Showing 3001 words to 6000 words out of 270738 words

Chapter 2 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mun ba?in jini a wajen danginka" Idanu ya lumshe kawai sai girgiza kanshi yake yi. ?an guntun siririn hawayen daya surnano mun na yi maza na share gudun kar Gwadabe ya buWe idanunshi ya ga zubar hawayena. Har Bus Winmu ta cika muka fito daga tasha bamu sake magana ba. Ko wanne cikinmu aikin tubka da warwara kawai yake yi a zuchiyarshi. Motarmu sai gudu take shararawa bisa titi, tun muna wuce titinan cikin gari muna wuce manyan gidajen sama, da manyan shopping mall har mu ka soma wuce ciyayi da fasassun kwalta, jagab_jagab Win hanya ne yasa Gwadabe yai ta mun aikin sannu har muka shiga cikin ?aramar hukumar Takai.


TAKAI TA KAWO TA SABA DA SAUKAR BA?I
Takai ?aramar hukumace take jihar Kano. Yanki ne wanda Allah ya albarkace shi da ruwan sama a sanadiyyar hakanne mutanen yankin su ke noma da kiwo da kasuwanci gashi Allah subuhanahu wata ala ya albarkaci garin takai da bishiyun dabinai masu yawan gaske, dabino ya wadaci jama'ar Takai sosai mota_mota ake fita da dabino domin kasuwancinshi. Garin Takai yankine wanda ya yi nesa da birnin kano da tsawon kilomita 80, yayi kusa da yankunan ?asar Bauchi, yankin da yake yawan kawowa ?asar kano farmaki a lokacin sarkin kano (Babba Zaki) Sanadiyyar hare_haren da yake yawan kaima birnin kano, Sarkin Kano Babba Zaki ya yanke shawarar a kafa ?asar Takai, kuma ayi ganuwa a garin. Hakanne yasa ya tura maya?a domin su zauna a garin. Bayan an kafa dausayin ya?i a garin Takai, Sarkin Kano Babba Zaki ya gina gidan sarkin kano a garin Takai kuma ya so ya koma garin Takai Win da zama." Muna sauka daga mota mu ka hau mashin ya wuce damu Unguwar Dibinai unguwa mai dogon tarihi kenan a garin na Takai. Dai dai ?ofar gidansu Gwadabe acaSanmu ya tsaya, ?ofar gidan cike ma?il da maza, mata kuma sunata shige da fice. Bara'u Abokin Gwadabe ne ya tarbeshi da fara'arshi, yasa hannu ya amshe Toye ya rungume.
"Madam Iyabo barka da isowa tsuntsun soyayya" Dariyar dole na yi mishi, dan muddun muka haWu dashi sai ya furta wannan suna daya raWa mana.
Bara'u barka dai da gida, ya yara da Sakinar?" Dariya yayi yace.
"Sakina tun safe tana cikin gida sun zo taya aikin biki. Yaran naku ma zaki gansu a ciki" ?an murmusawa nayi, Gwadabe ya dubeni yace.
"Iyabo ki shiga ciki, zan gaggaisa da ?an uwa da abokan arziki. Gasu Yaya Hambali can a ?ar?ashin bishiyar dabino suma "
To shikenan sai mun haWu, ka kawo akwati da jakar to" Dan nasan matsawar ban karSa ba da ?an uwanshi sun ?illa ido suka ga akwatinan a hannunshi to zan sha habaici da maganganun banza" Bara'u yace.
"Bashshi ki yi fama da kanki, yara zasu shigo miki dashi" Gwadabe yace.
"Kaima ka faWa mata, da ba dan bikinnan ya zame mata dole zuwanshi ba, ai da bama zata yi doguwar tafiya da ciki haka ba, baka ga wuyar da tasha a hanya ba wallahi. Bikin Auta guda in bata zo ba kai kasan akwai ?ura" Ni dai a wajen na yi shigewata cikin gidan na barsu a tsaye suna tattaunawa, Gwadabe bashi da aminin daya shallake Bara'u a wajenshi, tare suka taso, su kai wasan ?asarsu, har shayi tare akayi musu. Komawar Gwadabe Cikin birni bai rage amintakarsu ba sam, dan Sakina matarshi tasha zuwar mana ita da yara, sai su fi sati biyu. Nima dolena in na zo Takai a gidan Sakina nake sauka. Zuwana na ?arshe wanda daga shi ban sake zuwa ba sai yau ne kawai Babala tace bazan sauka a gidan Sakina ba, a cikin gida zan zauna, kuma ta kafa dokar ta haramta mun zuwa gidan Bara'u in kwana, ba dan komai ba sai dan a sake ?untatani.


Gwadabe:.
"Gwadabe lafiya irin wannan ramar da kayi haka?" Cewar Bara'u wanda ya kasa ha?uri sai da ya ja Gwadabe gefe dan su Wan zanta,bayan ya bi mazan dake ?ofar gida an gaggaisa. Gwadabe ya girgiza kai yace.
"Wallahi Bara'u kai kasan komai al'amuranne sai godiyar Allah kawai. Kasan in akace maka magidanci bashi da cikakkiyar sana'ar kanshi dole hankalinshi bazai kwanta ba. Karen mota nake yi har yanzu dai daka sani. Amman muna sa ran za'ayi mana freedom da yardar Allah muma a bamu mota, in hakan ya tabbata za'a samu sau?i. A hakanma ban fa zauna ba, buga_buga akeyi babu dare bare rana, muddin akace maka safiya ta yi, to fa in na fice duk abunda na samu yi nake yi. Nine kwashe shara, nine kwashe kwata, nine bin masu Bus na zuwa unguwanni ina karen mota. Kaga duk sana'oene na cin abinci kawai, abincinma bafa sau uku a rana ba. Duk ranar data carke wallahi sai dai in tura Iyabo gidansu ita da Toye dan su samu abunda zasu kai bakin salati, haka iyayenta zasu ci mata mutuncinta in taje musu, to amman ni hakan yafi mun. Ni kuma haka zan wuni neman aikin yi. Babban abunda yake sani cikin juyayi shine a wannan halin da muke ciki ko Bara'u? To Yaya Hambali, da su Sukairaju, Fodiyo, Yaya Harisu kai dukkansu. Su a wadace suke da abinci, dan Yaya Hambali kullum da nama ake miya a tukunyarshi. Ni kuma na sama raina in yinwa ita zata zame mana ajali ni da iyalina sai dai mu mutu. Bara'u bazan sake tambayar tallafi ko taimako a wajen kowa ba. Wula?anci wanne ne ni Gwadabe ban gani ba? Yanzu nan yau Yaya Hambali yace mu tattare yamanu_yanamu mu bar mushi gidanshi. Dan kawai Iyabo ta watsa ma Yaya Haula ruwan kashi ba tare da saninta ba, fitintinun gidan kaWai ya'isa yasa in yi rama wallahi."

Mrs Bukhari ce

Sai mun kasance a cikin wannan kayataccen labarin mai Wauke da dumbin darasi.
Tafiyar tana da tsayi sosai. Ku shirya tsab kafin fitowata

Inanan tafe ba da jimawaba in sha Allah =?M?
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm



NAMA YA DAHU..
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


Lamba ta biyu


Gwadabe:.

Numfashi ya ja, tare da jin wani irin turirin zafi a zuchiyarshi. Yana mamakin yanda ?an uwanshi suka juya mishi baya sabida Iyabo. Bara'u ya ja ajjiyar zuchiya yace.
"Wannan ja'iba har yanzu barta ta wuce ba Gwadabe?, Aure sama da shekaru shida, ga rabo a tsakani har yanzu basu sauke a?idarsu akan Iyabo ba? Naga ma ana wanke Arniya a aureta ba tare da ta bar arnancinta ba, kuma addini bai haka hakan ba, ballantana Iyabo wacce take musulma gabanta da bayanta. Shawarata anan Gwadabe shine ka yi ha?uri ka ba Yaya Hambali ha?uri kuci gaba da zama a ?ar?ashin inuwar dukiyarshi. Kuma nima na mara maka baya kar ka sake ka nuna musu ka gaza akan iyalinka, gara ka dinga turata gidan nasu duk wula?ancin da zasu yi muku. Gwadabe kai mutumin kirki ne sosai, bana mance alkhairanka gareni. Bazan mance ba lokacin kana samu kai ka biya mun sadakin Sakina, ka siyo mun turamen zani har guda biyar aka zuba a famtimoti banda abubbuwa da kai ta binmu mu abokanka dashi na alkhairi. Kai kayi silar fitan Tamu gada cikin garinnan na Takai ya shiga Kano. Ashe hanyar arzikin nashi kenan yanzu ina Tamu? Yana Habuja shi da iyalinshi, sun samu rufin asiri sosai. Allah bazai hofantar da mutum irinka ba, matsawar kaga ka ro?i arziki Allah bai baka ba Gwadabe ka Wauka cewar arzikin ?ila ba alkhairi bane a gareka. Kar in cikaka da surutu gara ka shiga ka samu Iyabo, wala Allah dangi su sassauta daga tsangwamarta in suka ga kaifin idanunka." Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu uku ?an muttala_muttala ya tura a aljihun koWaWWen jeans Win Gwadabe.
"Ka ba Babala gudunmawarka basai kace mun baka dashi ba, ta nuna a jikinka." Hannunshi ya ja suka nufi cikin gidan. Gwadabe sai murmushi yake yi gami da yabon ?o?ari na Aminin nashi a kanshi. Jifa_jifa Bara'u na yi ma Gwadabe aiken gyaWar miya, da shinkafa ?ar hausa. Abunda yake nomewa kenan, kuma ?ar gonar tashi ba wata babbar gona bace ga hidindimu masu tarin yawa a kan nashi.

Iyabo:.
?afafuna har rawa suke yi wallahi dana Wora ?afata a cikin gidan. Da Yaya Halima na soma cin karo ta tawo ita da ?awayenta, taci kwalliya, da halamun rakiya zata yi musu. Dariyar dole na ?a?aro nace.
Yaya Halima rakiya zaki yi ne. Ina wuni? Na furta da hausar bakina irinta yarbawan da suka ?ware a yaren Hausa. Dan babu kalmar da take bani wahalar furtawa sai dai nakan furtatane da irin Hausar bakina. Harara Yaya Halima ta doka mun, ta ?ura ma titsetsen cikina idanu ?ur. Tsaki ta ja mai ?arfi suka wuce ni ita da ?awayenta fuu. Jikina ya sake macewa mus, da jan ?afa na ?arasa shiga babban gidan nasu mai ?ofofi huWu, ko wanne shiyya da ?ofarshi, amman gidan gabaki Waya a haWe yake, ?an uwane dangin juna da yaransu da jikokinsu a cikin gidan. Babban wan mahaifin su Gwadabe shi ya tara kan wannan dangi a waje Waya, kasancewar mahaifinsu Allah ya albarkaceshi da yawan yara (kakan su Gwadabe kenan). Su rai Talatin da uku mahaifinsu ya haifa, matanshi biyu rak. Sai wan mahaifinsu Gwadabe yaji bari ya haWe kan ?annenshi su zauna waje guda domin ?arfafar zumunci. Irin abinda Babala tayi kenan akan Yaya Hambali daya haWe kan ?annenshi waje guda suke rayuwa gida Waya. Su Baban Nazifi da su Sukairaju kowanne cikinsu yana da Wakinshi da yake sauka in sabgar biki ta kawomu, akwai katifu da labuleye a Wakin. Gwadabe ne kawai bashi da Wakin sauka in mun zo. Hakan ya farune sakamakon ni ya aura ?ar ?abilar Yoruba bai auri ?ar ?alibarsu ta Hausa fulani ba. Ina shiga shiyyar Babala naci karo da su Yaya Haula, da Sawaiba matar Harisu, dasu Gude sune ?an gaba gaban murhu anata tu?a tuwon jama'ar biki. Duk suka kalleni suka watsar, nasu kam ai na daWe da sabawa. Ko da nayi sallama WaiWaikun mutanene suka amsani, suma ba?ine da suka shigo daga wasu ?auyukan dan taya iyalan wannan gida murnar biki. A sanyaye na gaishesu har zan wuce Yaya Haula tace.
"Ai kamata yayi ki ci Wamara da mayafinki ki zo ki tu?a mana tuwonnan yayi sumul kamar Amala, kinsan dai a gidan surukai kike. Cijewa nayi nace mata.
To bari in gaisa da su Babala sai in zo Yaya Haula" Shikenan iyakar abunda nace, Sai kawai Gude ta daka tsalle tace.
"Lallai Iyabo wuyanki ya isa yanka sosai. Gwadabe ya Waure miki kugu sosai. Ke har kina da ta cewa a cikin zuriyarnan, Worin dosono dake? Ai da gidanku kika je bikinku na kwalo_kwalo dole ki zage kici aiki dama yarbawa ba'a sanku da hutu ba sai wahala" Hawayen da suke shirin zubo mun nayi saurin mayarwa dan hango Babala tana nufomu. Tana ganina ta zabga mun harara mai muni. Babu shiri na zube a ?asa ko nauyin cikina banji ba.
Barka da fitowa Babala" Tsaki taja.
" In Kinga dama kin tashi daga wannan tsugunnon naku na gado. Kin shigo garin amman baki iya zuwa inda nake kin gaisheni ba, balle matan yayyena da ?annena su ci albarkacina a matsayina na mahaifiyar Gwadabe. Sai da kika ganni zaki wani zube a ?ar, ai ni na Wauka ba zaki barshi yazo bikin ba ma." Hawaye take ya tsinke a idanuna ya soma zuba shar_shar_shar, in furta kalma na kasa, in Wago in bata hakuri na kasa bakina yayi mun nauyi ainun.
"Haula menene yake faruwa nake jiyo hayaniyarku ne?" Babala ta faWa cikin Sacin rai. Abinda Yaya Haula take jira dama kenan ai kuwa sai cewa tayi da Babala.
"Ce mata fa nayi tazo ta tu?e mana tuwonnan yayi laushi irin nasu yarbawa. Shine ta nemi faWa mun magana Babala, so take ta fake da ciki ta ?i yin aiki. Lokacin bikin Rahina ma haka ta kwanta jinya ko tsinke ta?i Wagawa. Ko a can Kano Gwadabe shi ke mata har shara da wanke_wanke, balle kuma wanki da wankan Toye" Baki Babala ta ri?e tana jijjiga kai kawai.
"Ba shakka ashe har yanzu Yarbawa suna da ba?ar zuchiyar yin agumu. Abunda na dinga jiye ma Gwadabe kenan ya?i ganewa sabida tun ana neman aka gusar mishi da hankali. Ai sunan Gwadabe ya daWe a hannun Baba lawo ( Bokan yarbawa)" Hawaye kawai nake zubarwa rana zafi inuwa ?una. Ana cikin wannan ruguntsumin Gwadabe ya shigo yana rungume da Toye ga jakar kayanmu yana ja, Bara'u na ri?e da jakar kayan Toye. A tsaye suke suna gaisawa da dangin Babala, amman hankalin Gwadabe na kaina yanda yaga ina tsiyayar hawaye gani a gurfane. Ba shiri ya iso inda muke.
"Babala lafiya meke faruwa haka? Iyabo ke ba likita ya hanaki tsugunno ba, tashi tsaye" Ya faWa a sanyaye. Babala ta sauke gwauron numfashi ta dubi Gwadabe tace.
"Babu shakka Gwadabe, sannu me mata. Wato likita ya hanata tsugunno a tsaye kake so ta gaisheni kenan ko marar albarka? Yayi kyau ai ku sha kuruminku komai ma ya kusan zuwa ?arshe da izinin Allah" Tana faWar haka ta wuce fu tana share hawaye. Bansan me akayi mata har da zai sata zub da hawaye ba. A kullum naga Babala na kuka akanmu tsorone yake sake shigata dan kukanta a wajen Gwadabe babbar musibace wacce ko arziki bazai bari yayi ba. Gabana ya yanke ya faWi, take na ji jiri na shirin kayar dani. Me take nufi da komai ya kusan zuwa ?arshe to? Ko so take Gwadabe ya rabu dani kenan ya auri Bahaushiya ?ar uwarshi?. A baya haka Babala ta tursasa Gwadabe sai da yai mun saki Waya. Sakin daya sake rura wutar rikici tsakanin dangina da dangin Gwadabe kenan, wannan saki ba ?aramin ta da zaune tsaye yayi ba. Dan Iya Debisi da Babala sai da suka kusan raba abun faWe a layi. Har an kwashe mun jerena har ga Allah ko ni a wancan lokacin na ha?ura da Gwadabe. Allah ne yayi shan ruwan aurenmu bai ?areba ina dawowa na samu wannan ciki."
"Tashi daga tsugunnon Iyabo ki shiga ciki ke da Toye ki huta. Zan je in nemo miki abunda zaki iya ci, ko in sa Sakina ta yo miki"
Da ?yar na mi?e tsaye ?afafuna sun yi tsami ainun. Haula da sauran matan dake wajen duk sai suka ri?e bakinsu akan furucin da Gwadabe yayi. Shi kuwa kamar ya faWa ne dan ma ya sake cusa musu ba?in ciki.
A'a Gwadabe kar ka nemo mini wani abuncin. Duk abunda na samu zanci, ai jikin nawa da sau?i." Hannu nasa na sauke Toye daga kafaWarshi. Ya mi?o mun jakar hannun Bara'u na rataya. Jakar kayanmu kuma nace ya tafi mana da'ita gidan Bara'u tunda acan yake sauka mafiya yawan lokuta. Ina tafe ina jan ?afata. Sai kallon banza aketa watsomun, harda masu tsaki, da tofar da miyau. Duk inda naga taron mata sai na gaishesu zan wuce, kuma fa saina rusuna mu a al'adarmu akwai wannan tarbiyyar. Wasu su amsa ciki_ciki, wasu ba sa amsaba a haka har na isa Wakin Babala. Cike dam Wakin yake da ?annenta da yayyenta. Yaya Halima ma ta dawo daga Rakiya tana zaune tana cin tuwon shinkafa miyar kabewa sai ?amshin man shanu take yi. Laila na zaune a kusa da'ita ta ci ado sosai, sai wani hararata take yi. Ina shiga na zube a ?asa Waya bayan Waya na dinga binsu da gaisuwa, har Laila dana girma ban bari ba sai da na gaisheta.
"Sai ki tashi maza ki shiga cikin surukan gidannan ki kama aiki, baki ci ta zama ba" Cewar Baba Iyatu ?anwar Babala. Mi?ewa nayi ina shirin fita na jiyo Yaya Halima na cewa.
"Ki tafi da Wanki babu wanda zai kular miki dashi" Yaron na kalla yayi tsuru_tsuru kamar ba dangin mahaifinshi ya shigo ba. Duk ?in Gwadabe da dangina suke yi bai shafi abunda muka haifaba sam, amman banda dangin Gwadabe. Hannun Toye na kama muka fito tare. Da Gwadabe naci karo zai shigo ni kuma zan fita.
"Ina kuma zaki je ke da ba ishasshiyar lafiya gareki ba?" Ban ce mishi komai ba gudun kar in faWi wata kalma da zata zama lefi.
"Aiki zata je ta kama ma su Haula. Ko su zasu girka mata abinda zata ci ne rasa k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????unya?" Cewar Baba Iyatu. Da sauri na wuce shi ina murmushi wanda yafi kuka ciwo. Shi kuma ina jiyoshi yana musu bayanin hawan jini ne dani, kuma likita ya hanani yawan aiki da zurga_zurga. Ni dai gaba na ?ara dani akaita hada hadar girki har sai da muka gama na zauna a kan turmi ina ba Toye abinci a baki. Sakina ce ta iso inda nake da fara'arta. Nima cikin fara'a na tarbeta. Kwanon hannunta ta ajjiye a gabana.
"Maman biyu ga farfesun kifi Gwadabe yasa nayi miki. Yace shi kaWai kike iya ci ya zauna" ?an murmushi na ?a?aro na dubi Yaya Haula bata kallonmu amman kunnuwanta yana wajenmu.
Kai Sakina sai da ya saki wahala? Kinga ga tuwo nan ma ina jira Toye ya ?oshi ne sai in cinye ragowar, jikin yanzu da sau?i" Da sauri Yaya Haula ta yi Sangaren Babala na yi imani wata fitinar zata je ta kunno mun. ?akin Goggo Innawo mu ka shiga, ita Goggo Innawo ?anwar mahaifiyar Sakina ce a gidan take aure. Anan naci kifina muna hirar yaushe gamo.
"Oh Iyabo ashe rabon ?an biyu ne ya dawo dake Wakin ki. Irin rikicin da akaita tayi babu wanda ya zaci aurenku zai dawo, sai gashi har da cikin ?an biyu" Dariya nayi nace.
Sakina kinsan duk abinda ya samu bawa da sanin Allah. Shan ruwan aurenmu ne bai ?are ba. Duk rikici in Allah ya riga ya ?adarto a dakin Gwadabe zan ?are rayuwata, babu tsumi babu dabara ga duk waWanda basa son tarayyyarmu. Ni aurena da Gwadabe ya ?ara mun tsoron Allah, anan na sake gane ?udurar Allah. Irin bada?alar da ta biyo neman auren ai me girma ce, amman da yake Allah ya yarda da haWin ba gamu ba". Sakina tace.
"Wannan gaskiya ne. Mu kammu ba mui zaton aurenku zai yiwu ba. Duk da dai Gwadabe yana tsantsar sonki da burin son aurenki. Amman bai samu goyon baya a wajen kowa ba sai Bara'u. Bara'u kuma bashi da ikon zartar da hukunci a kan Gwadabe.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login