Showing 66001 words to 69000 words out of 270738 words

Chapter 23 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

jin daWi itama tana jin daWin hakan, dan karayar tata bawai ta warke sumul bane. ?an tsegumi suka sanarma da Mijin Dada ai ana ganinmu tare. Kwatsam muna kan siyar da Nono sai gashi ya zo dan ya zama ganau ba jiyau ba. Da ganinshi Dada jikinta ya soma mazari. Kwafa yayi kawai yaa bar tashar fu. Ranar dai haka muka ?arashe kasuwarnan cikin taraddadi. Wannan shine silar da na dena bin Dada wajen sana'ar tata.
Ta Sangaren Hamma kuma sha?uwar data shiga tsakaninmu shakuwace ta ban mamaki. Banda Dada da ?annena,shi kaWai nake gani ya yaye mun damuwata da kalamanshi masu sanya kuzari, gashi kullum sai naci tsire da lemun kwalba, Abunka da ?auye tuni ?an tsegumi suka tseguntama Hama ana ganin Hamma kullum da wata mace har dandali. Dan babu ranar da bama zuwa dandali, da Hama ta gane ai nice mijinta ke ?wa?wa, duk wannan far'a da haba_haba da take yi muni sai du ta dena. Har ta kai ta kawo ta dena kulani, ko na gaisheta ma da kyar take ka da baki ta amsa, harma abu ya zame musu rigima a tsakaninta da BoWWo. Daso kuwa tsakanina da'ita takun sa?ane, ta?i ta yarda ba soyayya muke yi da Hamma ba. Tunda duk shakuwarnan bai taSa cewa yana sona ko zai aureni ba. Ita kuma ma a lokacin har Baffa ya san da zaman Manga. Dan ance mishi zuwa kaka ya turo manya a gama komai. Ita kuma tayi tsalle ta dure kan cewar Allah ya kasheta bata son Manga. Baffa kuma yace ya bata kwana talatin ta fito da mijin aure in ba hakan ba ya aura mata Manga. Ni dai sai shirin tafiyata na sanya a gabana, nayi watsi da iskantakun Daso. Lokacin da labarin tafiyata ya shiga kunnen Dada bata ja ba, sai ma fatan samun nasara da tai mun. Baffa Musa ne yaso ya turje, amman su Dada suka haWu suka tausheshi. Yaya Hamma dai ko hirar tafiyar tawa nayi mishi sai ya gimtse fuskarshi shi yasa ko zancan ma ni bana yi mishi, shima baya so, yayi juyin duniya in janye wannan tafiya. Ni kuma fur na?i amincewa, har shanu biyu ya siyar da daddare sai ga kuWi dumus nera na gugar nera har nera dubu Wari cib
Mi?o mun yayi nasa hannu na amsa sai naga kuWine.
Bayani yaimun akan siyar da shanunshi da yayi, duk dan kada in tafi. Ni kuma na?i karSa fur, na bashi hakuri tare da yi mishi bayanin na riga nasa Hajiya Salamatu ta kashe kudinta da Sata lokaci. In nayi mata haka ban kyauta ba. Dole babu yanda ya iya haka ya mayar da kuWin aljihun ?ar shararshi, tare da sauke kanshi ?asa kawai. To ya akayi_ya akayi labarinnan ya je kunnen matar Yaya Hamma sai Allah. Nan ta da bori BoWWo na bani labarin irin rikicin da su ka yi ita da Yaya Hamma. Har sai da Yafendo ta shiga cikin lamarrin. Kuma jin abinda Yaya Hamma ya aikata yasa Yafendo ta fusata itama. Kun dai san fulani da maganar Shanu, dan tsabar Sacin ran da Yafendo tayi ?wace kuWin tayi a hannun shi Yaya Hamman, tare da gargaWin koma me zaiyi mun yayi mun ni ?ar uwarshi ce. Amman bata yadda ya sake taSa shanu ba, waWannan shanu gadon_gadone da suke fatan ?a?ansu Hamman da jikokinsu, da haularsu masu zuwa suita gadansu.
. Ana saura sati guda in tafi, sai Yaya Hamma ya soma rashin lafiya. Abu kamar wasa ?aramar magana ta zama babba. Tun yana zuwa kiwo har dai ya dena. To dake a Wakin Yafendo yake jinyar tashi, ana saura kwana biyu in tafi sai na je dubashi. Ina shiga sai Hama ta bar duk abinda take yi ta dawo Wakin Yafendo ta zauna. Harma tana shafan sumarshi a gabana dan inji haushi, shi kuma kunyata tasa ya ture hsnnunta. Ai ko abun ya mugun sokar zuchiyata ta yadda ni kaina sai da nayi mamakin yanda naji sautin kishin mutumin da bai buWe baki ya furta mun kalamin so ba. Sai dai iya so da kulawa a aikace yana nuna mun. A furucine bai furta ba, kuma na fahimci nauyi abun yake yi mishi. Kunya da kawaici irin na fulanine ya hanashi furta mun yana sona. Shigowar Yafendo da fura a hannunta ne yasa Hama tashi ta dawo ?asa ta zauna.
"Jabu ga fura ki sha" Ta mi?o mun. Hannu biyu nasa na amsa nace.
Use Yafendo.
"Hama kin baro aikin ki kin dawo kin zauna? Maza tashi ki koma kan aikin ki, kinsan zaki je tallan nono fa" Har cikin ranta bata jin daWin wannan katsalandan da Yafendo tayi mata ba. Amman ni kuma kamar in goya yafendo haka naji" Tare suka fice Waki ya rage daga ni sai Yaya Hamma. Shi kuma fishi sosai yake yi dani duk fa akan tafiyar tawa ne. Ni sai tafiyar ta fitar mun akai, kuma nayi mishi rantsuwar da ace da kuWina akayi mun komai da tuni na fasa. Amman yanzu in nace na fasa hajiya Salamatu ba ?aramin bacin rai zata nuna ba, kuma ?ila ita kanta uwani in ja mata.
Yaya Hamma ya jikin naka?"
"Da mutuwa ma zanyi kila hankalinki sai yafi kwanciya ko?" Sai naji faWuwar gaba har idanuna suka kawo ruwa. Cikin rawar murya nace.
Ko kusa bazan ji daWi ba. Kayi ha?uri tafiyar da zanyi ta dole ce, kuma bazan shige shekaru uku ba zan dawo. Kuma ina fatan in dawo in sameka a cikin aminci. ?an murmushin gefen baki kawai yayi mun.
"To ki shirya tare zamu tafi kanon. Bazan dawo ba har sai jirginku ya tashi. Idanu na zaro nace.
Ka rufa mun asiri kar kasa matarka ta bindigeni. Kai da baka da lafiya kuma sai in Waura maka wahala? Wallahi ka barshi. Hararata yayi mai cike da tsantsar so.
"Ai ratayayyen hakkine a kaina inga tafiyarki." Shiru nayi zuchiyata na doka mun tambura.
To Allah ya baka lafiyar Yaya Hamma. Ni zan zo in wuce" Sallama nayi mishi na fito da furata a hannuna a Wakin BoWWo na shanye furata.
Washe gari Dada ta kawo mana ziyara da su Cubu dan muyi sallama. Tayi mun nasiha mai ratsa zuchiya sosai. Nayi kuka kamar raina zai fita. A daren na kasa baccin kirki. Ina kwance Daso ta shigo ta tsaya a kaina.
"Sai ki tashi Yaya Hamma na kiranki. Jabu wallahi kiji tsoron Allah kinzo kin samu mutum da ?ar matarshi suna soyayyarsu gwanin sha'awa. Amman kinzo kin raba wannan soyayyar da sha?uwa, kin hana Yaya Hamma ya samu lokacin kan shi balle ita Matarshi ta samu lokacin shi itama" Tashi tsaye nayi ina jujjuya maganganun da Daso ta fesomun. Kai kawai na girgiza tare da cin alwashin sai na jero mata waWanda suka fi wanda ta faWa mun zafi. Ficewa nayi na barta da ?unan zuchiya. A zaune na sameshi yana zane a ?asa da tsinke. Zama nayi a gefe nace.
Barka da zuwa Yaya Hamma. Yaya jikin naka amman?"
"Jiki da sau?i Jabu. Ya shirin tafiya? Nasan dai an gama komai ba tun yau ba. Ke naga zumuWin tafiya ki barni kike yi" Sai naji duk jikina ya mutu. Shine yake ganin kamar ina zumuWin in tafi in barshi. Amman har cikin jikina inajin zafin kewarshi tun yanzu, bansan kuma ya abun zai zama in na tafi ba.
A ranar dai hirar batai armashi ba jikkunanmu a mace mu kai sallama. Harna taka zan shiga gida ya kira sunana.
"Jabu" Cak na tsaya. A hankali na juyo muka zuba ma juna idanu na mintunan da bazan iya faWar adadinsu ba. Ya kasa ce mun uffan. Fitowar Jatau ce ta katse komai. Bai samu damar faWa mun abinda yasa ya kirayi sunana ba, Jatau ya tareshi da zantuttuka. Cikin na shige na barsu nan.
Ina shiga na harari Daso nace.
Gobe zan bar garin. Kinga hakan zai baki damar cusa kan ki a wajen Hamma. Kinga in da rabo sai in dawo in sameki kina goyon Wanku na biyu ke da shi." Ina faWin haka ta kalleni tace.."haka kika ce mun Jabu?"
?warai kuwa haka nace. In kin isa ki maye gurbina a zuchiyarshi in zaki iya Ni kin ganni nan tafiyata tafi komai mahimmanci a wajena" Kwafa tayi tace dani.
"Zan baki mamaki Jabu, zaki san nima macace wacce Allah ya horema duk abun alfahari kinsan dai na fiki kyau nesa ba kusa ba, in banda ma namiji da gane_gane ko me ya gani a jikinki oho"
Ni ban ma sake bi ta kanta ba. Itako sai mita take yi da fillanci. Ina kwance shiru duk kewan yarana ya kamani, dama Baban yaran. Can kuma sai Hamma ya fado mun, da kuma alwashin da Daso taci mun. Da irin wannan tunani bacci yayi awon gaba dani. Asubar fari na yi wanka tsab. Ana fitowa masallaci na suri kayana a jakar leda na fito.
Na yi sallama da kowa da kowa. Ana cikin haka Yaya Hamma ma ya shigo. Muna fitowa BoWWo da mijinta na isowa suma. Sai da suka rakamu fa har Girai kana suka dawo mu kuma muka shiga cikin gari, Yaya Hamma ya samu a motar Kano. Sassafe motarmu ta hau kwalta. Sai da tafiya tayi nisa Yaya Hamma yace.
"Inaso ki mun wani al?awari Jabu. Nasan kina da ri?on al?awari na san hakan silar sha?uwarmu. To ki mun al?awarin da kika tabbatar zaki cika mun shi. Kar ki yaudareni in yayi miki tsauri ki ce mun ba zaki iyaba" A sanyaye nace dashi.
FaWi alkawarinka a shirye nake da in cika shi. Matsayinka ya wuce hasashenka" DaWi yaji sosai.
"Ki mun al?awarin ba zaki wuce shekaru ukunnan da kika Webarma kanki ba. sannan ki mun alkawarin ba zaki kula samari ba dan Allah. Sannan ki mun al?awarin ba zaki dawo kiji ke kinfi ?arfin zama tare damu ba. Bi ma'ana kar ki sake halayyarki, sannan ki mun al?awarin ri?e mutuncinki" Shiru nayi mishi ina murmushi kaina na ?asa.
"Au ke dariya ma na baki ko? Kin kyauta ai" ?ago kaina nayi na kalleshi.
Yaya Hamma na karSi duk al?awarurrukanka. Allah yai ri?o da hannayena in cika maka alkawarurrukanka. Amman ina da taambaya..."
"A'a Jabu ".. yayi saurin dakatar dani ta hanyar Waga hannayenshi. Ba shiri na yi shiru da bakina.
"Ni dai tunda kin Waukii dakon alkawarina ai Shikenan. Ni kuma zan yi zaman jiran dawowarki, tare da miki fatan samun nasara kuma" Daga haka kuma mu ka Sige da hirarraki, ya dinga bani labarai dangane da al'adun Fulani. Ni kuma dama na kasance ma'abociyar son tarihi ce da duk abinda ya shafi gargajiya ta ko wanne ?abila.
Allah cikin ikonshi da amincewarshi muka isa garin Kano. Kai tsaye gidan Uwani muka ya da zango. A gidanta muka ci abinci. Yaya Hamma ya fita zuwa masallaci dan rama sallolinshi, nima na rama nawa sallolin.
"Baki ga yanda kuka dace ba wallahi. Ashe kyakkyawane Yaya Hamman naki. Kuma na lura gaskiya yana tsantsar sonki. Munafuka kema fa kin soma sonshi. Ni dai amman bana bayan wannan soyayyar ruga ba wajen zamanki bane" Dariya mu ka yi dukka.
Hakane Uwani wallahi na tsunduma cikin sonshi. Shi kuwa dama ba'a magana dan shi ya koya mun yanda zan so shi. Sai dai fa akwai kura Uwani"
Sai da ta gama dariyarta tas kana tace mun.
"?urar me kuma Iyabo, akwai wata matsalar ne?" Nace da'ita.
E to akwai matsala ta Sangaren matarshi, da Sangaren yarinyar ?anwar Dadanmu Daso wacce nake gidansu a zaune. Matsalolin du manya ne daka iya dakile soyayyarmu. Matarshi tunda aka kai mata gulmar ana ganin mijinta a wajena, sai ta tayar da ?ayar baya, kullum cikin fitina dashi take. Ke har shanunshi daya siyar ya bani kuWin ban karSaba sai da su kai rikicin da har mahaifiyarshi ce ta shiga. ?anwata tana Aure a gidan Uwani tana auren ?anin shi hamma Win. Sai suka tsiri zaman doya da manja. Ita kuma Daso ko tsaiwa da zaurawa bata son yi kwata kwata duk sabida da shi. Akwaifa wani abokin mijinta mai rasuwa da yake tsantsar sonta. Yarinyarnan fur ta dire wai bata sonshi. Ni kumaa a jiya ta caccakamun magana akan wai Hamma na zaman soyayya da matarshi ni nazo shiga tsakani na hana aci soyayyarnan yadda ya dace. To kinsan mu mata, saina caccaka mata nawa maganganun nace ta aurshi in dawo in samu tana goyon Wansu na biyu. Ita ma cikin fishi sai tace zan gani. To jiya da ?yar nayi bacci Uwani " Dariya muka dinga yi ni da Uwani.
"Ni dai shawarar da zan baki wallahi ki raba kanki da wani auren ruga, kiyi fatali da wani Hamma. Kinga ?asar zamu bari Iyabo soyayya ba taki bace. Shigowar Yaya Hamma da Hafizu ne ya dakatar da tattaunawar tamu. Sun zauna babu daWewa nace.
Uwani Hafizu mu kam zamu tafi gida. Sai gobe kuma in Allah ya nuna mana." Tare su kai mana rakiya izuwa titi har sai da Bus Winmu ta tashi sannan suka juyo. Kwatsam su Iyaa suna tsakar gida suna wannan hira tasu mai kamar faWa muka shigo.
"Ah Ah ah ah Iyabo. Ikabo ( sannu da zuwa)" Nan ta mi?e ta soma rawa harda guntuwar wa?arta su Iyaa Beji na mata dariya. Dukkansu saida na bisu Waya bayan Waya na dinga zubewa a gabansu ina kwasar gaisuwa bisa ga al'adarmu. Yaya Hamma dai duk abinda yaga nayi shi yake maimaitawa.
"Lekan, Lekan woo ah" Lekan ya amsa da karfi sai gashi harda gudu.
"Ahh Antimi Iyabo Ikabo o ti dara osale ( Anti Iyabo Sannu da zuwa Ina wuni?)"
Owo bawo ni o se n se? ( Yaya kake Lekan)? Nima na tambayeshi da yarenmu. Hannu ya mi?a suka gaisa da Yaya Hamma kana yace mun.
"Owo mo dara Antimi ( Ina lafiya Anti)
"Mu u lo si yara re ( Kai shi Wakun ku) Cewar Iyaa. Ni kuma ta jaye hannuna muka shige ciki.
"Ashe dai zaki zo Iyabo? Nayi kewarki sosai. Sai inta mafarkin ki. Har sai da Debisi yaje ya dawo ya tabbatar mun kina lafiya sannan na samu nutsuwa. Sai kika ga Debisi ko?" Murmushi nayi mata nace.
Sai gashi Iyaa babu zato" Dariya tayi kawai kana tace.
"Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Dama dan ya samu nutsuwa ne yasa na ce ya aureki dan zaki fi ganin darajarshi da kimarshi sama da ko wacce mace. Amman sai ya nuna shi baya so. To wacce yake so din gasu can kullum cikin faWa, ko jiya uwar haka suna gidannan anata shari'ar da ni na gaji da'ita. Yanzu dan Allah da ke ya aura hankalinshi ba kwance ba?" Kasa amsata nayi, dan da kunya Debisi dai ita ta tsugunna ta haifeshi.
"Shi wannan Win da ya rakoki ko shine oko omo obirin Win nawa? (Sirikina). Kai na sauke ?asa nace.
A'a yaron ?anwar Dada ne. Dama zan tafi saudiyya aikataune shine ya biyoni in mun tashi sai ya koma shi kuma"
"Ah Ah orira ( abun mamaki) Saudiyya fa kika ce?" Sai ta mi?e ta shiga rawa tana jero mun wa?o?in sanya albarka. Har sai da ta tara mun matan gidan. Nan take kowa yaji abinda ke faruwa. Nan gidan ya kacame da wa?o?i da murna. Bayan sun tafi ne Iyaa ta bani Amala tace.
"Ki kaima ?an uwanki amala yaci abincin yarbawa" mayafina nasa na Wauki kwanon na fice zuwa Wakin lekan. Da sallama na shiga na samu yana kallon wani film na yarbawa. Shi kaWaine a Wakin sai lemun kwalba na limca dake gabanshi.



*?ar uwa ina fatan baki mance da kayan ?amshin Mrs Bukhari gidan ?amshi ba ko? ?ar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ?amshi. Matso kusa ?ar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ?amshi ya ri?e miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake sa?awa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ?amshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haWe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ?ara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ?amshin kifi Wanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ?amshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ?amshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ?ar mutan Maiduguri kin samu ?amshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai Wauke da abubuwa huWu manya kuma a kan kuWi ?alilan karki bari garaSasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE....
LITTAFI NA BIYU
3

A hankali na isa na zauna a gefenshi. Idanu kawai ya zuba mun sai naga yana kaWa kai.. Kwanon abincin na tura mishi gabanshi.
Ga Amala abincin bugun gaban yarbawa da fatan kana iya ci" Dariya yayi mun yace.
"Tun kafin ki zo duniya nake cin Amala. Ai nayi zaman oghomosho, sarkin garin Oghomoshon ma bafulatanine. Kinsan tun shekaru aru aru yarbawa suke a matsayin bayin Fulani. Hakanne yasa auratayya tayi ?arfi a tsakanin Yarbawa da Fulani. Sai kiga bafulatani sak amman sai kiji bai iya ko fillancin ba sai yarbancin. Haka sai kiga beyerabiya na zagargaza fullanci. Ki duba Dada yanda naga da yarbanci zalla take magana dake." Ajjiyar zuchiya na sauke nayi dariya. Shima dariyar yayi ya soma kantara lomar Amala miyar ewedu sai dalali take yi a hannunshi. Sai da ya cika bakinshi da ( phomo) ganda kana yace.
"Ni ko kibar matan yarbawa na birgeni, kuma Allah ya zuba musu sura masha Allah ." Dariya nayi sosai nace.
Ku da kuke da farare kuma siraran mata masu gashi" Dariyar shima yake yi mun.
"Jabu kenan. Ai cikakkiyar mace ?ar duma_duma daban take da siririya. Shi kyau a sura yake ba'a fuska ba ai. Bance sirara basu da kyau ba. Kuma bance yarbawa sun fi filani kyau bane. So nake ki fahimta, wani namijin mai sha'awar haWa shinkafa da doya ne. Wani kuma taliya kaWai ta wadatar dashi" Cikin karantar yanayinshi nace dashi.
To kai a wacce matsayar kake ne?"
"Koma a wacce nake zaki sani ne"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login