Showing 135001 words to 138000 words out of 270738 words

Chapter 46 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

kawai sai inji kishi kinsan Allah bana sanin sanda nake lailayon mata uwar ashariya. Kinga ina girma a wagga lamari?"
Dariya suka kwashe dashi. ?ararrawa aka buga dole Hadiza na jin daWi ta tafi aji dan ba yara darasi. Data dawo suka Waura, Sadiya ta zauna ta karanto mata abubbuwa masu girman gaske ( Sannu a hankali zaku jisu a aikace cikin labarin) WaWannan maganganu su suka sake buWe kan Hadiza tayo farin ciki gaya. Ana tashi ta wuce wata ?ar ?aramar kasuwa dan yin cefanen naman rago ta siyo, sai bushasshen kifi, da cefanen tumaturi da su tattasai, attaruhu. Albasa an kaita dashi kusan rabin bihu ma. Sai kankana kwallo daya da lemun tsami manya na nera hamsin.
A gajiye ta shigo gidan, babu kowa a tsakar gidan Wakinta ta buWe ta shiga. Ta Wan kwanta ta huta bacci ya Webeta zuwa la'asar. Da sauri ta mi?e ta fito, daidai Shafa ta fito daga banWakinta da halamun alwala ta Wauro"
"La Yaya yaushe kika dawo?"
"Na dawo bayan azahar, nayi tunanin ko bacci kikeyi shi yasa ma ban tasheki ba ni kam. Kinga bacci nayi yanzu na farka" Shafa tace.
"Ai kuwa bacci nima na tashi yanzu. Dan Wazu naso yin baccin amman an Wanyi rikici a gidan akan shanya abinda ya hanani baccin kenan" HaSa Hadiza ta ri?e.
"Akan shanya kuma, to dawa dawa su kai faWan?" Shafa tace.
"To matar wancan Wakin na gaba can, da matar Wakin dake kallo nakine. Sunyi faWa sosai harda fashe bokatai fa" Baki Hadiza ta taSe.
"To Allah ya kyauta, bari inyi sallah " Tayi wucewarta banWaki, Shafa itama ta shige nata Wakin. Tana idar da Sallah ta sauya kayan jikinta zuwa wata ?ar doguwar riga mai sau?i haka, ta fito domin soma girki. Matan gidanma kaf Winsu suna kitchen anata Suruntu. Gida ya kaure da ?amshi kifine, kazane kowa dai da abinda yake girkawa. Sanwar miya Hadiza ta tsayar. Tana tsintar waken da zata zuba a miyar. Baba Suwaiba ta fito tsakar gidan tana sababin danme za'a hana surukarta shanya.
"Ke Fatima ki fito fitsararriya kwashasshiya fito inji me kika taka" A madadin ita ta fito sai Sabitun ya fito da kanshi. Rashin kunya yayi mata, dama basa ganin kowa da gashi a gidan. Nanfa rikici ya Salle rikicin da sai da Malam da Baba Fhatsima suka yo tattakin shigowa. Daidai Baba Suwaiba tayi Wamara ta nufi Sabitu da duka.

Malam
"Yayi kyau Suwaiba Nagode gaya. Ku kuma duk ku watse ko wacce ta shige Wakinta. Gobe da safe daku da mazajen naku ina nemanku a gida bakwai na safe. Kai kuma Sabitu sannu da Uwar t????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  aka kake sa'insa sabida Wiban albarka ko?" Iyakar abinda Malam yace kenan ya juya ya fice. Idanu Hadiza da Baba Fhatsima suka haWa. ?unci da damuwa ?arara a shimfiWe a fuskar Baba Fhatsima. Kai ta gyaWa ta bi bayan mijinta. Suna fitowa Baba Suwaiba ta biyo bayansu. Tsautsayi malam bahaushe yace baya wuce ranarshi. Kuma shi dana sani ?eyace. Malam na ganin fitowar Suwaiba yace.
"Na sakeki Suwaiba. Aurena dake ya ?are, na gaji da ba?in ciki da takaicin da kuke Wauramun ina shanyewa tsawon shekaru. Zuchiyata tarwatsewa kukeso tayi, ko faWuwa kuke so inyi in mutu in bar baya da ?ura. To ta faru ta ?are kije dan kanki." Baba Fhatsima ta dafe ?irjinta. Baba Suwaiba kuma ta fashe da ihu harda kururuwa. Malam ya tafi ya barsu su biyun a tsaye yana tafe dafe da kanshi da yake jin kamar zai tarwatse.
"Ki ?arama bokanki kuWi Fhatsima burinki ya idasa cika. A baya har hauka kika sa nayi na fito tsirara. A yanzu kinsa Malam ya sakeni ni Suwaiba. Ki rubuta ki ajjiye akwai ranar Waukar fansa tana tafe duk daren daWewa ni Suwaiba saina saki zubar da hawaye." Cikin kuka take maganar. Murmushi Kawai Baba Fhatsima tayi tace.
"Allah ya kyauta. Nasha tabara na sha yasin"
"Ki ?ara da amanan rasulu. Fhatsima sai naga bayanki dake da yaranki duka, dani kike zancan" Har Baba Fhatsima ta ?ule Baba Suwaiba na zage_zage.
Wannan lamarin ya rura wutar hatsaniya mai girma hatsaniyar da a tarihin rayuwar iyalin malam ba'a taSa yin irinshi ba. Dan abun yakai harda faWa da makami a tsakanin yaran Baba Suwaiba da su Auwala da suke kare uwarsu. Baba Fhatsima sai kulleta akayi ita da Malam a turaka. Yaya Tasi'u kuma ganin abun ya wuce gona da iri sai ya kira ?an sanda aka fita da yaran Baba Suwaiba zuwa police station domin yima tubkar hanci.
Malam yana goye da hannunshi a bayanshi sai kai kawo yake yi harda hawaye a idanunshi. Abun a tausayane ace dattijon magidanci yana hawaye ku kanku kunsan abun yakai intaha. Tunaninshi yake mayarwa baya a lokacin da suke rayuwarsu ta talauci da tsantsar soyayya shi da Fhatsima. Fhatsima tayi mishi son da harya koma ga Allah ma bazai samu macen da zata soshi rabin haka ba. Gashi a sakamakon giyar jini a jika da giyar kuWin da bai taka kara ya karyaba ya Webo ma kanshi kara da kiyashi Waukar marar sani. Yau shine aka tura a Waki ?a?an cikinshi na fito na fito dashi kan uwarsu. Fhatsimar daya raina a baya ita da ?a?anta a yanzu sune garkuwarshi. Madallah da mace tagari, madallah da uwa tagari.
A daren Malam ciwonshi ya tashi bil ha??i gaga_gaga aka wuce dashi asibiti. Hankulan kab ?an gidan a tashe yake gaya. Dan WaiWaiku daga cikin ?a?anshi masu mishi fatan mutuwane kawai sukai baccinsu harda minshari. Masu son rayuwar malam sune suka kasa rintsawa har zuwa wayewar gari.


IYABO:.
Satinmu uku a asibiti. Sai godiyar Allah domin jikin Dada ana samun haske sosai, har hira muna yi da'ita.
Da safe da Yaya Hamma ya shigo ya mi?o mun Madara mai zafi a cikin gora. Sai Dada ta dubemu tace.
"Hamma ko bayan babu raina Jabu itace matarka. Nayi imanin a hannunka zata samu nutsuwar data rasa a baya. Ina mata fatan samun miji tamkar mahaifinta Adetoye. Mutumne mai yakana wanda yasan darajar mace." Yaya Hamma yace.
"Dada ai Jabu ?anwatace ko bani na aureta ba sai inda ?arfina ya ?are a kanta. Wannan aure duk dangi suna farin ciki dashi, Jabu zata dawo cikin danginta."
Dan a wannan lokacin labarin soyayyarmu ya bazu, Hama kuma kamar mahaukaciya haka ta zama. Dan soyayyar da muke ma juna ni da Yaya Hamma soyayyace wacce baki bazai iya faWeba, al?alami bazai iya rubutashi ba. Idaninmu a rufe suke ruf. Duk wani bugun zuchiyata ankai an kawo da soyayyar Hamma yake bugawa. Shima nunamun kulawa yake yi irin kulawar da banyi zatonta a wajen bafulacan daji ba.
Ina ba Dada Madara a baki tana sha kamar a mafarki saina hango Uwani tafe da Saleem Yana biye da'ita har zuwa gadon da muke. Gabanane ya yanke ya faWi muka ?urama juna idanu ni da Saleem babu um babu um_um. Kallon kewa da tsantsar so Saleem yake yi mun. Ni kuma ina mishi kallon tausayi da dana sanin saninshi, domin son maso wani babban ciwone, na WanWani Wacinshi akan Debisi. Saye Saleem yake cikin ba?ar jallabiya wacce ta sake bayyana sirrin kyanshi, gemu, ?asumba, yalwataccen gashin ido haWe dana gira, da sumar kanshi su suka zame mishi wani irin adon da suka bashi wani kyau me sanyi, rawanine yane a kanshi mai fari da ba?i, sai ba?in agogo a Waure a tsintsiyar hannunshi, ?afarshi saye da ba?in takalmi me kyau, ga ?amshinshi duk ya cika wajen . Ana cikin wannan kallon_kallo Yaya Hamma ya shigo shi da Baffa Musa. Uwani ta gaishe da Dada tayi mata yaya jiki. Saleem sai sallama kawai yayi mata, shi ba hausaba, Dada ba turanci ba
"Jabu ba?i kikayine?" Cewar Baffa. Shi ko Yaya Hamma gaisawa su ka yi da Uwani tunda dama ya santa. Saleem ya mi?o mishi hannu suka gaisa. Cikin harshen larabci Uwani take mishi bayanin Dada ce mahaifiyata, Yaya Hamma kuma wanane, sai Baffa Musa wan Dada.
Tsugunnawa yayi har ?asa ya gaishesu da turanci. Baffa Musa yace.
"Jabu wannan ai sai nake ganin ba bafulatani bane kamar Balarabe ne ko, amman ba larabci yake yi ba?" Yaya Hamma na Wago na duba. Shima ni yake kallo sai naga idanunshi sun sauya launi kamar yasan abinda ke wanzuwa, dan kallon tuhuma yake yi mun. Duk saina ruWe na dibibice ainun na kasa amsa maganar Baffa sai Uwani ce tace.
"E Baffa Balarabe ne daga ?asar Saudiyya yazo wajen Jabu. To munje can gidan shine akai mana kwatancen asibitinnan muka tawo" Siraran hawayene suka zubo a idanuna dana kalli Yaya Hamma yana tsaye akan ?afa Waya, ?irjinshi sai hawa da sauka yake yi. Da sauri na share hawayen nawa dan kawar da zargi, ina cikin tsaka mai wuyar fita, bana fatan in aikata abinda zai sosa ran Yaya Hamma. Yana da mugun kishi akan abinda yake so, a bayama da bai kai ga furta mun so ba yayi kishin Debisi, balle yanzu da maganar Aurenmu tayi nisan da ba da ban ciwon Dada ba da tuni ina Wakina. Baffa Musa ma yace ana sallaamar Dada daga asibiti washe gari za'a Waura auren in yaso daga baya in Yaya Hamma ya gyara inda zan zauna na tare.
"Yazo wajen Jabu?" Baffa ya tambaya yana jimamin lamarin. Hamma ya kalla shima, shi dai baice komai ba sai idanu.
"E Baffa akwai kayanmu ne a hannunshi na sare_saren dana faWa muku nayo. Uwani kayanne suka iso?" Na tambaya da sauri ina kashe mata idanu. Uwani ta riga tasan me nake nufi sai tace.
"Kaya Alhamdulillah sun iso suna Kano a gidana" Shi kuwa Saleem ni kawai yake kallo. Yaya Hamma kuma ya sauke kanshi ?asa yana kallon ?afarshi, sai wasa da ?afarshi dake kan wadda ya tsaya akai yake yi.
"Dada Allah ya ?ara sau?i. Jabu bari mu ganki mana zamu jiraki a waje" Uwani na faWin haka ta dubi Saleem tace.
"Yalla Saleem" Saleem ya dubi su Baffa yace.
"Assalamu alaikum"
Yasa hannu a ajjihu ya zaro kuWinsu na Saudiyya masu tsoka ya ajjiye a gefen ?afar Dada. Yabi bayan Uwani suka fita. Illahirin jikina ni kuma rawa yake yi. Yaya Hamma na duba, ni yake kallo a lokacin idanunshi kamar garwashi ?irjinshi ya tsananta hawa da sauka, ya riga yasan akwai wata a ?asa, dan ance marar gaskiya ko a ruwa zufa yake yi.
"Jabu kije ki samesu mana kar ki barsu suita faman jiranki" Inji Dada da bata san dawar garin ba. Kofin madarar na ajjiye da jan ?afa wallahi na fita. Soyayya gaskiya ce, a wannan lokacin na ji haushin Uwani ainun nasan da gayya tayi maganar domin ita tafi sona da Saleem fiye da Hamma. Ina fita na hangosu a zaune a wani benci, nan na nufesu na isa da sallama siririya a bakina illahirin jikina a mace mus. Murmushi Saleem ya sakarmun na farin ciki. A zahirin gaskiya nasan Saleem yana sona, na yarda da girman son da yake yi mini. To amman Yaya Hamma yayi tasiri a rayuwata baki Waya, salon soyayyarshi ya wuce salon da zan tsaya kwatantawa, jin sonshi nake yi tamkar mahaWin rayuwata.
"Alhamdulillah nagode Allah buwayi gagara misali daya sake ?addara saduwarmu dake IYABO. Ha?i?a wannan ranar tana da daraja a wajena." Cewar Saleem kenan dake magana da turanci hannunshi a sama halamar ro?o, haka kanshi yana kallon sama. Ni kuma nama rasa ta cewa. Gabana sai faWuwa yake yi, tunanina da hankalina yana wajen nemo kalaman da zan wanke kaina dasu a wajen Yaya Hamma.
"Iyabo gani na biyoki da batun aurenmu. Inaso a gama komai insan inane matsayata kafin in koma ?asata, dan in tafi ma da iyayena sahihiyar magana" Ya sake dabaibayeni da wannan kalami a karo na biyu. Shirun nawa yayi yawa, Uwani ce ta zungureni na dawo cikin hankalina, na dubi Uwani ta gallamun uwar harara, na dawo da kallona ga Saleem shi kuma wani irin kallon soyayyar gani kasheni yake yi mun. ?ofar Wakin majinyata na duba, Yaya Hamma na hango a tsaye ya kakkafeni da idanu. Da yaga mun haWa idanu sai kawai ya gyaWa kanshi ya nufi hanyar ficewa a asibitin da wani irin mugun sauri. Ai saina mi?e ina shirin binshi da sauri. Uwanice ta finciko hannuna ta dangwarar dani a bencinnan na dawo na zauna daSas.
"Wallahi Iyabo ki shiga taitayinki akan wannan Hamman naki abu sai kace taliyar Hausa ke ko kunya ma ba kya ji. Soyayya sai kace asiri, irin auren wahala da ci bayan da kike son yi kenan, a irin ?auyen da ke kikeson kiyi zaman aure kenan a bukka zaku gudanar da soyayyar? Baki da hankali Iyabo wallahi. Hamma asiri ?ila yayi miki in ba asiriba banga dalilin da zaisa ki ma?ale mishi irin haka ba. Arziki na kiranki ke kinfi son ki zauna a talauce. Ki tuno da irin bautar da kikayi a tafiyar aurenki na baya. Jibeshi ?azamin banza sai tsawo kamar taliyar murji amman a haka kike so. Ji wani irin hawa da sauka na iskanci da ?irjinshi yake yi wai shi mai zuchiya. Ke kuma da kin Wibi ?afa zaki bishi mu ki barmu a gantale a zaune ko?."
Murya ta sassauto.
"Iyabo kiyi ha?uri ki amshi Saleem a matsayin miji, wallahi zaki ji daWi. Kiyi tunani ni ?awarki ce. Ko Dada da kikeson ki taimaka ta dalilin auren Saleem zaki fi samun damar taimakonta. Nasan kina da ?udirin zama tare da ?an uwanki ko dan gyaruwar addininsu kamar yadda muka tattauna. Amman Iyabo ai zaki iya saka su a makaranta ba dole sai kece zaki koyar dasu yadda zasu bauta ma Allah daidai ba. Ya fa kamata ki duba"
( ku zaSa mun miji masoya wannan labari. Ku kanku nasan kun shiga cikin tsaka mai wuyar fita ko? Ina kuma gani Iyabo. Sannan kar kuyi fishi dani akan faWawa son Hamma da nayi. Hamma ya wuce duk tunaninku. Sa?onninku sun iso gareni ina godiya da soyayya. Akwai wata baiwar Allah data bani dariya da take cewa inna auri Hamma ba zasu yi mun adda'a ba sai dai suce Allah shi ?ara. Wallahi nayi dariya sosai. Ku dai ku biyo labarin kuji )


Anan ?arshen littafi na biyu ya tsaya.
Zamu je hutun kwana goma kafin mu Waura daga inda muka tsaya a labarin wasafa farin girki. Yanzu wasan ma zai soma
=?O?
Duk mai son turare yayi magana dan Allah da wuri
*ASSALAMU ALAIKUM*
_GODIYA MARAR ADADI A GAREKU MASOYA WANNAN LABARIN_
_NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN SUKUTUM ?INSHI ZUWA GA AMINIYATA, SAHIBATA, MASOYIYATA, SURUKATA, KHADIJA MAIDOKI, MATA A WAJEN PRINCE, ?AR GABAN GOSHIN YARIMAN MIJINTA._ ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MIKI A DUK INDA KIKE


NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE

LITTAFI NA UKU
GAWURTATTU UKU
NA
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


SHAFIN FARKO (1)

IYABO:.

"Iyabo da wuya ta kasheki gara daWi ya kasheki. Ki tuno da irin taimakonmu da Saleem yayi mana a lokacin da muke da bu?atar taimakon . Dubi Ahalinshi yadda suka karSeki duk da kina matsayin ba?ar fata, beyerabiya. Ki duba kuWi da Saleem ya kashe miki. Kayanmu gashi sun iso suna gidana. Ki duba Saleem ya baro ?asarsu yazo gareki Iyabo. Irin sakayyar da zaki mishi a ?asar taku kenan?" Uwani ta Waureni tamau da dukkan jijiyoyin jikina. Illahirin jikina a mace yake murus.
Gaskiya Saleem bai cancanci irin wannan tarbar daga gareni ba. ?an murmushi nayi na dubeshi. Ya riga da ya gane akwai matsalane, dan yanayinshi ya sauya, jikinshi kuma yayi sanyi.
"Zuwana ya haifar da matsalane Zauja? Ya tambayeni da larabci.
A'a Saleem. Ya hanya ina fatan kazo lafiya?" Murmushi yayi tare da sauke ajjiyar zuchiya har yana dafe saitin zuchiyarshi.
Hararata Uwani tayi, ta mi?o mun wata jakar kwali wadda sabida ruWu ni ban ganta tare da jakarnan ba sai yanzu.
"Gashi wannan tsarabarki ce daga surukarki"
Fizgewa nayi dan a wuya nake da Uwani. Dariya tayi kawai tace.
"Iyabo kenan. Ba?in halin naku na yarbawa masu kwalo_kwalo ya motsa kenan?"
Banza nayi mata, na mayar da hankalina ga Saleem tare da yi mishi godiya da tsaraba, na tambayi lafiyar mahaifiyarshi da danginshi duka.
"Duk suna lafiya kuma sunce a mi?o miki sa?on gaisuwarsu gareki. Kuma sunyi mun fatan nasara. Meke damun Mamane haka, sannan me yasa aka kawota wannan asibitin, kuma Wakin duk mutane." ?an murmushi nayi. Duk wannan abun fa hankalina yana ga Hamma.
Babu komai asibitin yana da kyau. Kuma jikinta ya warware an kusan a sallamemu mu koma gida in sha Allah."
"To Shikenan zanje in yi sallah inna dawo sai mu tattauna, kuma a gabatar dani ga magabata ayita ta ?are ko zan samu nutsuwar zuchiya."
Kwatancen hanyar da zaiga masallaci nayi mishi. Yana tafiya na dubi Uwani nace.
Yanzu Uwani yaya zanyi? Ni da Hamma lokaci kawai muke jira, ina tabbatar miki da ba dan ciwon Dada ba da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Wallahi Uwani ni zuchiyata tafi nutsuwa da Hamma fiye da Salim batun ?auye ko ?auyanci kuma ni naji na gani zan rungumi aurena in zauna a ?asata ni yafi mun rufin asiri. Ki tuno irin ba?ar azabar da muka sha a hannun larabawa. Shi Salim Winnan kinsan mazinacine gangaran, tantirin mazinaci ma kuwa, dani dake da Faty duk fa mun sani. To ina sane bazan auri mazinaciba, ni abun hannunshi bai tsole mun idoba, Uwani kiyi tunani. Zina yaWo take yi ta lashe zuriya, ki duba mazajen larabawa da yawansu kamar Ayu suke dan tsabaragen son mata"
Jim Uwani tayi can ta dubeni tace.
"Yanzu ke dai kinji kin gani Hamma dai kike so zakiyi ha?uri da duk abinda in kika shiga zaki gani, shin tunda kin kawo hujjojinki na ?in auren Saleem shin Iyabo me zai hana ki nutsu ki yi kasuwancinki da sannu Allah zai Sullo miki da wani, shin ko a matse kike?"
Sosai kuwa, muna fatan ganin alkhairi. Nifa na tsorata da sha'anin larabawa ko karen hauka ya cijeni bazan auri Salim ba. Uwani ki mishi bayani an riga an haWani auren zumunci da Wan uwana wanda suka gaisa saura sati Waya ma ayi bikin in samu mu rabu lafiya" Mun daWe muna tattaunawa, Uwani ta jima tana bani baki akan nayi nazari kafin yanke hukunci. Ita a tunaninta dan gudun dana sani. Ni kuma babu dana sani a soyayyata da Hamma. Har Salim ya dawo bamu tsaida matsaya ba. Ciki na shiga na kawo mishi madarar shanu a gora yasha sosai sai santi yake yi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login