba Fhatsima na shan fura. Yaya Tasi'u yana zaune a gefe yana cin ?wadon zogale."
"Hadiza kaddai kune jiya da daddare kuke ta faman dukan ?yaure?" Cewar Yaya Tasi'u kenan. Murmushin dole tayi mishi tace.
"Mune Yaya Tasi'u shigowar dare muka yi. Ina wuni yasu Safara'u, da Anti Badi'a?"
"Basa nan sunyi tafiya shekaran jiya suna da biki"
"Baba ina kwana mun sameku lafiya?" Abunka da uwa tuni ta gano Hadiza na cikin damuwa ga idanunta sun farfaWa.
"Lafiya lau ya mutanan Takai, inasu Sakina da Toye?" Sai Hadiza ta Wan sauke kanta sai hawaye shar_shar. Yaya Tasi'u ya mi?e tsaye yace.
"Sakara bata da aiki sai shirme. Baba ni zan wuce wajen aiki saina dawo" Baba Fhatsima tace.
"To a dawo lafiya. Kar ka manta da maganarmu akan Balaraba kayi tunani ina sauraren amsarka daga yau zuwa gobe" Bayan Yaya Tasi'u ya fice Baba Fhatsima ta mayar da hankalinta akan Hadiza.
"Wani abunne ya faru a Takai Win. Ko ke da mijinkinne, ko kuma abokiyar zaman taki ce? Ki nutsu kiyi mun bayani" Cikin shesshe?a Hadiza tace.
"Baba Tunda muka shiga Takai Gwadabe yaga Shafa da Wanta shikenan ni da Ummi ya juya mana baya. Sai fishi yake yi, kuma fa har gidan tsohuwar Matarshi a Kano saida abokinshi ya rakashi suka je. Ni fifikon da yake nuna mun ya isheni" Baba Fhatsima tayi shiru cikin karantar yanayinta tace.
"Hmm Hadiza ho. Wallahi in kika yi saken da Gwadabe yaga wallanki to wallahi kin shiga uku zaman bazai miki daWi ba. Hala kin isheshi da ?orafine, ko kuma wata damuwar ke damun ranshi har kika ga ya canja. Ko kin tambayeshi dalilin canjin nashi?" Hadiza ta girgiza kai halamar a'a"
"Kinji irin shashancin naku ai yaran yanzu. Yanke hukunci ba naku bane, zaunar da miji zakiyi cikin kulawa da nuna damuwa da sannu saiya warware miki cikinshi. Da haka mace take zama sirrin mijinta abokiyar shawararshi. In kikayi sake Shafa ta samu wannan kambun bake ba. To abubbuwa da dama zasuita faruwa da mijinki, ?alilan daga cikine zaki iya ji. Masu yawan yaci ya birne da abokiyar zamanki. Hadiza namiji wawane, kuma sau?in sarrafawa garesu Wallahi. Abinda yasa na kira namiji da wawa shine. Shifa kulawa da tarairaya, sai ladabi da biyayya,iya girki, iya kwalliya, tsabta iya Wauke lalurarsa. Shine fa namijin kuma shine zaman auren. Ana mallakar miji da kissoshi sunfu kala saba'in bari in jero miki kaWan a cikinsu.
Akwai kirsar magana
Akwai kirsar tafiya a gaban miji, ko kishiya
Akwai kirsar rauni, yawan kuka
Akwai ta shagwaba
Akwai kirsar nuna ma miji ke kullum bai isarki a shinfiWa
Akwai kirsar shimfiWa
Akwai kirsar sa sutura
Akwai kirsar iya girki
Akwai kirsar ciyar da miji abinci a baki
Akwai kirsar yima miji wanka
Kirsoshin suna da yawa, ko wanne guda Waya kika Wauka zaki zama ta daban. Kuma zaki zauna daram a zuchiyar mijinki. Shine zakiji yana faWin alkhairin Allah ya kaima wance. A gaban matarshi zai iya yabon matar data mallakeshi da Tata kirsar namiji ba kunya gareshi ba. Ko kiji yana da wancece da yanzu tayi mun kaza, ko tace kaza. Namiji ya barki da sakakken baki. Su basa raina sauyi, ko jin daWi duk ?an?antarshi. Abubuwa da dama mun Wauke kanmu akai bamu Waukeshi da mahimmanci ba, shigowar boko duk ya wanke muku kanku kun dena biyayya. Mu a zamaninmu a wani gari da Malam ya taSa kaini muka zauna lokacin sana'ar Malam sai da gishiri da manda ne. To gidan da muke haya akwai wata Fatu bafulatanar Gombe ce. Akan rashin sa ruwa a buta mijinta ya saketa sai garinsu ta koma. To wani akan shara zai iya rabuwa da mace. Wani duk waWannan ?anunun abubbuwan harma da manyan bai dameshi ba babu ruwanshi.
Amman kinsan babban abinda maza suka wasa shine tsananin kishi, zargi, ?orafi, bin diddiginsu dan ganin laifinsu, ?azanta. WaWannan abubuwan dana jero duk halinki ne banda ?azantar shi yai silar mutuwar aurenki na fari.
Ke ba zaki zama mai kawaiciba, ki gani ?iri_?iri ki nuna baki gani ba. Kiji ki toshe kunnenki. Dole sai anayi ana haWawa da halin ko in kula, koda hakan zai dameki.
Hadiza ki kiyaye abinda zai maisheki bora, Gwadabe fa yana ha?uri dake" Hadiza taci kukanta mai isarta. Baba Fhatsima batai yun?urin hanata ba har saida tai shiru dan kanta kana tace.
"Sai ki kiyaye. In ranar kwananki ya zago saiki bashi ha?uri a bisa kusakuranki da kinfi kowa saninsu. Kuma cikin lallami ki doki cikinshi ya baki labarin matsalarshi. Ke kuma saiki magance mishi damuwar. Inta adda'ace kice zaki taya shi da adda'a. In kuma na shawarane ki bashi shawara, inma na nasihane ki mishi. To zaki ga ko farin cikin ya shiga kece ta farko. Ke namiji sau?in kai gareshi in baki kwaSeshi ba sai kiga har asirin kishiyarki ya fasa miki shi babu ruwanshi. Tashi ki koma Sarayinku"
Sallamar Shafa ce ta katse musu hirarsu. Baba Fhatsima ma ce ta amsa mata ta shigo suka gaggaisa.
"Malam baya nanne Baba? Shafa ta tambaya"
"Bayanan sun tafi taron biki cikin Zinder sai da yamma zai dawo. Ya kika baro mutun Takai dana Habuja?" Murmushi Shafa tayi tace.
"Duk suna lafiya Baba. Ga wannan turmin zanine wana yace in kawo miki"
Ta mi?a ma Baba wannan turmin zani holan. Baba Fhatsima taita godiya. Anan dai ta tafi ta bar Hadiza dan saida taci ragowar zogalen da Yaya Tasi'u yaci ya rage, ta kora da fura kana ta tafi.
Tana komawa gidan ta samu suna abinda suka saba. Wannan karon da matar Mammada da matar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login