Showing 84001 words to 87000 words out of 270738 words

Chapter 29 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

muka isa inda zamu je ba sai da asuba. A ?ofar wani babban gidan bene motarmu ta tsaya. Muka sassauko kowa a wahale, wasu tsofaffi daga cikinmu sai taimaka musu muka yi suka fito tsabar jigata duk sunyi fitsari a jiki. Hajiya Mangala ce ta fito daga cikin motar ta ta nufomu.
"Yalla muje ciki, kun sha hanya, a yi wanka a karya sai kowacce ta kwanta ta huta kuma" A baya muka bita zuwa cikin gidannan. Ko wacce na faman tiri_tiri da kaya. Ni da Uwani ne kaWai bamu da wasu wadatattun kaya, a jaka Waya ma muka haWe kayan. A bene na shida muka tsaya. Mu dai duk inda Hajiya Mangala ta Waga ?afarta anan muke sa tamu ?afar. Wasu Wakuna ne a jejjere reras a wani dogon falo, ko wacce ?ofa da number a jiki. ?aki na ashirin daga nan ta soma.
"Mutum goma goma zaku shisshiga, daga wannan Wakin zuwa har inda zai isheku. Amman wannan me lamba ashirin Win mutum biyu ake bukata. Ke da ke ku shiga nan tunda kune a tsaye a wajen." Ta nuna ni ni da Uwani muna tsaye ri?e gam da hannun juna.
"Amman kafinnan ko wacce ta bani fasfo Winta da wayar salula in tana dashi. Ko wanne Waki akwai land line da zaku kira ?an uwanku na Najeriya." Nan Uwani ta zaro wayarta ta mi?a, muka haWe fasfo muka bata, na sanar mata bani da waya.
Duk da haka sai da tasa wata mace ta caje kayanmu, ta caje jikinmu, hannunta har cikin wando, har ?asan mama sai da ta Waga, da gashin kai. Tana gamawa damu muka shige wannan Waki da sallamarmu. Wallahi Allah sai da gabana ya yanke ya faWi. Siririn gaske ne Wakin, iyakar tsayin katifa, babu masaka tsinke. Ga mata nan su takwas a kwance ko wacce a karamar katifa irinta ?an makaranta. Ragowar katifu biyun kuma jakunkuna ne akai a jibge. Daga bakin ?ofarnan da yake da Wan sararin da muke tsaye, babu inda zamu Waga ?afarmu mu ajjiyeta sai dai a katifar mutane.
"Uwani na shiga uku, kinga wani Waki kamar kwanciyar kabari. Kafin uwani tayi magana aka buWe Wakin. Wannan matar data caje mu ce.
"Dama nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
Ke ?ar Was, ?ar Was kina jina fa" Wacce aka kira da ?ar Was ta tashi zaune tana mi?a. Ni dai in ba gizo idanuna yake yi mini ba sai naga kamar namiji, akwai dai gashi a kanshi, amma ?irjinshi babu komai a shafe, duk da akwai ?un?umar macce wacce bata da nono, kuma macece, inta haifu sai kan nono ya bullo?o ta shayar da jaririn, to ina tunanin ko ?ar ?as ?un?umace.
"Oh ma'aikin Allah na Madina ni ?ar ?as. Yanzu Taraliya duk illahirin jama'ar dake Wakinnan saini kika ga damar tasa, sabida ri?a??em iskanci? To gani gani" Magana take yi da lan?wasa, gata da yanga" Wacce ta kira da Taraliya tace.
"Ba?i mu ka samu, kisa waWancan matan su kwashe kayansu a kafinsu, zasu kwanta su huta" ?ar ?as tai mana kallon uku saura kwata tace.
"Bayin Allah maraba da zuwa. Ke waccan tsalllako ga katifa can. Kiyi watsin ruwan tsarki da kayan da kika gani a katifar. Ke kuma ga bayan gidaa bayanki, faWa ki shilla wanka, inba haka ba zafi ne zai kasheku" Dariya Taraliya ta saka tace.
"Baki da dama yar ?as" Itama dariyar tayi tace.
"To ai gani suke daWi muke ji in mun baro gida Najeriya. Tunda sun shigo sai du a haWu aci wuyar tare ai. Duk wacce ta kwace ta tafi Najeriya ta ba da labari" Take naji wani zum_zum. Tsoro ya kuma shigata. Ina tsaye Uwani ta shiga tsallake matan dake kwance. Aiko ta faWi akan wata mace tim, ga uwani ba kaWan ba. Matarnan ta saka ihu da kururuwa.
"Haba baiwar Allah wannan ai iskanci ne, ji yanda kika faWo mun so kike ki karyani?" Cike da fitsara take maganar gata yarinya ?arama.
Kiyi ha?uri baiwar Allah " Na faWa ina daga tsaye. Ta bani amsa da cewa.
"Babu komai. Sannunku da zuwa ba?i" Da ?yar Uwani ta yin?ura da rarrafe ta isa waWannan katifun biyu ta ajjiye jakar kayanmu ta zauna. ?ar ?as ta dubeni tace.
"Wannan tsaiwar ta babu gaira babu dalili dame yayi kama. Kin zo kin tsaya mun a ka, sai in tayar miki da aljanu Allah. " A tsorace na shige ?ofar dake kusa dani. Wani bayan gidane tsukukun gaske, komai dai tsab, ga ruwa a fanfo ga bokiti. TuSewa nayi na shesshi?ama jikina ruwan sanyi, dan a ji?e kayana suke da sufa sharkab. Jiri da ciwon kai na yinwa duk yabi ya addabeni. Alwala na Wauro na fito kayan dana cire su na mayar na saka hijabina na fito. ?ar ?as tana zaune tana kallon ?aramin mudubi na hannu.
Uwani tsallako kije kiyo wankan" Uwani da tayi jigum tace.
"FaWuwa zanyi matsawar ban saka abinci a cikina ba. Bani da nutsuwar wanka, ki ?yaleni kawai" Kai na girgiza dan nima yinwar shirin kayar dani take yi. Kafin ince wani Abun sai ga Taraliya ta buWe ?ofa ta mi?o mun gurasa guda huWu a hannu, da wani romon miya. Nasa hannu na karSa ina jujjuya abincin.
"Ku biyu ke da abokiyar tafiyarki. Ku yi da jiki maza, zaku fita yanzu da Hajiya Babba" Dan?arewa nayi a tsaye mamaki na neman ruguza nutsuwata. Da ?yar naja ?afata na tsalllaka na samu uwani. Loma shida gurasarnan tayi mun. Jima nayi kamar yinwar na sake tsokanowa wallahi gashi ko ruwa ba'a bamu ba. Sai ?ar ?as muka ro?a ta bamu gora Waya ?arama.
Uwani daure ki je ki watso ruwa, ana binmu sallah fa, kuma kinga ance zamu fita." Uwani dai bata ce komai ba ta tsallake matan dake ta bacci hankali wance.
?ar ?as dan Allah inane gabas, sannan a ina zanyi Sallah?" A yangance ?ar ?as ta ce.
"Ga gabas kin ganta. Batun inda zaki yi sallah kuma katifarki zaki jingine a bango kiyi sallah. In baki da dadduma sai ki shimfiWa Wankwalinki"
Harna rama sallolin da ake bina hawaye bai dena zuba a idanuna ba, zuchiyata ta karaya ina hango mana wahala da wula?anci a gabanmu. Uwani itama katifar ta gingine ta soma rama sallolinta. Bata kai ga gamawa ba Taraliya ta le?o kiranmu.
Uwani bata idar da sallah ba Taraliya"
"Tayi sauri ta sallame, dan Hajiya Babba ba'a Sata mata lokaci. In ranta ya Saci baku ba cin abincin rana a cikin gidannan" Uwani tayi Sallama, ta dubi Taraliya tace.
"Akwai sallar isha a kaina ban rama ba fa" ?ar ?as tace.
"Shawara ki tashi kuje, in kun dawo kya rama. Ba a yin musu da duk umarni. Ke wata rana ma kina ganin lokacin Allah zai shiga ya fice baki yita ba. Wata rana ma sai dai ki rama sallolin cikin dare a kulle a Wakin da aka baki a matsayinki na ?ar aiki." Jikinmu na rawa cike da tsoro da tsinkewar zuchiya muka fice a Wakin, kayanmu da jika. Haka aka turbutsamu a mota, wasu akan cinyar wasu. Duk wanda na kalla sai inga tana share hawaye, imma da mayafinta, imma da gefen zaninta. Zukata sun shiga damuwa da ruWu.
Wani gida aka kaimu, akaita mana aune, aune, bamu muka gama ba sai yamma lis. Basu bamu abinci ba, an dai raba mana ruwa munsha. ?akinmu muka tura muka shiga. Babu kowa a Wakin, katifun dukka suna jingine a bango. Dur?ushewa nayi ?asa na sau kuka mai tsuma zuchiya da gangar jiki. Uwani na jan majina tasa hannu bibbiyu ta Wago ni.
"Iyabo tun a itofiya jikina ya mutu. Amman sai ?ara sama mana ?arfin guiwa nake yi. Hankalina bai kai ?ololuwar tashi ba sai da muka shigo Wakinnan mai kama da kabari. Muna cikin tsaka mai wuya a ?asar da ba uwa ba uba, ba dangi." Kukane yaci ?arfinta.
Uwani mu dokara ga Allah. Allah ya ga xuchiyarmu mu neman kuWi muka zo yi. Amman na fahimci kamar bayi haka aka Wauke mu. Shawarar da zan baki, mu kai kukanmu ga Allah kawai. Da zamu samu hanyar komawa gida Najeriya ma da mun koma" Taraliya ce ta turo ?ofa, hannunta ri?e da gurasa kamar dai irin wadda aka saukemu da'ita.
"To Wallahi kar ku sake ku sake ambaton Najeriya ma. In kuka kuskura wannan kalmar ta shiga kunne abokan zamanku, zasu isarma da Hajiya Babba. Ba zaku ji da daWi ba. Sannan ku dena damun kan ku, ku da za'a tura gidan aiki. A can Waki sukutum za'a baku ku kaWai a ciki. Kuma sai abinda kuke son ci zaku ci. Wannan zaman na Wan lokaci ne. Ku dai Allah ya taimakeku ku samu shigewa da wuri. Dan naji Hajiya Babba na maganar gobe za'a soma raba ?an aiki. Ku zauna kuci abincinku." Godiya Uwani tayi mata, har zata fita uwani tace.
"Wai irin abincinnan kullum ake ci ne? Sannan wannan yayi mana kaWan mu biyu" Dariya tayi bata ce uffan ba ta fice ta barmu a tsaye jigum. Jiki a saSule muka rama sallolin da ake binmu. Muka lasa wannan abinci dan sai dai a kirashi da lasawa kawai. Muna zaune kowa dai da tunanin daya addabi zuchiyarshi. Yaya Hamma ne ya faWo mun, dole na Wan murmusa harma naji kwaranyar wani ruwa mai sanyi a zuchiyata.
"Uwani ya kamata mu tambayi land line Win da akace akwai a ko wanne Wakin ai. Ko dan ki samu ki kira mijinki ki sanar mishi isowarmu ko? Nima inason in kira Burodami in sanar musu da saukarmu"
"Hmmm Iyabo mu nutsa mu gane kan gidan tukunna, kinganni yanzu haka yinwa kamar zata kasheni wallahi, gashi jikina ko ina ciwo yake yi mun kwanciya zanyi ko zan iya runtsawa a wannan halin da muke" Katifarta ta yar, ta Waura jakar kayanmu a katifarta, dan babu waje, kowa da kayanshi yake matashin kai. Ni dai ina zaune in tuno Dada, in Tuno Gwadabe, in tuno ?a?ana, in tuno Yaya Hamma da kuma Daso data haWa zuchiyata da fargaba. A wajen a zaune bacci ya kwasheni ban sani ba kasancewar jikinmu a nune yake sosai, ga yinwa sai ta galabaitar dani. Allah cikin ikonshi sai da Asuba na farka, a ?asa na kwana abina. Matan Wakin namu wasu na kwance sunata baccinsu, yayinda wasu kuma suke Sallah, cikin masu Sallah harda ?ar ?as, abunda ya bani mamaki shine banga ?ar ?as da mayafi ko hijabin Sallah ba, banga kuma wannan yala_yalan gashin dana gani a kanta jiya ba, sai suma irin ta maza.
Da ?an daudu muka kwana muka tashi ni Iyabo?" Na furta a zuchiyata ina mamaki, raSewa nayi ta bayanshi na wuce zuwa toilet na Wauro alwala. Ni dai har na idar da sallah ban dena mamakin ?ar ?as ba. Sai hirarta take yi da mata ana tafawa, gata da barkwanci sosai. Ni dai naga matan Wakin daga wannan mu ganta ta shigo da tea da biredinta, sai muga masu kaza gashasshiya, da masu wata doguwar shinkafa wacce ni tunda uwata ta haifeni banga shinkafa da kyau da tsarin wannan shinkafa ba, gashi taji naman kaza, ?ila itace shinkafa kaza da muke jin labari.
"Bayin Allah ni ban gane ba tambaya ce dani dan Allah" Cewar Uwani data tashi tsaye. ?ar ?as ta mike ?ugu a hannu yace.
"Na taSoki da alheri wai kishiya ta taSa kishiya da bakin wuta. FaWi tambayarki in rabtaSo miki amsa, dan dana Wumama cikina da kaza da laban kwanciya zanyi sai azahar kuma" Uwani tace.
"Mu tunda muka zo wata bushasshiyar gurasace ake bamu, da wani romo da bamu san na meye ba. Bugu da ?ari ma ba isarmu yake yi ba. To sai kuma naga ku ko wacce da abinda ta saka a gaba tana ci, muna son ?arin bayani." Ni kaina da Uwani bata yi musu wannan tambayarba, da ni zanyi musu. Yinwa tana addabarmu ainun, har ?irjina ya soma nauyi. ?ar ?as ya doki cinyarshi yayi juyi da ihu kafin yace.
"Wannan gurasa da romo duk muma mun cita kafin mu yage rigar bauta, mu sa ta ?anci. Duk wannan kayan ci na albarka da kike ji da gani, ko wacce da guminta na halak ta siya. In baki da kuWi cin gurasa dole, batun ?oshi kuwa kima fita zancan wannan. Kuma anan ba mai taimako wani, ko wacce ?asarta ta baro ta fito biWar kuWin halak" ?ayar matar mai Suna Madina ta dubemu ta Waura mana da cewa.
"Idan kuka ?ara ha?uri da sannu komai zai wuce muku. Wuyarta ku soma aiki, kuWi kam sai dai ku tura gida ma, abinci sai kun ture. Kunga irin ba?ar azabar ni dana sha kafin in samu gidan aiki? Hmm abun yana da munin da ina faWa muku zai karya muku zuchiya. Ku dai kuyi ta yin adda'a shine kawai" Taraliya ce ta mi?o mana wannan gurasa ta masifa. Sai dai yau matan Wakinmu sun taimaka mana anyi mana karo_karo na abinci shine muka samu muka ji dama_dama. A ta?aice dai munfi kwana goma muna zaman jiran a kaimu gidan aiki. Anata Wauki WaWWaya. Uwani da ?yar ta samu lambar hajiyarsu ta shiga ta sanar da'ita isowarmu, sai ranar hankulansu suka kwanta da suka ji muna cikin ?oshin lafiya,. A ranar aka tafi da Uwani gidan aiki, ranar nayi kuka kamar raina zai fita. Itama tana wannan kukan aka fita da'ita. Ni kaWai na wuni ?walam a Waki, sai da nayi la'asar ne na shiga Wakin dake jikin namu na tarad da su Hadiza suna Waki suma a zaune suna Wan taSa hira a tsakaninsu.
"Iyabo kin le?o ne, ina Uwani na ganoki ke kaWai?" Cewar Hadiza. Tare da'ita muka tawo daga Kano. Sai da na zauna kana nace.
Uwani ta tafi gidan aiki Hadiza"
"To nayi mata barka wallahi muma nan duk zaman jiran hakan muke yi. Duk da ance aikin gidan larabawa ba ?aramin aiki bane na azaba. Wasu fa wai har dukansu akeyi a gidan aikin." Idanu na zaro nace.
"Yanzu Hadiza da girmanmu sai a kamamu da duka?" Dariya ma maganata taba ?an dakin. Hadiza tace.
"Hmmm Dattijuwar da take bamu wannan labarin kinga fa katifarta" Ta nuna mun katifarta a jingine"
"Har bayanta ta nuna mana duk shatin bulala. Wannan dalilin ne yasa ta baro gidan aiki tana bu?atar a sauya mata gidan aiki. Duk matan dake cikin Wakin ku fa da yawansu matsala suka samu a gidan aiki shi yasa kika gansu, za a nema musu gidan aikine" Ni dai jikina du yayi sanyi sosai. Na dubi Hadiza nace.
In babu damuwa zan dawo Wakinku Hadiza, can Wakin namu basa zama, in suka fita sai dare, wasu ma sai su kwana biyu basu dawo ba"
"Jeki maza ki Wakko kayanki kinji, ai sai abun yayi miki yawa."
A Wakin su Hadiza kwanana biyar. Naji labarai masu tayar da hankali, da irin matsalolin da ba?a?enmu suke fuskanta a gidajen aiki iri daban_daban kuma masu haWarin gaske. Nifa tun daga Itofiya na soma Wan daka ce ban baro ?asara Najeriya ba. A ranar dana cika kwana goma a Wakin su Hadiza nima akace in haWo kayana waWanda zasu Waukeni aiki zasu tafi dani. Hawaye na soma zubarwa da girmana, na suri ledar kayana, duban su Hadiza nayi da muka sha?u a kwanaki gomannan nace.
Allah ya sake sada fuskokinmu da Alkhairi, ni na tafi, ku taya ni da adda'a nima zan dinga yi muku" Ina kaiwa nan Taraliya ta figi hannuna zuwa wajen mota. Wata balarabiya da mijinta na gani a gaban mota, ni kuma Taraliya ta dannani a gidan baya. Motarnan na soma tafiya na runtse idanuna hawaye sai kwaranya yake yi a idanuna. Tafiya muka yi mai yawan gaske zuwa wani garin kuma. A cikin katafen wani ?erarren gida motar ta tsaya. Ni dai ganin sun fito, nima saina Salle murfin motar na fito. Balarabiyar ta dubeni tace dani.
"Yalla" Zungui_zungui dai haka naita binta a baya. Muka shiga wani ?atoton falon da ko a mafarki ban taSa ganin irinshi ba. Garjejen falone jere da wasu jajayen kujeru marasa ?afa, duk da na kasa tantance kujerune ko fululluka manya aka jejjera oho. Duk girman falonnan kafet ne mamala a ciki, ga taushi, falon sanyi da ?amshi yake fitarwa, ga matattakalar hawa bene daga can gefe, ga Wakuna kusan goma a cikin falon. Ni dai ina biye da'ita zuwa wani ?aramin Waki dage jikin matattakalar hawa bene daga ?ar?ashi haka. ?wan?wasa ?ofar Wakin tayi, da sauri wata dattijuwa ba?ar fata ta buWe, sai na ganta da atampa a jikinta, kuma tayi mun kama da Bahaushiya. Da larabci wannan balarabiyar tayi mata magana tana nunani halamar dai bayani take yi mata a kaina. Tana gamawa ta haura sama abinta. Wannan Dattijuwar tace.."Sannu baiwar Allah, da ganinki ?ar ?asata Najeriya ce ko?" Tana faWar haka saina fashe da kuka. Hannu tasa ta jawo ni cikin ?aramin Wakin. Mai Wauke da gado mai hawa biyu, da katifa a jingine a gefe, sai tulin kayan sawa. A bakin gado ta zaunar dani tace.
"Ki dena kuka yarinya. In dai arziki kika fito nema da guminki kin samu. Dan ana biya sosai a gidannan. Amman fa akwai aiki masu yawa sai kinji kamar zaki mutu. Bayana, ?irjina duk ciwo suke yi mun. Aikin ya gagareni shine naima Hajiyar gidan magana inason zan koma Najeriya a samo wacce zata zama madadina. To gashi Allah ya kawo ki. Zan zauna dake na kwana bakwai in kula dake har sai kin gaggane aikin sai in tafi. Akwai wata yarinya itama aiki take yi da Wayan shashin na gidannan. Amman ita bata jin Hausa daga wata ?asar take. Yanzu bari in baki tea da biredi ki ci, sai in zaga dake ki kama aikin ki. Sunana Takarofi"
Kukana na share, nace da ita.
Sunana Iyabo"
"Ayya beyerabiya ce ke ashe? Amman kinji Hausa sosai. Ina zuwa to" Fita tayi tana Wingisawa, nabi bayanta cike da tausayawa sosai da ido. Bata fi minti goma ba sai gata ni?i_ni?i da kayan karyawa. Lafiyayyen biredi da kakkauran tea har da bota da wainar ?wai. Cin haWama nayi ma biredinnan. Takarofi sai kallona take yi. Bayan na kammala tsab sai tace in biyota muje. Nan ta zaga dani lungu da sa?o na gidan, da duk wani aiki da zan dinga gabatarwa. Time table na abinci ta nuna mun gasunan a rubuce reras da turanci. Ko wacce rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login