Showing 147001 words to 150000 words out of 270738 words

Chapter 50 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

a kumatuna lumshe idanuna nayi na kaWa kaina na zauna a kan gado ina karanta wasi?ar jaki. In ?ulla fari in ?ulla ba?i zuchiyata bata gamsu da kukan yarinyarnan ba wallahi. Duk da naga yadda take kukan fitar hayyaci. Amman babu komai ai hama ba zata dauwama tana cin nasara a kaina ba. Wannan dai ta shammaceni. Bari mu gani gobe kuma dame zata zo. Kwanciya nayi ina kallon sama sanyi na ratsani. Irin wannan weda ta ma,auratace, naso yau yadda wedarnan ta bada haWin kai mu raya wannan dare. Amman babu damuwa gobe ma ranace.
Da tunane_ tunane bacci yai awon gaba dani mai cike tab da mafarkai marasa daWi. ?arfe ukun dare na mi?e a bahun na Waura alwala na soma sallar nafila har zuwa ketowar alfijir. Saida na sallaci asuba na kwanta a kujera dan tsabar bacci kaina kamar zai fashe.
Kamar a mafarki nake jiyo muryar BaWWo da Uwani a kaina. Ina buWe idanuna ilai kuwa sudinne. Uwani ri?e da takaddar kajin da Hamma yai watsi dasu.
"Iyabo ya kaza haka a yashe a ?asa ga Amarya kuma akan kujera, Allah yasa lafiya?" Uwani ta tambayeni. Sai da nayi Ajjiyar zuchiya kana nace.
Ina kuwa lafiya Uwani. Har Waki aka shigo aka janye ango har yanzu banma sashi a idanuna ba. Ke jiya ni naga bariki." Shewa Uwani tayi, ta nemi waje ta zauna niko na labarta mata halin da ake ciki. Hararata tayi tace.
"Kin bani kunya. Karfa ki bari zaman saudiyya da kikayi ki bari ya tashi a banza. Wacce yaudarace baki gani ba. Ga zaman gidan Gwadabe wanne siraWine baki tsallakeba? Ko da yake nifa Hama burgeni tayi, ai baki ga komai ba Iyabo"
To Uwani ya zanyi ni mamakine ya hanani kataSus. Amman bawai zan bari ta takani yadda taso bane sam. Jiyanma ta shammacenine wallahi. Na kuma barta ne kawai in halinta ne zata sake. Zigata akeyi shi yasa duk take wannan abubbuwan."
"To gaskiya karki sake bari hakan ta faru. Yanzu dai wannan kajin ai sai mu zauna muci mu kora da lemu rabonmu ne"
Wanke bakina na fito nayi a ?ofar Wakina na koma ciki, muka zauna mu uku saida muka ta da kajinnan biyu ?ananune sosai muka kora da lemun kwalba.
Ko da aka kawo mana Wumamen tuwon masara bamu ci ba mayarwa mukayi. Rishona na fitar ?ofar Waki na dafa ruwan wanka nayi, na sha kwalliyar les fari tas.
Su Anti Ramata ne suka shigo da shirinsu na komawa gida tsab. Nasiha suka sake yi mun dai a gurguje. Burodami Kokodeen ma ya shigo yai mun nasiha suka kama hanya.
Haka dai muka wuni a Waki ma?ota sai shigowa ganin Amarya suke yi ba ?a??autawa. Da rana Hama ta girko shinkafa da miya aka kawo mana, miyarnan ba?i sosai kamar anyi sauwarta da ruwan rubutu.
Daga ni har Uwani bamu ci ba. Yafendo ce ta aiko mana da fura da yawa. Dada kuma ta aiko mana da farfesun kaza, shi muka ci muka ?oshi. Wajajen azahar yaran Baffa Musa, da yaran Yafendo A'i, da su Karima harda Daso duk suka taru akaita hirar zumunci. Mafi yawan hirar da fulatanci suke yi sai hausa jifa_jifa. Daso dai ba komai take sa musu baki ba, niko na sake sosai a cikin ?an uwana. Sai da sukai sallar la'asar sannan ko wacce ta kama hanyar gidanta. Ritsona na fitar gefen Wakina na Waura ruwan zafi. Uwani ta shiga gyara mun Wakin dan duk ya hargitse. Ruwan zafin na tafasa na cika filasaina du biyun na sake mayar da wani ruwan na wanka. Kafin ayi sallar magriba na fito daga wanka.
Saida nayi salla kana nayi zaman dirshan na shafe jikina da mai, nayi kwalliya mai sau?i na sanya doguwar rigar yadin boyel me ruwan ba?in bulu ( blue black). Na saka Wankunne da sar?ata fashion ja kasancewar akwai ?aramin keb a wuyan rigar boyel din anyi da jan zare. Na feshe jikina da turare shar.
"Bari in nemo miki gaushi ki soma amfani da turaren wutanki Wan saudiyya wallahi ba dai ?amshi ba."
Fita tayi da kaskon turaren wutan. Tana fita Safiya matar ?anin Hamma ta yo sallama ta shigo hannunta ri?e da langar tuwo da miya ta ajjiye.
"Ga abinci Adda Jabu. BaWWo har yanzu bata gama girki ba shine nace bari in kawo miki" Murmushi nayi mata nace.
To Nagode kwarai Safiya" Tana fita uwani ta shigo da gaushi.
"Gashi kishiyarki ce ta bani. Kinga wata yaluwar atampar data saka wai ita tayi kwalliyar yamma? Wuyan rigar baya ko zama tsabar yadda yayi mata yawa, ta ko rambaWa jar hoda fuskarnan tayi jawur."
Dariya muka tuntsire dashi. BaWWo ce ta shigo da tiran abinci. Shinkafa jallof tayi da kifi, sai fura da dambu cikin jug Win silba.
"Adda wannan nono da Dambun na Yaya Hamma ne. Kullum sai ya sha babu fashi nasan baki sani ba shine nayi miki. Ga abincinku. Adda Uwani muje muci namu Yaya Hamma ya dawo yana wajen shanu"
Kwanukan abincin Safiya na mika ma BaWWo.
Ungo ko yaranki sa ci, wannan ya isheshi ni a ?oshe nake"
Ta karSa suka fita. Suna fita na ta da sallar Isha. Ina zaune ina lazimi Yaya Hamma ya shigo da sallama hannunshi ri?e da ba?ar leda babba.
Da sauri na mi?e na amshi ledar hannunshi na ajjiye a gefe.
Zama yayi a kujera yana sauke ajjiyar zuchiya da gani a gajiye yake dan idanunshi sun lumshe da ?yar yake buWesu.
A gefenshi na zauna.
Sannu da dawowa Yaya Hamma " Hannuna ya ri?o ya matse a nashi, ya zuba mun idanunshi da yake lumshesu.
"Amarya kinyi kyau. ?akinki yayi kyau sosai, tsarin ya burgeni"
Murmushi nayi mishi kawai.
Ina ka shigane tun jiya rabona dake.
Murza hannuna yayi yace.
"Ke dai bari, yadda naci burin daren jiya bai kasance yadda na tsarashi ba. Yarinya ba ita ta samu bacci ba sai asuba, ina dawowa masallaci kuma na wuce gidan Baffa Musa yana nemana. Acan na daWe daga nan kawai saina wuce wajen aiki dan nasan gidan cike yake da mata. Aimun afuwa in ran gimbiyata ya Saci, ba da nufi komai ya faru ba. Su Inusa ma ?orafi suke yi mun wai ban kawosu sunci tuwon Amarya ba"
?an murmusawa nayi nace.
Ai babu komai. Ciwo ya doke komai ai, ciwonma na yarinya ?arama. Su Iyaa sun tafi yau, uwani kuma sai jibi so take tabi BaWWo suje cin kasuwa akwai abubuwan da take son ta sassarane"
"Uwani baiwar Allah. Wannan ?awancan naku yana bani sha'awa gaskiya. Ina muku fatan ya dore har ku haWa ?a?anku auratayya"
Ameen. Yanzu dai me kake son ka soma, wanka, ko cin abinci? Naji sai warin rana kake yi"
Duk wannan hirar a shingiWe yake a kujera hannuna yana cikin nashi yana murzawa.
"To wanne kika ga ya dace dani? Ni wanka ai sau Waya nake yi, wani sa'inma sai in kwana biyu gaskiya banyi ba, sabida yanayin aiki da kiwo"
Dariya nayi, shima dariyar yayi yace.
"Sai kinyi ha?uri mijin naki ?azami_?azamine"
A'a ba haka bane. Kar ka damu wannan duk ya kau daga yau. Wanka sau biyu safe da dare in sha Allah. Bari in kai maka ruwan wankan ka watsa sai kazo mu ci abinci, ga nono da dambu yana jiranka"
Ina faWin haka na mi?e na juye ruwan filas Waya a bokitin ?arfe, na fita waje randata tana bakin ?ofata na surka mishi ruwan, na haWa mishi da soso da sabuluna na kai mishi.
Yaje yayo wankanshi tsab, na dangwalo mishi dakakken gawayi wanda aka cakuWa da alim nace.
Goge bakinka tas Yaya Hamma "
Murmushi yayi ya amsa ya tsugunna a ?ofar Wakina ya jima yana goge bakinshi. Ni kuma ina ciki na haWa mana tea na zuba mana abincin BaWWo. Na zuba miyar stew da uwani tayi mana taji soyayyan kifi sukunbiya.
Tare a plate Waya muka ci abincin, kaWan yaci ya Wauki nono da dambu ya sha, ni kuma na sha tea.
"Akwai kazar amarci a ledar dana shigo da,ita ki Wakko"
Ai sai dai da safe mayi karin kumallo da'ita a yanzu gaskiya na ?oshi.
Gaga_gaga muka kammala duk abinda ya dace, muka Wauro alwala muka yi sallar nafila bisa Shari'a. Daga nan al'amura suka soma sauya salo, daga ?asa zuwa kan gado. A hankali abubbuwa masu daWi da wuyar fassaruwa sukaita gudana. Har abinda aka daWe ana mafarki ya tabbata a tsakaninmu. Abinda ya curemu muka zama guda kenan. Abinda ke ?ara soyayya da sha?uwa a tsakankanin ma'aurata. Yaya Hamma yayi mun bazata, dan banyi tunanin tattali irin wacce na samu ba, asalima ban kawo irin wannan tattalin ga mutumin ?auye ba, sai gashi ya kere tunanin Iyabo. Dan wallahi Gwadabe da wasa bai taSa kaini irin wannan duniyar ba. Shima kuma na fahimci na kaishi duniyar da babu fulani a cikinta.
Wannan yanayin ya ?ara mana so da shau?in juna sosai. Bayan komai ya lafa muna kwance muna mayar da numfashi, Yaya Hamma ya juyo ya zuba mun idanunshi masu haske kamar madara. Abu Waya da ya bani tsoro shine na fahimci Yaya Hamma kamar baya aski ko ince baima taSa yi ba irin yadda na fahimci yawan gashin. Amman nasa a raina zuwa washe gari zai aske shi tas.
"Jabu soyayyarki ta kasance ta daban a zuchiyata. Kin kafa babban tarihi a wannan daren mai Wumbun nasara da tarihi. Allah yayi miki albarka. Nagode da kika tallafi soyayyata baki hofantar dani ba. Wallahi Allah shine shaidata da ban sameki ba, komai zai iya faruwa dani, ina nufin komai.
Ina ro?onki komai sauyin yanayi dana zamani kar ki gujemun, kar ki juya mun baya"
Mun jima a wannan daren muna ma junanmu al?awarurruka masu nauyi da girma. Daga ?arshe tare dashi muka je banWaki mu ka yi wankan Sallah. Duk da yana no?ewa tare da jin tsantsar kunyata, har rufe idanunshi da tafukan hannunshi ya dinga yi. hakan bai hanamu yin nishaWi ba. Yanayi ne mai kyau, irin yanayin da na jima ina mafarki kenan Allah baisa na samu tare da Gwadabe ba, sai gashi na samu a wajen Yaya Hamma.
Bacci mu ka yi mai daWin gaske, baccin da saura ?iris Yaya Hamma ya rasa sallar asuba. A gurguje ya zura rigarshi mai warin hammata da warin awaki ya fita. Idanu na lumshe tunanina yana mayar dani daren jiya da ni'imomin dake kewaye da daren. Marata na shafa ina fatan Allah yasa Yaya Hamma yayi ajjiyar jininshi a marata in haifa mishi kyakkyawan santalelen saurayi me kama dashi ya samu abokin shawara.
Da ?yar na fito nayi alwala wani irin mu?u_mu?un sanyi ake busawa sosai.
Ina idarwa na kunna risho na dafa ruwan tea na zuva a filas na Wakko wannan kaza na Worata akan plate. Na mayar ma da Yaya Hamma ruwan wanka.
Yana shigowa na kai mishi ruwan wanka, ya tafi ya yo wankan. Ni kuma na shiga cikin gidan.
Matan gidan duk suna kitchen Win tsakar gidan ko wacce girki takeyi a murhunta. Wani irin murhu garesu ginanne mai kyau, da laka ake ginashi, sai Wan ramin dora tukunya. Duk ramuka bibiyu akaima ko wanne murhu, nawa yana kusa dana Hama sabo dal dashi har fenti akeyi mishi.
?akin Yafendo na shiga muka gaisa sannan na fito na nufi kitchen din. A dokin ?ofar kitchen Win na tsaya. Hama na dafa madarar shanu ta Wago muka haWa idanu. Ta wani turSune fuska wuyan rigarnan nata a sauke nonuwanta rabi da kwatansu duk a waje. Wani tsohon kitsone a kanta duk ya furje. Ga gashi dai yala_yala amman babu gyara duk abun katifa ya rirri?e gashin haka ma kan yaranta yake. Babbar ?arta me sunan Yafendo tana gefenta ri?e da kofi hancinta sai yoyyo yake yi. Duk sanyin da akeyi kan yarinyarnan ba Wankwali, ?afarta babu takalmi ba suturar arziki.
Maman Dada ina kwananku?
Hama ta juya kai ta mayar da hankalinta akan madarar da take dafawa. Sai su Fatu da Safiya ne suka amsa muka gaggaisa. BaWWo ta gaisheni tare da cewa.
"Yanzu nake son in kawo muku madara ku karya"
To sai in tafi da'ita. Maman Dada kayan Yaya Hamma zaki bani yayi wanka yana son sauyawa"
Sai ta saki muciyar da take juya madara ta juyo a fusace.
"Shine ya aikoki ko zuwa kikayi ki sanar dani ya kwanta dake kome kike nufi Jabu? To bazan bayar da kayan ba shi bashi da ?afar da zaizo ya Wauki kayanne."
Taja dogon tsaki ta fice fu a kitchen Win, saida taso bangazata na matsa da mugun sauri.
Dariyar Uwani na jiyo daga bayana. Harda tafinta Uwani ?ar duniya kenan. Nima darawa nayi kawai.
"Sai ha?uri Jabu. Yanzu Maman Dada a cikin fishi take" Cewar Safiya wacce na lura tana da hankali.
Ba komai Safiya komai zai daidaita. BaWWo bani madarar"
Madara ta mi?omin cikin kofin silba na nufi inda Uwani ke goge bakinta.
"Wannan kishiya taki sai kinyi da gaske. Irin wannan daga miki murya da take yi haka, sai kace uwarki?"
Ke dai bari Uwani. Bari in sallami Yaya Hamma zan zo in sameku, ?ila ma muje kasuwar tare in ya barni dan inason in yi siyayyar kayan miya da abinda ba za'a rasaba ?ila yau muna da ba?i masu cin tuwon dare.
"To Shikenan sai kin shigo maza aje a kula da megida"
Komawa nayi Waki na tarar da Yaya Hamma yana karyawa.
Harka soma karyawa Yaya Hamma?
Murmushi yayi mun.
"Na gama ma. Inaso in fita kiwone yau nama Sata lokaci sosai."
Kallonshi nayi ya mi?e tsaye nace.
To Allah ya tsareka ya dawo da kai lafiya.
Yauwa Yaya Hamma nace abokan naka su nawa ne zasu zo zan musu girkinne?"
Hularshi ya mayar kanshi kana yace.
"Mu shida ne."
To dan Allah inaso zan raka Uwani kasuwa siyayyarta da yawa kuma nima ina bu?atar zan Wan yi siyayya".
Jim yayi kamar bazaiyi magana ba dai. Sai yayi dariya kuma yace.
"Da ?afa suke zuwa cin kasuwar fa, mota wuya take yi sosai in zaki iya to kuje sabida dai Uwanine amman da bazaki ba"
Nera Wari biyu ya bani yace.
"Ga kuWin cefananki nan sai ki sai abinda zaki siyo acan yafi arha. Ki karSi garin tuwo da Wanyan man shanu a wajen Hama zan mata magana ta baki"
A gurguje mu kai sallama ya fice. Kayan karin na tarkata na fito na nufi tsakar gidan. Yaya Hamma yana ?ofar Wakin Hama da sandar kiwonshi, mijin BaWWo kuma yana kaWa shanun waje.
Bance musu um ba na wucesu kamar ma ban gansu ba.
Tare da su BaWWo muka ci kazarnan da tea muka kora da dafaffiyar madara.
"Bari inje in harhaWa kayan nonona sai inzo mu tafi Adda Uwani"
Fita tayi, fitarta ke da wuya uwani ta soma zolayata. Da dariya na bita kawai. BaWWo ta gama haWa ?orenta na Nono ta le?o tai kiranmu akan muje. Muna fitowa Hama na Waura ?oren nononta a ka, ta fice tana tsaki.
Yafendo muka je mu kaima sallama.
"Jabu har da ke za'aje?"
E Yafendo inaso inga kasuwarne" na bata amsa ina sauke kai ?asa.
"To Shikenan. Nima yanzu ina gamawa zan biya ta wajen Adda Daso kafin in wuto kasuwar."
To Yafendo muma in muka dawo zamu biya can uwani zata maata Sallama.
A wannan kasuwar naga tarin ?auyawa iri da kala. Ga masu tuyar ?osai da masu saida burodi, komai akwai a wannan kasuwar gasu da arhar nama, ga kayan hatsi, gasu nono, mam shanu, madara, suturu, harda shanu da tumakai, kaji, zabbi, rediyone tocila, su kayan miya Wanye da bushasshe babu fa abinda babu. Ga maza da matan Fulani dam?am wasu sunzo siyayyane irinmu, wasu kuma kasuwanci ya kawosu irinsu Hama da BaWWo. Haka mu ka shawo siyayya nan muka baro BaWWo.
Bayan mun dawo muka ya da zango a gidan Dada anan muka tarar mai nagge yazo ya tusa ?eyar su cubu yace ba zasu zauna a hannun Dada ba. Su Baffa Musa suna zazzaune ana mayar da zancan Dada sai hawaye take yi muka shigo.
Baffa ne yai mun bayanin halin da ake ciki, da korar Amaduyal da yayi a gidan nashi kan yace bazai iya dena zuboma Dada abinci in matarshi ta dafa ba. Shine ya ?wace shanayen dake hannun Amaduyal Win ya fito musu da kayansu. Ajjiyar zuchiya na sauke bayan na gama jin komai nace.
To babu damuwa, su Cubu su je su zauna wuya bata kisa. Amaduyal kuma ga Wakinan ku share kai da matarka ku zauna.
Shanu dama ina da burin siya ko babu yawa zan dan?ama ka dinga yi mun kiwonsu, a jiki ku dinga samun madara, nono da man shanun da zaka kula da iyalanka da abincin da Dada zata ci. Dada ki dena kuka Allah zai rufa mana asiri." Baffa Musa ya sauke ajjiyar zuchiya yace.
"Shikenan an samu masalaha. Jabu sannu da zumunci Allah ya baki waWanda zasu yi miki kema. Mai Nagge kuma ina ?ara jan kunnenki kar ki kuskura wani abun ya shiga tsakaninku, ko bayan raina kar ku tayar da maganar shanun Daso daya danne ya zama mallakinshi mugun mutumne wanda zai iya kashe duk wanda zai tayar da wata magana akan shanunnan. Duk shanun da kikaga yana gadara dasu na Daso ne wanda ta samu a gado, labari aka bani rugga_rugga sai yawon bin bokaye yake yi kuma duk akan a rufe bakinmu kar mu tada zancen Shanu ne. To mun yi shiru zamu haWu a gaban Allah"
Ba komai Baffa mun bar maganar in sha Allah. A dai nema mana shanu sai mu siya manya da ?anana sabida shi Amaduyal ya soma fita kiwo, duk da gidan babu inda za'a iya garke.
To anan nake cewa daku mu tara ranar monday in Allah ya kaimu.
To ina ?an team Hamma goga dai ya ciri tuta.
Ina masu ?in Hamma me zaku iya cewa ina sauraren ra'ayinku.
Mrs Bukhari


Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login