Showing 144001 words to 147000 words out of 270738 words

Chapter 49 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ta kasance" Cewar Iyaa Beji kenan. Iyaa Kokodeen ita kam hawaye take ta sharewa. Take nima na fashe da nawa kukan sai shesshe?a nake yi. Ni wannan maganganun duk sun isheni. Ni ba yarinya ?arama ba, kuma ni nace naji na gani ba sai su sa albarka su bini da ido ba? Haka aurena da Gwadabe akaita koke_koke da tashin hankula iri daban_daban gashi a aure na biyu dana auri jinina bata sauya zani ba. Ko babu komai ni inaso in zauna a kusa da kannena da mahaifiyata. Tunda da tun farko an barni a hannunta da a wannan ?auyen zan rayu, kamar yadda itama ta rayu."
Kaya na sauya, akwatin kayan sawata dama yana tare damu. Ruwa daya tsagaita Yusufu yai mana jagora bayan mun rama sallolin da ake binmu har magriba munyi, an kawo mana jallof Win shinkafa da Dada tasa aka dafa domin tarar ba?i. Yafendona Dada ta aika aka kira duk suka haWu aka rankaya kai Amarya da ?afa.
A kacame gidan yake sosai anata kacaniyar biki. Tsakar gidannan ta damalmale da ruwa da abinci da yara suka zubar. Rumfunan gidan cike da mata da yara anata haya_haya. ?akin Yafendo KaSoji aka wuce dani kai tsaye. Anan muka tarar da su Yafendo A'i da yaransu mata dake gidan aure.
"Lale lale. Amaryarmu tazo gida.
Sannunku mutanen Kano"
Waje aka basu na zama aka taresu da lafiyayyen tuwo miyar ta wadatu da naman saniya da man shanu. Yafendo A'i tace.
"Ga abinci kuci, ayi sallah sai a shiga da Amarya Wakunan matan gidan kafin a shiga da'ita Wakinta. An gama jera mata komai. Tun Wazu mata suke zuwa kallon Wakin Amarya tubarkalla masha Allah" ?an dariya Iyaa Kokodeen tayi a matsayin amsa kawai.
A nan mu kai Sallah, BaWWo ta shigo ta sameni.
"Adda ragowar wasu muhimman kayanki duk suna Wakina gudun kar a Sarnatar miki. Akwai ?unshi wasu buhunhuna duk na shiga dasu Wakina"
Yauwa BaWWo su waWannan buhunhunan ki barsu a Wakinki zuwa gobe zamu ware kayan amfanina ragowar gidan Dada za'a Kai mun."
RaWa naima uwani a kunnenta, ta mi?e suka fita ita da BaWWo. Yafendona tace.
"Iyayen Jabu ku taso mu kai amarya Wakunan matan da tazo ta tarar a gidan bisa ga al'ada kafin a kaita Wakinta"
Gaba suka tusani Yafendona da Iyaa Kokodeen. Ragowar kuma aka nuna musu Wakina suka kama hanya.
Da Wakin Hama muka soma, Wakin ma cike yake da ?awaye babu masaka tsinke. Duk sun tarune domin suna son ganina, ance musu daga Saudiyya na dawo. Sai da wasu dole suka fita kafin mu muka samu waje. Yafendona ta nuna mun gefen gadon Hama tace.
"Jabu ga bakin gado zauna muyi a gurguje ki samu ki shiga Wakinki sanyin yayi yawa" ?ofanuwa nayi a bakin gadon, fuskata ba'a rufe take ruf ba ina iya ganin kowa da komai, duk wanda ya kalleni zai iya ganin fuskanta.
Hama fuskarta ta kumbura tayi jawur da halama taci kuka ta gode Allah. Dan ina zama ta bani baya sai jijjiga ?afarta take yi. Ga Daso a gefenta sauran manyan ?awayen nata suna tsakiyar gadon sai ?aremun kallo suke yi. Ni ko ina lure tsab da motsin kowa.
"Hama ga ?anwarki mun kawo miki. Duk da dai zata iya girme miki amman dole kece sama da'ita tunda ke ta shigo ta samu. To Jabu dai ba ba?uwa bace ku daure ku haWe kawunanku domin a zauna lafiya. Jabu dai ?ar uwa take ga Hamma da mahaifiyarta da mahaifiyar shi uwa Waya suke uba Waya kin sani. To ayi ha?uri a martaba wannan hala?ar" Hama dai ta?i buWe bakinta tayi magana har saida Daso ta zungureta kana tace.
"Allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkairi " Yafendona tace.
"Ameen to Jabu muje a kaiki ragowar Wakunan"
Haka mukaita shiga Wakunan matan ?annen Hamma daga ?arshe suka wuce dani bukkata dake wata ?ar kwana can ?arshen gidan sai an shiga lungu. Tun daga ?ofar lungun akayi blue Win fenti har cikin bukkarnan data kasance Wakina. Da bismillah na shiga ina karanto adda'a duk wacce tazo bakina.
A takure bukkar take sosai kasancewar kayana da yawa sai ya zamana babu ko wajen da zan iya sallama. A kujera aka zaunar dani. Uwani da BaWWo sai gyare_gyare suke yi mini. Anti Ramata tace.
"Allah me iko. Yau wannan shine Wakin auren Iyabo"
Sabida rashin waje ishasshe basu jima ba duk suka fice, Waki ya rage daga ni sai su Uwani.
"Iyabo kujerunnan dole ki rabu da wasu gaskiya. Ni ina ganin waccan 2 sitter Win kawai za'a bari in kinaso ki samu fili. Sannan kayayyakin kitchen Winki fa duk mun lode miki a sib Sangare Waya baki da kitchen, da kitchen da banWaki duk na gandune, kinga ai ba zamu yi miki jere a kitchen Win gandu ba.
To Uwani duk yadda ya dace ayi kawai"
Nace da'ita ina takure a kujera"
"To yanzu dare yayi zuwa gobe da safe duk saimu gyara komai ni da BaWWo. Kun haWu da angon naki kuwa Iyabo?" Idanu na lumshe nace.
A'a bamu haWu ba, ?ila ma sai gobe dare yayi, gida kuma haWe da iyaye"
Mayafina na cire na koma kan gadona da yasha lafiyayyen zanin gado mai laushi. Fentin Wakin nabi da idanu, bai biyu ba yayi wani roWi_roWi. Na Waga kaina azara tana kallona ina kallonta. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Uwani nace.
Uwani wannan azarar babu yadda za'ayi a rufeta?"
Dariya ce ta kama Uwani sai da tayi mai isarta sannan tace.
"Zamu rufeta zuwa gobe ko da zanin gadone, dan dama nace zan shiga gari in siyo cottin a zagaye miki Wakin dashi zaifi fasali fiye da wannan fentin ?an ?auyen a hakanma naga ke kaWaice mai fenti me kala duk farar ?asace a shafe a nasu bukkar, azara ai ke kika siya da kuWinki Iyabo. Ke dai zuwa goben dai ki kwantar hankalinki Amarya a gidan Hamma."
Dariya muka saka dukkanmu nace.
Baki da dama Uwani Uwargida a gidan Hafizu, Hafizu ikon Allah"
Wata uwar harara ta watso mun. Na sake fashewa da dariya. BaWWo tace.
"Bari in kawo muku fura da nono Adda" Ta fita sai gata da Fura da nono cikin ?warya, tayi mana sallama ta fita dan a lokacin goman dare zai iya yi. Muna daga gado muna hira da Uwani muna shan fura.
"Iyabo nifa harna hango miki alkhairan kasuwanci. Wallahi in Allah ya dafa miki me kuWi zaki zama, kita sare_sarenki. Nima kafin in tafi zan sari man shanu. A hannun BaWWo tunda yanzu lokacin arharshi ne."
Mun daWe sosai muna tattaunawa kafin bacci yayi awon gaba damu.
Washe gari aka kuma tashi da hatsaniyar biki. Uwani tun wurwuri suka shiga gari ita da BaWWo. Daga ni sai Anti Ramata a Wakin, sai wajajen takwas na safe matar ?anin Hamma ta kawo mana shayi ruwan bunu da ?aton biredi sai ?osai cikin kula.
Ni banci biredin ba ma, ?osai biyu naci sai ruwan bunun dana sha. Cubu ce ta le?o Wakin tace.
"Adda na kai miki ruwan wanka ki je ki watsa"
Dama tuntuni wankan nake son yi inje mu gaisa da Yafendo, da ragowar matan gidan.
Hijabi na saka na fita hannuna ri?e da kwandon soso da sabulu.
Ruwan wankan yana cikin sabon bokitin ?arfe in le?a ruwan sai naga wani garin magani yana yawo a cikin ruwan. Baki na buWe ina mamaki, ba shiri na kelayar da ruwan na fito da bokitin a hannuna. Da hannu na yafito Cubu dake gindin murhu. Tana ?arasowa na dam?a mata bokitin.
Ungo ki zubo mun wani ruwan zafin. Kafin ki zubo ki Waurayo bokitin sosai. Wancan zamewa nayi ya zube"
KarSa tayi ta zubo mun w?ni ruwan nayo wanka zuchiya cike tab da fargaba.
Ina fitowa na kintsa cikin riga da siket na atampa, na yi kwalliya sama sama na yafa mayafina wanda na bishi da turaren feshi.
Ina fitowa tsakar gidan ido ai sai ya dawo kaina.
Anan zan dakata sai Allah ya kainmu gobe.


MRS BUKHARI



Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667



*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230



*?ar uwa ina fatan baki mance da kayan ?amshin Mrs Bukhari gidan ?amshi ba ko? ?ar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ?amshi. Matso kusa ?ar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ?amshi ya ri?e miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake sa?awa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ?amshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haWe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ?ara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ?amshin kifi Wanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ?amshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ?amshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ?ar mutan Maiduguri kin samu ?amshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai Wauke da abubuwa huWu manya kuma a kan kuWi ?alilan karki bari garaSasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
09153081057
Ga masu san magana dani kai tsaye ta whatApp ga number na
Masoyana sunata mun ?orafin babu number na a jikin littafi kuma suna son muyi zumunci, ?orafi ya ?are.

NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE

BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA UKU (3)


*Yau juma'a karku manta ranar lahadi kayan promo zasu tawo arewa.* *WaWanda basu turo kuWinsu ba su turo dan Allah*



Kunsan masu ?iba yadda sutura take amsarmu, haka kwaliyarma take amsarmu. Abunka kuma da Amaryar birni a ?auye. Ni dai harna iso gun_gun matan dake kallona basu dena ba.
Ina kwananku" Nai musu jam'u dan Hama ma tana cikinsu. Tsirari daga cikine suka amsa, na yi wucewata na bar musu ?amshin turarena a iska.
Dan?ari na ji wata ba?uwar murya ta faWa ko me take nufi da hakan oho.
Sallama nayi a ?ofar Wakin Yafendo na shiga. Duk ?annen Dada suna ciki karyawa suma suke yi, su Iyaa Kokodeen ma suna ciki.
A ?asa na zube na bisu Waya bayan Waya na gaishesu. Ko wacce da fara'a ta amsani. Saina nemi gefen gadon bono na takure kaina a ?asa nayi shiru kamar ruwa ya cinyeni. Can Yafendo A'i tace.
"Jabu sai kin ?ara da ha?uri dan zama da kishiya ba abu bane mai sau?i ba. Musamman ka haWa miji da bafulatana, bafulatanar ma ta Camaron basu Wauki kishi da wasa ba. Mu ma da kika ga mun yi ?arko har zuwa yanzu, ha?uri da kawaicine, da ?arfin adda'a.
Kema ina baki shawarar ki ri?e wannan abubbuwan zaki samu riba duk daren daWewa. Ki zamto mai kawo haWewar kai ba mai ?o?arin ganin an samu rabewar kai ba. Hamma dai Wan uwankine jini ba ruwa bane, kar ki bari wata ta kutso kanta cikin rayuwar aurenki ki kula sosai. Kuma kin nuna mana soyayya, kin yi abun a duba Hamma zai nuna miki shi Wan halak ne"
Ta jima tana nusar dani tare da bani satar amsa dangane da yadda zafin kishin fulani yake mazansu dama matan nasu. Daga ?arshe tace inyi komawata Wakina"
Sallama nayi musu na fito. Kaina a ?asa na wuce matan da suke tsaye cirko_cirko dan son sake ganina. Uhm bance dasu ba nayi kwanar lungun Wakina nayi shigewata.
Uwani na gani akan turmi tana ta faman zagaye mun Waki da farin citton me les les. Yayi matu?ar kyau sosai.
Ashe kun dawo Tabalbalin? Sannunku da ?o?ari"
"Mun dawo har mun shiga aiki. Ance yau ango zai shigo Wakin Amarya ai gara mu samu mu kammala komai a nitse. Kinga wasu fararen labulaye masu kauri dana siyo inaso ko yayane mu raba Wakin biyu ta yadda ko an shigo ba za,a ga wanda ke kwance a gado ba ko ya kika gani?"
Lallai wannan dabarace mai kyau na kuma ji daWinta sosai na baku wu?a da nama"
Anti Ramata da Cubu kuma kujeruna suka fitar dukka waje muka haWu muka sake ma Wakin fasali babu laifi yafi na farko kyau. Kujerar doguwa guda Waya kaWai aka mayar, sauran nace BaWWo ta Wauki 2 sitter Win sauran 1_1 Win akai gidan Dada a ajjiyema Cubu in aurenta ya tashi sai a kai mata. Muka gyara komai abincin gara na Webi wanda zan Soye na tura ?ar?ashin gado, dama na sai maggi dun?ule katan guda, na daka yajin barkono da yajin daddawa, na sai kayan tea na dayawa, na sai tocilolina masu batura hatta baturan na sai abina, Uwani tayo mun miya, mun tawo da risho da kalanzir, ?ananun abubbuwan bu?ata dai wanda nasan zanyi amfani dashi duk na sai kayana na adanasu. Cikin awa uku Waki yayi shar dashi gwanin ban sha'awa. Mata masu zuwa ganin Waki har daga ma?otan ?auyan zuwa sukaita yi basu taSa ganin kaya irin nawa ba, yadda aka raba Wakin biyu shima ya burgesu sosai.
Haka dai aka wuni cur ana sha'anin biki. Wuninnan cur kuwa ruwa akaita makawa. Sai magriba ruwannan ya tsaya na samu nayi wanka na sake kwalliya. Anayin isha su Uwani suka watse suka barni ni kaWai a Wakin ?walam akan kujera na ?urama tocila idanu. ?aga kai nayi na kalli yadda su Uwani suka rufe azarar saman Wakin da farin labule cikin hikima. Na daWe a zaune ina karanta wasi?ar jaki ga turaren tsinke sai ?amshi yake fitarwa daga saudiyya na siyo. Wajajen goman dare har bacci ya soma surata akan kujera na jiyo shigowar Yaya Hamma. Da sauri na buWe idanuna dan na tsorata sosai.
"Tsoro kikaji ne Jabu naga kin tashi a zabure?"
Saye yake da wani yadi green yala_yala Winkin ?ar shara, kanshi babu hula sai suma data zame mai ado ta kwanta ta laSe a dogon wuyanshi. Sai ?amshin turaren sasarobia yake yi, hannunshi ri?e da leda mai zane"
Da sauri na mi?e tsaye ina shirin amsar ledar hannunshi. Saijin hannunshi nayi ya ri?e ?uguna ya jawoni na faWa jikinshi. ?am ya ri?eni, nima na ri?eshi ta baya ri?o na ?warai. Munkai kamar minti biyu cur muna sha?ar numfashin junanmu. Ni dai wani abune ya shiga yi mun yawo tun daga dunduniyata har zuwa kaina.
Ji mukayi an bankaWo labulen Wakin an shigo. Ga wani irin kukan jinjira na fitar hayyaci. Da sauri muka saki juna. Hama ce a tsaye ri?e da jaririyarta dake canyara kuka. Wuf Hamma ya amshi yarinyar yana tambayar Hama meke damunta.
"Baccinta take yi lokaci Waya saita soma firgita tana zabura tana mi?ewa, sai kuka ka dai ganta" Jijjiga yarinyar ya dinga yi, amman yarinyarnan kamar ?ara zugata akeyi sai canyara ihu takeyi bakinta na rawa. Kafin kace me matan gidan duk suka yo ?ofar bukkata suna tambayar ba'asin wannan kukan.
Hamma ne ya fita da yarinyar rataye a kafaWarshi.
Ina jiyoshi yana musu bayanin da Hama tayi mishi da fulatanci.
Ni kuwa ina tsaye a inda suka fita suka barni, ga ledar kaji tarwatse a ?asa. Tun inajin muryoyinsu harna dena jiyowa, kukan yarinyar yayi nesa sosai.
Wallahi saida nayi awa guda cur a tsaye in kai mari in kai gwauro ina tubkewa da warwarewa.
Labulena aka Waga Hama ce fuskarta a sake tace.
"Amarya sai ha?uri auren mai mata angone yace in sanar miki zamu kai yarinya gidan magani, wai ki kwanta kiyi baccinki, in mun dawo zai kwanta????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
a Wakina sabida jikin yarinyar" Numfashi naja sama nace.
To Ubangiji Allah ya bata lafiya, gaskiya ya kamata ya zauna tare daku har sai ta samu sau?in jikin nata"
Labulen ta sake. Ni kuma wasu siraran hawaye suka gangaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login