Showing 234001 words to 237000 words out of 270738 words

Chapter 79 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ciki sosai na wuni zuchiyata fes. Minti_minti sai Usman da murmushinshi ya faWo mun. Gashi har magriba tayi bai kirani ba balle inji yaya ya samu masu jiki.
Ina zaune ina cin shinkafa da miya da latas Batula ta dawo daga unguwa hannunta ri?e da leda ta nemi waje ta zauna.
"Kin ko kira Dr a waya kinji ya mai jikin?"
Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
A_a tsoron kira nake yi ko yana tare da matarshi kinga ai ba zata ji daWi ba ko? Amman tun Wazu nake jiran wayar tashi"
"A_a ba haka za'ayi ba to. Ki rubuta mishi sa?o ki tura mishi zaifi sau?i"
Ai kamar gara kiran wayar ma ko. Kinga bana son haddasa wata fitinar bari dai in kira"
Na danna lambarshi na kirashi. Ai kuwa ringing biyu sai ya Waga.
Wata ajjiyar zuchiya ya sauke mun kafin yace.
"Ai da harna soma fargabar ko dai ni kaWai nake kiWana da rawanane ashe ba haka bane"
Murmushi nayi mishi nace.
Ba haka bane, ya mai jikin ka sameshi, da fatan ka sauka lafiya?"
"Jikin da sau?i yanzu na baro asibiti. Dama na barine inna gama magana da Alhajinmu inna fito in kiraki kafin in wuce gida, sai kika rigani"
Daga haka muka Salle da hira dai, kafin daga bisani mu kai sallama.
Sai yanzu hankalina ya kwanta. Batula na kamu da yawa wallahi" Dariya tayi mun.
"Ai dole ki kamu Hajiya. Kinga muci kaza ki ajjiye wannan ji?a??iyar shinkafar. Ko ba shinkafar Anty bace? Ai bata iya girki ba ku da kuke siya kuna ?o?ari.
Ni dai ta baje mana kwaWayi mu kai tayi.
Gaga_gaga al'amura suka ci gaba da kankama a cikin kwana goma ni da Usman mu ka yi wani irin sha?uwa na mamaki. Na fahimci yana mugun son soyayya ashe gaskiya ne da akace dattijai mayun soyayya ne.
Yau mun wayi gari ina da babban ba?o a hanya. Tun safe ni da Batula muke ta girki dan ya sanar mun ?arfe taran safe jirginsu zai sauka kuma abincina yake son ci.
Wannan karon jallof Win couscous nayi mishi mai wadatar kayan lambu da anta. Sai soSo mai abarba da kankana. Taran nayi ya kirani yace jirginsu ya sauka.
To Shikenan ganinan zuwa ni da ?awata Batula zata yi mun rakiya, zata taya ni dakko maka yaranka"
"To tunda hakan kika tsara amman da ai gidan zan shigo kawai ma ba sai anga matata na sunturi a hotel ba ko?"
Sai kunya ta kamani nace mai.
To Shikenan bari in sanarma Hajja Mama, sai ka iso"
Ina ajjiye wayar na shiga uwar Wakin Hajja Mama na sanar mata yadda mu ka yi da Dr"
"Wannan gidan namu zai shigo? Lallai Dr ke kam yana ji dake. Shi da ko unguwarnan tamu baya iya shigowa sai gashi Dr yau shine zai zauna a Wakina? To mu yanzu zamu tafi shago in ya iso ki shigo dashi cikin uwarWakina. Amman yana tafiya ki kullemun kar aimun sace_sacen da aka saba"
KwaWo da mabuWin ta bani suka fice a gidan. Sake gyara uwarWakin nayi duk da dai fes yake nice harda kunna turaren tsinke. Awa biyu sai ga waya yana ?ofar gida in fito in mishi iso.

Tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana.
Iyabo tayi bazawari Wan soyayya, itama ta kamu da son shi. Gata da aurenta wannan masifa da mi tayi kama.
Mata masu bin bokaye wallahi muji tsoron Allah. Ina Hama zata kai girman wannan zunibin nata duk akan rijalu?
Ya Allah kasa mufi ?arfin xuchiyoyinmu Ameen.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

ramlex266: Ina mata da suka amsa sunan su ba Muna mata ba....

Ina macen da take so ta zamo tauraruwa a gidan mijinta,itace uwargida itace amarya...
ramlex266: Uwargida ko Amarya shin minene matsalar ki a wajen miji?

Rashin dandano ko ni'ima?
Bushewar farji qayau kamar busashen ciyawa?
Rashin samun gamsuwa a wajen maigida ko rashin sha'awar ce ga baki d'aya?
Budewar farji kamar kofar wambai ko qarni/wari ke damunki
ramlex266: Kina so ki zama tauraura kuma sarauniya a wajen oga a rasa gane sirrin naki? Ki zamo yar gaban goshi sai yanda kika ce wato kin mayar da oga mijin kafin ta ce? Ba boka ba malam gyaran shimfida kawai Hajiya to ki nemi hjy ramlex domin qarin bayani
ramlex266: 07069722234 ko 08064421211


Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801


Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU
ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA HU?U

(7)


GWADABE:.

"Kai a naka dawa kaga yafi dacewa kaje a babin adalci a cikinsu wacece tafi kyautata maka tafi son abinda kake so?"
"Kai tsaye Shafa ce. Hadiza fa dan dole nake zaune da'ita. Jibi jiya ana hira ana dariya sai taSe bakinta yarinyarnan take yi. Ta Wauki kishin duniya ta Waura akan Iyabo. Ita tana gidan Wan fulaninta abunta."
Bara'u yace.
"To a gaskiya ka tafi da Shafa kawai, ni fa amman shawarace. In kuma kana gudun matsala yi ?uri'a duk abinda suka Wauka sai ka Wauki dangane. A babin maslaha kenan wannan. Amman zanso ace Shafa ta Wauka ko dan albarkacin kawaici da Iyabo da take goyama a bayanta"
"Wallahi nima haka. Bara'u ina ma Shafa so mai kyau mai haWe da mutuntawa da darajawa, ita gani take nafi son Hadiza, a zuchiyata kuma ba haka bane. Wallahi in ranta ya Saci sai inji har shakkarta nake ji, kuma fa bawai zata yi mun magana bane. Itace makwafin Iyabo wajen ha?uri. Yarinyarnan Iyabo da take goyo ina jin sonta sosai dannewa kawai nake yi."
Bara'u ya kwashe da dariya suka tafa.
"Wallahi Gwadabe kai mugun Wan iska ne. Mata na gidan aurenta ka kasa ha?ura da'ita gaka da mata WanWasa_WanWasa itama Shafa naga sai fashewa take yi dan na fahimci kanason ?atuwar mace mai jiki zaz tsoka.
Dariya suka saka harda tafawa. A gidan iyayen Bara'u suka samu suka shiga suka yo wanka sannan suka shiga Wakin zaure suka sake kaya gidan suna cike da mutane ma?il.
Bara'u ne ya kirawo Sakina mai jego tasha kyau.
"Ki karama Gwadabe matanshi su sameshi a Wakin zaure. In abinci yayi a tawo mana dashi."
"To amman Bara'u kayan cikin tunkiyarnan yayi kaWan an soyashi baka ganshi ba, nace ko za'a ?aro mana naman kasuwane?"
"Ni ina naga wani kuWin Sakina. Kajinnan guda huWu dake cikin keji kisa a yanka sai ku haWa ai dai shikenan ko?"
"I shikenan zansa Alawiyya ta ?aro mun biyu ana Ummanmu su zama shida sai a haWa. Bari in turo maka su. Dama Hadiza ta?i sakewa sai takure kanta takeyi. Ni naga duk ta lalace ta dena gayen ma ta Waurama kanta kishi mai tsanani." Harararta Bara'u yayi yace.
"Nima ai auren zan sake in sha Allah. Tunda Gwadabe yayi biyu nima kinsan sai nayi"
Dariya tayi harda guWa.
"Allah dai ya kawota lafiya. Kaine dai sai mu rabaka biyu ko wacce taja nata. Ni wallahi sai in barma amarya kai kacokan in rungume ?a?ana."
Nan ta wuce Bara'u tayi cikin taron mata.
Bara'u na ba Gwadabe labarin diramar da suka yi da Sakina sai dariya suke ?ya?yatawa sai ga Shafa ta shigo da tran abinci ni?i_ni?i ta dure, ta sake fita sai gata da ruwa. Iyabo ta mi?a ma Gwadabe yayi maza ya amshe abunshi ya rungumeta. Bara'u daya Webi abincinshi sai ya bashi waje.
Shafa ta zuba ma Gwadabe abinci ta saka cokali ta Webo ta kai bakinshi kenan Hadiza ta shigo ri?e da Wiyarta. Tana ganin haka ta sake murtuke fuska. Shafa ta sake ciko cokali ta ba Gwadabe. Hadiza ta kai iya wuya dan ko nunawa ba sui sun gane tana Wakin ba sai wani taSa shi Shafa take yi, itace harda goge mishi baki.
"Ko dai inje ne in kuka gama taSarar ni sai in dawo."
Gwadabe cikin cusa haushi ya kalleta yana zare idanu yace.
"Ya ilahi baki ga abinci nake ci ba, ko so kike saina ?ware? Sannan da kika shigo wa kika kula ma?
Hadiza ta dubeshi tana mamakin akan Shafa ne yake yi mata haka. Kai kawai ta girgiza ita kuwa Shafa sai ciko cokali take tana bashi ga wata dariyar iskanci da suke ta yi.
A fusace ta mi?e har ta sa ?afarta Waya a waje Gwadabe yace.
"Kul kika sake kika fita na faWa miki kenan. Shin ke a komai sai kin nuna rashin ha?urinki ne mtws?"
Kamar dai ba zata dawo ba sai dai ta dawo ta zauna.
Hannunshi ya dun?ule ya mi?ama Hadiza yace.
"ZaSi Waya hagu ko dama?"
Hannun ta ?arema kallo ta rasa wanda zata Wauka. Sai kawai tace.
"Shafa ta soma Wauka"
Gwadabe ya mi?a ma Shafa hannun sai tace ta zaSi dama. Hadiza tace
"Na Wauki hagun"
Ware hannayen yayi ya nuna ma ko wacce abinda ta Wauka.
"Ke me kika ciyo Shafa?"
Tana dariya tace.
"Tafiya naci, wayyo Allah daWi mijina"
Murmushi yayi yaji daWi sosai da abinda Shafa taci har ga Allah da ita yake son tafiya. Hadiza kuma ?wafa tayi tana hawaye tace.
"Wallahi, wallahi bazan yadda ba. In Qur'ani zaku haWiye kuna aman ayoyi bazan yadda ba bakinku Waya ba. In dai adalcine dani ya dace ace an tafi babu wani ?uri'a."
Murmusawa Gwadabe yayi yana kallonta da mamaki yace.
"Hadiza kenan. Ai ko a gidanku malam da ?uri'a aka san shi. Kuma bai taSa sauya wadda taci ba. Na lura ke dai bakya son ganin ana zaune lafiya. Ba dan ina jin tsoronki ba zan yi ?uri'a a takadda ku sake zaSa duk wacce taci itace kawai."
"E na yadda da hakan. Amman wannan kam ban yadda dashi ba ina."
Gwadabe ya girgiza kanshi kawai ya nufi wajen akwatin ?arfen dake Wakin ya yagi takaddu ya yi rubutu ya dun?ule ya kawo musu. Hadiza sai girgiza take yi tana ciccika tana babbatsewa.
"Ke ki soma Wauka"
Cikin fishi ta warci ta gaban Shafa."
"Allah ya kyauta" Cewar Shafa. Ai sai Hadiza ta daki ?irjinta tab tace.
"Ya kyauta abunda yafi haka ?ar abu ta kazan...."
Gwadabe yasa hannu ya tsinka ma Hadiza mari lafiyayye. Ya dubi Shafa yace.
"Yi ha?uri My love, baki ji dai ciwo ba ko?"
Murmusawa Shafa kawai tayi. Hadiza kuwa tuni ta shiga taitayinta tana dafe da kuncinta tana ma Gwadabe kallon mamaki. Shi ko sai hura hanci yake yi.
"Shafa Wauki naki. Ko wacce ta faWi abunda taci"
Shafa tasa hannu zata Wauka kenan Hadiza ta ajjiye wanda ta Wauka ta warce wanda Shafan zata Wauka. Gwadabe ya taSe bakinshi kawai. Shafa tace.
"Tafiya na Wauka"
Ai sai Hadiza ta fashe da kuka ta mi?e da ?arta a hannunta.
"Shikenan ka nuna mun matsayina a wajenka. Ka fifita Shafa a kaina. Da ita kake so lallai kayi tafiya. To ni dai sai dai ka sauwa?e mun wallahi Allah na gama aurenka tunda har ka iya dukana a gaban wannan yarinyar. Ga atampar da mitsiyaciyar matarka ta bamu banso"
Ta kwaWo mai atampar a fuskarshi tab.
Idanu ya lumshe yana ambaton Allah dan wallahi ji yake yi kamar yaita dukan Hadiza a Wakinnan haka yake ji. Shafa ce tayi saurin ri?e hannunta hankalinta a tashe.
"Sakemun hannuna dan kutumar.... Ta mulmulo zagi ?ato ta cunkusama Shafa. Cikin wata iriyar tsawa Gwadabe yace.
"Ki sake ta ta tafi nace miki kafin in illatata a Wakinnan dan wallahi zan iya nakasata"
Tsawar ta gigitasu dukkansu da sauri Bara'u ya shigo ya tadda su a birkice. Bangazarshi Hadiza tayi ta fice.
Sai gata da akwati tazo wucewa Sakina sai magana take yi mata ta?i saurarenta.
Haka Bara'u ya bi Hadiza waje shima da sauri.
"Ungo yarinyarnan ki shiga gida. Sannan ki soma shirye_shirye umara zamu tafi"
Shafa ta buWe baki zata yi magana Gwadabe ya mata wani kallo. Mu?ut ta haWiye maganarta ta karSi yarinyarta ta koma ciki. Sakina tace.
"Gwadabe a ri?a ha?uri kasan sha'anin mata sai ha?uri. Duk da dai Hadiza kam tana da matsala. Tun dai da aka ambaci Iyabo, tare da gabatar da tsaraba shikenan na kasa gane mata. Ko aikin girki ta?i yi, sai tunane_tunane take yi. Ayi ha?uri amman ko dan gudun lalacewar zumunci.
"Babu komai Sakina nagode. Kuci gaba da taronku bari in je in samu Bara'u '
Yasa kai ya fice kiciSus sukai da Bara'u a ?ofar fita.
Hannunshi ya jawo suka nemi ?ar?ashin bishiya suka zauna a kututture.
"Tabb yau ni naga kishin mata. Yarinyarnan yi tayi kamar fa zata zageni. Dan idanunta gaskiya sun gama rufewa. Tayi tafiyarta abunta ta?i fur ni kuma ba matata ko ?anwata ba balle in jawosu da ?arfin tuwo ba.
"Rabu da'ita Bara'u. Gara data tafi dan in ina ganinta zan iya aikata abinda zaku yi mamaki. Kasan menene tun kafin Hadiza ta sani cikin uku zan yima tubkar hanci ai banji a jikina zan iya ci gaba da rayuwa da'ita ba. Gobe sassafe zamu juya muma.
"Kai abun ya matu?ar bani mamaki yanzu abinda zamu yi muje masallaci muyi sallah sai mu ci gaba da tattaunawa "
A masallacin jikin gidan Zul?i sukai Sallah Zul?in ma ya fito tare dashi akayi sallar. A cikin masallacin harda Da'u sai kallon Gwadabe yake yi. Gwadabe ma yana ta kallonshi yadda kuka san bai gane Da'u ba. Sai dai a ?asan ranshi tausayin Da'u ne dan?are a ranshi ganin yadda ya rame ya fita hayyacinshi. Shi ko Gwadabe yana cikin shiga ta alfarma kallo daya zaka yi mishi ka gane yana cikin kwanciyar hankali. Jikin Da'u a mace ya fita daga Masallacin ya juma a jingine a ?ar?ashin bishiya yanata tunanik ko ya koma su gaisa da Gwadabe ne ya faWa mishi Babala bata da lafiya? Wata zuchiyarce ta gargaWeshi da yin hakan yana gudun kar Babala tayi fishi dashi, dama yanzu hakan ma a cikin fishi dasu take tana faWa musu sun gaza a kan lafiyarta. Tunda dai Yaya Hambali ya ?wace dukiyarshi daga garesu Babala ta juya musu baya suma matansu da yaransu suka kasance abun kyara kamar Iyabo a da.
Gwadabe dai suna zaune har Zul?i ya salllami jama'a ya dawo wajensu Gwadabe.
"Yaya ake ciki ne, wanne hukunci ka yanke Gwadabe munyi waya da maigidana yace in kawo ka"
Idanu Gwadabe ya lumshe yace.
"Na amince Zul?i. Amman sai dai haWuwar ta zama yau in Yana da lokaci matsalace na iyali ya taso gobe nake son in juya"
Zul?i yace wannan babu wani matsala. Bari zuwa bayan magriba ai sai muje mu ganshi ko Bara'u. A tsaida magana ka cike form na jam'iyya shikenan ka zama member. Sai dai fa kaga lokacin ya kusan gabatowa an riga an kaWa gangar siyasa ba zaka samu lokacin kan ka ba, kaine meeting a Abuja, kaine meeting a cikin Kano haka za'aitayi. Sannan zamu samu malamai da zasu dinga mana adda'a akan lamarin".
"Duk babu wata damuwa. Allah dai ya nuna mana lokacin.
A daren su Gwadabe suka shirya zuwa gidan Chairman na nan Takai sun shafe tsawon awa uku cib suna meeting. Daga ?arshe komai ya daidaita ya Webo kuWi ya ba Gwadabe yace ya soma ri?ewa a hannunshi na Winke_Winken suturu.
Godiya sukai mishi suka yi mishi sallama. Kai tsaye Zul?i ya kai Gwadabe gidan shugaban party na nan takai akai mishi rijistar ya zama member.
Washegari Gwadabe ya je gidansu Shafa ya Wauketa suka kama hanya dan jiya a gida ta kwana.
Cikin dare sosai suka isa, dalilin da yasa Gwadabe bai je wajen malam ba kenan. Sai da safe bayan ya gama kintsawa harda jakar magungunanshi ya rataya sai ya shiga gidan har turakar Malam. Hadizan tana ciki Malam da su Baba Suwaiba sun tusata gaba anata mata faWa harda Yaya Tasi'u da Yaya jamilu.
"Yauwa Gwadabe shigo ashe ka dawo?"
Cewar Malam kenan.
A hankali Gwadabe ya shiga ya dur?usa ya gaishesu Waya bayan Waya kana ya nemi waje ya zauna.
"Gata tunda ta dawo ake tuhumarta dalilin dawowarta dan tayi fur ta?i komawa Wakinta. A Wakin Asshi ta tare. Yau da safennan Sabitu ya mammaketa da ?yar iyayensu mata suka karSeta. Tunda dai gaka ko zaka iya faWa mana menene


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login