Showing 192001 words to 195000 words out of 270738 words

Chapter 65 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mun"
A'a Dada ni ban baki ba sai kece zaki ban in karSa" Kallon tausayi tai mun tace.
"Babu komai Jabu karSi"
Godiya nayi mata. Har munje ?ofar gida tace.
"Jabu. Amaduyal ya sanar dake halin da ake ciki kuwa akan kiwonki kuwa?" Gabana ya faWi, a raunace nace.
A'a Dada wani abune"
"Kuje in kunje kafin ki wuce gida kizo ina nemanki zamu yi wata magana"
To
Kawai nace mata muka kama hanyar asibiti. Mun sha gwajab_gwalab haka dai muka isa. Layin mata masu awo har bakin babban asibitin Girei mai suna. Girei teaching hospital.
A lokacin kyauta ake raba kati komai ma daya shafi awo kyauta akeyi. Domin a hakanma ba wani zuwa asibitin daga cikin ?auyuka akeyi ba. Sun gwammaci mace taita nakudarta har ta mutu ma akan su kawota asibiti. Ni dai ina zaune akan layi na yi tagumi ina tunanin rayuwa da irin halin da nake ciki. Sau?ina Waya babu abinda har yanzu ya canja daga so da kulawar da Yaya Hamma yake mun. Saima abinda yaci gaba, kullum a cikin rarrashina da ban baki yake. Ga rai daya Wauka yasa akan wannan cikin nawa. ?an murmushi nayi na shafi cikin nawa daya fito sosai kamar wanda ya kai wata shida. Yanayin yana mun kama da yanayin cikinsu Taye da Kahinde.
Sai wajen azahar aka kira sunana na bi matar data kira sunana a baya, ta bani roba naje nayo fitsari na dawo mata dashi.
"Malama Jabu ai babu ciki a tattare dake. A text Win da mu ka yi miki na fitsari bai nuna mana kina da juna biyu ba. Amman bari mu miki text Win jini."
Take jikina ya soma rawa zufa na keto mun. Ga motsin Wa a cikina amman ace bani da ciki, ga ciki ?ato?
Allah cikin ikonshi wallahi anyi text Win jini maganar Waya ce ciki dai babu shi. Sai janaral asibiti Adamawa suka turani jibi inje za'aimun sikainin. Ta yi rubutu a wata takadda ta bani.
Da ?yar na tashi na fito, cike nake da mamaki, fargaba da tsoro duka dai. Amman in naji motsin rai a cikina sai inga kamar dai basu iya aikinsu bane.
Anan Girai na sai kayan miya, da kuka, da maggi. Muka hau akori kura zuwa Jabbi lamba. Gidan Dada muka shiga da sallama
Amaduyal ma yana ciki da kuWi a hannunshi yana ?irgawa ga wasu ma a hannun Dada.
"Adda kun dawo" Cewar Amaduyal. Wani yawo mai kauri na hadiya, da ?yar nace.
Mun dawo Amaduyal yau baka je kiwon ba?"
Shiru yayi baice komai ba.
Hassana Webo mun ruwa in sha ?ishi nake ji"
Hassana ta kawo mun ruwa mai sanyi cikin kofi na shanye, Dada sai kallona take a mugun firgice nake.
"Lafiya Jabu akwai wata matsalar ne?"
A'a Dada gajiyace da rashin kyan hanya ya galabaitar dani" Yanayinta bai nuna ta aminta da abinda nace ba,ta dai mun sannu, kafin tace.
"Jabu kinga wannan kuWaWe dubu Wari biyu da sittin gasu. KuWin shanunki da awakanki ne. Kinga ga kaji can a bawo guda huWu nasa an yanka su dan ko ba'a yanka ba mutuwa zasu yi. Ungo wannan kuWin ri?e"
Hannu nasa na amshi kuWin ina murmushi kawai.
"Jabu kisan kadarar da zaki siya ki ajjiye kar ki bari kuWinnan ya lalace su kaWai suka rage miki. Sannan inaso ki zama mace mai juriya da jajircewa, ki yarda Allah shi kaWai yake iya Waurama bawa kaddara me kyau da marar kyau. Wata rana zaki huta. Kamar yadda kika sha wahala ni kika fitar dani a matsala. Kema in sha Allah zaki haifi waWanda zasu fitar dake a matsala. Duk runtsi kar ki rabu da Hamma. Hamma yana sonki kuma zai iya zame miki garkuwa ko bayan raina. Kiyi ha?uri kar ki zargi kishiyarki hakan kar yasa ko bayan raina ki aikata mata wani abun a matsayin ramuwar gayya. Da sannu zata gurbe duk abinda ta shuka. Akan Hamma duk take wannan burinta ta fitar dake a Wakinki. Ke kuma ki nuna mata kina ma Hamma son da sai dai mutuwa ta rabaku"
Hawayen dake zuba a idona na share.
Babu komai Dada, na kuma gode da wannan shawarar. Amman inaso zan ba Amaduyal ko da jari ne ya nemi wata sana'ar a cikin wannan kuWin."
"A.a ri?e kuWinki ki nemi kadara ki siya. Zai yi noma kuma ya samu aikin tu?a babur zai dinga jigilar shigar da mutane ?auyuka"
KuWin na raba Uku na mi?a ma Dada fur ta?i karSa, haka dole na ha?ura na saka kuWin a jakata. Na zari wasu daga ciki na ba Hassana tamun cefanan tumaturi ta auno mun shinkafar Hausa da Maggi. Suma su Dada nai musu cefane nace su yi girki na basu kaji biyu. Hassana ta rakani har gida da kayan cefanan.
Ina tafe kamar mahaukaciya har gidan namu na wuce tafiya fa kawai nake yi, sai da Hassana tace.
"Adda kin wuce gidan fa" Kana na juyo naga zahiri na wuce gidan. Da Sallama a bakina na shiga gidan. Yafendo tana tsakar gida, ita da Yafendo A'i.
"Jabu kin dawo" Cewar Yafendo A'i. Wajensu na nufa na zube a gabansu muka gaisa.
"Ai Wazu mun shiga wajen Adda Daso ma take sanar mana siyar da dabbobinki da akayi basu da lafiya. Allah yasa da abinda suka tare. Kinsan ba kowa kiwo ya karSaba shi yasa. Naji kuma sana'ar taki ma jarin duk ya karye miki shima. Jabu kiyi ha?uri jarabawace. Allah daya baki shi zai kuma baki wani, ki Wau dangana."
Suka haWu sukaita ?arfafani sai na ji sanyi a raina. A Wakin Yafendo ma nayi Sallah na kwanta a ?asa sanyin na mun daWi.
"Ga madarar shanu Wazu na tatso miki" Yafendo ta mi?o mun na karba ina sha suna hirarsu da fullanci. Allah yayi mun ?wa?walwar saurin jin yare gaskiya. A halin yanzu abu WaWWayane suke faWa wanda bana ganewa. Mayarwar ma inayi amman ba sosai ba dai. Sai da nayi la'asar na shiga Wakina na gyara tas na fito. Kara naje nayo na hura wuta na wanke kajinnan tas na Waura a wuta. Na Wakko dutsen ni?a na gwafe naita ni?a tumaurinnan dasu attaruhu nafi awa Waya ina abu Waya. Ni kaWaice a gidan Yafendo ta tafi raka Yafendo A'i zuwa gidan Baffa Musa, daga can zasu je gidan Yafendona. Ni dai inata aiki jikina sukuku. Masu tallar nono an dawo sun sameni na gama suyar kaza na zuba a jar miya ina soya miyar. Ga shinkafa ina zaune inata tsinta da akwai ?asa sosai.
"Kun dawo sannunku" Safiya da BaWWo ne dama kaWai suke amsa sannu da zuwa in nayi musu. Ni dai inata aikina bayana da wuyana duk yabi ya ri?e gam. Sai magriba na wanke shinkafar na zuba. Naje nayo wanka nayi Sallah. Ina idar da Sallah na fito na raba abinci. ?aki_Waki saida na zuba ma kowa dake shinkafa abun Waukanice barinma mai miya da nama.
Ina Waki shiru ina sauraren motsin da cikina yake yi, idanuna a lumshe ina mamakin yama za'ace anyi awo bani da ciki. To in hakanne meye a cikina yake motsi?
Shigowar Yaya Hamma ne yasa na buWe idona na yi saurin karSar ledar hannunshi.
Kayan miyane a ciki da maggi.
Sannu da zuwa Yaya Hamma ya aikin. Wanka zaka soma ko cin abinci?"
Zama yayi a ?asa ya jingina da kujera yace.
"Yaya j??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iki_jikin. Kin ga likita da kuka je asibitin?" Sai gabana ya faWi. Amman saina jure nace.
Naga likita yaronka yana cikin ?oshin lafiya" murmushi yayi yace.
"Allahu ya rabaku lafiya. Allah ya baki lafiya. Bari in soma wankan inzo in baki labari"
Ruwan wankan naje na juyo mishi na dawo.
Saina ga jini digo uku a ?ofar Wakina. Gabana ya yanke ya faWi wata fitinar ce kuma ake so in taka kenan?
Cikin gida na shiga na Wakko tsintsiyar sharar tsakar gida da ragowar ruwan BaWWo dana gani a bokiti nazo da bismillah a bakina na wanke jinin tas, nayi adda'a na shige Waki ina mamaki.
Ina zuba mana abinci Yaya Hamma ya shigo ganin shinkafa da miya harda kaji yasa ya zauna yana kallona.
"A ina kika samu kuWi haka Jabu?" Murmushi nayi mishi kawai nace.
Kai dai kaci zan maka bayani "
"A'a aimun bayanin tukunna dai. Kaddai zuwa kika yi kika ari kuWi Jabu. Nasanki dai akwai Soye sirri bana jinki"
Da dai naga ya fara zargi saina sanar mishi abinda ake ciki. Na Waura da cewa.
KuWin yana jakata na adanasu. Amman dan Allah inaso sati mai zuwa ka yarje mun in je Kano. Inaso zan kaima su Iyaa Debisi ziyara, da Uwani" Shiru yayi kawai yana kallona irin kallon tausayi. Murmushi kawai nake yi dan murmushin yana kwarara mun zuchiyata.
"Allah yayi miki albarka. In sha Allah Jabu zan ri?eki da amana ni dai nayi miki al?awarin ba zaki yi kuka dani ba. Batun zuwa Kano bazan hanaki ba. In lokacin yayi ki shirya kije. Amman meye tunaninki akan kuWin me kike ganin zaki yi wanda kuWin bazai rushe ba?"
To ka soma cin abincin tukunna muna hirar."
Yana cin abinci yana santi, ina mishi dariya. In ina tare dashi yaye mun dukkannun damuwata yake yi. In ina farin ciki mancewa nake yi ina da damuww ma a rayuwa.
Gida nake so in siya ko me Waki biyu ne a zuba mun haya. Kasan ina da gidan dana siya a kusa da gidan Uwani, da ?an haya ma a ciki. To ko ta kusa dasu na kuma samu sai in siya, ko kuma in sai fili"
Saida ya cika tsokar nama a bakinshi yace.
"Allah sarki bansan kina da gida a Kano ba yaushe kika siya?"
Bayan aurenmu. Lokacin dana shiga kano
A wannan lokacin Uwani taimun tayin wajen saina siya"
Kai ya girgiza yace.
"To ki sake siyan gidan ko filin kadarace babba musamman dake a birni ne, ba kamar ?auye ba. Ga kayan miya na siyo miki. Na fita yau da ?afar dama. Na samu gadi a gidan wani Alhaji a Girei. Daga takwas na safe zuwa shidan yamma zan dinga tafiya. Akwai wanda yake yin na kwana. Duk da nima yace inta kama zan dinga kwanan. Nera dubu huWu a wata"
Nan na shiga murna tare da yi mishi adda'a. Da ?yar naci naman kazannan ya zauna a cikina.
Da safe da nayi dumame kuma sai naji inaso naci da yawa.
Da Yaya Hamma zai fita na zari dubu Hamsin na mi?a mishi a hannunshi. Ya kalli kuWin ya dubeni yace.
"Me za'ayi miki dashi?"
Nakane na baka kayi noma dashi. Dan girman Allah kar kace mun ba zaka karSa ba. Dan girman Allah Yaya Hamma"
Murmushi yayi yace.
"Nagode Allah yayi miki albarka"
Ameen ko kai fa. Gobe ance in koma asibiti akwai gwaji da zasu sake yi mun. Nasan inka koma Wakin uwargidanka bazan ganka ta daWi ba." Dariya yayi tare da girgiza kanshi yace.
"Allah ya nuna mana goben lafiya. Sai mu fita tare ai, ni in wuce aiki ke ki wuce asibiti."
Hakan kuwa akayi Bakwai ma mun fice a gidan, har bakin asibiti ya rakani, ya wuce wajen aikinshi. Da naga ya ?ule na fito nayo babban titi na hau mota zuwa gari.
Allahu Akbar a babban asibitin ma magana Waya ce anyi duk gwaje_gwaje, da hoto, da sikainin amman basu ga komai ba. A zahiri ga ciki sun shaida kuma yana motsi, amman a awo babu ciki babu dalilinshi.
Tunda uwata tai sanadin zuwana duniya ban taSa ji ko ganin abun almara irin wannan ba.
Halin dana shiga ya wuce gaban misalin da za'a musalta har ?wa?walwar mai karatu ta Wauka. Ku kwatanta da kanku, in kece wanne irin ruWu zaki shiga? To irinshi na shiga nima.
Gaga_gaga na dawo gida. Na ja bakina nayi gum babu wanda yasan halin da nake ciki. Ai saina dena bacci, nice sallar dare, nice sadaka. Ko aikin girki nake bana rabo da ambaton Allah. Salatin annabi kuwa sai inyi a rana fin dubu biyu.
Da sati ya cika na shirya kayana a akwati na fito naima matan gida sallamar zanje ganin gida. Da ?ar tsarabata a buhu harda nono a jarka, da man shanu duka dai wata tsaraba data dace. Yaya Hamma bai bar tasha ba har saida motarmu ta bar tashar. Ko dana juya baya ina hangoshi ta tangaran Win motar yana ma motarmu odabo.
Wasu siraran hawayene suka sulalo a kumatuna, a hankali na lumshe idanuna, inata tunano abubbuwan da sukaita faruwa, lallai in haka kishiya take irin hama kishiya bala'ice, masifa ce. Hama ta wargaza mun dukkannin farin cikina, ta hanani sakewa da masoyina sam. Bata ?aunar a zauna lafiya, in bata zageni, ko taci mun zarafi ba bata samun kwanciyar hankali. Amman ina tausayin ranar da zata soma girbe abinda ta shuka, ranar da zata zama abun tausayi. Dan ?arshen mai biye_biyen bokaye ba ?arshe bane me kyau. Macen data mutu akan wannan Gwadaben bata ba shiga aljanna, ba faWata bace faWar Allah subhanahu wata'ala ne. ( Jan kunne. Yake ?ar uwata ki sani bin bokaye shirkace. Allah baya gafartama wanda ya mutu yana shirka, kuma babu shi babu jin ?amshin aljanna. Shin akan Wa namiji kike son kai kanki ga halaka, kina mace kina zaluntar ?ar uwarki mace? Mace ta haukata kishiya, ta kashe kishiya, ta kashe yaran kishiya, ko ta kassara rayuwarsu. Sai kace munzo duniyane domun mu tabbata. Da muna tuna Allah, da azabobubshi, da muna tuna juma'ar da bata da ?arshe, da muna tuna wuta, mu tuna aljanna wallahil azeem wasu abun ba zamu yi ba. Ke kina nan kina tabkama kishiya asiri, wata ?ila rayuwarki ma ba mai tsayi bace kije ki faWi ki mutu Shikenan kin gama yawo. A duniya ba riba, a lahira ba riba, kizo a banza ki koma a wofi.
Allah ya ?ara tsare imaninmu ameen)
Bayan la'asar muka shiga kano Shigata kano ya famamun ciwukan da har abada ba zasu warke a rayuwata ba.
Allah sarki Gwadabe alkhairin Allah ya kai muku tare da yarana a duk inda kuke. Allah ya wadataka ya horema samun macen data kere Iyabo ta kuma"
Ni dai kai tsaye gidan Tabalbalin na wuce, nafiso saina gama da harkar asibiti kafin inje gida, kwana biyu rak zanyi a gida in koma. A shago na tadda Uwani tanata cinikayya da mata, ta buWe dilar kayan jirarirai. Ga Hafizu a cikin shagon yanata rataye wasu kayayyaki a hanga. Shagon an sake gyarashi yayi kyau har doguwar kujera aka saka an sake yawan kantocin, an yi sabon fenti. AcaSana na ajjiyeni a bakin shagon Hafizu ya iso ya sauke mun buhun kayana, da fantimoti na.
"Alaja kece a tafe, maraba" Cewar Hafizu. Murmushi na kakaro nace.
Wallahi nice Hafizu nace mutuniyar kwana biyu shiru ni bari in leko. An wuni lafiya ya Amarya da yarinyarta ko yarone?" Baki ya washe.
"Duk kowa yana lafiya, ai tama haihu jiya Wallahi an samu Uwani" Baki na kuma washewa. Saida na sallami mai acaSa nace.
Ah ka kyauta. Uwani muka samu, wannan yarinya kace mafaWaciyace"
Tare muka shiga shagon na Uwani, ta ko haWe rai tamau. Ni nasan bazai wuce akan sunanta da akasa bane, ga cikinta ya fito sosai itama.
"Iyabo maraba. Jiya fa nayi mafarkinki kuma wallahi marar daWi harma nayi sadakar ?osai mai zafi. Ga waje ki zauna a karSo miki lemo" Waje ta nuna mun na zauna. Ta ba Hafizu kuWi ya siyo mun lemo da sakwara.
Hmmm Uwani damuwoyi sun yi mun yawa a kannan nawa. Ina tsoron kar in faWi in mutu mutuwar farar Waya. A baya matsalata uwar mijice, sai facaloli. A yanzu matsalata Hama ce, haWa miji da mace mai asiri bala,ine. Ni wallahi har gara in haWa miji da makira. Ita duka biyu ta haWa Uwani. Jibi ga ciki a jikina ga motsi, kuma yana girma. Amman gwajin duniya Uwani likitoci basu ga wannan ciki ba wai babu komai fa a cikin. Kaina ya Waure, bacci wannan bana iyawa. Banda bala'e_ bala'en daketa sauka akan dukiyata. To ta faru ma ta ?are tunda yanzu komai nawa ya ?are tas"
Hawaye na sharce bayan na ?arashe maganata. Uwani kuwa kasa?e tayi tana kallona kawai.
"Iyabo na shiga uku. Wannan tashin hankali har ina. Babu ciki likitoci basu ga cikin ba kikace. To mijin naki wanne mataki ya Wauka akan hakan? Kinga jikina rawa yake yi Iyabo"
Hamma baisan abinda ake ciki ba sam. Na Soye mishi Uwani kar kiso ganin yadda ya Wauki rai ya ?allafa akan wannan ciki. Shi burinshi ya haWa jini dani Uwani. Wallahi tsoro da fargabar me kaje kazo ne ya hanani ce mishi komai. Ina cikin tsaka mai wahalar fita."
Kuka na fashe dashi, nayi shi ?a?as sai naji zuchiyata ta Wan rage naunyi ni da kaina nayi shiru. Uwani bata hanani kuka ba. A ko da yaushe Uwani takance kuka shima wata hanyace ta rage nauyin zuchiya da cunkushewarta.
"Hmmmm ki kwantar da hankalinki Iyabo. Zamu zagaye asibitocin Kano. Kuma in sha Allah za'a dace. Akwai wani malami zan Waukeki muje zai taimaka miki." Dawowar Hafizu ne ya katse mana hirarmu. Lemon montin dew ya ajjiye a gabana. Da kular sakwara.
"Hajiya tunda kinyi ba?uwa zan tafi. Sannan ki daure kije ki duba me jego da takwararki"
Uwani ta dubeshi sai naga tayi dariya, ta zuge lalita ta ciro kuWi ta bashi.
"Ga albashinka nan" Yayi saurin cewa.."
"A'a ki ri?e a wajenki. A tsintamun kayan jaririya a cikin kwashe irin na Wari_Wari ko tsinke ban siya ba"
KuWin Uwani ta mayar tace.
"Gasu can ?an Wari_Warin ka Webi na iya kuWinka"
Ni dai ina jinsu, Sakwara nake ci hannu baka hannu ?warya ga ganda sutu_sutu a miyar. Sai da Hafizu ya fita nace.
Uwani ki ?yale Hafizu haka dan Allah "
"A'a fa Iyabo. Barni da Hafizu inda kika gammu. Nifa a haka nayi matu?ar ?o?ari da kai zuchiyata nesa tunda har na iya Waukarshi aiki nake biyanshi duk sati yake samun naci da iyalinshi. Banyi ?o?ari bane nifa nake ci da kaina da nawa yaran. A shago ina siya mai abincin rana. To me kike so, in goyashi in yi yawo dashi kome? Kinfa san komai duk ba akan Hafizu naje na afka bala'in da Allah ne yayi ina da tsayin rayuwa ba. A ?arshe me yayi mun?"
Anan zan dakata sai ranar monday kuma
MRS BUKHARI



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IW4UEOnp70d9ho1A7dH1Ba


Kina son yin adashen kayan Sallah daga wajen Anty Zee misa colaction?
Ga link maza ki garzaya kema ayi dake tana kawo kayayyakinta daga ?ashashe daban_daban masu inganci da rahusa.
Nima a wajenta zanyi adashen kayan Sallah na.
Ina masoyana kui maza ku shiga ayi daku
NAMA YA DAHU....


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login