Showing 42001 words to 45000 words out of 270738 words

Chapter 15 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

gefe. A ?yamace nayi bawali na fito, inda zan Waura alwala ta nuna mun, naga gidan kamar komai da tsari suke yinshi. Nayi alwala muka fito a tare. Har zuwa wannan lokacin Ina jiyo muryar Dada tana magana. Da ?yar nayi sallolin da ake bina nayi jigum akan buhun da aka shimfiWa mun nayi Sallah. Abinci wannan budurwa ta kawo mun a cikin ?warya an rufe ?waryar da faifai.
Ya sunanki ne?" Na tambayeta ina Wan fara'a.
"Sunana Cubu"
Kin sanni?" Na sake jefo mata tambaya.
Sai ta girgiza mun kanta halamar A'a. Sai na yi Wan murmushi nace.
Ke yarinyar Dada ce?"
Sai da tayi dariya sosai kana ta bani amsa ta hanyar Waga mun kanta halamar e" Kwaryar abincin na buWe tuwone da wata miya ba?a ?irin ba koriya ba, sai wani irin ?amshin ganye take yi marar daWi, amman dake ina jin Wan karen yinwa ba shiri na nutsa hannuna a cikin tuwon. Wallahi da ?yar na iya haWiye tuwonnan, ko da na haWiye dambe mu kai ta tayi, yana shirin dawowa ni kuma ina ?o?arin mayar dashi, dan gudun kar suce na ?yamacesu. Inaga Cubu ta fuskanci bazan iya cin tuwon bane, sai ta mi?e ta kawo mun madarar shanu. Dana kafa kaina sai da na shanye madarar tas. Ina sauke kofin nayi gyatsa, sai ga Dada ta shigo tana sharar hawaye cikin dabara, dan ita a tunaninta ma bamu ganta ba. Zargina ya tabbata akwai wani babban abu da aketa Soyemun tsawon shekarunnan da ba'ason ni in sani. Ni kuma ina ganin lokaci yayi daya kamata in sani. Bakin gado ta zauna kanta a ?asa kamar yadda ta saba tace.
"In kin gama cin abincin Cubu ta rakaki gidan ?oWWo acan zaki kwana, ?anwatace a gidan itace uwar mijin BaWWo uwarmu Waya ubanmu Waya babu wata matsala. In Allah ya kaimu gobe na dawo tallan nono zan biyo gidan in same ki. Cubu ?anwarki ce ?anwar ?oWWo, yar Yusuf. Amma. Akwai Amaduyal shine a sama da ?oWWo sai dai shi baya zama, yanzu haka suna togo, sun fita kiwon shanu tsawon shekara biyar basu dawo ba, amman ana jin labarinsu, suna yo aike gida, matarshi Sa'ada tana cikin gidannan, da yaranta biyu" Kai na gyaWa. mamakin daya kamani shine jin Dada ta ambaci tallan nono, kenan itama tallah take yi kamar yadda na ga wasu guggun mata a Jere Banyo da ?oren tallarsu? Iko sai Allah ai yaci ace Dada tana zaune ne tana morar haihuwa ba wai ace har yanzu aikin wahala take yi ba. Mi?ewa nayi tsaye Cubu ta Waukarmun jakar kayana.
To sai Allah ya kaimu goben Dada"
Na yi magana a mugun sanyaye. Cubu da Yusufu ne suke gaba ina biye dasu a baya, ina kallon gari maza suna kwakkwance a tabarma, wasu kuma sunyi da'ira suna cin abinci. Yayinda samari masu jini a jika suke ta sha'aninsu kawai. Ta wani dandali muka zo wucewa nan naga kyawawan ?an mata farare, da kyawawan Samari. ?an mata na wa?a samari na yi musu tafi. Wasu kuma keSe suke a gefe guda suna musayar kalaman ?auna. Rayuwar ?auye akwai ban ?awa a cikinta, bugu da ?ari akwai nishaWi sosai. Tafiyace mi?a??iyar gaske mu kayi kafin mu iso gidan BoWWo, duk na gama galabaita, ga gajiyar hanya da dama ban huceta ba, ga wannan tafiya me nisa da muka sake yinta. Suna kwance a tsakar gida mu kai sallama muka shiga, mazan gidan kuma kafin mu shigo sai da mukai musu sallama. Da sauri BoWWo ta taso ta tare mu." Ina tsaye bansan me Cubu tace da'ita ba. Kawai sai naga ta rungumeni ta fashe da kuka.
"Adda Jabu ashe zan sake ganinki a rayuwa? Cike zukatanmu suke da maraicinki" Ta faWi hakan da kwaSaSSiyar hausa. Nima hawayene suka gangaro kan kumatuna. Nan BoWWo ta shiga dani cikin gida tana ta nunani, ni dai Adda Jabu kawai nake jin tana ambato. ?akin Yafendo KaSoji ta kaini ?anwar Dada surukarta kenan. Kanta ta dinga jijjigawa tana nanata sunana. Abunda na fahimta ?anenane kaWai sukai farin ciki da ganina. Hannuna BaWWo ta jawo muka shiga cikin bukkar data kasance Wakinta, Su Yusufu na biye damu. BoWWo ta kalli su Cubu tace.
"Sunanta Adda Jabu. Yayar Amaduyal ce, Dada ce ta haifeta itace yarinyarta ta farko. Ina tunanin sanadintane ke sa Dada ?unci da zubar hawayen da tun tasowarmu muka tsinci Dada a wannan halin." Runguma suka kawo mun dukkansu ukun, babu nuna ?yama ba komai. Hawaye masu Wumi sukaita zurubtu a kumaruna, hankalina a madadin ya kwanta sai ya sake tashi. Ni kaina na jima ina tausayama rayuwar Dada, na daWe ina zargin bata jin daWin rayuwa akwai wani babban lamari data ?unsa a cikin ranta yake nu?ur?usar rayuwarta. A wannan daren mun yi hira sosai da ?annena na yaushe gamo, dan su Cubu sun?i tafiya a cewarsu sai dai du mu kwana a zaune.
"Adda Jabu ki ce su tafi, Baffa zai yi faWa sosai, ko ma yazo gidannan a darennan. Gobe Cubu zata kai nono cikin gari, Yusufu kuma zai fita da Shanu kiyo Kuma zata burga madara ta fitar da man shanu da asuba."
Jim na kuma yi jin abinda BoWWo take faWe.
Cubu tunda kinsan hakane, ku yi ha?uri ku tafi gida. Ni ina nan na dawo rugarnan kenan, daku zanci gaba da rayuwata" Da kyar na lallaSasu suka tafi, suna tafiya sai ga mijin BoWWo ya shigo ya mi?o balangu a ba?ar leda. BoWWo ta gabatar mishi dani a matsayin babbar yayarsu. Cike da jin kunya ya sake gaisheni yana sosa ?eyarshi shi a dole kunyata ce ta kamashi. Kai fulani a kwaisu da kunya da kawaici sosai. Fitar mijin BoWWo ke da wuya mu ka jiyo sallamar wata mata da BoWWo ta yo kiranta da suna Hama ?warya ta ajjiye mun a gabana tace.
"Use ba?uwa"
Farar bafulatana doguwa gata da ba?in gashi. Da fara'arta muka gaisa duk da hausar kamar ta yara ?an koyo suke yinta.
"Adda wannan matar wan su Yuguda ce, mijinta shine Babba a gidannan, yana fita aiki cikin birni.
Allah sarki, sannu Hama nagode sosai da fura" Murmushi ta kuma yi mun ha?oranta kamar ?an?ara dan haske, a gaskiya Hama kyakkyawar macece banga wata makusa a tattare da'ita ba face ta rashin wayewa, da ?azanta kuma dan ?afarta duk faso fasonnan ya Webi wata annakiya ya adana. Ga gashi iya gashi amman kitson a furje kuma cike da yayin katifa. BoWWo tace.
"Hama wanna itace Babbar yarmu Adda Jabu, ba lallai bane ki san labarinta ba. Nima naci da bin diddigi yasa na san labarinta. Ta taSa zuwa rugarnan da daWewa lokacin muna yara ?ananu." Tare da Hama mu ka ci balangunnan mu ka taSa hira dai haka. Duk da gajiyace ainun a jikina, ga tunane _tunane da suka haWu suka cukurkuWe mun rayuwata. Duk wani bugun zuchiyata bugawa yake yi da so da ?aunar Gwadabe na. Haka tausayin mahaifiyata da son jin matsalarta suma su ka dabaibayeni. Ina fatan in zame mata sanyin idaniya, maganin zubar hawayenta.amman ta yaya tunda mijinta ma bai karSeni a matsayin ?a ba, tunda gashi a darennan ya kasa ha?uri ko da kwana guda ne in yi. Ko ma Iyaa Debisi ta faWa mun yana da faWa, bauWaWWen mutum ne ainun. Tunani, da zafi, da sauro su suka hanani huce gajiya ta hanyar saka ha?ar?arina a ?asa, katifar yayin dana kwanta akai sai sossokeni kawai take yi. Babu shiri na mi?e na fito tsakar gidan, duk yawan matan gidan suna kwance a tsakar gida bisa katifun yayi. A kan tabarma na kwanta iska na Wan hura ni kaWan. Da haka Sarawon bacci yayi awon gaba dani izuwa asubar fari, kwaramniya da kukan shanu ne ya farkar dani. Ashe nonon shanu ake ta tatsa, su kuma sai kuka suke yi. Wasu daga cikin matan na gansu suna burga nono da wani itace mai kama da maburgin miyar yau?i, wasu kuma suna ta aikin dahuwar madarar shanu, yayin da wasu suke sharar garken Shanu, wasu kuma girkin safe suke yi. Ina buWe idanu Hama dake shara tace.
"Jabu kukan nagge ya tashe ki ko? " Tai maganar tana murmushi. Nima Murmushi nayi mata kawai, na mi?e BoWWo dake zaune a cikin jerin matan da suke ta burga nono ta mi?o mun buta, tai mun nuni da ban Waki.
Ruwa na kama na fito na Waura alwala na shige ciki. Na jima ina ro?on Allah yayi mun mafita, ya kuma sassauta mun soyayyar Gwadabe a ruhina, bazan ro?i ya cire mun soyayyr ba dan abadan Gwadabe bazai gaza samun gurbi a rayuwata ba. Tunano ?a?ana yasa hawaye suka zubo mun a kumatuna, ba shiri na mi?e na fita. ?aya bayan Waya na dinga bin matan gidan muna gaisawa, mun shiga Wakin ?anwar Dada ma mun gaisa. Cikin garken shanu BoWWo ta jani wai in taya ta mu tatsi nonon Saniya ta dafa mana mu sha. A baya na bita zuwa cikin garken shanun a nan muka tarar da Hama a ciki ita da mijinta suna shafa ma wata saniya magani jikinta duk kuraje ya fito.
"Wannan itace ba?uwar tamu BoWWo? Ai Hama yanzu take faWa mun cewar mun yi bakuwa kuma ma ?ar uwa" Cewar mijin Hama wani dogo siririn bafulatani sosai, ga gashi a kwance a kanshi lub, na lura kamar yafi kowa tsayi a gidan, ko dan ya fi kowa sirantane oho.
"E Yaya Hamma itace ba?uwar tamu, Ita ce sama da Amaduyal, daga ita sai shi, a birni take aure can Kano" Murmushi ya sake faWaWawa yace.
"Sannu da zuwa, baki tawo mana da yaran ba?" ?an murmusawa nayi bayan mun gaisa nace dashi.
Na baro yara a gida sabida makaranta" Baice komai ba sai Wan murmushi da yayi, ya kaWa shanu sama da talatin suka bi bayanshi da ?ar sandarshi da halama kiwo zashi. Ni dai ina raSe a bayan Hama tsoron shanun nake yi, ina dai kallo BoWWo na tatso nonon wata farar ?atuwar saniya mai ba?in ido, ita kuma Hama tana dai ta shafama wannan saniya magani a duk jikinta, kuWa sai damun saniyar suke yi tana ta kaWa kanta. Fitowarmu daga cikin garken kenan sai ga su Cubu sun shigo gidan, amman ta wata ?ofa da ban ba ta ?ofar da muka shigo jiya ba. Idanu na ?ura musu, su basu da fari can Winnan . Yanda duk suke kallona a kunyace su nai mun kallon so da ?auna shi yafi komai burgeni sosai. A barandar dake ?ofar bukkar BoWWo muka zauna.
"Adda Jabu wadannan duk ?annenki ne iyakarmu mu huWu ne, shi Amaduyal shi baya nan. Iyakar yaran Dada kenan, nasan baki san iyakarmu ba, kamar yadda suma duka babu wanda ya sanki sai ni, nima saninna gani Waya ne." DaWi ya lulluSeni ganina a cikin ?an uwana cikin Dadana, kuma sai kirana suke da Adda Jabu fuskokinsu da zuchiyoyinsu a cike da fara'a. Nawa bazai ma musaltuba. Tuwon farar masara aka kawo mana Wumame da ba?ar miya kamar kwalta, ko miyar meye wannan oho, sai madarar shanu mai zafi, tuwon sai ?amshin man shanu yake yi. Loma Waya da nai karambanin sakawa a bakina da ?yar da ma?yar?yata na iya haWiyewa tare da danneshi da Madara mai Wumi. Muna zaune a wajen ina Wan musu tambayoyi suna bani amsa, wata hausar ma da ?yar suke fahimtar me nake nufi sabida tayi musu girma. A bakinsu naji ai kullum Dada tana zuwa cikin bini kai nono, fura, da man shanu. Tsawon tasowarsu da hakan suka san iyayen nasu, su kuma yara maza kiwon shanu suke fita yi, in suka girma har gari_gari suna iya fita kiwon shanun. BoWWo tace.
"Ko ni ma kullum ina fita tallar nono, mu da kuWin wannan nonon muka dogara, bamu da wani abunyi sai kiwo. In mace ta siyar da nono, a ciki zasu ci su sha, su yi sutura, har su tara kuWin magani in wata saniya ba lafiya a nema mata magani dashi. ?an mata kuma da ba aure a kansu, da kuWin tallar nononsu ake yi musu kayan Waki da komai da komai, wata ma har ta tara kuWi itama ta sai Wan mara?i da haka har su zama garken da yaranta zasu ci gado suma. Matan ma a wasu gidajen suna fita kiwo. Ko su Cubu suna zagayawa amman da awaki ba shanu ba." Jigum nayi ina ta kallonsu jikina a mugun mace. Dama duk uba uban tsarabar da Dada take yi mun in zata zo ganina da kuWin tallar nono take yowa?" Sai naji zubar hawaye masu zafi, tare da saka Wamarar sauya ma Dada wannan rayuwar tallan da izinin Allah.
Ana cikin haka sai muka jiyo sallamar Dada ita da wasu mata su su biyu, sai namiji guda Waya sun shigo kai tsaye kasancewar gidan duk dangin junane. ?akin Yafendo KaSoji suka nufa, mu kuma muka mara musu baya zuwa cikin bukkar.
"Zo Jabu ki zauna a kusa da Yafendonki." Wata mai kama da Dada ta faWa. Kusa daf da ?afafunta na zauna kaina a?asa na gaishesu cike da ladabi. Suma cikin karramawa da haba_haba suka amsa.
"Wannan ?annenane duka. Ga Yafendo A'i, ga yafendonki mai sunanki kin zauna a kusa da'ita. Zai Baffanku Musa gashi, sai Yafendonki KaSoji gata nan itace surukar BaWWo,. Ta nuna mun mahaifiyar mijin BoWWo. Kafin ta Waura da nuna mun su Cubu tace. " Wadannan kuma duk ?annenki ne kece babbarsu, Amaduyal baya nan shi kuma na faWa miki tun jiya." Murmushi kawai nayi dan na lura a damuwa Dada take sosai.
Yafendo Jabu ce tace.
"Zan Waukeki in tafi dake gidana, can ma akwai Daso shekarunku zasu yi Waya mijinta rasuwa yayi ya barta da yara tara. Zan zagaya dake dangi su ganki, zaki Wan jima kafin ki koma ko?"
A sanyaye nace.
Na dawo nan da zama baki Waya ne, auren nawa ya ?are. Kuma dan Allah a hannun Dada nake son zan zauna"
Gabaki Waya suka kalleni, banda Dada domin ita bata wani gane Hausa har sai da ?an uwanta su kai mata tafintar abinda na faWi. Da sauri ta Wago ta kafe ni da ido cikin yaren yarbanci tace.
"Yanzu sai da wannan auren ya mutu, dangin mahaifinki sun ?i barinki kiyi zaman auren ko? Dama tun farko da dan tani akabi da Debisin dai zaki aura domin shi yafi cancanta da sanin daraja da kimarki. Ita Iyaan taki ce ta amince miki ki dawo hannuna da zama alhalin tasan komai, zamana tare dake Jabu bazai yiwu ba. Tun jiya da kika shigo garinnan ban runtsaba har zuwa wayewar garin yau. Abinda nake so dake shine ki bi Yafendonki ki zauna a hannunta akwai Daso zaku dinga zuwa tallar nono tare, komai ma zaku ringa yi a tare. Amman ina mai baki shawarar ku koma birni inda kika fi wayo ki ci gaba da zama rayuwar Ruga cike take da ?alubale, kumama ba iyawa zakiyi ba. Nima in kuWaWena suka haWu zan je in dubo yaran naki. A hannun dangin ubansu kika baro su?"
Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna, tabbas akwai matsala shin mijn Dada baya ?aunar ganina kenan, baya son ya samu ladan ri?on marainiyar Allah, ko da wani abunne wanda ni ake ta Soye mun ne? Duka waWannan amsoshin na adanasu inaso duk lokacin dana samu lokaci mai kyau da Dada zata amsamun, ta bani tarihin mahaifina cikakke. Dan bansan wasu abubbuwa a game dashi ba sosai. Na dai san sunanshi, sai hotonshi babba dake kafe a falon Iyaa, sai hirarshi da watarana ke shigowa cikinn zance haka in su Iyaa na yi a tsakar gida.
Baffa Musa yace.
"Allah shi kyauta. Ni ina ganin tabi Jabu ta zaunaa a hannunta ko babu komai zasu dinga Webe ma juna kewa ita da Daso. Kuma komai zasu iyayi. Dan in hanuna nace ta komo bani da wata budurwar ?a a gabana ma. Tunda tace tana son zama a zuba mata ido, in taji wuyar da bata sababa da ?afafunta zata koma Birni aradu"
Yafendo kaSoji tace.
"A barta a hannuna tana ganin BoWWo sai hankalinta ya kwanta, kuma anan akwai Hama naga tun jiya da tazo suke hirarsu tare, kuma akwai matan ?annenta a cikin gidan ?ila tafi jin daWi. Kema Adda Daso zuwa ganinta zai fi miki sau?i. Zasu dinga zuwa tallar nono da Hama dan kar damuwa ta dameta."
Baffa Musa yace.
"A'a ki barta dai Jabu ta tafi da'ita can wajen nata. Ita kanta Daso tana bu?atar wacce zasu dinga shawartawa dan gudun damuwa. Ke Jabu ki je ki Webo kayanki sai ku tafi, Allah bashi in ita Daso mahaifiyarki ta samu daidaito da Mijinta kya dawo hannun nata, duk da nasan mutumme bauWaWWe ga taurin kai da dagiya. A kan ki meye ba'ayiba a shekarun baya da suka shuWe. Ita yar mahaifinkiToyosi ai tasan komai ya?i an yishi"
Bani da zaSi dole haka na kinkimi jakata na bi Yafendona zuwa gidanta, tafiya mu ka yi mai Wa karen nisa, kamar ma ba ?auye Waya suke da Dada ba, kuma fa a ?afa su kamar ma basa son hawa AcaSa. Gidanta kam ita kaWaice a yadda na lura daga ita sai mijinta da yaranta.
"Jabu ga Wakin Daso ki shiga ki ajjiye jakarki, zan tafi tallar nono yanzu, ki shirya sai in kai ki wajen Daso ku zauna kina tayata mi?a Nono. Mu nan ba'a zama daga masu kiwo sai masu fita tallar Nono " ?an murmushi na ?a?aro kawai. Bukkar data nuna mun ciki na shiga na ajjiye kayana a gefen gadon ?asa, a kusa da inda naga jakar kayan da nake zaton na mai Wakin ce Daso. Taya Yafendo Waukar ?waryar nono Waya da buhun bakonta nayi. Muna tafe muna cin karo da mata da yara kowa da ?waryarshi ta nono a ka za'a tafi talla. Maza da samari kuma sai wuce mu da garke_garken shanu suke yi suna shiga jeji kiwo. Rayuwar ?auyen ta matu?ar bani sha'awa, gasu da tsabta ainun kamar ba ?an ?auye ba ma, ?an ?azaman basu da yawa. Wannan akori kurar muka kuma shiga cike da mata masu tallar Nono, sai yarata yaren Fulani suke ta faman yi, ni dai ina cikinsu ?walam har muka iso babban titin mota inda matafiya ke wucewa, anan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login