Showing 54001 words to 57000 words out of 270738 words

Chapter 19 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mallakar hankali suke. Ko dan su ya kamata ku sarara dan kune allon kwaikwayonsu, kai tunda kaine babba ka dena biye mata"
"Shikenan Iyabo. Amman Uwani da kike gani bata da daWi. Kwananta goma cib tana gaba dani, bansan sam abinda na aikata mata ba. Motsi kaWan sai habaice_habaice"
"Iyabo wai ki zo mu tafi kin kuma tsaya wani lallaSashi" ?wafa tayi ta kawar da kanta. Har muka isa gida tana zazzago mun mita.
A falo na kwanta ni da yaran, kafin gari ya waye kuwa suka ji?ani shakab da fitsari sai da nayo wanka kamar mai kwanan turaka dan har kaina sai da ya ji?e da fitsari. Ai kuwa Uwani ta shiga jibgar yarannan kamar Allah ya aikota, haya_haya tsakaninta da Hafizu bai tsaya ba sai da ya gaji ya bar mata gidan tukunna. Ni na fitar musu da katifar na zuba ruwa katifar ta hau yarari tana gudana a tsakar gidan. Uwani kuma ta wanke musu kayan tas ta goge ledarta tsab da ruwan toka, gabaki Waya zarnin ya Wauke. Dumamen tuwo tayi mana bai ma isaba saini na ba da hamsin aka siyi gasara da siga Uwani ta dama mana. Muna karyawa Hafizu ya le?o
"Ki kawo mun abincina ina tsakar gida" Yana faWa ya saki labulen tare da jan dogon tsaki. Kai mishi abincin tayi ta dawo muka ?arashe namu, a gurguje muka fita a gidan bayan ta sallami yara ?an islamiyya.
Ni ko Uwani kin je kin dubo su Toye kuwa?" ?an murmushi Uwani tayi tace.
"Na yi tunanin Hamma ya goge miki tunanin Gwadabe ne ai Iyabo da baki tambayesu ba" Dariya nayi nace.
Ko kusa meye tsakanina da Hamma da har zai ture matsayin uban ?a?ana a zuchiyata? Shi fa Gwadabe Mijinane, shi ko Hamma Wan uwanene kuma wa a gareni mai kulawa dani. Uwani kinsan Allah son Gwadabe nunkuwa yake yi a duk ranar duniya, bana jin zan iya sauraren wani da sunan aure a zahirin gaskiya" Ajjiyar zuchiya na sauke take ?irjina su kai mun nauyi.
"Naje kusan sau uku dubo ?an biyu. Allah cikin ikonshi ban samu ganinsu ba, har shi Gwadaben. Sai da mu kai zageni in zageka da wanna figaggiyar matar wan Gwadabe Haula take ko Zuriya oho" Gabana ya yanke ya faWi nace.
Shikenan duk yanda akayi rayuwar yarannan ta koma ?auye, ni da naso yaran su samu ilimin zamani tunda ni da Baban nasu iyakarmu kammala sakandare. Yarana sun zama ?an ?auye shikenan" Kuka na saka a hanya muna tafe kafin mu samu abun hawa. Da ?yar da siWin goshi Uwani ta shawo kaina. Amman fa har muka isa gidan Hajiya Salamatu bana cikin hayyacina, muna zuwa aka kwashemu a golf kusan mu tara zuwa hajj kam, anan muka amsa tambayoyi dai haka bamu jima ba duk yawanmu kuma akwai sanayya sosai tsakaninsu da ita Hajiyar. Muna bakin ?ofar Hajj kam Win a tsaye Uwani na kuma tausata wata mota fara sol tayi tsaye a gabanmu, ita bata wuce ba, gashi ta tare mana ganin gari" Wani dattijone ba?i mai haiba da kwarjini ya fito. Saye da yadin boyel mai ruwan ?asa, kansa saye da hular zanna bukar, ga zobe ga agogo, ga takalminshi sau ciki irin na ?an gayun maza. Abun almara sai muka ga ya tsaya a gabanmu. Gemu mai shi kombineshon Win fari da ba?i na kalla
"Assalamu alaikum ?an mata" Ya furta da muryar kamana muryarshi da kauri irinta tsayayyi dakakkun maza, sai buso ?amshi yake yi"
"Ba dai ?an mata ba. Ko wacce da yaranta, kuma ai ko da wasa ba mui kama da ?an mata ba" Cewar uwani balbalin kenan, ni ko fa bance komai ba. Wannan dattijo yayi murmushi har ha?orin makanshi fari ya bayyana.
"Allah ya ba manyan mata ha?uri. Dan Allah kuna da aure ne?" Ya tambaya, sai naga fuskarshi ta cika da fargaba.
"Ni dai ina da aure. Amman Iyabo a kasuwa take" Sai ya sauke ajjiyar zuchiya tare da murmusawa yace.
"Alhamdulillah. To Hajiya in ko babu damuwa inaso mu Wan yi magana a gurguje, dan gudun kar in katse muku hanzarinku" Carab uwani Tabalbalin tace
"Babu komai bari in matsa in baku waje" Ai kuwa sai ta karasa wajen matan da muka zo tare dasu tayi tsaiwarta
"Sunana Buhari Namoriki. Nazo shiga Hajj kam ne Allah yasa nai tsuntuwa dake. To a gurguje zanso jin sunanki da unguwarku sai in zo gida in sameki yafi mutunci" Ajjiyar zuchiya na sauke. Idanuna suka cika bam da ruwan hawaye, sai nake jin kamar tsaiwa da wani namiji da sunan soyayya tamfar cin Amanar Gwadabe ne"
"Malama Iyabo baki ce komai ba" Na ji sunana raWau a bakinshi.
Sunana Iyabo kamar yadda ?awata tace. Unguwarmu kuma ni ba ?ar garin bace ma, zuwa nayi gobe zan koma ina mai baka ha?uri" Murmushi yayi yace.
"Ai mai son Wan tsuntsu shi ke binshi da jifa. Kuma garin masoyi baya nisa, in kika bani dama ko adireshi zaki ganni"
Ba ko wanne garin na masoyi bane baya nisa. Ka ganni ?ar ?auye ce a jeji nake rayuwata, babu wutar lantarki balle har sabis ya isa mana, gashi ban shirya aure ba. Wallahi ko zan yi aure bazan auri ?abilar da zata zama tana ?in ?abilar dana fito ba" na ?arashe zancen cikin rishin kuka. Hajiya Salamatu na hango ta fito, a wajen na tafi na bar Buhari a tsaye. Har motarmu ta fice fit yana tsaye yana ?arema motarmu kallo.
Ko da muka isa gida Uwani Tabalbalin ta balbaleni da faWa akan me zance ma Buhari haka? Ta tambayeni ne na bata labarin yanda mu ka yi.
Uwani ai ni da Bahaushe sai dai zumunci. Amman bazan sake auren Bahaushe ba. Bama yanzu zan yi aure ba kin ganni nan. Mu da muke da tafiyar da zamu yi har tsawon shekaru uku, da dakon soyayya kike son inje inyi wanna shekaru? Dame zanji, da mutuwar aurena, ko da mayar mun da yara ?auye, ko da matsalar Dada?" Da rishin kuka na masifa nake maganar. Uwani sai ita ta sakko, zama tayi ta dafani.
"Kina da gaskiya ?awata. Amman da ba irin rabuwar da kuka yi ba kenan. Rabuwa salamun_salamun yafi, domin bakasan inda rana zata faWi ba. Batun yaranki da zan baki shawara ki Wauka da kin sa ?afa kin yi fatali da sha'anin, domin yafi ?arfinki. Ba dole sai sun yi karatun boko darajarsu zata Wagu ba, akwai arzikin da yafi noma ne? Babu shi da noma yaranki maza zasu iya azurta Iyabo, ita mace aure dama ka iya kaita jeji ma, ki bisu da adda'a zata bisu har gadon baccinsu Gwadabe kuma nasan ya cika jarumi, kuma yayi miki halacci. Amman cireshi a zuchiyarki wajibun ne saki ukune a tsakaninku. Ke ko saki Waya yayi miki yaci ki ha?ura kema kiyi fatan samu sabuwar rayuwa a gaba. Kawo Wari a siyo taliyar murji mu Sararraka ina da maggi da ragowar manja. Kullum aikin kenan nike faWi tashin neman abun rufin asirinmu, ke Iyabo har wanki da guga inayi a cikin gidannan, yawon wanke_wanke a gidajen masu hali ko shagunan cin abinci har ya zamemun jiki" ?ari da hamsin na bata dan yara ma in suka dawo sa lasa. Ita da kanta ta fita ta siyo, tare mu kai hidimar komai muka baje a tsakar gida, Maman Shamsu tana zaune a kan turmi tana fige kasa tana wa?o?in neman masifar da ta saba. A tukunyar muke ci, mun Webama yara nasu, Hafizu kuwa nayi ro?on duniya ta dibar mishi Uwani tace bai isa yana zaune a majalisa yana aikin bin matan mutane da ido ta ajjiye mishi abinci ba.
"Amman iyaa Debisi da shi kanshi Debisin basu san kin shigo Kano ba?" Sai da na haWiye taliyata na tsotse yatsuna daya ji?e da romon da ya ji kafi zabo kafin nace.
Babu wanda yasan na shigo. Gobe zan daka sammako in koma. Zanje inci gaba da jiran lokaci in Allah ya kaimu. Kuma inaso in tattauna sosai da Dada ta san ?udurina, ta goyi bayana akan tafiyar da kuma batun Mahaifin su BaWWo. Zan soma zama dasu BoWWo tukunna mu tattauna in ji ra'ayinsu. Kuma naso in Wan dinga ba matan Rugar ilimin addini iyakar abinda na sani, ko dan karatun sallarsu ta yi kyau. To basu ma da lokacin kayinsu ne shine matsalar. Amman su ?an uwan nawa zan tsaya a kansu kafin in tafi in Wan gyara rayuwar tasu"
Washe gari asubar fari Uwani ta rakani tasha, ta Wan tsintomun kayanta kala biyu da wanda na sauya a jikina uku kenan. Naso in mata turjiya amman ta?i sam dole haka na karSa. A tashar na Wan sai maganin ciwon kai, da maganin ciwon ciki, da maganin zazzaSi , dana rage zugi ko wanne kati_kati. Inaso in bayar a kaima Dada ta Wan dinga sha, sauran kuma in ajjiye a wajena. Taran safe motarmu ta Waga.


Gwadabe:.
Takai.
Tun a ?ofar gida ya hango motar Yaya Hambali a gefe guda, kuma ya ga Nazifi na zance da Nana ?anwar Layla.
"To Gwadabe ni da Toye zamu wuce gida, in kun gama ganawa da Baba Magaji dasu Babala ka sameni a gida" Cewar Bara'u kenan.
"To Shikenan sai nazo. Ka isar da sa?on godiyata ga Sakina" Yana faWar haka ya shige cikin gidan. Da Nazifi da Nana babu wanda ya kalli Gwadabe balle su gaisheshi. Zumunci ya riga da ya taSu, ana rikice_rikice a gaban yara suna ji suna gani, sai su taso da raini da rashin ganin girman wanda aka watsar a gaban idanunsu. Wanda ake mutuntawa kuma a gabansu, sai su taso da ganin girmanshi ainun.
(Wannan kuskuren namu ne iyaye. Mu guji yin abinda bai dace ba a gaban yaranmu. Shi fa zumunci da haWin kan haula babu abinda ya kai shi daWi)
Gwadabe yana tafe yana girgiza kai, ciwo yake ji a zuchiyarshi sosai ta yanda zumuncin gidansu ya lalace. A falon Babala ya tarar da kowa da kowa. Babala da nata tawagar haka ma ?annenta su Goggo Iyatu Baba Magaji yana tsakiya.
"Gwadabe kaine tafe da yamma haka?" Cewar Baba magaji.
"Nine Baba Magaji. Mun same ku lafiya?" Gwadabe ya bi kowa da gaisuwa Babala da Goggo Iyatu fur su ka ?i amsawa. Baba Magaji yace.
"Zauna nan." Ya nuna mishi kusa da Yaya Hambali. Yana zama Yaya Hambali ya matsa, har yana share sangalalun hannunshi inda jikin Gwadabe ya gogeshi. Da mamaki Gwadabe ya dubeshi, shi kuwa ya zuba mishi Uwar harara.
"Marar kunya ji yanda kake ?are mishi kallo sai kace sa'anka" Cewar Yaya Halima da bata fiye son a zauna lafiya ba dama" Baba Magaji ya yi mata da?uwa tare da cewa.
"Ungo naki Yau ga mutuniyar banza. Shi Hambali baki ga share hannunshi yake yi in da jikin Gwadabe ya goga ba? Sai kace wani karfa. To magana dai ta ?are kai Gwadabe meye hujjarka na nuna zafin ?iyayyarka ga ?ar uwarka Laila? Dan naji labarin komai" Gwadabe ya Wago kanshi yace.
"Ba ?in Laila nake yi ba, face ?in munanan halayanta abun ?i. Na farko Laila babu wanda bai san Sarauniya bace. Ko yanzu a taronnan in ba'ai da gaske ba sai ta raba wani da abunshi. Sannan da aure a kanta bata dena bibiyata tana turo mun da sa?onnin ?auna ba. Wannan manyan dalilan yasa bazan taSa iya auren Laila ba" Kafin ya rufe baki Goggo Iyatu da Laila suka fashe da kuka wi_wi. Ganin haka yasa Babala soma shesshe?ar kuka itama. Baba Magaji yayi tsam yana bin kowa da ido Waya bayan Waya yana karantar yanayinsu. Yaya Hambali cikin zafin ranshi yace.
"Uwar ?a?an naka ma naga Sarauniyace. Wacce iriyar sata ce bata tabka mana a cikin gidaba? Ai kai kasan komai tunda kai ke biyan kuWin duk abinda ta sata. Ita ka zauna da'ita sai Laila jininka ce ba zaka iya aura ba?" Gwadabe yace.
"Wallahi ko tsinke Iyabo bata taSa sata ba. Duk wannan kitumurmurar Laila ne. Ita ke satowa ta jefa ma Iyabo a Waki. Ni kuma ina biya ne dan ba son ganin ana tashin hankali nake yi ba"
"Babu shakka Gwadabe "
"Duk ya isheku haka ku saurara mun. Iyatu ku yi mun shiru ya isa haka nan" Sai da Wakin yayi shiru kana yace.
" Duk wannan kumfar bakin da kuke yi ba daidai bane sam. Layla dai kowa yasan mai dogon hannuce, tunda har maraWi wajena Iyatu ta kawota ai mata magani. A lokacin hekarunta baifi goma ba. Sata kuwa da ta dinga yi a ?auyannan abun yayi muni. Ina bayan Gwadabe na ?in amincewa da auren Laila. Tunda kunce satarta shafar aljanune sai ku dage ku nema mata magani. Kuma da ace ni nasan irin tsangwamar iyalin Gwadabe da kuka yi da tuni nayi ma tubkar hanci tuni. Ko yanzu ma dan saki ukune a tsakani da ko kun ?i ko ku so sai ta dawo tunda itama musulmace ahalul kitabi ma aurensu akeyi ballantana ita musulma gaba da baya."
Falon yayi shiru sai hawa da saukar numfarfashi kawai. Baba Magaji yace.
"Yaran dasu ta tafi ne Gwadabe?"
"A'a Baba Magaji bata tafi da su ba. Shi Toye yana hannun Bara'u Sakina zata ci gaba da kulawa dashi, za'a sa shi a makaranta. Su kuma ?an biyun na kaisu wajen Tamu a can Abuja shi ya bu?aci hakan" Baba Magaji ya jijjiga kai yace.
"To Allah ya saka musu da alheri. FaWuwa tazo dede da zama ni zan tafi da Gwadabe maradi yaje ga su Auwala can suna aikin ha?ar zinariya, yaje shima ya jaraba wata ?ila arzikinshi yana can. Akwai ?annenka mata ma a cikin gida, in kuka daidaita da Waya daga cikinsu kaga sai ayi tuwona maina ku yi zamanku a can. In ma aikin ha?ar zinariyar bai maka ba akwai aiyuka da zasu dace da kai" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kuma yaji daWin hukuncin da Baba Magaji ya zartar, shi kanshi yana da bu?atar yin nesa da danginshi ya fita neman na kanshi. Kuma yaji aikin ha?ar zinariyar ya kwanta mishi a rai. Ya je can maraWi ya samu sababbin ?an uwa da zasu so junansu.
Babala ba haka taso taron ya watse ba, amman bata da ikon cewa komai. Haka tana ji tana gani washe gari Gwadabe da Baba Magaji suka wuce maraWi a bisa jagorancin Bara'u zuwa tashar mota.
Wannan shine dalilin barin Gwadabe Kano, ya koma maraWi hannun wan mahaifin Babala"

JIHAR MARA?I DAKE CIKIN JUMHURIYAR NIJER
Cikin unguwar Ali Wan tsoho.

GWADABE:.
Bayan saukar su Baba Magaji a abun hawan da suka hau zuwa layin Ali Wan tsoho. Duk inda Baba Magaji ya sauke kafarshi nan Gwadabe yake ajjiye tashi turyan_turyan har zuwa ?ofar gidan Baba Magaji mai Wauke da cikowar almajirai yara da ?ananu. Almajiran malam suna hango malam magaji, wasu gardawa biyu suka taso suka nufo su.
"Malam maraba da dawowa sannu da zuwa ba?o? Malam ba?in gaddi mu ka yi ne" Baba Magaji yayi Dariya ya dafa wanna gaddi yace.
"Ba ba?in gaddi bane. ?an wajen ?aunata ne cikin ummata. Amman da dare zai zauna ya dinga biWar karatu, da kuma Asuba. A karSi jakar hannunshi ku shige dasu wajen Fhatsima." Gwadabe ya bi bayan Gaddawannnan biyu har zuwa cikin gida. A tsakar gida suka tarar da matan malam Magaji su hudu reras ko wacce da abinda take yi. Haka yan matan gidan, wannan na sukola, wannan na girkin abincin siyarwa, wannan na dakan fura, duk dai gasunan.
"Almu ba?i mu ka yi ne, cewar Baba Fhatsima. Wanda ta kira da suna almu yace.
"Malam ne ya tawo da shi ya. Kuma yace mu kawo shi wajenki." Fhatsima ta yi murmushi tace.
"Yaro shiga wannan Wakin ka zauna. Ke I'ne zo ki kai ma ba?o ruwa ya sha" Gwadabe har ?asa ya dur?usa ya gaishe da matan Kawun nashi. Babu dai yabo babu fallasa suka amsa mishi, cikin su ukun babu wacce ta yi mishi kallon arziki. Baba Fhatsima tace.
"Tashi yaro kaji ka shiga daga ciki, za'a kawo maka ruwa" Jakar Baba Magaji ya amsa a hannun Almu da Wan kunshin kayanshi kala biyu wanda Bara'u ya ?unshe mishi. ?akin ya shige da sallama. Wata budurwa tana kwance a ?aramin gadon bono ta juya bayanta ta yanda mai shigowa ba zai ga fuskarta ba. Kayinta babu Wankwali sai ba?in madaiaicin gashi mai wal?iya da yai ma kan nata ado. Ba gashi bane mai yawan daya wuce misali ba. Gashi ne wanda bai ko kai tsakiyan bayanta ba, iyakarshi gaba da kafadunta kaWan. Gashin dai ya sha gyara sai walwali yake yi. Gwadabe ya Wauke idanunshi daga kallon gashin ya bi Wakin da kallo, Wakin ya sha labule mai Wawisu zagaye da bangon Wakin dukka. Ga Wan katakon kwalliyar labule zagaye da Wakin, a saman labulen an yi jeren kwanukan sulba ?ananu sai Waukar idanu suke yi. Ga gadon bono ga gado mai rumfa maulidi, ko wannne gado ya sha lallausan zanin gado mai geza da heart a tsakiya. Kasan Wakin kafet ne ja mai kwalliya malale takota ina. A gefen gadon bonon an ajjiye babban tulun ruwa mai fenti, an rufe bakin tulun da faifayi. Ga wasu manyan kumbuna da kwallaye anyi ado dasu, banda wata kwaba mai ?ofofin tangaran ita kuma kwabar an ?awatata da kwanuka da fileti na tangaran nau'i daban daban. Sallamar da Gwadabe ya ji ne yasa ya nutsu ya dena ?arema Wakin kallo. Wata farar doguwar yarinyace ta shigo, hannunta ri?e da kofin sulba mai murfi ?ato. A gabanshi ta dure kofin, ta zauna harda lan?washe kafarta kamar mai Waukar karatu.
"Ga ruwa Yaya ka sha kafin abinci ya nuna sai ka ci" Murmushi Gwadabe yayi mata.
"To nagode ?anwata" Kofin silban ya buWe ya kafa bakinshi a kofin ruwan ga sanyi, Gwadabe sai da ya sha fin rabin kofinnan kana ya ajjiye ya rufe kofin.
"Gidanku Malam ya je, ko kaima almajirci kazo yi?" Ta jefo mishi tambayar, kafin ya bata amsa suka jiyo ana kiranta.
"Ine ke dibo fito ku tafi ga musa mai baro yana jiranki" Zumbur ta mi?e ta dubi Gwadabe tace.
"Zan fita tallen abinci, amman ba jimawa nake yi ba. In na dawo ma ?arashe hirarmu" Da idanu Gwadabe ya bita kawai, ta fita cikin hanzari. Tana fita Baba Magaji ya shigo, Baba Fhatsima na biye dashi. A ?asa Baba Magaji ya zauna, Baba Fhatsima kuma ta zauna a bakin gadon bono.
"Fhatsima kin gane Wana Gwadabe kuwa, Wan wajen ?aunata Babala, yaro mai yawan ?uraje?" Baba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login