Showing 48001 words to 51000 words out of 270738 words

Chapter 17 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mu ka dinga bin abokanmu muna raba musu alawar gaiyata. Kowa yazo da sile da sisinshi. In abun ya tabbata zaiyi kyau sosai "
Tamu yace.
"Wato kai Bara'u baka da mantuwa sam.
Ni ai tunanina in rama halaccin da Gwadabe yayi mini, ko banyi mai daidai da abinda yayi mun ba, in kamanta mishi. Gwadabe na baka Shafa halak malak. Nine maWaurin aurenta dama. Zan mata bayani duk lokacin da ka samu nutsuwa sai ka neme ta, a hankali tunda ba sauri akeyi ba sai ku daidaita tsakaninku. Yara kuma zanci gaba da ri?onsu ko kun yi auren ma, in sha Allah ni zan aurar dasu da hannuna. Zan kuma so in haWe su aure da nawa yaran dakan Waka shi?an Waka"
Gwadabe bai yi musu jayayya ba bare turjiya. Kwana Waya su kayi a garin Gwagwalada suka juya washe gari, bayan Gwadabe yayi sallama da ?an yaranshi, abinka da yara sun shige cikin yara ?an uwansu sai adabo ma suke ma uban. Ganin yaran sun sake ne uban ya Wan ji ?arfin guiwa kuma.

Ruga

Iyabo:.
Tabarma Daso ta Wauko ta shimfiWama Yaya Hamma daga can gefe guda. Jatau ne ya shigo da garken shanunshi guda yana tafe yana wa?ar fullanci, hannunshi da ?ar tsaraba.
"Jatau yau kai ka soma shigowa gidan?" Da Hausa tayi mishi wannan tambayar. Shi kuma hankalinshi duka yana kaina, ina son in Webo ruwa a randar ?asa in kawo ma Yaya Hamma.
"Ba?uwa mu ka yi ne Daso?"
"E ba?uwa ce kuma ?ar gida, Yayar su BoWWo ce tazo daga birni"
Sai ya washe bakinshi muka gaisa cikin girma da arziki. Na dure ma Yaya Hamma ruwan sha a gabanshi na koma kan turmi na zauna. Jatau da Hamma nan suka kacame da yare, daga bisani Jatau ya wuce da shanunshi izuwa maWaura.
"Jabu zo ki zauna sabida ke nazo gidannan da yammannan" Daso dake hura wuta tace.
"Ko ni na faWa a rayina, sabida Jabu ne kazo Yaya Hamma"
Sai tayi murmushi, nima murmushin na mayar mata, na ?arasa kan tabarmar da Hamma yake na zauna a gefe.
"Na ji labarin mutuwar aurenki ?anwata. Abun ya dake ni ainun, naji tausayinki sosai. Amman mu zamu baki farin cikin da har sai kin mance da komai a matsayinmu na dangin uwa, muma zamu taka tamu kalar rawar, tunda kika zaSi ki rayu damu a ruga, kika ha?ura da rayuwar maraya duk da acan ki kai wayau. Kiyi ha?uri kinji am?"
Wasu hawaye ne suka gangaro mun. Ban aune ba sai kuka mai gunji ya tawomun babu zato. A tiSi tiSi_tiSi da kayan mazaunai na shige bukkarmu na zauna akan gadon ?asarnan na shiga sana'ar kuka. Wani tu?u?in ba?in ciki da takaici sai yanzu ne komai ya soma dawo mini. Kuka na zage nayi na ban mamaki. ?an uwana suka bani sarari na dirji kukana yadda yayi mun nayi shiru dan raWin kaina. Sai zuchiyata ta Wan washe ta rage nauyi. Na yi zaman tunani a zaune bansan iyakar adadin ba. Sai shigowar Yafendo na gani kawai. Da sauri na share guntun hawayena ina duban fuskarta. Sai naga fuskarta cike da damuwa, da dukkan alamu damuwa da damuwata ce take yi. Ledar hannunta ta mi?o mun nasa hannu na karSa kafin tace.
"Ban isa hana ki kuka, ko hanaki damuwa da tunanin yaranki ba Jabu. Kinga Daso tun bayan rasuwar mijinta kullum sai ta yi kuka zuchiyarta babu daWi. In Hamma yazo gidannanne ma take samu tayi farin ciki. Ni kuwa ban taSa hanata kuka ba. Rabuwa da miji ciwonshi bashi da misali sam, musamman mijin da kuke soyayya da zaman lafiya. Ace mutuwace tayi muku yankan ?auna. Ko kuma wata ?addararce ta raba ku ba da son rayukanku ba. A lokacin da mahaifinki ya rasu Adda Daso ta shiga wani irin mawuyacin hali. Mahaifiyarki har jinya sai da ta kwanta na tsawon wata shida masu kyau. Har gaban abada ba zata dena tunanin mahaifinki ba. Musamman data haWu da azzalumin namiji magoki. Da girmansu haka bai bar dukansu ba. Zuwan da ki kayi ma dan kawai ta ro?eshi ya barki ki zauna a wajenta har ki gama kwanakinki ki tafi. A daren zagi da cin zarafi babu wanda baiyi mata ba, har marinta sai da yayi"
Da mugun sauri na Wago. Wata kibiya ta soki ?awon zuchiyata, siraran hawaye suka gangaro kan kumatuna masu zafi.
Yafendo yanzu kamar Dada da girmanta da yaranta manya sai mijinta ya daketa harda zagi, a halin da take rayuwa kenan?" Zama Yafendo tayi a kusa dani tace.
"A haka Adda Daso take rayuwa da azzalumin mijinta. Har da tsohon ciki a jikinta dukanta yake yi. Ko a cikin BoWWo yayi mata wani dukan da tai ta zubar da jini, duk muka cire rai da cikin. Sai daga baya cikin ya tashi. Amman sai da BoWWo ta shekara biyu cir a kwance a cikinta kafin ta haifeta. Wannan kuma ana tunanin da sa hannun uwar gidansu akan lamarin. Kuma ya karSe shanunta na gado ya haWe da nashi shanun, Adda Daso bata ribatar komai. Shanune masu tarin yawan gaske, kinga gaa nawa garken can Jatau ya dawo dasu, sai hauhawa suke yi. Ita kuma bata san adadin yawan haihuwar da nata shanun suka yi ba, dan nata mata ne, namijin guda Waya ta samu. Ke Jabu in nace zan ta baki tarihin mijin mahaifiyarki zamu kwana mu wuni a nan bamu ?are ba. Shi yasa ko da yaushe take cike da tunanin marigayi mahaifinki. Soyayya da kulawar daya bata ne, yasa ta fifita soyayyarki fiye da soyayyar duk yaranta. Duk Wan abinda ta samu burinta ta tara in zata kai miki ziyara ta miki hidima, kinji na rantse miki tun bayan rasuwar mahaifinki ban sake ganin annuri akan fuskar Adda Daso ba, sai yau data zo gidannan tana sanar dani zuwanki garinnan, damma a hakan ta kwana cikin tashin hankali akan mijinga."
Kukane yaci ?arfina, zuchiyata sai luguden daka take ta faman yi. Ina jin duniyata na wujijjiga rayuwata. Tausayi da zunzurutun kaunar Dada ya sake Wamfaruwa a raina. Yafendo ta dafa ni nayi firgigit na kalleta.
"Ki tashi ki Wauro alwala ki yi sallah. Wannan ledar dana baki Hamma ne ya ce a baki. In ki ka yi sallah sai ki fito tsakar gida in gabatar dake ga ?an uwanki"
Jikina a sanyaye na Wauro alwala nayi sallah. Na daWe ina adda'a, a lokacin zazzaSin dake jikina ya rabkeni ainun, ko idanuna bana iya buWewa. A halin da Daso ta shigo ta same ni kenan. Abu kamar da wasa_wasa sai na rasa numfashina, jikina kuwa kamar garwashin wuta. Sai da na shafe tsawon wata biyu da kwana goma sha Waya cur a kwance babu lafiya, sai maganin gargajiya akeyi mun, hatta ruwan wankana da ganyen magani a ciki, kuma Yaya Hamma suke kawo mun magani da Wan abinda zan sa a bakina, Yaya Jatau ma yana kawo mun Wan abun kwaWayi, matarshi ma kullum zata shigo ta duba lafiyata, kuma in Yafendona, da Daso sun tafi tallen Nono, Hari itace ke zama dani matar Jatau. A wannan jinyar naga gatan dangin uwa. A wannan kwanciyar sai da dangin Dada suka zo kab suka gaisheni da jiki, a lokacin na gansu suka ganni. Dada kuwa kullum cikin suntiri suke ita da su cubu da Yusufu, BoWWo kuwa da hama suma kullum babu fashi sai sun zo dubani. " A cikin wata uku cib jikina yayi ?wari babu laifi, lokacin iddata ta cika cib, lamarin da ya Wan ?ara jagula lafiyar jikina kenan, sai da Yaya Hamma ya dinga bani baki, tare da lafuzza tausasa, har mamaki nake yi in naji yana furta wasu lafuza masu kwantar da zukata. Da yamman wata asabar bayan Daso ta dawo daga tallar nono muna Waki mu na Wan taSa hira, fuskarta cike da farin cikin ganin jikina yayi kyau yau. Duk da na rame fiye da tunanin masu karatu, fuskata ta yi fayau. A jinyar dana kwanta na samu kulawar mutane uku da bazan mance da hidimar da su kai mun ba. Daso, Yaya Jatau, Yaya Hamma. Duk kwanan duniya Daso itace mai bani abinci a baki, tare da gyara mun kwanciyata, ko amai nayi itace ke kwashewa. To a wannan kwanciyar jinyar nayi jinin al'ada hatta da tsumman jini da Wan kamfaina Daso ke wanke mun da ruwan toka ta shanya su, wanda zai maka irin wannan aikin ba ?aramin masoyinka bane. Yaya Jatau kuma kullum in zai dawo daga kiwo yana kawo mun wani gashasshen hanta mai yaji, shi nake ci da daddare, shi kaWai ne nake iya ci ba tare da naji tashin zuchiya ba. Yaya Hamma kuwa shi ya dinga bin ?auyuka ruga_ruga dan sama mun magani, wani gari wani ganye, ko kiwo ya?i ya mai da hankali akai har sai da ya ga samuwar lafiyata. Kuma kullum a cikin yi mun nasiha da tattausan laffuzza yake. Muna Wan hirarmu muka ga an buWe labulen kaban dake ?ofar bukkarmu. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi ri?e da kwano. Daso ce ta mi?e ta karSi kwanon ta dure a gabana tana dariya tace.
"Nasan ai nata ne ko Yaya Hamma? Shi yasa na dure mata a gabanta" Dariya yayi tare da nunata da yatsa yace.
"Kin ganki akwai zolaya. Ai itace marar lafiya a gidan, shi yasa na kawo mata tasha romo" Sai tace.
"Nima in na kwanta jinya ashe zaka kula dani sosai irin kulawar da ka ba Jabu?"
Dani da'ita duka sai muka kafe shi da idanu. Sai da ya zauna a ?asa ya tan?washe ?afarshi kana yace.
"Ai kamar ratayayyen hakkine a kaina in kula daku, ko da a gidan mazajenku kuke balle kuma kuna gabanmu.
Jabu ya ?arfin jikin, yaya ha?uri ds rayuwa, da ha?urin zaman ?auyanmu mara wuta balle ruwan daWi?"
?an murmushi nayi nace.
Jiki Alhamdulillah sau?in yana samuwa sosai. Babu abunda zance sai godiya. Kuma ina godiya da wannan Wawainiya da kukaita yi dani" Bayan na bashi amsar na sauke kaina ?asa.
"Ai ya zame mana dole, ki daina godiya ma Jabu"
Mi?ewa tsaye yayi.
"Ba dai tafiya ba?" Cewar Daso.
"Tafiya zanyi. Dama abinci na kawo mata. In kuma ?ara ganin jikin nata. Amman dai ku shirya zuwa dare zan zo mu le?a dandali Jabu taga yadda muke wasanninmu gwanin sha'awa, wala Allah hakan ya rage mata raWaWi."
Dariya nayi musu kawai. Aini na rabu da nishaWi tunda na rabu da Gwadabe, dan nishaWi na wajen tsuntsun soyayya. Amman a fili saina amsa da cewa.
Allah ya kaimu"
Ko dan in ?arfafasu tunda burinsu suga na saki jikina na mance komai.
Da haka mu kai Sallama, bamu muka fito daga cikin bukkarmu ba saida mu ka sallaci sallar isha. A tsakar gida muka ci fsrfesun da Yaya Hamma ya kawo mini harda Yafendo da Jatau, dama Hari Matarshi.
MRS BUKHARI ce.

*?ar uwa ina fatan baki mance da kayan ?amshin Mrs Bukhari gidan ?amshi ba ko? ?ar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ?amshi. Matso kusa ?ar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ?amshi ya ri?e miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake sa?awa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ?amshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haWe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ?ara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ?amshin kifi Wanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ?amshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ?amshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ?ar mutan Maiduguri kin samu ?amshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai Wauke da abubuwa huWu manya kuma a kan kuWi ?alilan karki bari garaSasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM

14

Muna gama ci sai ga Yaya Hamma ya shigo. Yana saye da wani yadi mai ruwan bula Winkin ?ar shara, yadinnan duk ya gaji yayi laushi sosai sai laSewa a jikinshi yake yi. Wandon jikinshi kuma na koren yadi ya saka ya Wauko hular tashi ka fiye naci irin hular da fulani suke mugun so Winnan ?ar madina mai fara da ba?a a jiki, ?afarshi kuma saye da takalmin roba mai ruwan bula duk ya fashe, sai ?amshin wani turare mai gafin ?amshi yake yi, daya isa wajensu Yafendo dake akwai fitilar aci bal_bal na gango kwalli rambaWe a fararen dara_daran idanunshi har zazzagowa yayi. Bayan ya gaisa dasu Yafendo yayi ma Baba bayanin yazo ya kaimu dandaline, sai ya fita waje ya bamu sarari dan mu kintsa.
"Daso maza ku tashi ku shirya abun nema ai yau ya samu ko?"
Dariya mu ka yi mata kawai. Ni dai mayafi kawai na Wauka, saye nake da koWaWWen riga da zane. SaSanin Daso da sai da ta shafa kwalli harda janbakin majigi tasa ma labSanta. Cikin zaulaya nace.
Harda kwalliya ko za'a samo mana bazawari ko?" Dariya tayi kawai tace.
"Kayya, ai tunda na rasa ChubaWo ban sake tsaiwa da kowa ba. Ni abunma wani iri ba fasali yake yi mini"
E dole zaki ji banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Amman ya muka iya haka Allah ya zaSar mana. Fatan shine Allah ya sadamu da mazajen da zasu ji tausayin rauninmu. Gara ma ke Daso mijinki rasuwa yayi fa. Ni fa Gwadabe yana doron duniyarnan rabamu akayi a bisa tursasawar mahaifiya da danginshi" Siraran hawayene ban aune ba suka biyo kan kuncina.
Dafa kafaWata Daso tayi jikinta a mace tace.
"Mu yi ha?uri kawai mu rungumi ?addararmu. Allah yana sane damu, bai mance mu ba. Ta yiwu ya shirya mana kyakkyawar rayuwa a gaba. Ta yiwu kuma wahalar rayuwarmu ne zai fara. Amman duk abinda ya samu bawa ya fauwala shi ga Allah "
Wannan gaskiya ne. Muna fatan kyakkyawar rayuwar a gaba. Allah ya sadamu da mazajen da dan so zasu ji kamar su mallaka mana numfashinsu dan mu daWe mu yi ?arko. Mu je mun bar Yaya Hamma a waje yana ta faman jira" Kafinma in rufe baki muka jiyo Yafendo tana kwaWa kiran sunanmu tana yaren Fullanci. Ba shiri muka fito tare da ficewa a gidan. Ko da muka kama hanya, sai cin karo muke yi da mata da samari suna nufar dandali. Ina gefen hannun daman Yaya Hamma, Daso na gefen hagunshi mun sanya shi a tsakiya. Sai hira yake janmu dashi, Daso ce ke bashi amsar duk abinda ya tambaya. Ni tunanin Gwadabe da yarana, da kuma tunanin ta wacce hanya zanbi dan ganin na sanya Dada a farin ciki dariya da walwalarta ta dawo kawai nake. Wani shashe na zuchiyata sai kawai katsaham yace.
"Me zai hana ki nemi Uwani in dai bata tafi ba, kema tayi miki hanya ki tafi. In kika tara kuWi ne kawai zaki iya Wauke mahaifiyarki ki rabata da azzalumin mijinta, ki kuma rabata da tallan Nono. Wannan shine hanya mafi sau?i. Tunda ba kya kashe mata aure ba tare da kin shirya mata gidan da zata rayu da yaranta ba, kuma ba zaki hanata tallan nono ba har sai ke kin samu abun yi, ko kuWi a hannunki da zaki ma rayuwarta hidima kamar yadda mahaifinki yayi mata kafin ya rasu" Nan take sai nake ganin kamar ma na samu mafitar cire Dada cikin ?angin rashin ?ancin da take ciki. Dan a shirye nake ko matakin shari'a ne zan bi muddin ya?i sauwa?e mata igiyar ?addararran autenshi. Lokacin dana kwanta jinya take yawan sintirin zuwa dubani. Cubu ranar ta shigo da kuka take labarta ma Yafendo cewar Dada tana gida Baffansu ya daketa ya kumbura mata fuska, sabida sintirin zuwa dubani da take yi wai ya isheshi sai kace nice kaWai ?ar data haifa. Lamarin da yasa ?annena suka haWe kansu suna kuka, tare da adda'ar Allah ya kawo ma Dada mafita ya cireta a wannan ?angin. Daga ranar kullum ?wa?walwata cikin tunanin sama ma Dada mafita nake, ko da kuwa zan rasa tawa mafitar. Sai yau Allah yayi na tuna abinda nake ganin zai iya kawo ?arshen hawayen Dada. Tafiya Kano ya kamani gobe da izinin Allah, dan bahaushe gwanin iya tsara zance cikin hikima da azanci yakance da zafi zafi ake dukan ?arfe, ko kuma yace da safe ake kamun fara"
"Jabu tunanin me kikeyi haka mai zurfi har mun iso dandali baki sani ba? Na lura jefa ?afafuwanki kawai kike yi" Cewar Daso wacce ta kafeni da idanu, Yaya Hamma shima ido ya zubamun, suna sauraren abinda bakina zai furta da sunan amsa. Iska na jawo daga huhuna na furzar kana nace.
Tunanin rayuwa kawai nake yi Daso. Ai baka isa ka raba zuchiya da tunani, ko da ayyane_ayyane ba" Na ja bakina na tsuke. Na kura maa wutar karar dake ci bal_bal a tsakiyan dandalin ido, wajen yayi haske sosai ina iya hango kwalliyar mata da maza. Wutar nake kallo yanda take tartsatsi. Amman abinda zuchiyata take ciki yafi ?arfin tartsatsin wutarnan, jin zafi nake yi daya wuce doka da oda. Hannuna Daso ta kama muka nemi wani benci da babu kowa muka zazzauna. ?an berorin ?an mata sai wasannin gaWa da wa?e_wa?en su na fulani suke yi. Samari sun kewayesu sai tafi da Waga sandunansu suke yi.
"Kinga dandalinmu ko Jabu?, Allah yasa wasannin al'adunmu sun burgeki?" Cewar Yaya Hamma wanda yake zaune kusa dani. Murmushi kawai nayi mishi na sauke kayina ?asa ina kallon yatsun ?afata.
"Jabu tunanin menene ya bujuro miki duk ya sauya kamanninki? Kinga lafiya abun tattalawace ga duk wani rayayye. Me zai hana ki tausaya mana ki dena wannan tunanin ko dan lafiyarki da farin cikin masu son ganinki cikin ?oshin lafiya?" Kallonshi nayi na mai murmushi idanuna cike da ruwan hawaye. Shima murmushin ya bini dashi, kafin ince wani abun sai ga wani matashi ya ?araso gabanmu da sandarshi rataye bisa kafaWunshi.
"Hamma in babu damuwa inaso ka bani dama mu zanta da Daso. Na jima ina bibiyarta domin ta bani damar ko sauraren abunda ke tafe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login