Showing 222001 words to 225000 words out of 270738 words

Chapter 75 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

abunda kikyeeso atura muki ko menene har supplement domin gyaran jikin domin ba iya Kaya muka tsaya ba wasu abubuwan ma sai ka shiga group Dina zakasha kallon sabbin abubuwa masu kyau da Kuma sauki
Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230

NAMA YA DAHU....

ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

LITTAFI NA HU?U (3)

IYABO:.

Muka haWa kai da matan gida, da ?awayen Hama na ma?ota, da danginmu kusan mu rai ashirin, ko wacce da goyonta, wasu da yara a hannu raSe_raSe muka nufi gidan suna. Sai an hau keken shanu ake isa ruggar su Hama. Rugarma babu yawan bukkoki Wan ?aramin wajene. Tun daga nesa muke hango mata sunata shiga gidan sunannan.
Da sallama muka shiga yuu.
Yara na guje_gujensu manya anata hidimar gyaran kayan miya, masu tsintar shinkafa nayi.
Gidan nake kallo ko da dai taro akeyi amman da gani gidan ?azamai ne babu ko shakka. Kuma irin gidajen talakawan fulaninnan da ko akuya basu mallaka bane.
Abun mamaki duk dangin Hama sun san Daso sai ambaton sunanta akeyi. Ni dai ina biye dasu har cikin wata bukka.
A ciki muka tarar da Hama Ware_Ware a gado da jaririyarta a gefenta. Kanta an yarfa mata kitso jelarnan har gadon bayanta, ga ?unshi tayi jawur dashi, har jaririyar akaima ?unshin hannu da ?afa. Akwai wasu dattijai biyu a Wakin, da wata yarinyar mace a zaune a kan gadon da hama take.
?aremun kallo Hama ta shiga yi, tana kallon suturata, wani irin mugun kallo take yi mini. Hmm
Waje muka samu mu mu uku muka zauna ragowar suna daga waje.
Sannu mai jego, ashe kin sauka. Ina wuninku?"
Na ?arashe zancan da gaishe da matan Wakin. Ko sun fahimci nice kishiyar Hama sai naga anyi mun amsawar wula?anci. Ni dai daman nasan za'a rina sai naja bakina na tsuke. Duk motsi Hama idanta na kaina. Ita bata gaisheni ba, ni dana daure na gaisheta sai tayi funfurunfus ta?i amsawa tana daga ?wance suna magana da Daso. BaWWo ce ta mi?e zata Wauko mana jaririyar Wayar yarinyar macen dana ce muku tana zaune a bakin gado sai tayi carab ta dam?e hannun BaWWo"
"Yarinyar bata da lafiya kar ki ma soma Waukarta mai son ganinta ya ganta a haka" Maganar da tsawa_tsawa da iskanci take yi. Hassanne ya soma kuka sai na suntoshi zafi na shirin kashemu. Ya haWa zufa yayi sharkab. Duk matan Wakin wallahi sai suka zuba ma yaronnan ido. Da naga haka saina mi?e tsaye.
Zan Wan fita daga waje in basu Mama, nan Win akwai zafi. Ga wannan ?ar gudunmawatace babu yawa"
Na ajjiye ledar na ja hannun BaWWo muka fice."
"Lallai saifa kin tashi tsaye. WaWannan yaran maza kyawawa sune yaran kishiyar taki shine kike kwance kike bacci? Ai in dai da yarannan to yaranki sun zama bola a wajen Hamma"
Karab a kunnena duk da dai da fullanci tayi maganar na ji tsab abinda tace Win. Bansan kuma wacece ba dai.
Ni dai na ja turmi a tsakar gida ina shayar da biyu ina tofesu da adda'a. Yaran duk wanda ya kallesu Allah sai ya ?ara. Sabida haskensu gasu da jiki kunsan yaro mai ?iba anfi sonshi, gasu ?an biyu abun yayi musu yawa. Muna dai zaune su BaWWo sun shiga anata aiki dasu. Ni dai bansa hannuna ba kuma bazan kuwa saka ba in ji da kallon banzan ma da akeyi mini. Muna zaune da Safiya da Adda A'i yarinyar Baffa Musa muna ta hirarmu har azahar ba'a gama girki ba, har mu kai Sallah. Ni kuma yarannan gasu da tsotso yunwa ta kamani sosai. Kuma ni ko karen hauka ya cijeni ai bana sa abincin gidansu hama a bakina ba.
Wallahi aka sauke abincinnan akaita rabo ni dai har abincinnan naga babu har an zuba ma tukunyar abincin ruwa. Ba'ace ku ga naku ba, amman fa iyakar mu mu ukunnan da muke zaune dan BaWWo dasu akai komai an zuba musu to batayi tunanin ba za'a bamu ba saita cinye abunta.
Hmm sai wajajen uku na yamma aka kawo mana abincin. Shinkafa da miyace a mugun ja?ale shibkafar kamar fate, miyar kuwa yadda kukasan markaWaWWiyar kabewa wai miyar stew ce.
Ni dai gaskiya loma ban sa a bakina ba. Awarar nono na fita na siya naci na danne daa ruwa. A hakan ma Sai naji zuchiyata na tashi da ?yar na mayar da aman da nake ji. Muna yin sallar la'asar muka nemi hanyar garinmu. Nasha habaici sosai. Ko wacce figaggiya sai kaji tana me za'ayi da ?iba, ai anfi yayin mata sirara. Wata ma bata da maraba da cry fish amman sai fi'ili. Saida muka fito na sauke ajjiyar zuchiya na sha?i iska da kyau.
Washegari na tashi da kunce tsaraba da rarrabawa. Wajajen azahar na wuce gidan Dada acan muka wuni cur miyar dana tawo da'ita rabi na zabtare na kawo mata. Acan na iske Cubu da yarinyarta.
Cubu wai har yanzu ashe baki koma ba?"
"Bata koma ba kin ganta nan. Ni nasa an kira mun mijin nake tambayarshi ko lafiya. Yarinyarnan in laifi tayi ni ya sanar mun ya daga zuwa wankan gida zai hana yarinya komawa Wakinta. Ha?uri dai kawai ya bamu. Ni fa jikina ya mutu gaskiya ruwa baya tsami banza"
Jikina ya mutu nima. Tabbas ruwa baya tsami banza akwai wani abun a ?asa. Kishiyoyima ai ba zasu barta ba. Amman babu komai akwai Allah.
Shinkafa fara na dafa mana har dare mu ka ci Dada nama huWu manya nasa mata da kifi, da ganda tana ci tana shi mun albarka. Ni dai tun bayan la'asar daf magriba saina soma jin wani sabon yanayi a tattare dani dai haka. A daddafe nayi Sallah ina zaune nayi tagumi sai nake jina kamar wata marar lafiya haka. Ganin Walibaina sun soma shigowane yasa na Wan sake kaWan na ?warara kaina. Nan muka soma karatuttukanmu bayan mun gama na baje musu kayayyaki. Allah cikin ikonshi janbaki da gazal WaWWayane kawai yayi ragowa du sun kwashe komai nerata dubu ashirin cas a cikin jakata. Bayan nayi Sallah saina goya biyu nayi ma Dada sallama muka kama hanyar gida ni dasu BaWWo. ?arayin Yafendo naje na kai mata nata shinkafa da miyar nai musu sallama na shige Waki na kwantar da ?an biyu ina zaune ina harhaWa kan kuWaWen ciniki, da kuWaWen da nazo dasu, da wanda Burodami Debisi ya bani. Sai naji gabana yayi mummunar faWuwa. Ba shiri na dafe ?irjina na runtse idanuna.
Daga haka sai nayi maza na mi?e tsaye na cusa kuWaWennan a jaka. Na saSa biyu a bayana, na mayar da mayafina na suri ?aramar jakar da kuWina ke ciki.
Wallahi tiryan_tiryan ba saina fice a gidanba na naushi hanya, inayi ina haWawa da gudu_gudu. A lokacin wata guguwace nake jin tana tashi a kaina, ji nake kamar zan rasa rayuwata inna ci gaba da sha?ar iskar JaSSi lamba. Hakanne yasa na shiga gudu_gudu burina in bar rugar kawai. Babu wani tunani a kaina, bana iya tunanin komai burina na barin garinne.
Ina fitowa kan iyaka na samu mota ta cika zata Girai saina faWa motarnan. Ina zaune shiru kaina na wani irin zafi da ciwo. Gaga_gaga muka iso Girei. Na kuma samun motar cikin gari nanma na shige. Banfa san ina zanje ba, ni dai burina inyi nisa kawai.
Muna shigowa tasha aka saukemu. Nayi tsayuwata a gefe nayi shiru. Nafi minti sama da talatin a wajen.
Wani Wan wuniyonne yace.
Hajiya ga rumfa can da ?an uwanki mata kije ki zauna mana. Hala kema fasinjar Lagos Wince? Gashi motar ce ta samu matsala tashi sai gobe da sassafe. Ko kin fita ba zaki samu abun hawa ba"
Haka nabi bayan bawan Allahnnan izuwa rumfar da matannan suke. Harda masu goyo. Waje na samu na zauna shiru. Hankalina baya jikina bansan meke mun daWi ba sam. Amman nasan nice Iyabo, Hassan da Usaini ?a?anane iyakar abinda kaWai nake tunawa kenan fa, duk rayuwata da asalina ya goge a kaina bansan kowa ba sai kaina da ?a?ana fa. Allah gwanin iko da hikima. Allah ya tsare duk mata da sharrin kishiya mai asiri. Gata ayi fito na fito, ko makirci ko kuita cin uwar sabada a tsakar gida. Duk macen da aka taSa yima asirin gusar da hankali da tunanine kaWai zasu fahimci Iyabo.
Gaga_gaga cikin dare kowa yayi bacci, ammanni ina zaune na zuba ma yarana dake bacci saman cinyoyina idanu ina kukan da bansan dalilin yinshi ba.
Sai in dinga jin kamar ana kiran sunana. Wannan dare shine dare mafi muni a rayuwata. Sau?in dana samu asussuba muna idar da Sallah akace mu shiga mota. Ni dai matan da muka kwana rumfa Waya nabi muka shiga wata ?atuwar mota muka zazzauna mazanmu da matanmu dukka. KuWin mota akace mun biya nera dubu biyar.
Na ?irga na bayar. Matar dake kusa da kujerata na tambaya.
Dan Allah baiwar Allah motar inace wannan wanne garin zata je?"
"Lagos zata je ke Win bakisan motar ina kika shiga ba har kika biya kuWi?"
A_a ba haka bane"
Iyakar abinda nace kenan. Idanuna na lumshe na dinga hawaye. Motarmu ta fice a tasharnan duku_duku muka kama hanya, tafiya muke yi, muna wuce ?auyuka, da garuruwa. Mune har azahar muna tafiya sai lokacin na ji zuchiyata tana Wan rage nauyi da sanyi haka. Da muka shiga wani gidan mai inda zamu yi sallah muci abincine ma sai naji inajin yinwa musamman da naga balangu, da zire, da abinci anata siye. Sallar na soma yi, sai na sai tuwon sakwara da miyar egusi, da ruwa na koma mota. Kari Waya naci tuwon Wayan kar n na ba ?an biyu suka ci suka sha ruwa. Nabkin Win jikinsu ya ji?e sharkab. Sake fita nayi na sayi ruwa na cire musu nabkin Win na wanke musu kashi, na ?ulle tsummokaran a leda a wajen na barshi. Ina shiga motar direba ya tashi mota dama ni ake jira. ?ankwalin kayana na zare na keta shi biyu dashi nayi musu sabon ?unzugu. Gaga_gaga mukaita tafiya kiki_kiki mune la'asar magriba, isha. Ni dai ina zaune ina kallon titi wani irin sanyin ni'ima da kwanciyar hankali na saukarmun wanda bai da tamka. Yarana na kalla suna cinyata suna wasansu. Murmushi nayi na shafi kansu, bana iya tuno kowa da komai, yarannan dake cinyata su kaWai na sani abun mamaki ko? Wallahi babu mamaki a duniyarnan babu abinda ba'ayi sai in bai zo kan ka ba ko kan wani naka ba shine zaka yi mamaki, ko kan ka ya?i Wauka ma. Misalin ?arfe taran dare motarmu ta shiga gareji mun iso cikin yardar Ubangiji. Duk muka sakko ?afafuwanmu a kumbure. Ni dai babu wanda na sani bansan inda zan nufa ba. Titi kawai naje na tsaya inata kallon motoci suna wucewa.
Lagos gidan cunkoso kenan. Motoci iri iri sukaita wucewa, ga jama'a a ?afa sai yawo suke yi. Da dai naga wankin hula yana shirin kaini dare saina koma cikin tashar na shiga rumfar wata bahaushiya mai saida masa da tuwo na zauna. Wata matar shagon ta iso inda nake tace.
"Tuwo ko masa kike bu?ata?"
Masa zaki zuba mun. Amman kafinnan dan girman Allah ku taimaka mun da masauki ni ba?uwace bansan kowa ba a garinnan"
Kallona tayi da kyau ta dubi yaran hannuna tace.
"Amman baiwar Allah da yarannan kika shigo bariki maimakon ki barsu a gidan ubansu. Nasan bazai wuce takaicin rijalu bane ya sa kika fito yawon duniya ba. Zan kawo miki tuwo in mun tashi zan haWaki da Hajiya mai shagonnan ?ila ta taimaka miki da masauki amman bafa kyauta ba. Nan Lagos kika shigo kowa kika gani a nan kuWi ya fito biWa. Masar nawa zan sa miki?"
Nera Wari uku na bata ta wuce bata jima ba ta kawo mun masar. Hassan na sunto na soma ba, daya ?oshi na ba Usaini ma kafin na ci nima muka sha ruwa na takure a gefe. Jama'a sukaita shigowa wannan shago. Dare yanata tsalawa.
Wannan dai mata itace ta zo inda nake tace.
"Baiwar Allah kizo muje office Hajiya ta ganki."
Mi?ewa nayi da saurina nabi bayanta. Ma'aikata sai mi?a ma mutane abinci suke yi. Ga ?an mata tsula_tsula cikin kwalliya suna tafe da yanga. Matanma kamar zaSarsu akeyi ko wacce babu muni a tattare da'ita.
Cikin ofishinnan muka shiga. Wata shirgegiyar Hajiya kamar ni tana zaune ga kuWi cikin robar fenti babba a gabanta sai haWasu take yi. Ga wasu bandir_bandir a gefenta ta haWa. Taci uwar bilicin, ga kwalliya ta alfarma sai cin cingam take yi"
"Hauwa wannan ce matar da kike faWamun, yo baiwar Allah zaki fito bariki da yara har biyu keko taya zaki samu aiki? A_a wallahi ni bazan iyaba. Kuma kinyi ?iba da yawa ma'aikatana kinga ?an madaidaitane masu jawo hankalin maza dai." Ni dai nayi shiru ina saurarenta. Wacce ta kira Hauwa tace.
"Hajja Mama a duba na fahimci kamar gudowa tayi, dan ko jaka bata ri?o ba na kaya. A duba dai" Da harara matar ta bini.
"Menene sunanki, kuma daga wanne garin kike?"
Sunana Iyabo Hajiya. Bansan daga wanne garin nima nake ba, amman dai garinmu da nisa gaskiya "
"To dake dai naji kince sunanki Iyabo. Ke beyerabiya ce, ku yarbawa an sanku da juriyar aiki. Zan taimaka miki zan tafi dake gidana zaki zauna a hannuna. Amman duk sati zaki biya nera dubu biyu kuWin Waki, kullum Wari biyu ake biya. Ina bayar da abinci wannan ba matsala bane tunda kune masu aikin abincin. Zan duba inga a wanne gurbi zan saki. Sai dai inada sharaWi in kinsan yaranki masu kukane to wallahi kona Waukeki zan sallamekine ehe. Bazai yiwu na rufe shago biyun dare ba inaso inje in huta ace kuma yara sun hanani bacci ba"
Jikina na rawa na dinga jero mata godiya harda tsugunnawa. A ofishin na rama sallolin da duk ake bina. Na zauna a gefe Hajiyannan sai kuWi take ?irgawa, Hauwa na sake juyo mata kuWin daga ?aramar robar fenti. Yadda tsarin ofishin yake, wata ?ar ?oface kamar taga amman ta gilashi. Anan masu siyen abinci suke biyan kuWin abincin, sai suje su zauna a tura yara su kai musu abincin. Hajiya kuma tana Hakimce tana tattare kan kuWaWenta.
Wayarta ce tai ?ara ta duba tana ?irga kuWi.
"To yau kuma an tuno dani kenan Dr manya"
Wayar ta Wauka tace.
"Likita bokan turai kaddai ka shigo Lagos ne yasa ka kirani? Dan na fahimci abincin Hajja kaWai kake son ci, da zaran ka bar Lagos kiran waya ya ?are"
Na cikin wayar bana jin abinda yake cewa. Jim tayi dai tana saurarenshi kafin ta Waura da cewa"
"Ai in akwatin aure kake so ka samu balle akwatin me jego. Kai dai turo kuWi kawai Alhaji za'a haWama akwatin kayan fitar suna. Ina da tela duka Wauka wannan wanda ya taSa ma Amaryarka Winkin kayan lefe? To shi in harda dinkin ma za'ayi maka duka"
Sai ta kuma tin jim.
"To to Shikenan Alh sai na ji Alart sai kuma ka faWamun wacce kala uwargidan tafi so. Sabida asai mata kayan da zai ?ayatar da'ita. Sai na jika likita bokan turai"
Ta ajjiye wayar tana dariya tana ?irga kuWi abunta.
Muna wannan shago har biyun dare masa dai ta ?are tas tuwonne ma akwai ragowa. Nan aka shiga hada_hadar tattare kayayyakin daya dace. Akayi wanke_wanke da gyaran wajen tas. To a gaskiya zagewa nayi na tayasu aiki. Saina fahimci kazarniyata ta burge Hajja dama ni fatana kenan.
Muka kama hanyar gida da wata akwalar motar hajja. Kusan mu rai goma a mota Waya gashi ni ba kaWan ba ga yara a bayana. Sai sakkosu nayi aka ri?e mun su na saka ?an mata biyu a cinyata suka zauna. Munyi tafiya mai nisa kafin muka shigo wata unguwa.
Abun mamaki sai nake ganin mutane a layin kamar ma ba tsakiyar dare ba. Ga masu siyar da abinci nono_nono a jejjere. Ga kuma mutane a titi suna baccinsu, wasu a ?ofar masallaci, wasu akan teburan masu kayan miya.
A wani gida da akayi mishi katangar kwano muka tsaya duk muka sassauko. Ni dai biye dasu nake har cikin gidan.
Hmmmm fasalta ?azantar dake cikin wannan gida Sata lokacine, masu saurin amai da tashin zuchiya sai suyi. Haka dai muka shiga wani Waki Wan ?ub ciki da falo. ?akin duk shirgi, ga mata har guda biyar a kwance, banda waWanda muka tsallake muka shiga.
"Ke Iyabo. Ku raSa ta can lungun kujerar zaki Wanfi samun sakewa kar a tumurmushe miki yaranki, naga ma basu da rigima sai baccinsu suke yi." Cewar Hajja Mama kenan.
Inda ta nunamun na wuce da yarana. A tantagaryar ?asa na kwanta, na shinfiWa mayafina na shinfiWe yaran. Nayi shiru inata kallon sama kawai, so nake inyi tunani akan wani abu ko guda Wayane, amman koma nace zanyi iyakar abinda nake tunowa hanyar motane kawai inna matsa sai ciwon kai da tashin hankali kuma.Idanu na lumshe na shiga kallon matan dake cuccure a waje guda, sai tusa suke sakewa Waki ya cika da wari, ga masu gwarti sai ja da sakewa suke yi. Banci ya Waukeni baifi da minti goma ba akayi kiran assatu a masallaci. Kowa saiya tashi.
Kafin sallah gidannan ya karaWe da hacaniya sai girke_girke akeyi matan gidan na abincin saidawa. Hajja Mama ma tuni ta ba da oda an gangama tukwanen girki, ni kuma muna ta wanke farar shinkafar masa ni da wata mata dan zata yini a shekaru"
"Jiya kika zo garinne baiwar Allah. Na ganki da yara kuma. Ai yawon bariki ba'a fitowa da yara. Ko gudowa zaki yi ba sai ki bar yaran a wajen ubansu ba. Nifa yarana bakwai haka na tsallako na barsu kuma ni da komawa ganinsu saidai a darussalami"
Na dubeta nace.
Jiya nazo, yara bani da inda zan ajjiyesune."
"Sai dai zasu iya hanaki yin aikinki yadda ya kamata. Koma naga kina da ?wazo. Sunana Batula


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login