Showing 6001 words to 9000 words out of 270738 words

Chapter 3 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Ba da ban Baba Magaji ba da yanzu wani labarin akeyi. Ke dai Iyabo ki ta yin ha?uri wata rana sai labari. Ko wacce mace da irin ?alubalen da take fuskanta a gidan aurenta, muna barma cikinmu sirrinne kawai. Murmushi kawai nayi ina hango lokacin da Gwadabe yake zuwa taWi ?ofar gidanmu a idanuna. Tun yana zuwa ana barinshi da dai Iyaa Debisi ta ga abun da gaske ne na riga na kamu da son Gwadabe sai aka hana shi zuwa gida wajena. Ni da Gwadabe sai dai mu haWu a wajen da nake sana'ar tuyan ?osai da kafa da daddare a bakin titin unguwarmu. Gwauron numfashi na ja kawai mu ka ci gaba da hirarmu da Sakina. Sai da na huta na yi sallar azahar. Muna yin la'asar kuwa aka aiko yaran gidan wai in zo bakin murhu za'a Waura sanwar dare. FaWan irin wuyar da nasha Sata lokacine kawai, aikin kusan nice ?arfin yinshi, sukaita zamewa suna barina. Ga tuwon gidan bikin ?auye ba tuwo bane na wasa, ni na talga tuwonnan na dinga Wiba da ?o?o ina zubawa a tukunya lamba talatin sai juyawa ruwan zafin yake yi. Bayan na gama talge sai na koma wajen su Zuwaira mu ka ci gaba da wanke kwanukan da aka Sata da rana. Wanke_wanke ne bana wasa ba. Muna tsaka da wanke_wanken Su Yaya Hambali suka zo wucewa ta wajen. Dukkansu suke tafe harda Gwadabe wanda na ga idandunanshi sun kaWa sun yi jawur. Duk da magriba ta kawo kai akwai ?arancin haske. Kallona kawai yayi ya girgiza kai suka wuce zuwa shiyyar Babala. Haka kawai sai na tsinci kaina a cikin damuwa gami da faWuwan gaba, take sai jikina ya mace murus. Cikin dauriya na iya tsaiwa muka kammala duk aikin daya kamata

Gwadabe:.


Tunda ya shiga Wakin Babala, Babala ta tare shi da ruwan faWa itace harda kukan ta ji labarin Iyabo ta shanye shi, ta mai sheshi ?an aikinta. Duk ta hanyar da yaso ya Sullo mata dan ta fahimci dalilin da yasa yake mata aiki, amman Babala ta fututtuke. Su Goggo Iyatu suma suka ara suka yafa, mai makon su rarrashi ?ar uwarsu sai ma sake zugata da su kai ta yi.
"Wallahi Kyauta wannan lefinki ne. Dan wallahi da nine Tanimu ya kwaso mun ?abila da sunan matar dazai aura. In sama da ?asannan zata haWe bazai aureta ba. Ki duba yanda ya shure soyayyar ?anwarsa Laila fa Kyauta. Da ba dan na kai zuchiyata nesa ba da zumuncinmu ai ya taSu" ( Kyauta sunan da dangi ke kiran Babala dashi kenan. Babala kuma sunan da ?a?a da jikoki ke kiranta kenan) Cewar Goggo Iyatu kenan. Goggo Jummalo tace.
"Ai yanzu ma bata Saci ba Iyatu. Har yanzu Gwadabe zai iya auren Laila. Tunda har Laila ta iya kaso aurenta domin tana son Gwadabe .Ya kamata a wannan karon ya aureta ko dan dole dan ubanshi a nuna mishi mu muka haifeshi ba shi ya haifemu ba. Wallahi a wannan karon aurenshi da Laila babu wata makawa." Da sauri Gwadabe ya Wago jin labarin mutuwar auren Laila ba ?aramin kiWimashi lamarin yayi ba. Ga wata magana da Goggo Jammalo take faWe, shi yanzu ina ya ga ta yin aure alhalin abinci ma da ?yar yake iya kaiwa gidanshi, har yanzu bai soma sana'a a matsyin ogan kanshi ba. Ta yaya ma zai auri Laila? Wannan ma maganace da bata dace ace an ma tare shi da'itaba, duba da irin halin talaucin da yake ciki, da kuma babban dalilinshi na ?in Lailan a bayan. Da ?yar Gwadabe ya yakice ya bar Wakin Babala yana yarfe zufarshi. Yana hanzarin barin shiyyar ya jiyo muryar Laila a bayanshi tana kiranshi.
"Gwadabe ji mana dan Allah " Cak ya tsaya bai juyo ba, bai da niyyar juyowar. Sai itace ta tako har inda yake, ta fuskanceshi.
"Gwadabe guduna kake yi ne?" Kallonta Gwadabe yayi, tare da girgiza kan shi.
"Tayaya zan guje ki kina gudan jinina Laila? Na ga ai mun gaisa ko, ko akwai wani abunne bayan wannan?" ?an murmushi Laila ta yi tare da cewa.
"Babu komai. Ka ji labarin mutuwar aurena, da musabbabin mutuwar tashi ko?"
"Ai kina jiyo duk bayanin da su Babala suke yi mun. Allah ya daidaita tsakaninku da mijinki. Laila in da gaske dan ni kika fito daga Wakin ki, kin tabka babban kuskuren da zaki jima kina cizon yatsan ki. Sam ni Gwadabe bani da ra'ayin ?arin aure, lafiya lau muke zaune da Iyabo, bata rage ni da komai ba, ta bani dukkan lokacinta da zuchiyarta. Haka zalika ni ma zuchiyata tana gareta. Ina mai baki ha?uri a karo na biyu." Yana dasa aya ya wuce ya barta da jin kunya.
Yana tafe yana mamakin irin ?iyayyar da su Babala suke yi ma Iyabo, duk da dai shima irin wannan tsanar akayi mishi a gidansu Iyabo. Da dama a cikin gidansu Iyabo basa ko amsa sallamarshi. Bayan sallar la'asar kuma Babala tasa akayo mata kiran kab yaran nata, dan Haula ta tsokata mata abinda ya faru a can gida Kano da safe kafin su tawo. Shine wannan wucewa da Iyabo taga sunyi. Bayan sun gurfana a gaban Babala da Goggo Iyatu, da Goggo Jammalo, da Goggo Takura. Duk waWannan ?annen Babala ne, babban wansu Baba Magaji shi yana MaraWi tare da iyalinshi. Nan Yaya Hambali ya soma yi ma Babala bayanin abinda ya faru, harda ma waWanda suka wuce.
"Babala Iyabo ta gama mallake Gwadabe, shi yake yi mata komai da kika sani. Wallahi Babala har ruwan wanka sai Gwadabe ya kai mata, haka zaki ga ta fito tana kallon su Haula WaWWaya. Duk abunda Gwadabe ya samu akanta yake ?arewa tas. Ai kin ganta sai ?iba take narkawa, shi kuma yana ?arewa kamar wanda ake lasa. Ni shi yasa nace su bar mun gidana kawai, dan ba ?aunar buWe idanu nake in ganta a cikin gidan ba Babala. Tunda har Gwadabe ya soma takamun burki, wataran sai duka. Kafin akai ga hakan gara su tashi kawai, ina da bu?atar wajen nasu dama zan zuba dabino a ciki. Babala irin taSarar da Gwadabe da matarshi suke yi a cikin gida kare fa bazaici ba. Wallahi sai ki ganshi da gajeren wando yana barbaWa mata garin Amala ita tana tu?awa sunayi suna wa?ar yarbawa. Wannan ba?in ciki da mi yayi kama" Yaya Harisu yace.
"Gaskiya ne gara ya kama mata haya a can nesa damu Babala. ?azantar da baka gani ba tsabta ce. Dan wannan yaron baya ko jin kunyar idanunmu, wallahi zaki ganshi a tsakar gida yana wanki tana mishi shanya, wataran har wa?ar yarbawa zaki ji suna rerawa abun takaicin ya iya wa?ar. Gwadabe ya rasa wacce yake so duk dangi, duk cikin ?abilunmu na Hausa fulani kyawawa, sai wannan buskutar beyerabiyar ce ta ja hankalinshi." Haka Waya bayan Waya kowa ya goyi bayan Gwadabe ya bar ma Yaya Hambali gidanshi. Shi kuwa gogan yayi ?uri yana jiran irin hukuncin da Babala zata yanke. Gyaran murya tayi tare da cewa.
"Na ji bayananku kab, kafin ku koma za ku ji hukuncin dana yanke. Zanyi shawara da ?an uwana, akan batun matarshi kuwa wannan ?abilar? Alkadarinta ya riga ya kusan karyewa. Ku tashi kuje in Allah ya kaimu gobe zaku ji hukuncin dana yanke" A sanyaye Gwadabe ya bi bayan ?an uwanshi. Zuchiyarshi cike da ?una gami da taraddadin me ka je ka zo.



Iyabo:
. Sai zuwa bayan isha na samu hutu. Duk mun baje a tsakar gida muna shan iska. Ina kwance akan tabarma nayi matashin kai da hannuna. Toye yana zaune a gabana. ?an uwa sai hira da shewa suke ta ta yi abun gwanin ban ?awa, ni kuwa mujiya na kasance a cikinsu, komai a tsorace nake yinshi, bana son in Sata ma dai_dai da yaron gidan na goye rai. Ina gani Wazu yarinyar Asiya matar Lawal tana dukan Toye, babu wanda ya kula. Gashi ba sa'arshi bace dan zata yi shekaru tara da doriya ma. Sai da ta gaji dan kanta ta barshi.
Ina kwance barci ya soma dibata Yaya Halima ta zo inda nake tai mun ?erere a ka.
"Mandiya hamsha?iya sai ki taso ga can kayan miya da su alayyawo zaku gyara, gobe da asuba za'a aza tukunya" Da sauri na mi?e ina faWin wash dan wani irin ?ara ?uguna yayi mun mai zafin gaske. Toye na kwantar ya riga ya soma bacci a zaune. Tunda muka zauna zaman aikinnan ba mu bar aikin ba sai wajajen sha biyun dare, sannan kowa ya kwanta. Da asussuba kuwa washe gari muka tashi da aikin tuwo, dan kafin takwas na safiya mun kammala tuwonnan tas mun malmalashi mun jera a fantekoki. Zuwa ?arfe sha Wayan rana gidan biki ya cika dan?am da jama'ar biki, sai haya_haya kawai kake ji. Daga waje ma haka ?ofar gidan take dan?am da maza ?an Waurin aure. Yaron Sakina ne yazo ya kirani.
"Umman Toye wai inji ummata kizo ki yi wanka" Allah sarki ni Iyabo. Kowa a gidan sai wanka akeyi ana kwalliya, yara da manya. Amman ni babu wanda yai mun ta yin wanka. Bin bayan yaron nayi har zuwa gidansu. A falon Sakina na samu Gwadabe da Bara'u suna zaune suna cin tuwon biki. ?ur ya ?ura mun idanu, take na ji hawaye na shirin zubo mun, har numfashina na karkatsewa. Fitowar Sakina daga uwar Wakine ya katse kallon ?udan da muke ma juna.
"Maman biyu tun Wazu nake ta jiranki ki zo ki karya ku yi wanka ke da Toye, sai mu ka ji shiru kuma" Kujera na samu na zauna duk illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo, kuma babu inda bai yi mun tsami ba, zazzaSi ne kau a jikin nawa ma, ga jiri da ke damuna.
Ke dai bari, aikin abincin bikine bai bani damar zuwan ba. Kinga ko karyawa ma ban yi ba. Bara'u ina kwana ya akaji da taro?" Na faWa kaina a ?asa.
"Lafiya lau Iyaa Toye Tsuntsun soyayya, ya jiki_ jikin?"
Alhamdulillah. Na dubi Gwadabe nace. Ekaro oromi ( ina kwana mai gida?) Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Kin tashi lafiya, ya jiki_jikin naki? Wato kina ta aiki bayan kinsan likita ya hanaki aiki mai wuya ko? Gobe ma kowa zai watse daga yau biki ya ?are, tunda yau za'a kai Amarya Wakinta ai" Boyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, dan jina nake tamkar a ?aya wallahi. Zame jiki Bara'u da Sakina su ka yi su ka bar mana Wakin. Suna fita Gwadabe ya dawo kusa dani ya zauna.
"Iyabona" Ya faWa muryarshi na rawa. Kuka na fashe mishi dashi.
Gwadabe na ro?eka da girman Allah ka sauwa?e mun zuwa taron biki ko suna na danginka. Ba ?aramin muzanta nake yi ba. Ka ware mana wasu lokutan domin ziyarar danginka, amman ba lokacin wani sha'ani ba." Shiru yayi yana kallona idanunshi suka kaWa su kai jawur.
"Ki ?ara ha?uri bisa wanda kike yi da dangina Iyabo. Nasan kina takura sosai, kuma kina shan ba?a?en maganganu marasa daWin saurare. Amman ni ko na so barinki a Kano, kinsan ba yarda Babala zata yi ba. Kuma hakan zai ?ara haddasa wata fitinarne. Iyabo bana son kukan ki, ki share hawayenki gobe da wuri zamu bar Takai ki yi haquri kinji?" Sai na ji tausayinshi ya kuma kamani, ga Soyayyar damuwa ina gani shinfiWe a fuskantar shi, duk da yana ta ?o?arin ganin ya Soye mun halin da yake ciki. Amman na san Tatsuniyar gizo bata wuce ta ?o?i. A hankali na furta.
Gwadabe na ganka a cikin damuwa meke damunka, kar kayi yin?urin Soye mun, dan bama Soye ma juna damuwarmu. A kai nane ko Gwadabe?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da kamo hannayena dukka biyun ya Wan matsesu kaWan. Idanu na lumshe ina cike da tsantsar tausayin aurenmu.
MRS BUKHARI

*DAN ALLAH KUIMUN AFUWA NA SAURARI ?ORAFE_?ORAFENKU AKAN KU WATA BIYU YAYI MUKU YAWA. AYIMUN AFUWA MU BARSHI A WATA BIYU, NA SAKE TURO WANNAN PEJINNE DOMIN IN MUKA DANNAR ?IRKI DASHI. NAN DA WATA BIYU ZAKU JINI DA CI GABAN LABARIN NAGODE*=?O? https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm


NAMA YA DAHU.
ROMO ?ANYE
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI




Lamba ta uku

"A game da abinda ya faru a gida can Kano ne kafin mu tawo. To da Yaya Hambali, da su Yaya Harisu duk sun amince akan Yaya Hambali ya tashe mu a gidanshi mu yi nesa dashi. To Babala tace dai a barta tayi shawara da su Goggo Iyatu. To kinsan Goggo Iyatu kusan ita take sake zuga Babala akan ki. Sabida Laila ?ar wajenta da Allah bai yi mun yi aure ba kamar yanda suka tsara tun muna tsumman goyo. To kinji abinda ya Waga hankalina kenan, tunda nasan bani da kuWin da zan iya kama mana ko Waki Waya, balle ciki da falo." ?ur na zuba mishi idanu.
Gwadabe duk abinda Allah yayi a kan mu me kyau ne. Allah ba zai ba danginka ikon tozarta mu ba da ikon Allah. Kayi ha?uri jarumina duk a akaina ake yi ma hakan." Murmushi yayi gwanin tausayi yace.
"A tunaninsu matsa mun lamba da zasu ci gaba da yi, shi zai sa aurenki ya sire mun. Billa aurenki kullum sake zame mun yake yi kamar yau aka Waura iyabo na. Kema ki ?ara ha?uri wata rana sai labari . Sannan ina da babban albishirin da na cancanci garjejen farin goro Wan shagamu. Allah ya nufa nima na zama matu?in Babbar mota na tashi daga karen mota. Ma'ana an mallakamun mota." Sakina ce ta shigo hannunta ri?e da langa da kofin silver ta dure shi a gabana.
"Sakko ki ci abinci ki yi wanka mu samu mu koma gidan biki, yau biki zai ?are Amarya zata kwana a Wakinta" Godiya na yi ma Sakina.
"Gwadabe Bara'u yana ?war gida wai kaje ku tafi" Da sauri ya mi?e, mu kai sallama ya fice dan yanzu za'a Waura auren ?ar autar tasu. Ni ko a gurguje na karya na yi wanka zuchiyata fal murna na san a ?alla zamu samu sassauci daga talaucin dake addabarmu. , Sakina ta yi ma Toye wanka. Leshin ankon bikin Bose da mu ka yi wata shida daya wuce na saka. Leshi ne me tsada, dan ko sanda aka fitar da leshin na cire raina da yi, amman Gwadabe sai da ya je ya ciyo bashi yai mun domin ya fitar dani kunyar dangina, leshin ya sha Winkin buba da zani, na saka sar?a fashion me kyau wacce Gwadabe ya siya mun a legas da suka je. Mayafina da takalmina ma sababbine wanda matar Tamu ta aiko mun daga Habuja, da naso in bari sai na haihu in yi fitar suna dashi. Gwadabe ne ya ?i yarda yace lallai sai dai in sa a bikin gidansu nima in fito da kyau, dan su Yaya Haula suma sun yi Winke_Winken biki kala uku_uku. Ni kuma bamu da kuWi leshin da na sa basu san na Winka ba, tunda mu ka yi bikin na Siyeshi a ?asan akwati abunka da tattali irin na talaka. Fitowa nayi shar dani har ?ar hoda da jan baki na murza. Toye kuma riga da wandon Atampa na saka mishi da hular ashoke irin na yarenmu. Sakina ta ri?e mishi hannu muka nufi gidan bikin. ?ofar gidan ta?i wutuwa sabida tsabaragen dandazon maza ?an Waurin Aure, sai ma?ota muka faWa akan in an sassauta ma shiga cikin gidan. Sai wajajen kusan azahar ?ofar gidan ya sarara da mutane muka samu muka shiga cikin gidan. Da Laila na soma haWa idanu, sai naga ta shiga ?arame kayan jikina kallo har kirjinta na hawa da sauka irin na tashin hankali. Ni mamakine ma ya kamani. Ban bi ta kanta ba kai tsaye shiyyar Babala na wuce domin in sake gaishesu. Kowa na cikin Wakin kallona yake yi baki a sake, Yaya Haula kuwa tsabar kallona da ta shagala tana yi sai da ta zuba ruwan miya a ?afarta mai zafi kafin ta dawo hayyacinta. Koddibuwace babba a jikinta, amman leshina ya tsole mata idanu. Yaya Halima kuwa wuyana take ta kallo kawai. A tsarge na gaggsishesu bi da bi, suka amsa a dadda?ile in da sabo na riga dana saba tuni. Na Wan zauna jim sai ga Amarya ta shigo Wakin ita da ?awayenta su su biyu. Ta tsugunna ta gaisa da kowa amman kallo wannan ban isheta ba.
Sauwama Amarya an sha kyau" na ce mata ina Wan ya?e. In kun tanka yarinyarnan ta tanka. Abunda ya kawota ta yi ta fice da ?awayenta. Bayan na zauna kamar na awa Waya haka sai na koma tsakar gida, dan naga atana alwalar sallar azahar. ?akin ?anwar mahaifiyar Sakina anan nayi Sallah, mu ka ci tuwo da Sakina, na koma tsakar gida muka shiga rabon tuwo ka'in da na'in. Ban zauna ba sai da aka gama rabon abinci kab tukunna. Zuwa bayan laa'asar kuma dangin ango suka tawo da fantimotin aure, daga nan kuma zasu tafi da Amarya. Ayarin su Asiya na bi mu kai ta fita da kayan Wakin Amarya ana sakawa a mota. Su Yaya Haula da Zuwaira harda su a ?an kai Amarya, mutane sai da suka cika Bus guda, sai ?aramar motar Amarya da ?an ?awayenta. Muna shiga cikin gida muka tsaida sanwar tuwon dare ba mu muka nitsa ba sai wajen takwas na dare, sai lokacin na samu kaina na galabaita sosai, marata ciwo take yi mun tun rana haka na kwana da ciwon marar nan. Da sassafe muka kuma tashi da aikin gyaran gida da karin kumallo. Kokko da ?osai mu ka yi, bayan an kammala karyawa ba?i suka shiga haramar komawa garinsu, sai wanka akeyi. Sai da mu ka yi wanke_wanke muka share wajen tas kafin na samu bokiti na samu ruwan wanka mu ka yi ni da Toye. Gwadabe ne ya neme ni a tsakar gida ya same ni.
"Ki hanzarta ki shirya yanzu zamu kama hanyar Kano. Ana mun lodi a mota zamu kai kayan Legas." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
A shirye nake ni kam tsab.
"To ki shiga ki yi sallama da matan gidan, sai ki same ni a Wakin Babala" Yana faWar haka ya juya da sauri. Ni kuma na shiga bin Wakuna inai musu sallamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login